Showing 57001 words to 60000 words out of 61883 words
Chapter 20 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
nake son zama Baffa, in aka bani bindiga in harbe Baba Bukhari da Hajiya da Yaya Umar da Aunty Lawisa"
"Ikon Allah kai dama don ka harbe mutane za ka zama soja?" Goggo ta tambaye shi.
"Eh da lokacin kafin su Ummiena su mutu lawyer nake ce mata zan zama in na girma, amma yanzu na fasa soja zan zama"
"To mai ya sa kake so ka harbe su iyayanka ne da ƴan uwanka" Baffa ya faɗa.
"Bama jin daɗi a gidansu fa Baffa kayanmu a yage kamar mu ne almajirai, suke ta saka Aunty HAWWA aiki wata rana su mare ta kuma basa bamu abincin da suke ci, ga shi mu tafi school a ƙafa ga nisa in na gaji Aunty ta goye ni kuma fa akwai motoci masu yawa a gidan amma mu ba a barmu mu hau" Ya ƙarasa faɗa kamar zai yi kuka. Kallon kallo aka shiga yi da Baffa da Goggo suna jinjina ƙwaƙwalwar yaro da bata mantuwa ko ka masa alheri ko saɓanin haka yana sane da kai.
"Ka yi haƙuri ka ji yaron kirki yanzu ba ga shi ka bar gidan ba Allah yana son masu haƙuri da masu yafiya" Baffa ya ce yana rataya masa jakarsa a bayansa tare da shafa kansa. Shiru ya yi bai yi magana ba.
"SABEER zo mu tafi" Yaya Usman da ya shigo ya ce. Yanzu ya sakarwa SABEER sosai yake jansa a jiki don ya ƙara samun fili a zuciyar HAWWA da zai gina soyayyarsa. Yana ɗaga musu hannu suka fita.
Ita ma sallama ta musu ta fita don ta san yanzu mai napep ɗinta ya zo. Sanye take cikin riga da wandon farare tass babu sirki a jiki, rigar tana da ɗan tsayi iyakarta cinyarta sai ƙaramin hijabi da bai kai cibiyarta ba, ƙafarta cikin farar socks da baƙin ƙafa ciki, jakarta baƙa rataye a bayanta sai wayarta a hannunta. Tun bayan fitowar su SABEER yake kallon ƙofar yana jiran fitowarta bai san mai ya sa ba kuma bai san dalili ba yarinyar tana matuƙar birge shi halayenta kyawawa ladabi da biyayyarta uwa uba girmama ta gaba da ita ya jima bai ga mai halayya da sanyin hali irinta ba.
Sautin ƙira'ar karatun ta da ya ji ranar da Baffa ya bashi kaya ya kai cikin gidan, sosai ya ji daɗin karatun tana ba kowane harafi haƙƙinsa, tun daga ranar ya ji ya bata matsayi na musamman, tun daga ranar ya ji yana son ganinta wanna dalilin ya sa yake yin sakkon zuwa wajen aiki don ya sanyata a idanunsa, saboda sai ya ji idanunsa sun kasa jure jiran har sai ta dawo daga school zai ganta, idan ya koma gida tunaninta ya yi ta yi masa kai kawo a zuciya.
Fitowarta daga gidan ne ya tsananta bugun zuciyarsa ya ƙaru dakyar ya saisaita kansa yana ɗan satar kallonta farin siririn gilashin da ta sanya ya ƙawata fuskarta tare da ƙara bayyana dogon hamcinta da yake kwance a kan kyakkyawar doguwar fuskarta. Ko kaɗan bata lura da shi ba, hankalinta ya yi school bata son malamin da zai shiga da safen nan ya hana ta shiga kawai haka yake yi idan har ya riga ka shiga da minti biyu to ba za ka shiga ba. Ta yi mamakin ganin mai napep ɗin bai zo shi da kullum a wajen take samun sa, lambarsa ta binciko a cikin wayarta ta shiga doka masa kira sai dai a kashe wayar, fuska ta marairaice tamkar za ta yi kuka, hakan da ta yi sai da ABBAS da yake dakon kallonta ya ji abin ya daki zuciyarsa, da a ce za a masa tambayar waye baya son ya gani cikin damuwa to bayan Mamarsa HAWWA zai ce, amma shi bai yarda wai so bane tun da ya yi ittifaƙin ya daina soyayya daga kan SALIMAH ba zai ƙara son wata mace ba da sunan soyayya wannan yanayi da alamomin da suke farmakar zuciyarsa game da HAWWA ya ƙaryata zuciyarsa da kuma FAROUQ ya ce kawai kyawawan halayenta ne kawai suke birge shi har yake jin ta tamkar ƙanwarsa. Yanzu idan suka zauna da FROUQ ba shi da magana sai ta HAWWA ta gaishe ni da safe da yamma da za ta je islamiyya ma ta gaishe ni ta yi kaza ta yi kaza amma in ya ce ya kamu da sonta sai ya ce ba haka bane.
Kallonta yake har ba ya son ƙiftawa, ganin narai-narai da ta yi da fuskar sai da ya ji tamkar ya je ya tambaye ta damuwarta duk da yanayinta ya nuna masa mai napep take jira. Wata ajiyar zuciya ya sauke ɗagowar da ya ƙara yi sai kuwa suka yi ido huɗu da ita, da sauri ya sadda kansa yana danna waya duk sai kunya ta kama shi. Ita kuma sai lokacin ta gan shi, cikin takun ta mai tattare nutsuwa ta tako zuwa wajensa. Subhanallahi kawai yake ambata don tana tunkaro shi bugun zuciyarsa yana ƙaruwa.
"Yaya ABBAS" Har tsakiyar zuciyarsa ya ji sunan sai yake ji a duk lokacin da ta kira shi tamkar duniya babu wanda ya fi iya kiran sunansa ya yi daɗi sama da HAWWA.
"Na'am ƙanwata har an fito" Ya ce yana ƙarfin halin kallon fuskarsa wani abu ya fusge shi, wanda ba don yana ƙaryata kansa a kan ba zai so wata bayan SALIMAH ba da sai ya ce so ne ya fusge shi, ji ya yi dama a ce ta tsaya a haka kawai yake kallon fuskarta ba ya jin zai taɓa gajiya amma fa a hakan ma wai matsayin ƙanwarsa.
"Na fito Yaya amma ban ga mai napep ɗin ma kuma wayarsa a kashe ko ka ga zuwansa tafiya ya yi?" Tamkar kar ta tsaya da magana sosai yake jin kalamai da sanyin murya yadda take magana yana shiga dodon kunnensa tare da ratsa ɓargo kai hatta ƙasusuwansa bai bari ba, ji yake tamkar muryarta ma tana gudana a jikin jijiyoyin jikinsa. Yadda ta langaɓar da kai tana yin tamkar ta yi kuka sai ya ji tamkar ya zama tsuntsu ya sunkuce ta ya kai ta school ɗina minti ƙalilan don kar ya ga alamar damuwa shimfiɗe a fuskarsa.
"Ki yi haƙuri mana, ba sai kin shiga damuwa ba, ban gan shi ba amma na yi mamakin rashin zuwansa" Ya samu kansa da bata haƙurin laifin da ba shi ya mata ba sai don kawai ba ya son ta damu, sannan ƙoƙarinsa na faranta mata don ko shi a ranar da ta fara bashi haƙuri da Yaya Usman yana faɗa masa maganganu haƙiƙa ya ji sanyi a ransa. Shiru ta yi ganin kiran ƙawarta Afrah ya shigo wayarta, ɗagawa ta yi.
"Wai ya baki taho ba har yanzu? Sai an hana ki shiga"
"
"Mai napep ɗin ne bai zo ba amma bari na samu wani ko machine sai na taho" Wani abu ne ya caki zuciyar ABBAS jin wai za ta hau machine sai ya ji wani abu kawai ba ya son ganin ta hau bayan machine ɗin wani namiji har gwara napep a kan machine, kafin ya ce wani abu sai ga Baffa ya fito.
"Hauwa'u baki tafi ba dama?"
"Bai zo ba Baffa ga shi ina neman makara kuma layin nan da safe abin hawa wahala yake" Wannan maganar ta yi dai dai fa zuwan FAROUQ abokin ABBAS da yake ta kiran ABBAS a waya zai tura masa lambar wani abokinsu da yake nema da gaggawa amma bai ɗaga ba ya je gida Mama ta ce masa ya tafi wurin aiki shi ne ya biyo shi. ABBAS kuwa wayarsa a silent take ya ga kiran FAROUQ na farko kafin ya ɗaga HAWWA ta zo sai ya sha'afa da kiran wani FAROUQ kasancewar wayar bata ƙara shi ya sa bai sake tunanin kiran yana shigowa ba bare har ya bi kira. Tun kan ya ƙaraso ya hangi ABBAS ɗin HAWWA tsaye daga gefe a gabansa, shi dariya ce ma ta kufce masa saboda ya tabbata ABBAS ya kamu da son yarinyar amma ya ƙi yarda da haka, ya ƙyale shi sai son ya gama masa dabaibayi yadda a lokacin bai isa ya yi musu ba.
Baffa barka da safiya" ABBAS da FAROUQ suka haɗa baki wajen faɗa. Amsa musu ya yi sai kuma ya ce.
"FARUQU idan ban ɗora maka nauyi ba don Allah miƙa Hauwa'u makaranta mai adaidaita sahunta bai zo ba(SHIN KIN KARANTA LITTAFINA ƳAN ADAIDAITA SAHU? IDAN BAKI KARANTA BA AN BARKI A BAYA DOMIN NA ƊATA LOKACI SOSAI WAJEN ƘAYATA LABARIN IYA ANSAI DA JABIRU SUN TAKA MUHIMMIYAR RAWA A LABARIN DA NAIRA 500 KACAL ZA KI SHA KARATU).
Kafin FAROUQ ya ba Baffa amsa ABBAS ya yi karaf ya ce.
"Babu wani ɗora nauyi Baffa ai sai a miƙa ta bari na karɓi mukullin sai na miƙa ta" Shi kansa ABBAS bai san maganar ta fito ba ji ya yi tamkar an fusge ta. Sosai Baffa ya ji daɗin cewa zai kai ta, ita ma sai fuskarta ta washe jin za a kai ta ba tare da ta makara ba. FAROUQ sosai ya yi ƙarfin halin danne dariyarsa don ya gane kishi ne ya sarƙe ABBAS shi ya sa ya ce shi zai kai ta da alama ba ya son ta hau bayan machine ɗin kowa.
"Bani mukullin" Ya faɗa cikin majewa don ya ga FAROUQ ɗin yana satar kallon Baffa da HAWWA yana masa wani murmushin na gano ka. Shi kuma abin da ya sa ya maje ya san har kullum dai zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato FAROUQ yana zarginsa da kamuwa soyayyar HAWWA wanda har yanzu yake ƙaryatawa. Tada machine ɗin ya yi ta hau suka fara tafiya Baffa yana ɗaga mata hannu tare da fatan dawowa lafiya ita ma hannun ta ɗaga masa daga nan suka tafi FAROUQ kuma ya shiga bincikar wayar ABBAS zai ɗauki lambar kafin ya dawo masa da machine ɗin ya wuce gida.
Tuƙi ne yake yi mai cike da nutsuwa, ƙamshin turarensa da nata yana dakar masa hanci, yadda suke tare a machine ɗin sai yake rawa a zuciyarsa ina ma su cigaba da kasancewa a haka, daɗin da yake ji a ransa sai ya ji tamkar bai taɓa riskar kansa a cikin irin hakan ba.
"Mai ya sa bakya sa niƙabi idan za ki je school?" ABBAS ya tsinci kansa da tambayar da shi kansa bai san ya yi ba.
"Niƙabi kuma Yaya?"
"Au ashe ba islamiya ba ce " Ya ce cikin wayancewa yana tuhumar kansa dalilin da ya sa ya yi tambayar ma. A dai dai titin da za su tsallaka wanda zai sada su da school ɗin su HAWWA suka hango Yaya Usman ya taho, ganin HAWWA a bayan machine ABBAS yana ja ransa in ya yi dubu ya ɓaci shi a haka nan ma ya tsani ABBAS amma shi ne don gigiwa ya ɗakko masa abar ƙaunarsa a machine, wacce yake fata da burin mallaka a matsayin mata kuma uwar ƴaƴa. A fusace ya taho har yana neman karawa wani mai napep, shi kuma ABBAS sai a lokacin ya gan shi haka ma HAWWA.
"ABBAS kai ABBAS" Ya shiga ƙwala masa kira tun kan ya ƙaraso. Ɗan dakatawa ABBAS ya yi tare da gangarawa gefen titi ya tsaya, shi ma Yaya Usman ɗin gangarawa ya yi inda suke ya sauka daga nasa machine ɗin ya tunkari ABBAS rai a mugun ɓace sosai a fusace yake ta yadda ABBAS yake mamakin dalilin tsayar da su da kuma dalilin ɓacin ransa. HAWWA jikinta ne ya ɗauki mazari don ta san yadda yake a fusacen nan dakyar ne in ba rashin mutunci zai yi wa ABBAS ba sosai ta ji damuwa ta sarƙe ta lokaci guda don bata son abin da za a ɓatawa ABBAS rai kamar yadda ta lura shi ma yanzu ba ya son a ɓata mata...
*SALIMAH*
Yana kai wa inda nan ne ta san ya kai ƙarshen magan kai kawai ta ɗaga masa ta tashi da ɗan gudu tana tashe bakinta jin kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata, ƙofar ta buɗe ta fice takalmanta ma a hannu ta riƙo su, shi kuwa Alhaji kafaɗa ya ɗaga alamar can ta matse mata, sauran matan sallama suka masa suka kama gabansu.
Baram ta banka ƙofar da za ta sada ta da falon nata jifa ta yi da takalman a falon tana kallon tangameman falon da ya gaji da haɗuwa da tsaruwa amma wai ake mata batun zai zama mallakin wata a gobe, bayan ƴan uwa da abokan arziƙi nan suka kawo ta ƙawaye duk sun san nata ne amma saboda cin fuska za a ce wai ta bar wa wata bayan ta san yana da halin da ko gida ɗari zai iya siyawa amarya amma saboda kwamacala zai ce a part ɗaya za su zauna shin wane irin miji ta aura? Fiiii ta hau sama ta je ta shiga ƙarewa ko ina kallo tana kuka wiwi tabbas akwai tashin hankali a kalamansa da dokokinsa amma duk abu ne wanda a duhu yake ba wani zai gani ba sai dai in ita ta faɗa wannan batun zaɓar ɗaki kuwa dole duk wanda ya zo sai ya gane tun da dole za a ga amarya ba ma wannan ba wa za ya faɗawa za a mata kishiya? Bayan ta yi wa mutane kurin cewa daga ita Alhaji Tahir ya rufe ƙofa ita ce ta gaban mota ita ce ta shiga taro amma kwatsam a ce a kwana uku rak wannan matsayin ya zagwanye?
Ƙasan ta sake sakkowa kamar wata mahaukaciya sabon kamu duk ta zauce ta firgice ita gabaɗaya ta ruɗe da rabon part ɗin nan da aka ce da yake duniyar ce a gabata ita dokokinsa za ta iya fatali da su amma batun part ɗin nan tamkar cewa ya yi ta raba ranta biyu ne ta bada rabi, part ɗin da ko Ummarta bata zo ta gani ba amma za a raba a ba wata bayan su sauran matan gidan kowacce gashin kanta za ta ci.
"Ko dai hannu aka saka mini? Ko dai shiga tsakanina aka yi da shi' Wani sashe na zuciyarta ya jefa mata tambaya.
"Waye zai shiga tsakaninku kawai butulci ne irin ma maza shi dama namiji ai butulu ne a wani ƙaulin ba ɗan goyon baya ba" Wani ɓangaren na zuciyarta ya sake saƙa mata hakan. Baki ta damƙe tana jin ruwan hawayenta yana biyowa ta bakinta yana sauka haɓarta wai ita SALIMAH ce yau namiji ya saka ta zubar da hawaye a cikin kwanakin cin amarcin ta amarcin da bai ciwu bama, ba ma wannan ba yau ne kwanan nata na uku zai cika amma mai zai yi da daren nata na yau wanda ya rage ƙwaya ɗaya tal? Ko dai ita ce ba ya son kasancewa tare da ita ta rasa kalar tunanin da za ta yi hakan ya sa take zaune tamkar mutuntumi ko gunki ta daɗe a wajen ita kanta bata san iya awannin da ta kwashe a wajen ba a ƙatshe ta lallaɓa ta koma bedroom ɗin da yake ƙasa inda aka ajiye ta jiya ta zame ta kwanta ba wai don ta rintsa ba sai don duniya ta rasa mai za ta yi ta ji daɗi a ranta. Ta yanke hukuncin ta zaɓi ƙasa saboda idan ta zaɓi sama duk wanda ya zo zai gane an raba part ɗin ta biyu tun da dole za su ga amaryar a nan kuma dole a jefa mata ayar tambaya. Tamkar taɓi-taɓi haka take kwance garau har aka faran assalatu dakyar ta lallaɓa ta tashi tana jin wani zafi a jikinta kamar zazzaɓi, alwala ta yi ta yi sallah sallar da ita kanta tana karatun sallah amma bata san mai take karantawa ba saboda tunani ya cunkushe mata ƙwaƙwalwa maimakon ta mayar da hankali ga sallaar ta yi addu'ar neman mafita amma haka ta sallame ta tashi ta koma makwancinta.
Wayarta ta ɗakko iphone 16 ɗin tana ƙarewa wayar kallo tana tuna android ɗinta ta gidan ABBAS wacce bashi ya ci ya saya mata don ya faranta ranta shi kuma yake riƙe keypad amma bata gode masa ba a raine ta karɓa ga shi yanzu tana fa wayar da ake yayi sai dai kash! Cukurkuɗaɗɗun al'amuran da suka taru suka yi wa rayuwarta ƙawanya sun disashe duk wani walwalarta.
Sunan Umma ta kamo tana son kiranta ta sanar mata matsalolin da suka kunno kai a sabon gidan auren da suka ci buri amma tana tsoron ran Ummar ya ɓaci saboda tana ƙaunar Ummarta a duniya ota kaɗai ta rage mata tate suka kasawa su tsare amma kuma dole ne ta faɗa mata tun da ita ce mahaifiyarta kuma ƴan magana sun ce abin da babba ya hango yaro ba zai hango ba ganin ƙarfe shi sai kuwa ta doka mata kira. Umma da bayan ta idar da sallah ta zubo ruwan zafi a plask ta haɗa kakkauran shayi da ya ji madara da milo tana zaune tana haɗawa da biredi tana lumshe ido ga ƙaran jannareton da wani matashi yake zuwa ana tada mata gida sabo ga plasma tangamemiya abun sai wanda ya gani, kiran da ya shigo wayarta ne ya sa ta tashi ta ɗakko ganin SALIMAH sai murmushi ya suɓuce mata.
"Yarinya mai goshin arziƙi auren mai kuɗi da daɗi duk rayuwarmu ta sauya, bare yanzu in kika bararraje ai duniya sabuwa mu gaba ta kaimu gobarar titi" Shi ne furucin Umma bayan SALIMAH ta danne kukan da ya taho mata ta yi sallama, shiru ta yi tana tuna wannan zancen bai tabbata ba.
"Umma mun kama RUƁAƁƁIYAR IGIYA" Ta ce tana fashewa da kuka.
"SALIMAH RUƁAƁƁIYAR IGIYAR uban me wai?" Ta tambaya tana dangwarar da kofin shayi ya tuntsure, don a tunaninta SALIMAH ta jaza musu salalan tsiya ne wato ta saka ya sake ta.
"Umma aure za a ɗaura masa yau"
"Aure dai da na sani SALIMAH shi Alhaji Tahir ɗin ne zai miki kiahiya bayan na cikin gidan da kika tarar?" Kwashe komai ta