Showing 54001 words to 57000 words out of 61883 words

Chapter 19 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10814

su sauran matansa ƴaƴan masu da shi, ita kuma talaka, idanunta ta ɗaga ta sauke a kan fuskarsa da take haɗe kamar ta mayunwacin zaki, fuskar da take ganin ta fi kowacce fuskar muni a duniya yau, tana jin yadda zazzafar kalmar da ya jefe ta da ita ta talauci tana kai kawo a birnin zuciyarta.


"Haka ABBAS yake ji idan na ambace shi talaka ahalil fuƙara'u? Ashe dai kalmar talauci a dangantaka da ita ta sigar cin mutunci baka jin daɗi ko da kuwa kai talakan ne tun da ba kai ka ƙaddarawa kan ka ba, a karon farko da ta gane cewa ABBAS yana jin ƙuna a ransa, dama baka sanin munin abu ko kyansa idan kana yi sai ranar da aka maka.


"Talauci?" Ta tambaya tamkar an fisgo maganar daga bakinta.




"Eh, kuma na faɗa saboda kuɗi kika aure ni, ki kalli tazarar da take tsakanin farin fatarki da baƙar fatata, ki kalli ratar da kyan da kike da shi da munin halittata, ki dubi tsawon shekaruna da suka ɗara naki, a ƙiyasi a haihuwar kaji na kusa haifar ki SALIMAH ki hasko ni a idanun zuciyarki ina sanye da rigar talauci shin za ki yarda ki aure ni? "


"Kenan kuɗina su suka lulluɓe muni, shekaruna, da duk wani abu da za ki ga gazawata" Ya ɗora ba tare da ya jira cewarta ba


"Ki koma wajen zamanki aure babu fashi ki saurara ki ji dokokin gidan nan wanda su ne abu mafi a'ala a gare ki don saɓa su ba ƙaramin barazana bane a gare ki" Ya ce yana komawa ya zauna yana aika mata wani kallon mai cike da ma'anoni da dama amma ba masu kyau ba don tuni ya gane ba don Allah ta aure shi ba, duk da shi ɗin ma hakan take a wajensa sai dai shi ya aure ta don cim ma wata ɓoyayyar manufa( Littafin MAIMUNA IYAM) manufar da shi kaɗai ya santa kuma saboda cikar burinsa.


Durƙushewa ta yi a wajen, ba don bin umarninsa na cewa ta koma mazauninta ta zauna ba, sai don ƙafafunta sun kasa jumurin ɗaukan gangar jikinta, gabaɗaya ta rasa a wace kalar duniya take, shin a duniyar mafarki take ko kuwa a duniyar zahiriyya. Alhaji Tahir bai bi ta kan ta ba illa iyaka ya ɗora maganarsa da cewa.




"Abu na farko saƙo ne da yake damfare da ke ma'ana ina nufin ke ce baƙuwa a gidan nan dole ki san dokokina tun da su abokan zamanki tuni sun daɗe da sani, jajayen idanunta ta ɗaga tana kallonsa garau da ita tamkar wata sakarya ta rasa ma'aunin da za ta ajiye duk abubuwan da yake faɗa mata.


"Dokar ta farko ki sani part ɗina ba a shigarsa matsawar bana nan, ki kiyaye da wannan babban al'amari ne karya dokar nan babu ke babu part ɗina sai in har ni ina ciki!" Kallon tuhuma ta shiga jifansa da shi a wannan karon tana ganin an zo gaɓar da aka shallake tunaninta. A iya saninta ta yaya za a ce mace an saka mata dokar shiga ɓangaren mijinta sai in yana ciki sai ka ce wani marar gaskiya.




"Sannan abu na biyu a saman akwai ɗakuna guda uku a jere wannan ɗakuna in har ina part ɗin don kin shiga babu laifi sai dai akwai wani ɗaki daga gabas shi kaɗai a ware a gefe guda, ko a jikin bangon ɗakin daga saman ƙofa an rubuta ƊAKIN ALHAJI TAHIR, to wannan ɗakin ni kaɗai ne mamallakinsa ni kaɗai ne nake shiga babu wani mahluƙi da zai taɓa shiga, ko ya taɓa shiga ina gargaɗinki a kan kar gigiwa ko rawar kan ki ya sa ki shiga rufaffan ɗakin wannn" Ya ce yana nuna ta da yatsa alamar kashedi, ita gabaɗaya a sanyata a tsaka mai wuya yanzu kam mugun tsoron Alhajin ne ya ɗarsu a zuciyarta a gefe ɗaya tana tuhumar anya yana da gaskiya? Idan har yana da gaskiya mene ne dalili lo hujjarsa na cewa kar a shiga ɓangarensa sai yana ciki kuma kar a shiga wani ɗaki guda ɗaya tal da ya keɓance shin mai zai faru idan an shiga? Take ta yawo da tambayoyin a zuciyarta tambayoyin da bata da wanda zai amsa mata su shi wanda zai amsa mata ba shi da salamar da jinƙai irin na mijin da za a faɗa masa abu.


"Sannan ki sani ba a haihuwa a gidana!!! Wannan wani ɓoyayyan sirri ne, kuma ba don ana tsarin hana haihuwa ba wato palaning sai dai wannan ni na san dalilan da ba na bayyanawa kuma duk son ki da haihuwa ba za ki haihu ba kuma babu wanda zai haihu" Dumm kunnuwanta suka yi, nan ta shiga tunano inplan ɗin da ta saka har sau biyu a gidan ABBAS don kar ta haihu a gidan talauci yanzu ta cire ta zo gidan kuɗin da nufin ta buɗe mahaifa ta yi ta barbaɗa ƴaƴa in son samu ne ma ƴaƴan maza don su ci gado mai tsoka. Sai dai kash! Kenan babu haihuwar ƴaƴa masu rarrafen cafet to zaman mai za a yi babu haihuwa a aure? Ga ya ce babu fita daga gidan ma shin wane irin bahagon gida ta shigo, wane irin ƙangin rayuwa ta kawo kanta?.


"Ga mukullin part ɗin nan wannan naki ne idan ranar bakin ki ta zo za ki yi amfani da shi wajen buɗe babbar ƙofar part ɗin ta farko don a rufe take" Ya ce yana jefa mata wani mukulli ƙwaya ɗaya jal kamar rai. Kallon mukullin take da idanunta da hawaye ya mata shamaki da ganin mukullin raɗau, hannu ta kai ta ɗauka.


"Za ku iya tafiya " Ya ce cikin bada umarni.


"Godiya muke Allah tsare ka ya kawo amarya lafiya" Hajiya Khadija da Hajiya Aina'u suka haɗa baki wajen faɗa cike da ladabi. SALIMAH samun kanta ta yi da kasa furta komai ta tashi tsaye jiki babu ƙwari wannan ita ce rana ta farko da ta ji ta tuna zamanta a cikin gidan ABBAS zama ne wanda ta yi cikin kwanciyar hankali kulawa tare da nuna soyayyarsa gare ta duk da tana wofantar da komai nasa amma bai taɓa gajiyawa ba!.




"Yawwa na manta" Hajiya Aina'u da take tsaye ta miƙa hannu za ta buɗe handle ɗin ƙofar ta dakata tare da juyowa, ita ma Hajiya Khadija dakatarwa ta yi suna masu juyowa a tare suka dawo tare da komawa suka zauna. SALIMAH amarya ma ko a ce amarya mai barin gado ita ma sai ta dawo wannan karon ma a cafet ta zauna.


"SALIMAH" Ya kira sunanta ba tare da ta amsa ba ta ɗago kai tana kallonsa don zuwa yanzu magana ma wahala take mata




"Ba da ke nake magana ba?" Ya tambaya a zafafe.


"Na'am"


"Idan kin koma part ɗinki ki zaɓa ko sama ko ƙasa ki ɗauki ɗaya ki bar wa ƙanwarki amarya mai jiran gado ɗaya gidanta na yi niyyar ware mata kasancewar nan ɗin iya part uku ne sai nawa to amma sai ta ce mini ita a nan gidan take so ta zauna tare da ku ƴan uwanta don haka ki ɗauki ɗaya tun da ke ce ƙarama a cikinsu kuma sama ko ƙasa kaɗai ma ya ishe mutum rayuwa akwai isassun faluka da ɗakuna da kicin da bayi da komai na buƙata " Tun da ya fara maganar take kuka wannan karon ta kasa hana kanta zubar hawayen bata ma
so ta dakatar da hawayen saboda so take ta zubar da su ko ta samu sauƙin raɗaɗin abin da aka mata!!!...




FREE BOOKS


RAYUWAR MARYAMU
GIDAN MIJINA
ƳAN UBANCI
MAI FARAR ƘAFA
SANADIN KISHIYA NE
ALAƘAR YARINTA.


PAID BOOKS


ƳAR ƘANWATA 500
BEELAL BOOK 1 free book 2 paid 500


ƳAR ZAMAN WANKA 500
ƘARA'IN INNA DELU 500
JALLI JOGA 600
UNGOZOMA 700
ƳAN ADAIDAITA SAHU 500


MAMAN AFRAH
09013181851








*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*





NA






MAMAN AFRAH






☀️ *First Class Writers Asso* ☀️


Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation




*GARGAGAƊI*


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️


JAN HANKALI


Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.




SADAUKARWA


Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.









*END OF BOOK 1*


PAGE 15






*ALHAJI BUKHARI*


Rayuwa ta yi musu daɗi tun bayan da aka gama zaman makokin su HAWWA bayan suna raye, amma su da basu tabbatar ba babu wani ko ɗar a zuciyarsu don ko inda aka yi haɗarin basu je ba bare wajen ƴan sandan da suka yi binciken yadda abin ya afku ma'ana ko ba komai ai sa ji yaya ne tun da ba ɗan mutum ba ko akuyar da kake kiwo ce ka bi bayanta ka ji kadin abin dabba ma kenan bare ɗan mutum, ko don ba ƴaƴan su bane da ƴaƴansu ne da har yanzu tabon mutuwar bai bar zukatansu ba kuma ba zai bari ba har abada don ma dai su suke kiɗa da rawarsu su HAWWA suna can cikin ƙoshin lafiya.




Zaune suke a falo suna taɓa hira Hajiya Baba sai Lawisa da take zaune tana cin meet pie ga dambun nama a gefe. Yaya Umar ne ya shigo babu ko sallama don dama su basu yi wa ƴaƴansu tarbiyar yin sallama ba tun da dama yaro sai kana koya masa ne zai koya ko da shigowa ya yi bai yi sallama ba sai ka ce ya koma ya yi sallama, idan ya yi ka amsa sai ka ce ya shigo yau da gobe har zai zamana ba ya iya shiga wuri ba tare da ya yi sallama ba ita tarbiya sai an dage an jajirce.


"Baba kuɗi nake so" Ya ce yana yin kalar tausayi.


"Kamar nawa kake so?"


"Baba duka fa shekaran jiya ka tura masa miliyan biyu amma yau za ka ƙara masa gaskiya ni ma sai an ƙara mini" Lawisa ta ce tana zunɓura baki.


"To mene ne na ɗaga jijiyoyin wuya kuɗi akwai su mu ma facakar mu muke yi dama dukiyar marigaya ne wato ɗan uwana da matarsa da suka bar kadarori da kuɗaɗe sai aka ba marigaya su HAWWA ƴaƴansu to su ma sun riga mu gidan gaskiya kuma basu da masu cin gadonsu sai mu kun ga kuwa dole mu fantama, baki ga ko shi Umar da yake ikirarin yana son ta ba yanzu ko zancenta ba ya yi shegen yaro ya samu duniya!" Baba ya ce yana dariya.




"Ni ma fa ba son gaskiya bane kawai dai ina son in san wace ce ita to ita ba yarda za ta yi mu ke ba wai ita mai tsoron Allah, mu ma ai muna tsoronsa istigfari muke, da a ce dama an yi auren ma da na gama samun komai zan sake saki uku" Umar ya ce yana fashewa da dariya. Saboda sakarci yanzu ba a ɗauki zina a bakin komai ba zina ta zama ado wayewa iskanci kala-kala ba a tuno ranar mutuwa da kwanciyar kabari azabar kabari nauyin ƙasa kai makomar ma gaba ki ɗaya ita mutuwar da ba sallama take yi ba yama daga cikin hikimar ubangiji ɓoye mana sanin ranar mutuwar mu mai ya kamata mu yi? Istigfari da sanya tsoronsa a zukatanmu ma'ana mu aikata alkairi ko don gobenmu. Idan kana ganin shi mai gafara ne za ka aikata saɓo da gangan ka nemi gafararsa shin kana da tabbacin idan kana aikata saɓon ba za a ɗauki ranka a lokacin ba idan ka je ka ce mai?.




"Wannan yaron ya san ta kan tsiya" Hajiya ta ce tana kallonsa tana dariya.


"Ke ma kuwa to ba mu muka haife sa ba ai dole ya san ta kan tsiya" Baba ya ce yana ɗaukan wayarsa. Yanzu kuɗin nan da suke wadaƙa da shi sun ma daina ganin laifin shaye-shaye da laifukan da Umar yake aikatawa munin abin da yake ya ɓaci hatta Lawisa mu'amala take da maza amma saboda suna cikin iyaye masu sakaci da saka wayewa a gaba babu abin da suka fuskanta, duk wasu kadarori na su HAWWA sun sayar sun zuba a kasuwanci suna cin wasu.


"Yeee sai Baba" Lawisa da ta ga shigowar miliyan biyu ta ce tana tashi ta je ta rungume Baba, shi kuma sai cewa yake




"Ai babu ku babu talauci yara dole in ke cika muku aljihu don ni ma nawa a cike yake"


"Yihuhuuuu" Yaya Umar ya ce yana murna ganin na shi transper da Baba ya masa sun shigo.


"Kai kuɗin shan ice cream ɗin kuke yi wa ihu, ai ba wasu kuɗi bane wannan na zuwa wajen shaƙatawa da abokai da ƙawayenku ne don kar ake raina muku hankali yanzu akwai wasu kuɗi da za su shigo na kamfani da na saka a kasuwa za ku sha mamakin kyautar da zan muku" Baba ya ce yana fasa musu kai.


"Kai mutuwar wani tashin wani, rabon wani shi yake kashe wani, yanzu duk rabonmu ne ya kashe masu kuɗaɗen nan amma su lokacin suna raye basa wannan wadaƙar komai a sannu cikin nutsuwa da taimakon talakawa da gina masallatai da gidan marayu duk da suna yi wa ƴaƴansu gata amma basa iya mallaka musu ƙaramin kuɗi to a duniya in ɗanka bai ci ba waye zai ci" Hajiya ta ce tana taɓe baki.


"Ƙauyanci dai da rashin wayewa ai kuɗi da miciji maganinsu a kashe kawai t... ƙaran wayarsa ya katse masa maganar da yake ganin abokin kasuwancin sa ne wanda ya kwashe maƙudan kuɗaɗe ya tura masa zai taho musu da kaya a jirgin ruwa, ya sanar masa jirgin ya taho ma nan da kwana biyu zai iso da kayan.




"A yi shiru zan yi waya kun san harkar arziƙi wallahi Alhaji Lawal cewa ya yi muddin kayan nan suka zo muka siyar to ni fa na sha kwana, don sai an shigar da ni sahun gaba na waɗanda suke da muhaukacin kuɗi a Nigeri'a " Ya ce yana kallon Hajiya da sauran yara.


"Ka wayyo mun kusa daina zaman ƙasar baƙaƙen fata" Hajiya ta ce tana wani murmushi.


Hannu ya ɗaga mata ganin kiran zai katse ya ɗaga ya kara a kunne.


"Alhaji Bukhari akwai matsala fa" Aka faɗa daga ɗaya ɓangaren.


"Wace irin matsala, haba Alhaji Lawal na tsani a ambaci matsala a ko ina bare a wajenka kayan ne ba za su samu zuwa ba sai nan da kwana uku a maimakob biyu?"


"Ba wannan bane Alhaji Bukhari" Alhaji Lawal ya ce hankali tashe. Wani irin warɓar da Lawisa da ta jingina da jikinsa ya yi gabaɗaya gumi ya karyo masa tsaye ya tashi don jin wannan abu da aka kira da suna matsala, yana ganin ba zai iya fuskanta ko sauraronta a zaune ba shi ya sa ya miƙe tsaye. Hajiya ma tsaye ta miƙe tana kallonsa a kiɗime don ta san babu lafiya, Lawisa da Yaya Usman sai zare ido suke suna son sanin mai za a faɗa wa Baban nasu da duk ya rikice haka.


"Na shiga uku!!! Na lalace, wayyo jama'a... Cewar Baba da ƙarfi tamkar zai fasa gidan da ƙara yadda ya yi maganar gabaɗaya sai da gidan ya amsa, jif ya yanke jiki ya faɗi wayar da ban shi da ban.




Hankali tashe su duka ukun suka yi kansa, suna faman jijjiga shi amma ko motsi ba ya yi lumfashinsa ma ya ɗauke cak!.



*HAWWA*


Rayuwa ta yi musu daɗi hankali ya kwanta, SABEER an sanya shi a makarantar boko da islamiya private school Baffa ya saka shi sai dai ba wata mai tsada ba dai dai ƙarfinsa amma makarantar tana da kyau sosai, Yaya Usman yake kai shi yana ɗakko shi. HAWWA tun da Baba Sadiya ta sako mata takardunta a mota aka kawo ita ma aka sama mata tata makarantar ita mai napep yake kai ta ƙarfe bakwai da rabi ya dawo da ita ƙarfe biyu da rabi ita ma private ce ta mayar da hankali don ganin burinta na zama ma'aikaciyar jinya ya cika.




Yau ma kamar kullum ta tashi ta yi shirinta tsaf bayan ta ci abinci. Wayarta ta ɗauka ƙirar infinix da Baffa ya saya mata ganin bakwai da minti ashirin da biyar ta fito daga ɗakin lokacin Amrah tana ta shaƙar bacci ko karyawa bata yi ba da yake iya takardun ta na secondry basu yi kyau ba kuma ta gyara ma amma duk bata ci ba kasancewar bata da mayar da hankali kuma ma Baffa ne mai matsa mata a kan karatun ita a nata burin ta fi son a yi mata aure amma bata son wani karatu ko secondry ɗin ma dakyar ta ƙarasa.




"Malamar asibiti mai tabarau" Baffa ya ce yana kallonta da murmushi a saman fuskarsa.




"Ni dai ba za take mini allura ba Baffa bata iya ba fa kar a je in zama gurgu" SABEER ya ce yana saka littafi da pencil ɗinsa a jakarsa da ya gama home work.




"To ban da abinka SABEER ai koya za ta yi, a makarantar ake koya wa ko su wanda ka ga suna allurar ai karatu ne da suka yi ya sa suka iya babu wanda aka haifa da iyawa" Baffa ya ce yana dafa kansa.




"Ni dai soja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login