Showing 42001 words to 45000 words out of 61883 words

Chapter 15 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10811

gilas babu abin da ya dame shi da auren nata har ma ƙara karantawa yake yana murmushi sun ɗauka zai yaga ya shiga kuka yana roƙon ta koma gidansa. ABBAS kuwa ya ji babu daɗi da za su buɗa zuciyarsa da sun ga yadda ta yi baƙi amma ya danne hakan ne don kar ya ba haƙarsu ruwa.


Suna jan motar ya yaga katin yana mai raya wa a zuciyarsa cewa haka Allah ya ƙaddara kuma shi bai isa ya canja ƙaddara ba.






Ta saya dai zannuwan gadon MAMAN AFRAH masu kyau da inganci wanda basa kuɗewa kuma basa yin gashi, da turarukan wuta, da humra masu musulmin ƙamshi, sai kuma sahihin maganin sanyi da kuma kazar sababi da aka dafa mata sai daka da original man ayu mai buƙata ga lambar MAMAN AFRAH 09013181851.


Ta sha tsumi ta tsumu an sha ƙunshi da gyaran gashi gyaran fata kuwa tamkar fatar jarirai haka fatarta ta dawo sai sheƙi take ga laushi. An sha biki an kashe kuɗi an gayyaci masu hali an watsar da talakawa ta shiga ta fita kaya har da wanda bata saka ba daga cikin na fitar biki haka ma uwar amarya Umma.




Da daddare motoci guda talatin ne suka layu a layin gidan su SALIMAH wata motar ma mutum biyu ne ko ɗaya a ciki saboda motoci sun wadata!.




Motar amarya sabuwa ce dal sai sheƙin sabunta take haka aka tafi kai amarya da ta sha ado ta yafa mayafi sai farin ciki ya hana ta sukuni. A ƙogar wani tangamemen gida tamkar unguwa guda motocinsu suka yi masauki aka wangale tangamemen get ɗin motoci suka fara shiga a laye duk yawansu amma sai da suka shige gidan duka. Part ɗin ta aka nuna musu mai gadin ne ya nuna nan ƴan kai amarya suka nufa suna sharara guɗa, ta cikin mayafi take ƙarewa gidan kallo aljannar duniya don gidan ya fi na EESHART nesa ba kusa ba. A bakin gado aka mata masauki ana ta yaba tsaruwar gidan da kayan alfarmar da aka zuba mata. Nana dai masu kawo amarya suka mata sallama suka kama gabansu masu motoci suka ɗauke su ciki har da BASEERA kuwa ta rage daga ita sai EESHART da RUKY.


Tun suna jiran ango ya zo a yi siyan baki har suka fara gajiya ga shi SALIMAH ta kira wayarsa ya fi sau shurin masaƙi a rufe duka layikansa. Mai gadi RUKY ta je ta tambayo ya ce ai Alhajin tun da ya fita da safe bai shigo ba hakan ya sa ta yi tunanin ko yana tare da abokansa. Ganin goma da rabi sai EESHART ta ce ita za ta tafi da yake da motar ta ta zo sai ita ma RUKY ta ce bari ta bita ta rage mata hanya, haka suka mata sallama suka tafi amarya duk ido ya raina fata babu ango ga an zambaɗi magunguna da kazar sababi.




Bayan tafiyarsu ta haura sama ta shiga ƙarewa gidan kallo ta sama, amma gidan shiru sai hasken ƙwayaye da take gani daga kowane ɓangaren guda biyu inda ta yi tunanin nan ne ɓangaren matan nasa sai kuma wani guda ɗaya da yake duhu dilim babu haske ta yi hasashen ɓangarensa ne tun da ba ya nan shi ya sa ba fitilu.


Ƙasan ta dawo wai kar ya dawo ya ga bata nan ga tana jin yunwa bata ci abinci ba a cewarta sai an kawo kayan maƙulashen amarya.




Bakin gadon ta koma ta zauna tare da lulluɓa mayafinta ta zauna zaman jiran ango a haka gyangyaɗi ya fara ɗaukanta tun tana gyangyaɗawa har ɗaurin ɗankwalin ya kama gabansa jingina ta yi da allon gadon bacci ya ɗauke ta tana cikin baccin ta falka duba wayarta ta yi ta ga karfe uku da rabi na dare. Sosai ta yi mamaki ganin ta kusa kwana a zaune duk ma ba wannan ba ina ango yake ya aka yi bai zo ba kuma mai ya sa wayarsa a kashe? Waɗannan su ne himilin tambayoyij da suke ƙumshe a zuciyar sabuwar amarya SALIMAH...




Na rubutu yau🤦‍♀️ 10 readmore wayyo ni😫




MAMAN AFRAH 09013181851










https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1






*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*





NA






MAMAN AFRAH






☀️ *First Class Writers Asso* ☀️


Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation




*GARGAGAƊI*


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️


JAN HANKALI


Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.




SADAUKARWA


Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.






PAGE 12





Sai da yamma aka sallamo Baba daga asibiti abokansa wanda suke asibitin sun yi murna sosai don a yadda ya yanke jiki ya faɗi wasu basu tsammaci zai tashi ba tare da ya samu matsalar shanyewar ɓarin jiki ba. Ko da aka dawo da shi gida mutane suka ringa tururuwar zuwa duba shi, Umar kuwa sai da aka ɗura masa maganin bacci aka samu salama gabaɗaya ya haukace musu shi sai an nemo masa matarsa sai an ɗaura musu aure. Sai da daddare Baba da Hajiya suka samu keɓewa inda ya shiga labarta mata yadda abubuwa suka kasance wato yadda ya shammaci mutane ya faɗi wanwar don dakatar da ɗaurin auren.




"Ai wallahi Alhaji na tsorata sosai, duk tunanina faɗuwar gaske"


"Hahaha babu wani gaske kuma babu wanda ya gane shiri na ko shi likitan ina jin dukan iska ne bai san aikinsa ba domin cewa yake ɓacin rai ne ya kawo hakan ko ubansa ne ya ɓata mini ran oho" Ya ce yana fashewa da dariya ita ma Hajiya dariyar ta yi ta ce.


"Ai wallaho ta yi wa kanta kuma ta yi wa arziƙo dundu na tabbata har ta mutu ba za a samu wani mai ɗan maiƙo ya aure ta ba" Hajiya ta ce tana dariya.


"Rabu fa sakarya ni ai na ji daɗin hakan, dama saboda jama'a kar a ce na karɓi dukiyarsu na kore su amma ai da tuni sun daɗe da barin gidan nan, kuma da a ce na san idan za a mata auren guduwa za su yi da tun bayan bakwai ɗin ubansu zan tarki ɗaura auren kin ga da tuni wani batun ake ba wannan ba amma yanzu ma ta kwana gidan sauƙi lokaci bai ƙure ba abu ɗaya na sani mun jefar da ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda su je can su gaishe da na gaba" Cewar Baba yana kishingiɗa.


"Yo dama mana ai sun taimake mu sun taimaki kansu, dama in sun zauna ma za su rayu cikin uƙuba ne!." Hajiya ta ce.


"Yanzu dai babu mai cewa ni na kore su za a ji da ƙafafunsu suka gudu, kuma babu mai ɗarsa zargin wahala ce ta kore su tun da ga shi ƙarewar adalci ma ɗan cikina zan aura mata, batun dukiyarsu kuwa yanzu ne zan kwanta a kan dukiyar na ci karena babu babbaka duk da dama babu abin da ya hanani wadaƙa da dukiyar, to wa ma zai tuhume ni ai dai duk duniya kowa ya sani ni kaɗai ne ɗan uwan ubansu kin ga kuwa babu mai cin gadonsu sai ni"


"Gado kuma Alhaji mutuwa suka yi?"


"Yo sai sun mutu duk wanda ba a san inda ya dosa ba ba a san inda zai je ba, kuma ba a san inda yake ba shi da matacce duk ɗaya! Ni nan zan tara mutane a yi musu sadakar uku da sadakar bakwai ke har da ta arba'in ma, idan shekara ta zagayo in musu sadakar cikon shekara don tabbatarwa da mutane sun mutu! Zan ce ruwa suka faɗa ya tafi da su ko gawarsu bamu samu gani ba"


"Allah dai ya biya Alhajina, shi ya sa kake ƙara shiga raina kan yin kane-kane kwakwalwarka tana ja" Hajiya ta ce tana ɗora kanta a kafaɗarsa.


"Musamman a kan kuɗi!" Ya ce yana farawa tare da lakato hancinta.


"Inda ƙara volume, kin ga ana labarai kuma ga shi ana nuno mota ta kama da wuta" Alhaji ya ce yana maida hankalinsa ga TV.


"A safiyar yau ne wata mota sharon ta samu ibtila'in kamawa da wuta, motar dai ta haya ce ta ɗakko mutane daga garin Zariya za ta ke Kano, motar tana ɗauke da mutane da har yanzu ba a tantance yawansu ba, babu wanda ya tsira gabaɗaya ta ƙone ƙurmus" Mai karanto labaran ya gama faɗa.


"Allahu akbar! Rai baƙon duniya HAWWA da SABEER lokaci ya yi" Hajiya ta ce tana murmushin jin daɗi.


"Allah jiƙan musulmi yara sa'i ya yi" Baba ya ce yana kallon TV amma babu wani jimami a tare da fuskokinsu.


"Dama lokaci ne ya kira su ko uban me za su je yi a Kano ai shikenan"


"Kin ga ni yanzu na samu abin faɗa zan tara mutane in faɗa musu jiya yarinyar nan ta ɗauki ƙaninta sun tafi Kano sun yi haɗari mota ta kama da wuta sun mutu"


"Shikenan ƙurunƙus" Hajiya ta ce tana tafa hannu.


Washe gari tun da aka yi sallar asuba Baba ya sa aka sanar d mutuwar a masallaci mutane suna ya masa gaisuwa gari yana wayewa aka shimfiɗa tabarmi aka zauna zaman makoki Umar kuwa sai da ya yi ƙaramar hauka. Kowa ya yi jimami har da Baba Sadiya amma a zuciyarta ta san hakan ba gaskiya bane tun da ba gawarsu aka gani ba kuma ma ta san ba Kano suka tafi ba Kaduna suka tafi.






*HAWWA*




Amrah ta sha ruwan mamakin abin da ta mata kuma ya sha jinin jikinta ganin HAWWA ta zama fitsararriya, sai dai ta dangana hakan da rayuwar gidan da suke zaune bayan mutuwar mahaifansu.


"Ni kika mara kika hankaɗe HAWWA"


",Ni tawa fuskar ba fuska ba ce kenan, to ki dawo hayyacin ki ba zan taɓa saurara miki ba matsawar baki saurara mini ba"


"Haka kika ce?" Ta ce tana tashi tsaye tana aikawa HAWWA harara.


"Eh"


"Mu zuba mu gani!" Amrah ta ce tana yin ƙwafa.


Washe gari haka HAWWA ta shiga gyara gidan tas ta share ta yi wanke-wanke. Ruwan zafin shayi ta dafa ta yi wainar fulawa haka aka zauna Goggo ta zubawa kowa Usman sai yaba daɗin wainar yake don shi ko biredin bai ci wainar kawai ya ci da shayin da ya sha kayan ƙamshi.


"Usman"


"Na'am Baffa"


"Zan ba HAWWA kuɗi ka kai ta za ta sayo kayan SABEER da nata sai ku biya ta kai ɗinki sannan ta siyo da dogayen riguna kafin a hankali sai ake saya musu, da kaɗan-kaɗan shi ma SABEER ɗin a yanko masa yadi da shadda duk sai ku bada ɗinkin" Wani daɗi Usman ya ji a ransa jin zai fita da abar ƙaunarsa.


"To Baffa" Ya ce har ya kasa ɓoye farin cikinsa. HAWWA ma ta ji daɗin abin da Baffa ya yi murna wajen SABEER kuwa ba a magana sai tsalle yake wai zai sa kaya mai kyau tun da Abbie da Ummie suka mutu tsohon kaya yake sakawa kuma yaggagu sai dai HAWWA ta ɗinke masa da zare da allura. Tausayinsa ne ya kama Baffa da Goggo Amrah kuwa Allah ya ƙara ta yi a zuciyarta. Godiya HAWWA ta yi wa Baffa amma ya dakatar da ita ya ce ai shi Babbanta ne babu godiya a tsakaninsu.


"Mun gode Baffa saura ka saka mu a makaranta" SABEER ya ce yana dariya.


"Babu godiya SABEER kuma zan saka ku a makaranta kai duk wani abu da kuke buƙata da ɗawainiya da ku zan muku daidai gwargwadon samuna, ban yi alƙawarin yi muku gata kamar na mahaifanku ba kasancewarku ƴan gata kuma mahaifanku suna da dukiya amma ni ma zan yi iyar iyawata" Ya ce yana kama SABEER ya jingina shi a jikinsa.



Idanun HAWWA ne ya ciko da ƙwalla, tana tuno irin rayuwar da suka yi a gidan Baba, babu tausayawa babu tausasawa babu ja a jiki tamkar wanda basu da wata alaƙa da su amma ga shi Baffa yana nuna musu su ɗin ma suna da gata yana nuna musu cewa marayu ma ƴaƴa ne saɓanin inda ake nuna musu maraya bashi da wani tun da iyayansa basa raye ya rasa komai.



"Baffa in bi su mu siyo?"SABEER ya katse mata tunani.


"A'a SABEER yanzu zan fita ƙofar gida wajen aiki an jima idan sun kawo maka kayan sai a ɗauko riga da wando a maka wanka sai ka fito wajen ka ga yadda kayan jikin ka suke kunya zan ji a ce ka fita waje da ƙasƙantattu haka" Ya faɗa yana shafan kansa. Tsalle ya yi yana ta murna.


Hijabi HAWWA ta saka ta fito daga ɗaki.


"Amrah ɗakko mata hijabi mana dogo wanda zai rufe mata kayan jikinta" Baffa ya ce yana kallon yadda hijabin jikinya ya tsufa ya yaƙune yana ta tunanin wai ƴar gidan ƴar uwarsa ce wannan da kayan kamar almajira rayuwa kenan duk yadda ka kai ga samun gata don iyayanka suna raye ne amma da zarar ƙasa ta rufe idanunsu sai dai ka sa ido ka yi kallo saboda ba kowa bane bayan ransu zai mayar da kai mutum wani ma dama yana maka abubuwa ne saboda idanun mahaifanka da zarar sun gusa sai dai ka ga ana yi.


Cike da ladabi da biyayya ta amsa wa Baffan ta shige ɗaki a ranta tana ƙunƙune ba don Baffa bane ko ana ha maza ha mata babu wanda ya isa ya juya ta. Hijabin ta ɗakko mata ta karɓa ta cire na jikinta tana murmushi ta ce


"Ya mini kyau Aunty Amrah" Wani takaici ne ya turnuƙe Amrah ganin yadda hijabin jalbab ɗin ya yi wa HAWWA mugun kyau tamkar dama don ita aka yi kalar yadin ash. Murmushin yaƙe ta saki ta ce


"Ai kuwa dai ya karɓe ki ƙanwata kin fito fes abinki"


"Ni ma zan sayo irinsu idan muka je kasuwar" Ta faɗa tana murmushi tana kuma fakar idanun su Baffa ta taɓewa Amrah baki, sosai Amrah ta ji tamkar ta tashi ta hau HAWWA da duka. Ita kuwa Goggo bata kawo komai a ranta ba kasancewar ta san HAWWA har zuciyarta take magana saɓanin Amrah da take abu cikin kissa saboda ganin Baffa yana wajen bata san cewa ita ma HAWWA ta fara yi wa Amrar abinda take ganin za ta ƙwatawa kansu ƴanci ba ita da ɗan uwanta.


Sallama HAWWA ta musu ta bi bayan Usman Goggo tana musu a dawo lafiya SABEER yana ɗaga mata hannu har da bata saƙon sweet Amrah kuwa dama tuni ta cikawa rigarta iska ta shige ɗaki.


"Wannan yarinyar ta zo gidan nan don ta kashe mini kasuwa, bana jin akwai wani ɗa namiji da yana ganin tsinanniyar yarinyar nan zai zo gare ni har ya iya furta mini kalmar so? Ga ta haɗaɗɗiya ga kyau ga addini ga nutsuwa ta fi ni komai gaskiya sai na tashi tsaye a kan yarinyar nan in ban lallashi ziciyata ba sai na kwaɓe mata kyakkyawar fuskar nan tata da asid ya ƙone fuskar ta dawo abin tsoro" Amrah ta ce a zuciyarta tana jin tsanar HAWWA a ranta musamman da Baffa ya bata kuɗin sayayyar nan sai ta ki kenan yanzu ta zama tamkar kishiyarta za a ke musu abu tare bare ma da ta ji HAWWA tana cewa za ta saya irin hijabinta wato gasa ma za ta tsaya yi da ita.


"Don ma dai mazan basa gabana ina kula su ne don nake tatiƙe musu aljihu, ga wanda zuciyata can ta mutu a kansa wato kyakkyawan matashi wanda yake ji da lokaci son kowa ƙin wanda bai samu ba haƙiƙa in na mallaki ABBAS a matsayin miji kuma na dace yana matuƙar ƙaunata to ni fa na kasa na sayar" Ta ce tana yin juyi a katifarta tare da kamo hotonsa wanda ta ɗauke shi yana jingine a jikin banci ba tare da ya sani ba.


"Yaushe ne zan furta maka kalmar so, kalmar nan da ta daɗe tana yawo da addabar zuciyata, son ka wanda na kamu da shi tun ban san mene ne so ba, ma yi matuƙar baƙinciki a shekaru biyar da suka wuce lokacin da sanarwar ɗaurin aurenka ta same ni na yi baƙin ciki na yi kuka na shiga damuwa ganin za ka auri wata ba ni ba sai dai yanzu ina cikin tsananin farin ciki jin ka rabu da matarka sai dai ba a nan gizo yake saƙar ba shin za ka so ni? Har ka yarda mu yi aure mu rayu a inuwa ɗaya? A duk ranar da na furta kalmar so a gare ka kuma ka aminci sai na zubar da ruwa a ƙasa na sunkuya na kafa bakina na shanye shi tas" Ta ce tana shafa hoton nasa tana jin wani shauƙi na soyayya tana sawa a ranta a wannan gaɓar dole za ta yi iya yinta don ganin ta cim ma burinta muradinta ya tabbata na zama matar ABBAS.




HAWWA a waje ta samu mashin ɗin Yaya Usman ya ajiye shi, shi kuma yana can tsaye yana magana faɗa-faɗa.




" ABBAS to ni na ce ka ba Baffa kuɗin cinikin jiyan a kan mai za ka bashi, ai ka san dai ni ne magajinsa a kafintocin nan kuma komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login