Showing 27001 words to 30000 words out of 61883 words

Chapter 10 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10804

ɗauke hannun ta zaro mukullin da kuma wasu kula-kulai da wani abu da ta kasa gane mene ne, sai dai mai, tana fitowa da hannun ta ga mugun abin da ya kusa tarwatsa zuciyarta, condom ne da kuma sarkarta da ɗan kunne na gwal da suka he dubai ta siyo wacce ko sakawa bata yi ba.



Hannu ta ɗora a kanta ta shiga runtuma ihu tana ambaton ta shiga uku. Zaman dirshan ɗin da ta yi a wajen tana rasgar kuka tamkar an mata mutuwa, cikin kukan ta tafi da rarrafe ta ɗauki wayarta da take kan kujera da dokawa Alhaji kira, sai dai har ta tsinke bai ɗaga ba, kiransa ta yi a karo na biyu ringing ɗaya biyu ya ɗaga, kuka kawai take ta kasa cewa komai, Alhaji jin kukanta ya shiga tashin hankali don ya ɗauka ma mutuwa aka yi. Ganin ta ki cewa komai sai ya kashe wayar yna yi wa direbansa umarni a kan ya yi sauri akwai matsala a gida, abokin sa da suke tare a bayan motar ya shiga tambayarsa amma sai ya ce shi ma bai san mene ne ba.




A kiɗime suka shigo gidan Baban a gaba abokinsa yana biye da shi suna sauri tamkar su kifa, tun da suka doso gidan suke jiyo ihun kukanta, falon suka nufa suna zuwa suka ganta zaune dirshan tana kuka. Baba rasa bakin magana ya yi don ahi tsabar tashin hankali da rikicewa ko lura bai yi da Umar da yake yashe a falon ba amma shi abokin Baban ya gan shi.




"Yawwa kulawa kun iso ku mini ram da wannan ɓarauniyar ta sace mini makudan daloli a aljihu" Maganar Umar ce ta ankarar da Baba.




"Hajiya wai mene ne kike kuka kika tada mini hankali?".
.
."Yanzu Alhaji baka ga abin da ya saka ni kuka ba?"


."Ina yake?" Ya tambaya cikin rashin fahimta.


"Wai har tambaya ma kake? Kana ganin Umar a buge"


Wani dogon tsaki ya ja kafin ya ce


.."Wai a kan wannan ne kike kukan in ce dai kin daɗe da sanin yana shaye-shaye to mai zai ɗaga miki hankali ne har kika ɗaga mini nawa hankakin"


"Giya ce fa ya sha"


"Giya???" Ya tambaya hankali tashe yana rarraba ido.


"Giya ya sha, kuma ya ce akwai ta a ɗakinsa ko kwalba nawa ake so akwai a kasan gado, zan je in ɗakko na ga ɗakin a rufe shi ne na dawo zan ɗauki mukulli a aljihunsa, ina saka hannu na samu sarka da ɗankunne na wanda na siyo a dubai kimanin miliyan uku ya ɗauka, yanzu Umar mashayin giya kuma ɓarawo " Ta ce tana rushewa da kuka. Gabaɗaya gumi ya jika Alhaji.




"Kai kuna tsaye gaban manya kowa ya kama kunnensa dole a ladabtar da ku... Kafin Umar ɗin ya kai karshe maganar Baba ya karasa gabansa ya ɗaga hannu ya wanke shi da mari, da sauri abokinsa Alhaji Khamis ya rike shi yana ba shi baki.




Sosai hankalin iyayan ya tashi amma sun manta cewa su ne suka bar kashi tun ran kwasa, domin tun ran gini ran zane. Sun sangarta ƴaƴa babu kwaɓa babu tsawatarwa komai suka yi daidai ne da wayewa sai yanzu da abubuwa suka caɓe ne suka gane wautar da suka yi. Karasawa ya yi ya zauna a kujera yana ta faman huci basu san ta ina za su fara ba don lokaci ya kure musu ita tarbiya tana farawa ne daga gida duk abin da yaro ya yi ka tsawatarsa masa, ka nusar da shi itace tun yana ɗanye ake tankwara shi idan ya bushe a tarki lankwasawa karyewa zai yi.


Duk abin da ya zo ya yi da farko ka yi shiru to nan gaba ma zai kara yi da kaɗan da kaɗan sai abu yake yin gaba kafin ka ankara sai ka ga abu ya girmama ta yadda lokacin gyarawa zai gagare ka. Addu'a ita ce babban makami wajen tarbiyantar da yara, sannan kuma saka idanu a lamuransu tun suna kankana, ku lura su waye abokan su kuma su waye kawayensu nusar da su zama a class kusa da yara masu jin magana a aji ba masu wasa da rashin kulawa da karatu ba, waɗanda ko a islamiya suke bayar da harda.




Umar kuwa zaune ya tashi yana ta kelaya aman giya a falon Hajiya kuwa tana sharɓar kuka ta tafi ɗakin nasa tana buɗewa a kiɗime ta karasa kasan gadon gabanta yana tsananta bugu tana tsoran abin da za ta gani. Tana lekawa kuwa ta yi ido biyu da kwalaben giya tamkar dai shagon siyar da giyar zai buɗe saboda yawansu wasu sun kwalaben ne babu giya wasu kuwa giyar ce a ciki. Sosai ta yi mamakin yadda giya mai yawan wannan take zaune a gidanta amma bata sani ba ta fara tunanin sakacinta ne ya haifar da hakan da a ce tana saka ido a al'amuransa to ko bai daina duka ba zai rage amma ta bar shi sakakaka tamkar dabbobin da aka yi asakon su. Tana kuka tana fito da kwalaben sai da ta fitar duka sannan ta ɗakko guda biyu ta nufo falon lokacin Alhaji Khamis ya ba Baba baki ya zauna sai dai ganin Umar ba karamin bakij ciki da takaici ba yake kara masa. Haka ta karaso tsakiyar falon idanun nan nata jawur tamkar ta kwana tana kukan.




"Kika ishi mutane da cewa ana shan giya ashe kema kina sha" Umar ya ce yana ɗaga idanu yana kallon Hajiya da take ji tamkar ta hau shi da duka.




"Wai da gaske akwai a ɗakin kenan?" Baba ya ce yana tashi tsaye yana kallon kwalaben da mamaki.




"Sun fi kwalba talatin" Ta ce cike da takaici.




"Bani in yi kurɓa ɗaya" Umar ya ce don har lokacin a buge yake, a kufule Hajiya ta karasa ya wanka masa mari wanda ya sa sai da ya tuntura daga zaunen da yake.




"Kara masa shege tsinanne...




"A'uzubillahi haba Alhaji Bukhari ya haka, da bakin ka kake tsinewa ɗanka? Shin baka san baki shi yake kara kangarar da yaro ba? Akwai lokutan karɓar addu'a idan mutum ya yi tana karɓuwa ko lokacin da mala'iku za su ce amin. Shi ya sa ake son iyaye su rika saka linzami a harshensu suke yin furucin mai daɗi ga yaransu ko da kuwa yaran sun ɓata musu rai su yi kokarin danne zuciyarsu su faɗi kalma mai daɗi, ko da karamin yaro ne idan ya yi laifi kar ka ce masa shege ɗan iska, ko munafuki da sauransu, ka yi kokarin cewa Allah maka albarka Allah sa wannan abin da kake yarinta ce, amma furuci mai muni shi yake kara kangarar da yaro maimakon al'amura suke baya sai suke yin gaba bayan kuma duk halin da suka shiga mu ne dai a ciki" Alhaji Khamis ya katsewa Alhaji Bukhari maganar.






Dantse bakinsa ya yi yana jin yadda zuciyarsa take zafi so yake ya furzar da maganar ko ya ji sassauci amma kuma an taka masa birki da mummunan furuci.






Wani ashar Hajiya ta yi wa Umar mai maiko...






"Hajiya Rayyanatu ana ga yaki kina ga kura, ana hana wani maganar ke kina yi"


"Wallahi Alhaji Khamis yaron ne sai da haka kullum daga an hana shi sata sai ya koma sane"




"Kin ji fa, wai a nan fa kina nufin daga kin hana shi wannam sai ya koma wancan amma maimakon ki faɗi hakan sai kika ce daga an hana shi sata sai ya koma sane, shin sata abu ne mai kyau? Ko sane yana da kyau? Amma kina danganta ɗanki da shi ko zagi da iyaye suke yi wa yaransu tun suna kanana ba tarbiya ba ce saboda yara suna harda a kwakwalwarsu, sai kun ki yaro ya yi zagi sai ku kama shi ku duka kuna ikirarin ba kun hana shi yin zagi ba bayan kuma ku kuna yi kenan idan ba abu bane mai kyau mai ya sa kuke yi? In dai ana bada tarbiya sai an kiyaye da wasu abubuwan sosai saboda yara sun fi ɗaukan abin da ake yi a aikace fiye da wanda ake koya musu" Ya ce yana kallonta daga ita har Alhaji sai suka yi ɗif domin su basu san duk wannan abubuwam da yake faɗa ba saboda su dama ba wani damuwa suka yi da tarbiyar ba.




"Ai komai ya zo karshe a gobe zan ɗaura maka aure domin ka sani ma, babu fashi ko ka san annabi ya faku ba, idan ka ga kana da iyali ka hankalta" Baba ya ce yana nuna shi da yatsa.






"Kuma wannan shawara ce mai kyau aure yana sa nutsuwa da hankalta musamman in aka yi dace da yarinyar kwarai, sai dai ba a nan gizo yake sakar ba, shin a ina za ka samu matar? Ka san dai abokin kura guza kuma na san kalar zaren kalar yadin, ma'ana ba za a samu wata mace budurwarsa mai nagarta ba don babu nutsatstsiyar da za ta kula shi, kuma in ba ta kirki ba ce maimakon ya shiryu sai dani ya kara shiga dawa wato lamura su kara taɓarɓarewa" Cewar Alhaji Khamis.




"Akwai matar da yake so kuma nutsatstsiya ce" Alhaji Bukhari ya faɗa.




"Ikon Allah!" Ya ce da mamaki don ya san dai wace ce za ta yarfa da haka, kafin ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula na kankanin lokaci sai ji ya yi Alhaji ya ɗaga waya yana ta kiran mutane yana cewa akwai ɗaurin auren ɗansa da za a yi gobe karfe goma sha ɗaya na safe, haka ya ringa kiran jama'a yana gamawa ya shiga kwalawa Hawwa kira.


"Hauwa'u! Hauwa'u!! Hauwa'u!!!" HAWWA da take ɗakin tana ɗinke wa SABEER rigar islamiyarsa da ta yage da zare da allura ta daɗe tana ta yi kasancewar bata iya ba, ita hatta keken ɗinki ma bata taɓa ganin yadda ake ɗinki da shi ba sai dai in an ɗinko musu kaya ta saka kawai wata rana ma in ɗinkin bai yi mata ba ta ce Ummie ta bayar da kayan saboda gata da suke da shi amma sai ga shi yanzu rayuwa ta juya musu maraici ya sa har tana iya ɗinki da allura da zare, ga kayan duk sun tsufa sun koɗe ko ɗan aikin gidansu ba zai saka kayan da suka yi mugun tsufa haka ba, amma sai ga shi abin da suka fi karfinsa ya fi karfinsu dama yawanci gata na iyaye ne daga ranar da ka rasa su a duniya daga lokacin za ka fahimci girma da darajarsu babu wanda zai gane hakan sai maraya wanda ya rasa uwa ko uba ko ma ya rasa su gabaɗaya. Ko da za ka samu dukkanin gata a bayan ransu to ganinsu kaɗai ma rahma ne, daga lokacin da mutuwa ta yi yankan kauna a tsakaninku za ka gane girma da ɗacin maraici!.




Yar aikin da ta shigo ɗakin da sauri take faɗa mata ta jiyo Baba yana kwala mata kira, da sauri ta yi jifa da riga da zare da allurar hannunta, don ta san yanzu za a ce ta yi laifi a hukunta ta ita kuma bata ji ba saboda hankalinta yana a kan SABEER suna hira suna ta kyalkyalar dariya saboda su biyu ne farin cikin junansu.






Fitowa ta yi da sauri ta nufi sashen Baban ta shiga da sallama, tana shiga ta samu gefe a kasan tiles ta durkusa gwiyoyinta a kasa cikin ladabi ta ce.




"Ga ni Baba"


"Gobr da karfe sha ɗaya za a ɗaura auranku da Umar.... Idanu ta ɗago tana kallonsa gabanta yana bugawa da karfi, hatta jin ta sai da ya ɗauke na wasu sakkani don kunnen nan nata dummm ya yi.


"Alhaji ƴar aiki za ka aurawa Umar?" Alhaji Khamis ya tambaya yana kallon HAWWA wacce kayan jikinta suka tsufa hatta hijabin jikinta wuyan ya yi yawa ga shi daga gefe da yaga yadda daga gani dutsin guga ne ya kona. HAWWA jin an ce mata ƴar aiki sai da idanunta suka kawo ruwa duk da bata da bambanci da ƴan aikin, hatta kayan jikinta har gwara na wasu ƴan aikin, ita mutumin ma kallon sani take yi wa fuskarsa.






"Ƴar gidan Yaya ce marigayi"




"Wai HAWWA ce wannan?" Ya tambaya da mamaki.


"Ita ce" Hajiya ta ce, shi kuwa Umar lokacin ma bacci ya ɗauke shi yana yashe a tsakiyar falon don tun mangyarin da Hajiya ta masa sai ya kwanta duk kafafunsa a cikin aman da ya yi.


"Amma Alhaji Bukhari baka kyauta ba, yanzu ƴar zumun naka ce ka bari haka a wulakance? Yanzu da shi ne zai bar tsatsonka su wulakanta idan baka raye?" Ya tambaya cike da mamaki


"Dakata! Alhaji Khamis kar ka ɗora mini jakar tsaba kaji su bini, kar ku ka sa duniya ta zage ni ya zan ɗakko yaran su biyu in rike su cin su shan su sutura da karatunsu duk in ɗauki nauyi amma kake mini wata magana a karshe don in kara dankon zumunci ma ɗauki ɗana sukutum zan aura mata"


Murmushin takaici ya yi mai ciwo kafin ya ce


"A ina rufin asirin yake? Wannan ne gata, kalli suturar da take jikin yarinyar nan kamar wata almajira yanayin jikinta da na nutsuwarta bai yi kama da na wanda yake cikin farin ciki ba sannan maganar aura mata Umar kuma ai ita za a zalunta tun da duk wanda yake da dogon tunani ba zai ɗauki ƴa mai kamala da hankali kamar HAWWA ya aurawa mashayin giya ba d...


"Ya isa haka Alhaji Khamis! Wasa ya yi wasa ban da tsinkarin uwar miji, idan magana za ka faɗawa mutane da tada tarzoma haɗe da tada zaune tsaye to mun gode ka je umma ta gaishe da aisha" Hajiya Rayyanatu ta ce rai a matukar ɓace.


"Na ji kuma zan fita muku a gida amma ina so ku sani zalunci ba abu ne mai kyau ba, kuma cin dukiyar maraya haramun ne domin Allah maɗaukaki ya faɗa a littafinsa mai tsarki cewa, kada ku ci dukiyar maraya da zalunci, a wani wajen kuma ya ce hakika masu cin dukiyar maraya da zalunci ba komai suke ci ba a cikin su, illa wuta, kuma za su shiga cikin wutar sa'ira. Domin na sam tabbas kun hau dukiyar marayu kun yi kaka gida, saboda dukiyar da mahaifansu suka bari basu ba hatta ƴaƴa da jikokinsu sai sun mora, amma tun ba a je ko ina ba tun ana shekara biyu da mutuwarsu ga shi nan suturar kirki ta gagari ƴaƴansu suna rayuwa kaskantacciya, yanzu da iyayansu za su dawo duniya mai za ku ce musu? Tabbas duniya ta zo karshe zumunci ya ki daɗi amana ta yi karanci amma a juriya zuwa tafi wata rana tulu zai fashe! Na bar ku lafiya" Ya ce yana juyawa ya fice.




Daga Baban har Hajiyar ransu ne ya yi matukar ɓaci don kalamnsa basu shige su ba illa haushin sa da takaici. Haushi ne ya sa Hajiya Rayyanatu ɗaga kafa ta hamɓare Umar da ya yi shame-shame don asara yana sakin munshari. Jin an masa kafa ya tashi zaune a kiɗime yana rarraba idanu kamar shege a rabon gado.
[1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA*






NA




MAMAN AFRAH




*GARGAGAƊI*


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️


JAN HANKALI


Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.




SADAUKARWA


Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.





PAGE 9



"Sai ka tashi malalacin banza gobe ɗaurin aurenka amma maganar auren kana yashe kamar kayan wanki" Ta ce tana harararsa ganin ya saki wata uwar hamma.


"To a kai ni ɗakin amaryar tawa mana" Ya ce yana kallonta da lunsassun bugaggun idanunsa.


"Hajiya ki kyale wannan ba a hayyacinsa yake ba, da yana cikin hankalinsa da yanzu yana cikin farin cikin murnar auren nan"


"To Alhaji"


"Yanzu dai ita wannan ki binciko mata kaya a cikin kayan Lawisa wanda za ta saka goben'


"Wallahi ba za a ɗauko a kayanta ba wannan yarinyar da ta tsani a taɓa mata komai nata, kana gani yanzu kamar ita ce uwata ko raga mini bata yi ina faɗa tana faɗa"


"To ki ɗakko mata marar ɗinkawa a kayanki sai a bada ɗinki"


"Nawa ai sun fi karfin ajinta amma zan san yadda za a yi"


"Don Allah Baba ka taimaka mini ni bana son a mini aure karatu nake so na yi" HAWWA ta ce tana hawaye.


"Matsayinki na mai rangwamen gata wato marainiya, har kina da zaɓin kan ki? To ai karatun secondry ma sa kika yi ya ishe ki son ko yo zurfi a karatu shi mijinki da bai san ko bihim ba ki zo kina goranta masa to ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa" Cewar Baba.




Sai da suka gama faɗar abin da za su faɗa suka ce ta tafi, dama ba shawarar ta ake nema ba umarni ne, haka ta tashi ta fito ta nufi ɗakin Baba Sadiya tana zuwa Baba da take linke kaya ta je ta faɗa jikinta tare da fashewa da kuka sosai Baba ta ji abin ya taɓa ta lallashinta ta shiga yi har sai da kukan ya tsagaita, sannan Babar ta shiga tambayarta dalilin kukan nata, nan ta shiga labarta mata abin da ya faru, sosai ta tausaya mata kuma take jinjina rashin imani da tausayi na mutanen gidan uwa uba rashin amana.




"Baba ki bani wannan zoben da na baki ajiya"


"Hauwa'u shi kaɗai fa ya rage miki mai ya za ki karɓa suna ganinsa a hannunki za su kwace"


"Guduwa zan yi Baba, barin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login