Showing 48001 words to 51000 words out of 61883 words
Chapter 17 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
ringin ta katse, a karo na biyu wani kiran ya sake shigowa wani gajeran tsaki ta yi tare da miƙa hannu ta ɗakko wayar tana rayawa a ranta ko waye sai ta sauke ɓacin ranta a kansa, sai dai mai? Tana duba fuskar wayar ta yi tozali da suna angon nata yana wayo a kan screen ɗin wayar idanunta ta ƙara warewa ta tabbatar da shi ɗin ne da sauri ta tashi zaune ta danna ok tare da kara wayar a kunnenta, tana jin wasu tambayoyin da ta shirya domin yi masa su suna bijiro mata, ina yake tsawon kwanaki uku, mai ya sa wayarsa a rufe kuma mene ne dalilin wofantar da ita a matsayinta na sabuwar amaryar da ya ce ta fiye masa budurwa a matsayinta na bazawara...
*Gabaɗaya littafin RUƁAƁƁIYAR IGIYA book 1 za ku karanta a free wato kyauta, idan mun gama book 1 za mu yi book 2 wanda shi kuma zai kasance paid book wato littafin kuɗi, wanda yake da hali kuma yake da buƙata* .
NGD maman afrah🥰
09013181851
[1/11, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1
*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 13
*ABBAS*
Tun da HAWWA ta bashi haƙurin nan ya kasa mantawa da abin da ta masa, domin wannan abin da ta yi ya nuna ta san kima da muhimmancin ɗan adam wanda ba kowa ne ya san hakan ba bare har ya bada haƙurin laifin da ba shi ne ya yi ba, galibin mutane ko da a ce su suka maka laifi to baka isa su ce ka yi haƙuri ba. Wasu suna ganin hakan ci baya ne yayin da wasu suke ganin wanda za su ba haƙurin bai isa su furta masa kalmar haƙurin ba kuma ba komai ne yake saka hakan ba illa girman kai.
HAWWA ya furta hakan a fili yana son sanin dalilin da ya sa bata zama mai girman kai da ɗagawa ba irin na wasu ƴan matan zamanin da aka fi samu yawanci idan suna daidai shekarunta ake samun su da gigiwa rawar kai da kuma raini amma kuma sam ita yanayinta ya nuna ba haka bane.
"ABBAS yarinyar nan ta baka haƙuri ne kasancewar Yayanta ne ya maka laifin ba don wani abu ba" Wani sashe na zuciyarsa ya kissima masa hakan. Iska ya fesar daga bakinsa yana mai son mantarwa da duk batun ta dama kawai ta burge shi ne sannan haƙurin da ta bashi ya wanke masa kaso mafi yawa daga cikin ɓacin ran da Yaya Usman ɗin ya saka shi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran laifi ba bayan yana ganin za su yi sa'anni da Yaya Usman ɗin tun da a ƙalla shi ma ba zai wuce shekaru 30 ba. Juyi ya yi tare da miƙa hannu ya janyo katin ɗaurin auren SALIMAH wanda suka kai masa ita da EESHART fito da shi ya yi yana ƙare masa kallo musamman wurin sunanta da na angon nata da kuma date ɗin ɗaurin auren ma'ana ranar da aka ɗaura. Shiru ya yi yana ta tunanin shikenan SALIMAH ta yi aure ta bar shi ta auri zaɓin ranta mai kuɗi kamar yadda take da buri shi ta bar shi saboda talauci da halin babu.
Motsi ya ji da sauri ya tura katin ƙasan latifarsa ya kwanta lif. Mama da sallama ta shigo ɗakin yana daga kwancen ya amsa mata wuri ta samu ta zauna ta ce
"ABBAS"
"Na'am Mama" Ya ce yana tashi zaune amma ya kasa haɗa ido da ita saboda ba ya so ta gane halin da yake ciki ya san kuwa kallo ɗaya za ta masa ta gane.
"Mai yake damunka kwana biyun nan? Kai da ka daina saka kan ka ciki damuwa amma yanzu kake so ka mayar da kan ka ruwa? " Ta jefa masa tambayar tana tsare shi da ido.
"Mam...
"SALIMAH ce ko?" Ta katse masa hanzarin kiran sunanta da ya fara.
Idanunsa ya ɗago ya sauke a kan fuskarta yana jinjina yadda aka yi ta gane damuwarsa bayan ya san ya sanar da ita cewa shi yanzu ko tuna SALIMAH ba ya yi amma kuma shi kansa bai san ya aka yi daga ranar da ta damƙa masa katin ɗaurin auren sai kawai ya ji ya fiya tunaninta tabbas so ba ƙarya bane kuma ba ya fita ya bar zuciya sai dai ya lafa.
"Na ce SALIMAH ce ?" Kansa ya sunkuyar don ba zai iya mata ƙarya cewa ba ita ba ce.
"To kuwa ka sani haramun kake aikatawa ABBAS tun da yanzu ta zama mallakin wani dole ka yi yaƙi da zuciyarka na ganin ka ƙauracewa tunaninta "
'Mama ya aka yi kika sani?"
"Ai na ga katin ɗaurin auren tun ranar da ka shigo da shi a hannunka na lura kana cikin damuwa shi ne da ka tafi masallaci na buɗe na gani, kuma na san babu mai yin wannan ɗanyan aikin sai SALIMAH wato ta ɗakko ƙafa ta kai maka katin ka karɓa ka ga yanzu burinta ya cika ta mayar da kai tuwa wato cikin damuwa" Ɗagowa ya yi yana kallon Mama a gefe ɗaya yana raya cewa kenan SALIMAH da biyu ta bashi katin ɗaurin aurenta shi duk a tunaninsa don kawai ya gani ne amma in haka ne ba ƙaramar ƙiyayya take masa ba. Hannu ya kai ƙasan katifa ya zaro katin ya yayyaga shi tare da masa gutsin-gutsin.
" Da ya fiye maka dai tana can ta buɗe babin sabuwar rayuwa ta barka da dakon so ita kuma cikin walwala da jin daɗi da kuma daula, ya kama ta kaima ka fitar da matar aure ka yi aurenka hakan zai sa damuwar da kake da ita ta ragu ko da ba duka ni na rasa ma ya aka yi ka koma ruwa"
Shiru ya yi .
"Da kai nake magana fa ABBAS"
"Mama ni ina zan samu wata matar aure ni ai na gama aure a duniya!"
"Baka isa ba ABBAS" Mama ta yi maganar a zafafe cikin hargowa. Shi kansa sai da ya tsorata da yadda ta masa maganar har ya rasa abin cewa.
"Saboda wata wacce bata damu da kai ba babu yadda za a yi ka ƙi yin aure'
"To Mama ki yafe mini Allah huci zuciyarki, ni kawai ina ganin na gama so a rayuwata ba zan ƙara soyayya ba matan ma tsoronsu nake"
"Sai ka yi aure ABBAS ai a duniya ba a taɓa zama ɗaya kuma duk lalacewar zamani ba a rasa na kirki tuni idan ka saka tunaninta a kwandon shara za ka samu wacce kake so take sonka kai har ma ku zo ku yi rayuwa ka ji tamkar baka taɓa sanin wata SALIMAH ba" Jin ta kawai yake amma ya san da wuya kuma zai yi wahala hakan ya kasance.
"Tun da kana ganin kai ka gama zaɓin mace a duniya, to ni zan zama maka matar kuma ba zan maka zaɓen tumun dare ba, don aure kam babu fashi sannan ba gudu ba ja da baya!" Tana gama zuwa nan a maganarta ta tashi fuuuu ta bar ɗakin don tana ganin in har bata zage dantse ba to tunani zai yi tafiyar ruwa da hankali da tunanin ABBAS!.
"Da kallo ya bi ta tamkar wani sakarai, ji yake gabaɗaya Mama ta hargitsa masa tunani da lissafi, shi da a son samunsa ne ba zai ƙara yin aure ba gwara ya ringa azumi saboda ya yi wa mata kuɗin goro tun daga kan SALIMAH ya san dai an ce zuciyar mace( SADIYA ABDULRAZAƘ) Tana da tausayi da rauni amma dai ban da ta SALIMAH. Da a ce SALIMAH tana da tausayi da bata guke shi saboda talauci ba amma ya fawwalawa Allah komai kuma ya sa a ransa zai karɓi zaɓin mahaifiyarsa da hannu bibiyu wataƙila ya dace wataƙila ya samu mai share masa hawaye wataƙila ba maye gurbi ba har ma sai ta fi SALIMAH matsayi a wajensa sai dai shin wace ce wannan? Wace mai baiwa da sa'ar ce za ta tsinci dami a kale?!.
*SALIMAH*
Hannunta har rawa yake wajen riƙon wayar da ta kara a kunne, zuciyarta tana azalzalarta a kan tambayoyin da suke ƙunshe a birnin zuciyarta wanda take tunanin ta inda za ta fara jero masa su, don ba za ta iya jira har sai ya dawo gida ba ko ma a ina yake dole ta fallasa masa asirin zuciyarta na ɓacin ran da ta ƙunsa kuma ta yi dakonsa tsawon kwanaki uku ragas.
A ƙufule ta yi niyyar zayyano masa laifinsa don ta ji ko zai yi ƙarfin halin kare kansa? Domin ta yi alƙawarin sai dai a yi duk wacce za a yi amma ba za ta saurara ko ta lallashin zuciyarta ta bi abin a sannu ba. Sai dai me? Kalaman da Alhaji Tahir ya feso mata su ne suka sa ta guntse nata da ta guntso za ta amayar masa.
"Ki zo ɓangarena yanzun nan bana son ɓata lokaci, minti biyar kacal na baki!." Yana gama faɗar hakan ƙit ya kashe wayar ba tare da ya jira cewar ta ba, dama ya yi maganar ne bisa bada umarni ba wai neman shawara ba. Da kallo ta bi wayar bakinta a sake tamkar yawu zai zubo mamaki al'ajabi game da mutuwar zaune su ne suka taru suka saka ƙasusuwan da suke ilahirin jikin SALIMAH yin mutuwar kasko. Zuciyarta tana harzuƙata a kan cewa ya raina mata wayo game da rainin hankali gabaɗaya ma ya raina mata ajawali ita ɗin SALIMAH da maza suke buri da fatan su mallaka don su same ta yake neman buɗaɗa mata ƙasa a idanu? Ita SALIMAH da yake kaffa-kaffa da ɓacin ranta yake rawar ƙafafu a neman aurenta ita zai wa haka, ita SALIMAH da take bada umarni a gidan ABBAS kuma ABBAS ya bi ba tare da musu ko gajiyawa ba kuma ko da ita ce ta yi laifi sai dai a bi abin da take so amma yau ita aka yi wa laifi kuma ake bata umarni cikin halin ko in kula wato an dake ta an hanata kuka.
Bayan umarnin da aka bata na zuwa ɓangaren wai har da iyakance mata lokaci, a matsayinta na sabuwar amaryar da bata tare da ango ba bare ta yi tunanin har an ci moriyar ganga ne za a yada korenta.
Wani ƙunci ne da takaici ya cika mata zuciya wai ita ce ma za ta je part ɗinsa tana ganin wannan raini zai ja mata a wajen abokan zamanta wanda tsawon kwanaki ukun nan babu wacce ta yi tozali da ita.
"Kawai ki je a yi wacce za a yi tun da dai haka ya zaɓa ke kuwa kar ki raga masa a gaban uban kowa ki faɗi abin da yake ranki" Wani ɓangare na zuciyarta ya bata wannan shawarar. Ƙafafinta ta sakko daga kan gadon ta ɗauki takalmi plat ta saka tare da ɗora hijabi a kan rigar baccin jikinta. Ƙofar ta buɗe ta fito tana takawa tana jin yadda zuciyarta take zugi har wani ruwan hawaye yana taruwa a idanunta bayan hannunta ta sa ta goge wanda ya gangaro tana tafiya tana ƙarewa girma da ƙawatuwar tankameme kuma tamfatsetsen gida mai laƙabi da aljannar duniya sai dai ga ta a cikin gidan amma kuma a iya kwanani uku kacal ranta yana suyar da ta manta tsawon lokacin da ta ɗauka ranta bai ɓaci haka ba.
'Dama matan masu kuɗi ne suna shiga ɓacin rai? Ai ni na ɗauka basu san wani kalma mai suna damuwa ko ɓacin rai ba, a nawa zaton talaka shi ne mai damuwa saboda talauci ashe dai kowa yana da damuwa ko dai a kaina ne hakan ya faru?' Ta tambayi hakan a zuciyarta lokacin da ta zo tangamemiyar haɗaɗɗiyar ƙofar da za ta sada ta da falon Alhajin don part ɗin ya fita da ban da sauran duka ukun iri ɗaya ne amma ban da nashi da zubin ginin ma ya sja bamban da sauran.
Idanu ta runtse tana damƙe fatar bakinta da haƙoranta, so take ta danne ɓacin ranta ta yi ƴar kissa ko yaya ne amma ina! Sai ta ji ba za ta iya ba dole ta nuna masa kuskurensa wai ita ce ma za ta je turakarsa ai ko da a ce a can za su kwana to ya ci a ce shi zai zo ɓangarenta da kansa sannan ya faɗa mata dalilinsa na ɓatan dabin da ya yi tsawon kwanaki uku tare da lallashinta da bata haƙuri in ya so idan ta haƙura sai ya kamo hannunta cikin so da ƙauna in ma bai mata ɗaukan jarirai ba yadda indiyawa suke yi wa mata.
Dakewa ta yi ta tura ƙofar wani sanyin ac da ƙamshin turare ya buɗaɗe mata hanci, shagala ta yi da kallon girma da ƙawatuwar falon har ta manta da yin sallama yayin shiga. Ƙofar ta mayar ta rufe tana ganin ta zama baƙauyiya sai ta raina nata ɓangaren duk haɗuwarsa domin wannan ya dame shi ya shanye a komai. Ɗago kai ta yi sai ta yi tozali da Alhaji Tahir zaune a kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya fuskarsa tamkar kumurcin miciji babu alamar walwala kai za a iya alaƙanta yanayin da tamkar wanda bai san sunan wani abu dariya ba bare kuma a ce ya taɓa yin ta. Ko kallo bata ishe sa ba ai kuwa ta taho fuuu a fusace don ta zo ta ji amsoshin tambayarsa don gani take buƙatarsa ce ta tashi sai yanzu ya san da ta saboda zai nemi haƙƙinsa a wajenta.
Tahowar da ta yi tana ƙoƙarin ƙarasowa wajensa da yake da ɗan tazara tsakanin ƙofar da ta shigo da kuma inda yake tsakiyar falon a zaune kasancewar falon yana da girma sosai.
"Ki samu wuri ki zauna ban baki damar furta ko da uffan ba!" Ya ce babu alamun wasa a furucinsa. Kallo ɗaya ta ƙara masa ta ga ba wajen wargi bane yadda ya haɗe rai sai ta sha jinin jikinta. Kanta ta samu da bin umarninsa ba tare da ta san dalilin yin hakan ba wuri ta samu ta ɗosana mazaunanta tana jiran ta ji mai zai ce. Sai dai hankalinsa ya mayar wajen danna waya da alama ya ba bango ajiyarta!.
Kallon fuskarsa take wani irin muni da baƙi ta ga ya yi ga wani bajajjan hancinsa kunnuwansa tamkar na zomo. Tabbas kuɗi sun rufe mata muninsa har ta kai bata san mugun mummuna bane shi sai yazu yanayinsa ma sai ya ga kamar wani yare amma ba na hausa ba. Ƙaran buɗe ƙofa ne ya dakatar da ita daga kallon munin angon nata, ƙaran takalmi ƙwas-ƙwas da ake takawa shi ne ya tunatar da ita mace ce ta shigo, waiwayawa ta yi abin da ta gani ne ya so zautar da ita ganin wata kyakkyawar mata gashinta har baya yadda take tafiya ƙugunta yana juyawa a cikin siket ɗin jikinta shi ne abin kallo sosai nesa ba kusa ba ta ɗara SALIMAH a komai hatta mazaunanta sun san an yi dirarriyar mace, ko kallo SALIMAH bata isheta ba ta cire takalmanta tate da tako lallausan kafet ɗin ta ƙarasa har gaban Alhaji ta durƙusa ta ce
"Barka da dare shugaba, fatan an dawo lafiya" Ta ce tana mai sadda kanta ƙasa. Baki ta saki SALIMAH tana kallonta da mamaki ko ɗagowa bai yi ba sai hannu da ya ɗaga mata idanunsa suna bisa waya, tashi ta yi ta koma ta samu wuri ta zauna.
'Kenan ma sun san baya nan a daren amarcina har sai yau ya dawo lallai mutumin nan ya bar mini abin gori' Ta ce a zuciyarta tana mamakin durƙusawar matar wani ƙaran ƙofar ne ya ƙara katsewa SALIMAH tunani wata baƙar mata ce ƙatuwa ita ma ta shigo ta yi yadda ta farkon ta yi ita ma hannu ya ɗaga mata ta tashi ta zauna a mazauninta.
"SALIMAH waɗannan su ne abokan zamanki" Ya ce ba tare da ya kalle ta ba" Ita bata samu damar amsa masa ba sai ya ajiye wayarsa ya yi gyaran murya tare da cewa.
"Na tara ku ne a nan domin na sanar da ku gobe za a ɗaura mini aure zan rufe ƙofa ma'ana zan cike mace ta huɗu...!!!!"
[1/11, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1
*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a