Showing 30001 words to 33000 words out of 61883 words
Chapter 11 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
gidan nan zan yi ba zan zauna a rusa mini burina na karatun likita ba, burina na taimakawa al'umma mararsa lafiya, burin da tun ban san inda yake mini ciwo ba yake damfare a zuciyata"
"Haba Hauwa'u ina za ki dosa a halin yanzu?"
"Kaduna zan je Baba wurin yayan Ummiena da aka hana ya tafi da ni, kuma da kunnena na taɓa jin Hajiya tana waya tana cewa wurin malamai ta je aka masa mantau, wai ba zai kara tunowa da mu ba bare har ya zo neman mu, sai dai makarin abun shi ne idan ya yi ido huɗu da mu tun da ta san mu ba za su bari mu je gare shi ba" Ta ce cikin sanyin murya sosai Baba ta jimanta maganar tana kallon HAWWA sannan tana jinjina rashin imani na su Hajiya Rayyanatu.
"Kar ki damu zan baki ko ni ba zan so ki auri wannan yaron ba da shi kansa bai san kansa ba, amma wani hanzari ba gudu ba ta yaya za ku bar gidan nan bayan gobe ne ɗaurin auren kar ki tafi da igiya a kan ki'
"A daren yau za mu gudu Baba, ba zan bari igiyar aurensa ta ratayu a wuyana ba, ni dai ki taimaka mini Baba ki je kasuwa ki sayar mini da zoben ki bani kuɗin mu samu kuɗin mota " Shiri Baba Sadiya ta yi tana nazarin maganar tana son gano matsalar da za a iya samu idan aka aikata hakan ko aka san da saka hannunta a guduwar yaran sai dai irin halaccin da mahaifiyarsu ta mata da kirkin ta gare ta ba za ta bar ƴaƴanta su tozarta ba daidai gwargwado za ta yi iya yinta kuma ta shirya tunkarar kowane ƙalubale a kan hakan.
"Don Allah Baba" Muryar HAWWA ta katse mata tunanin.
"Hauwa'u dama zan je kasuwa siyayya da Hajiya ta aike ni sai na tafi da zoben na sayar miki na kawo miki kuɗin" Sosai HAWWA ta shiga mata godiya domin har ta hango sun bar gidan ta tsallake auren mashayi. Ɗakin nasu ta koma ta samu SABEER zaune ya jingina da bango yana gyangyaɗi a zaune ga rigar da take ɗinke ɓasa nan lokacin da aka kira ta a kan cinyarsa. Kai ta jijjiga cike da tausayin kansu da tausayin kaninta kasancewarsa karami wanda maraici ya masa dirar mikiya tabbas mutuwa tana da yankan kauna in ba haka ba mai zai raba uwa da ɗa ko kuma mai zai raba iyaye da ƴaƴa sai mutuwa, domin mutuwa ba ta duban girma ko kankantar wanda za ta raba da iyayan. A hankali ta samu wuri ta zauna a kusa da shi, tare da janyo shi ta ɗora shi a kan cinyarta, tana karewa fuskarsa kallo tana tuno yadda mahaifansu suke kaunarsu tare da lulawa duniyar tunanin ranar da ba za ta taɓa mantawa a rayuwarta ba, ranar da ya kasance rubutu a kan dutse wanda ba zai taɓa goguwa ba, ba rubutu a kan ruwa ba wanda zai gogu.
A ranar wata juma'a da yamma, HAWWA ta ce tana son zuwa gidan kawarta ziyarar juma'a ai kuwa SABEER ya ce sai ya bi ta, sai da Ummie ta saka baki sannan ta yarda za su tafi tare, lokacin da za su fita Ummie tana cikin kicin tana girki, a hanyar fita suka haɗu da Abbie zai shigo gidan.
"Sai ina kuma ƴaƴan Ummie?" Ya tambaye su yana murmushi mai nuna so da kaunar ƴaƴan nasa.
"Abbie Aunty HAWWA ce za ta je gidan kawarta ziyara shi ne zan raka ta" SABEER ya ce yana rungume Abbie.
"To kai da ba kawarka ba ya za a yi ka je?" Ya ce yana dariya saboda ya san yanzu HAWWA za ta ce wani abu.
"Sai da na ce fa ba zai bini ba amma Ummie ta ce sai ya bini" Ta ce tana kumbura baki.
"To ke da ɗan uwanki ai sai ku je dama ai na ga tare kuke uzurinku ko my HAWWA" Ya ce yana kama hannunta.
"Ai ni ma yawo nake son zuwa tun da yau babu islamiya ga shi na saka babbar riga da hula" Ya ce yana yi wa HAWWA gwalo. Sai da ya lallaɓata sannan ya kama hannunsu ɗaya a hannunsa na dama ɗaya a hagu shi yana tsakiya, ya raka su har wurin mota suka zaɓi wacce za su fita suka shiga direba ya ja suna ɗagawa Abbie hannu yana ɗaga musu har aka fita da su daga get ɗin sannan ya juya ya nufi cikin gidan.
Basu san mai ya faru ba sai dab da magriba direba ya zo a kiɗime ya ce su zo su tafi gida in ji Ummie sosai HAWWA ta yi mamaki don ta ce za ta kira shi a waya in sun gama amma kuma ga shi bata kira shi ba ya zo kuma ga shi duk ta gan shi a rikice, ko da ta tambaye shi dalilin rashin nutsuwarsa sai ya ce mata waya aka masa daga garinsu mahaifiyarsa ba lafiya. Ko da ya ɗakko su maimakon ya nufi gidansu sai ta ga ya nufi gidan kanin mahaifinta, da ta tambaye shi sai ya ce wai Ammie ce ta ce ya karɓo mata sako.
Tun kan su karaso gidan ta hangi yadda jama'a suka yi dandazo a kofar gidan, sosai ta ji faɗuwar gaba ganin mutanen babu alama ta abin farin ciki ko abu mai daɗi ne ya tara su, sannan ta san dai da ɗaurin aure ne ko makamancinsa da za ta sani saboda shakuwar Abbie da ta kaninsa Baba ta wuce a ce an yi wani taro ko da kuwa na wani ne da ban ba tare da Abbie ya sani ba. Ta shiga tashin hankali da ta gane mutuwa aka yi tun da lokacin Baba da Hajiya Rayyanatu so da kauna marar algus suke nuna musu kamar su haɗiye su. Don bata taɓa kawowa cewa mahaifanta bane. Tashin hankalin da ta tarar na gawar mahaifan nasu ya haifar mata da suman da sai da ta kwanta asibiti, ganin su kwance babu kyan gani yadda tukunyar gas ta yi bindiga suka kone har da wasu daga cikin ma'aikatan gidan.
Hannu ta saka ta sharenhawayen da suka gangaro mata tana jin tamkar yau abin ya faru. A ɓoye Baba ta kawo mata kuɗin zobe kulle.a bakar leda dubu ɗari biyu da hamsin da yake zoben da girmansa. Dubu ɗari ta ba Baba wanda dakyar ta karɓa shi ma saboda HAWWA ta nuna mata kuɗin ya musi yawa. Da za su kwanta Baba ta musu sallama saboda gudun kar ta fiya zama tare da su zargi zai shiga idan aka neme su aka rasa. Tana jin babu daɗi rabuwar da za su yi.
Tsakiyar dare wajen karfe biyu HAWWA ta tashi ta ɗauki ruwan da ta ajiye a kofi ta zuba a hannunta ta shafawa SABEER a fuska yana warewa ta shiga raɗa masa cewa za su tafi saboda dama ta faɗa masa cewa za su gudu Kaduna gidan Baffa Nasiru. Yanzu murna yake don haka kuɗin ta saka a wata karamar jaka marar nauyi da Baba Sadiya ta bata ta ce ta saka, sai da ta goye shi a bayanta ta rataya jakar a wuyanta ta tsaya ta yi ta addu'a a kan Allah sa su fita ba tare da wani ya gan su ba. Dama tuni ta zari mukullin kofar da za ta sada ta da get ɗin gidan haka ta fito cikin sanɗa ta fara lallaɓawa har suka zo kofar gabanta yana ta faɗuwa ta saka mukullin ta buɗe a hankali ta fita ta ja kofar wurin mai gadi ta nufa da yake sharara bacci da munshari tana zuwa ta shiga dube-dube cikin ikon Allah sai ta ga mukullin a cikin hularsa ta ga mukullin ta lallaɓa ta ɗauka ta buɗe get ɗin suka fita cikin sanɗa ta ja musu get ɗin. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ganin sun kuɓuto daga gidan, sai dai inda gizo yake sakar tana fatan su samu mafaka kafin da asuba su nufi tashar motar.
A wani kango suka samu mafaka inda suka yi addu'a suka shiga saboda gujewa abu mai cutarwa. A nan suka karasa kwanan da asubar tun gari bai yi haske ba suka fito wannan karon hannun SABEER ta kama suka kama hanyar tashar. Sai da suka kusa sannan suka samu napep kai su suka yi sallah ganin mota za ta tashi suka shiga motar ta tashi duka lokacin shida da rabi, sai da ta ga sun ɗaili hanya sannan ta sauke ajiyar zuciya tana rungume da SABEER wanda bacci ya yi awon gaba da shi kasancewar jiya basu samu wani bacci ba.
*SALIMAH*
Da tsananin murna da farin ciki wanda bashi da kwatankwaci ko misaltuwa da lokacin fa kwanakin iddarta suka cika, domin a wannan lokacin ne take ji ba ya ita domin ta samu cikakken ƴanci, ƴanci wanda take jin tamkar na wanda yake gidan yari ya samu fitowa daga ciki. A ganinta a yanzu ne take ganin tama da damar da za ta dama wacce ta daɗe tana jiran zuwanta a inda za ta ci karenta babu babbaka. Don tun da ya sayi kaya ta yi ɗinkuna na kece raini ɗinkuna na fita taro take jin kanta yana hayaki take jin kanta daidai da kowace shegiya da take jin ta samu dama. Kayan da suka janyo mata farin jini haɗe da kwarjini, kayayyakin da take shiga ta kece raini wacce ta kara fitowa da aji da mugun kyan da take da shi wanda a da take ganin talauci ya yi wa mutane shamaki da ganin kyan nawa kasancewar tana gidan ABBAS babu kayan da za ta yi tinkaho matsayinta na babbar yarinya amma yanzu tana ganin buri da mafarkin ta zai cika na zama matar manya.
Tun da ta yi idda ta fara ba mazan da suka yi mata caaa suna son samun dama a wajenta kasancewar bata yi idda ba sai ta ɗan dakatar da su amma tana kammalawa sai ta shiga rangaɗa musu kira ta wayar salula da yake tana karɓar lambobinsu. Hakan ya sa lokaci kankani ta sha kwana kamar yadda ta yi tsammani. Manyan mutane ne masu hannu da shuni suka fara rububin aurenta wannan ne ya sa ta karyata maganar BASEERA, da kuma RUKY don yanzu dai ga maza nan kowa yana so ta bashi dama ya dama, kowa yana bayyana mata irin tsantsar son da yake mata tare da koɗa irin baiwar kyawun da Allah ya mata. Wannan ya sa kanta ya fashe take ta jin takaici da ta kare a gidan talauci bayan ga rayuwar da ta dace da ita duk da tana ganin lokaci bai kure mata ba.
"RUKY kin ga abin da nake faɗa miki ko, zawarci ya danganta da irin kyau da aji da kuma iya kamun ludayin bazawarar yanzu dai idanunki sun gane miki dama bahaushe ya ce gani ya kori ji, kina gani har gajiya nake da amsa kiran maza a wayata kuma kaf cikinsu babu na jefarwa kowanne yana takama da dukiya yana kuma ji da kansa, kowanne yana nuna mini so da kauna da kulawa ga su wayayyun maza ba kamar wancan fakirin da na baro gidansa ba ga bakin talauci ga kansa kife a cikin kwarya ba ma tukunya ba"
"SALIMAH ba za ki gane bane, ai fa haka suke fitowa a farkon zawarci ai kamar budurwa ce da za ki ga farkon fara budurcinta za ki ga maza gasu nan manema kamar me amma da kaɗan-kaɗan za su watse sai wanda yake da gaske da aure yake sonta shi ne zai tsaya. To zawarci ma haka yake farko ga mazan nan kamar jamfa a jos amma tafiya in ta yi tafiya za su zame su barka wani dama rage dare yake zuwa kuma ABBAS ai wayayyan mutum ne ke ce baki bashi damar nuna miki kulawa ba da kin ba shi da sai ya mayar da ke sarauniyar mata"
"Hahahaha ni nawa ba irin na kowa bane, yadda nake mai kyan nan babu mai yarda na kufce masa, kuma ki daina kira mini sunan mutumin nan don muna iya yin uwar watsi da ke yanzu" Ta ce tana wani yatsina irin na wanda duniya ta ɗaga, ko kaɗan ba ta tunanin akwai ranar da duniya za ta nanata da kasa don ta ga yanzu tana murza kambunta yadda take so.
"Allah baki hakuri kawata kin san ni ruwa ya karewa ɗan kada shi ya sa nake ganin kamar kowa ma haka ne"
"Ban da kowar wake, ki bi sannu ki dangwali arziki ki bar shi nan, ni nawa zawarcin mai lasisi ne, kuma arzikin auren da zan yi sunansa kogi mai gudana wanda ruwansa ba ya taɓa kafewa" Ta ce tana saka hannu a jakarta pink wacce ta yi macin da leshin jikinta mai ratsin pink da takalmi da mayafinta. Dubu ashirin ta lissafa ta ba RUKY godiya ta mata tana ta mamakin yadda zawarawa suke wa SALIMAH ɓarin kuɗi tamkar basu san ciwonsa ba.
"Kina lokaci!"
"Faɗi ki kara RUKY ban rasa komai ba ga iphone 16 ga keypad hr biyu ga android nan kina dai ganin hannun Umma ita ma tana rike wayar dubu ɗari biyu da ashirin ai mu kam mun yi ban kwana da talauci"
"Na ga Umma ita ma yanzu ba kowa take kulawa ba, ranar nan yarinya ƴar makotanmu ta je siyan koko da kosai da sassafe amma ta yi ta buga gidan ba a buɗe ba wai sai ma karan jannareto da take ji har safe ba a kashe ba"
"RUKY kenan ai mu da sana'a sai dai mu ga ana yi, kina dai ganin yadda aka gyara mana gida kai gaskiya kuɗi ya yi a rayuwa mai kuɗi bai kwana da haushin kowa ba"
"Wai yanzu a cikin mutum ukun nan da kike ji da su duk cikin zawarawan ki, Alhaji Tahir, Alhaji Mubarak, Alhaji Abdullahi wanne za ki aura? Kowanne dai ji yake da ke kuma burinsa ya zama gwani wato zakaran gwajin dafi"
"Lokaci zai nuna" Ta ce tana jin kanta saboda ta san a halin yanzu ita allurar ruwa ce mai rabo ne zai ɗauka.
*BAYAN WATA GUDA*
Tafe suke a mota ita da Alhaji Tahir da ya zo suka je ya mata siyayya, suna hirar soyayya abin su, saboda ta nunawa ABBAS cewa ga irin matsayin da ta taka yanzu ta saka Alhaji Tahir ɗin ya biyo ta wajen kafintocin da ABBAS yake aiki wai za ta saya kujerar yar tsugunno irin ta tsakar gida, wai Umma ce ta ce ta siyo mata kuma kawai don ta kuntatawa ABBAS ne ta san in ya ganta hankalinsa zai tashi, shi kuwa Alhaji Tahir ya amsa mata da
"Ranki ya daɗe tauraruwar mata an gama ai sai yadda kika ce za a yi, matsayinki ya fi haka" Ya ce yana wani koɗa ta, wani murmushi ta yi wanda ya kara bayyana kyan ta, a daidai wajen ya gangara gefen hanya ya faka motar har yana cewa ta zauna ya fita ya siyo da yake bai san manufarta ba sai ta nuna masa ai Ummar akwai kalar wacce take so. Fita ya yi daga motar ya kewaya zai buɗe mata don ko yaushe shi yake buɗe mata ta shiga haka idan za ta fita ma. Sosai ta ki daɗi domin kuwa tarkonta ya kama, hango ABBAS yana ta yanka katako sai gumi yake ga shi inda suka tsaya saitinsa ne dole idan za ta fito zai ganta.
Zagayowa Alhaji Tahir ya yi ya buɗe mata kofar fararen kafafunta ta ziro wanda suke sanye cikin goldin ɗin takalmi, a adaidai lokacin wayar ABBAS ta yi kara ya fito da ita daga aljihu zai amsa kiran, a hankali ta fito sanye take cikin doguwar rigar bakar atamfa mai goldin, ta sha ɗaurin ɗankwali mayafinta yana yafe a kafaɗarta da yake yau yafawa ta yi ba kamar kullum da take sakalawa a gefen kafaɗa ba ta yi bala'in kyau laɓɓanta sai shekin lip stick ɗin da ta shafa suke. Yana danne ok ya kara wayar a kunne kamar an ce ya ɗago kansa sai ya hangi fitowar SALIMAH daga mota wani mutumi yana rike da murfin kofar da ta fito ɗin, sai wani kare mata kallo yake yana washe baki kamar tsoho ya ga budurwa ita kuma tana masa wani murmushi da shi kansa ABBAS a iya sanin da ya mata na matsayin matarsa tsawon shekara biyar bai taɓa ganin ta yi irinsa ba murmushi ne mai cike da ma'anoni da dama murmushi ne da yake nuna tsantsar so da kauna da nuna kulawa ga wanda ake yi wa shi.
"Ko don ba ta so na shi ya sa bata taɓa yi a gabana ba" Ya ce a zuciyarsa kirjinsa yana bugawa amma kaɗan ba wani sosai ba ambaton Allah da ya fara yi a zuciyarsa shi ya sa ya ji nutsuwarsa ta daidaita, a hankali ya ɗauke idanunsa daga kallonta ya yi tamkar bai san fa zamanta a wajen ba tamkar babu wata halitta SALIMAH haka ya nuna yana magana a wayarsa wanda ba da kowa yake wayar ba sai Mama har da dariya yake wacce ta bayyana hakoransa.
SALIMAH gefe ta matsa Alhajin ya rufe kofar. Duk da a jike take da kuɗi ko ɗazu ya mata transper na dubu ɗari biyar sannan da suka je shagon siyayyar ya bata dubu ɗari kuma duk kayan da ya ɗauka shi ya biya kuɗin amma yanzu ya fito da 50k ya miƙa mata ta karɓa. Tana taku ɗai-ɗai suna masu jerawa duk gurin kafintocin cike yake da ma'aikatan kowa yana ɓangarensa yana aiki amma sai ta tsallake wajen kowa ta nufi wajen ABBAS saboda cim ma manufarta domin ta fara zargin kamar bai gane ta ba tun da ta hangi lokacin da ya kalleta har kamar ma sun haɗa ido sai dai ta ga bata zame masa TV ba don ta san da ya gane ta zai saka gaba yana kallo tamkar ta