Showing 36001 words to 39000 words out of 61883 words
Chapter 13 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
tunani domin an ce zato zunubi ko da ya zama gaskiya.
An kawo musu abinci da ruwan sha, SABEER zagewa ya yi yana ta cin abincin saɓanin HAWWA da ta ci kaɗan saboda duk gajiya ta gama ratsa jikinta.
"Hauwa'u ya aka yi tsawon lokacin nan baki zo nan ba? Kin san mahaifiyarki mai yawan zumunci ce kuma tana zuwa da ku ke mai ya sa baki zo sada zumuncin ba tun da kika ga ni Allah bai bani iko ba? " Baffa ya tambaye ta yana kallonta tana wasa da yatsunta shi SABEER ya samu abin wasa yana ta uzurinsa.
"Baffa babu dama shi ya sa bamu zo ba, babu wanda zai barmu" Ta ce tana tuna wayar da ta ji Hajiya ta yi a kan an mantar da shi su.
SALIMAH
Har suka iso kofar gidansu ran SALIMAH a matukar ɓace da abin da ABBAS ya mata a ganinta ya watsa mata ƙasa a ido a yadda ta san ya mutu a kan soyayyarta a nata zaton ko ƙasa ta bashi zai rusuna ya karɓa da hannu bibiyu, amma wai ita SALIMAH ya nuna tamkar Allah bai yi ruwanta a wajen ba.
"Sarauniyar mata ina so mu tsayar da magana nan da sati guda a ɗaura mana aure li tare gimbiya sarauniya mai mulkin zuciyata" Muryar Alhaji Tahir ta katse mata tunani.
Wani mugun daɗi ne ya baibayeta jin maganar da ya zo danita duk da ba shi kaɗai bane maneminta zawarawa gasu nan kamar jamfa a jos amma maganar auren da ya zo mata da ita ya yi sara a kan gaɓa, tana ganin kamar dai ABBAS ya mata abin da ya mata ne saboda yana ganin tana zawarci ne ya raina mata hankali amma za ta nuna masa kallon kitse yake wa rogo sai ta je har wajen kafintocin da yake taƙama da shi ta kai masa katin ɗaurin aurenta in zuciya zai haɗiya ma ya mutu ko ma dai ya yi mushe...
https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1
*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 11
Hajiya Rayyanatu da bata san shirin Baba ba ko kaɗan bata san mai yake wakana a can ɗin ba tun lokacin da ya kashe mata waya, suna zance da maƙociyarta tana ta nuna cewa iya yarinyar ai kanta ta yi wa da ta gudu don su gaba ta kai su gobarar titi. Da yake ita da ita ɗin sammakal jirgi ɗaya ne ya ɗakko su sai take nuna mata ta hutar da su Hajiyar wahala. Ita dai fatan ta Allah sa kar a ɗaura auren a wannan halin ne suna ta dariya abin su da alama duniyar ta musu daɗi don a ganin Hajiyar da tafiyar HAWWA da zamanta duk uwar ubansu ɗaya, idan ma ɓaya suka yi su je dan kansu, ita dai fatan ta kar a ɗaura auren a bar mata ɗa da igiyar wata matar galihu in ban da ma suna son ya shiryu ai shi ba sa'an auren HAWWA bane domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa.
Kukan da Umar yake ta faman rafkawa tamkar wanda ake zare masa rai shi ne ya katse musu nishaɗin da suke ciki, dama su kaɗai ne a falon da yake bata ɗauki auren da muhimmanci ba ko gayyata bata yi ba ita ma Lawisa tana sama abinta. A kiɗime Hajiya ta tashi ta fito daga falon maƙociyarta tana take mata baya saboda abin ya ɗaure mata kai ya san dai matsawar an ɗaura aure babu abin da zai sa Umar yake faman yage baki yana kuka da kururuwa tamkar uwarsa ta bar duniya, amma dai ta fi son tabbayar da gaskiyar lamari saboda masu iya magana sun ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗin ji. Suna fitowa suka yi ido huɗu da Umar da yake tamkar mahaukaci sabon kamu ya cire babbar rigarsa ya yi ɗamara da ita a ƙugu ma'ana ya ɗaure a ƙugunsa ga hular nan ta kalli arewa masu gabas uwa uba fuskar nan sharɓar da hawaye har da majina yana kuka haiƙan direban yana rirriƙe shi, shi kuma yana fisgewa tamkar za a saka mahaukaci a turu.
"Baƙin ciki yake mini wayyo na shiga uku na lalace" Ya ce yana rusar kuka duk ya cika gidan da kururuwa abin da ya ɗauki hankalin ma'aikatan gidan suka fara fitowa daga ciki domin an ce gani ya kori ji sai dai suna zuwa da suka ga angon ranar a rikice sai suka sha jinin jikinsu.
"Duk wanda ya kara minti biyu a wurin nan a bakin aikinsa" Cewar Hajiya a ƙufule tana jin haushin su kowa ya ya dare ya koma ciki suke ƙusƙus ban da Baba Sadiya da ta shige ɗaki ta tuntsure da dariya don ta san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi ma'ana kukan nashi da haukar da yake ba ya rasa nasaba da tafiyar HAWWA.
"Wallahi Hauwa'u ta maka nisa yaro dama ba sa'arka bace ƙaddara ce wacce ta riga fata ta kusan giftawa a tsakaninku kuma Allah ya kare yarinyar kirki, ai Hauwa'u da nagartaccen miji ta dace ba kai ba sangartacce" Ta faɗa a fili tana zaumawa ta cigaba da abinnda take yi.
"Wai kukan uban me yake?" Hajiya ta faɗa tana zare ido ranta in ya yi dubu ya ɓaci.
"Auren ne ba a ɗaura ba taron ma ya watse shi ne yake kuka yana cewa wai Alhaji ne ya masa baƙinciki" Direban ya faɗa dariya tana neman kufce masa ya danne ganin gabaɗaya abubuwa sun caɓe sai ka ce wata dirama ake yi.
"To sai mai don ba a ɗaura ba aikin banza da wofi yarinyar da ta gudu yawon ta zubar ko a gida bata kwana ba ai dama ruwa ba sa'an kwando bane, kuma ko da an ɗaura ma ƙarshen alewa ƙasa!"
"Ta gudu?" Umar ya faɗa a kiɗime tare da yin kukan kura ya fisge riƙon da direban ya masa sai ga direba wancakar an jefar da shi gefe, yana kwace kansa ya zura a guje ya yi hanyar ficewa daga gidan, hularsa ta yi tsalle ta bar kansa.
"Wallahi wani abu ya same shi ka kuka da kanka ragon banza da wofi ka yarda ya jefar da kai gefe kamar wani kayan wanki in baka dawo da shi yanzun nan ba a bakin aikin ka" Hajiya ta ce tana zabga wa direban harara.
Mikewa ya yi tare da cire takalmansa ya marawa Umar baya, jin za a yanke masa hanyar cin abinsa. Daga nan su Hajiyar suna iya jiyo maganar Umar da ƙarfi yana cewa.
"Sai na bi HAWWA yawon ta zubar" Faɗa yake tamkar zararre.
"Hajiya amma yaron nan yana shaye-shaye ko?" Maƙociyar Hajiya ta tambaya ganin abin da yake ya wuce misali.
"Ah bushe-bushe yake ba shaye-shaye ba" Hajiya da maganar ta mata ciwo ta faɗa tana aika mata harara da jajayen idanunta da takaici ya sa suka yi ja.
An ɗauki kamar minti goma suna tsaye da ita da maƙociyar cirko-cirko ita dai maƙociyar bata ƙara cewa uffan ba ganin daga tambaya cibi ya zama ƙari.
Riƙe take da tsantsa sai huci take ta rasa mai ya sa take ta kiran Baba bai ɗauki waya ba, ta ma rasa takamaimai mai ya sa bai dawo gidan ba tin da an fasa ɗaurin auren, ya barta da ganin tashin hankalin da Umar yake duk zai janyo hankulan jama'a su gane halin da ake ciki. Suna nan tsaye sai ga Lawisa ta sakko daga sama riƙe da glass cup mai ɗauke da lemo a ciki.
"Hajiyancy uwar amarya da ango" Ta ce tana ƴar dariya don ita bata san mai yake faruwa ba.
"Ubanki ne angon?"
"Mai ya yi zafi shi ba wuta ba Hajjaku mutanen saudi arabiya" Ta ce cikin wasa tana kurɓar lemon hannunta.
Shigowar mai gadin gidan da direba da wasu ƙartan samari guda biyu sun iyo wa Umar cali-cali sai zufa suke na tseren wahalar gudun da suka sha a titi yadda ya hau kwalta yana zabgar gudu yana kiran sunan HAWWA daƙyar suka cim masa ana hayya-hayya aka kamo shi.
"Ango ranar ɗaurin auren ka sha ka yi tatul" Lawisa ta ce tana juyawa ta shige falo don bata iya ganin wannan kayan takaicin ganin ya fusge-fusge yana ambaton HAWWA sai ta ɗauka a buge yake bata san duk zafin so bane.
Ɗakinsa ta ce su kai shi su saka cike da takaici ana saka shi a ɗakin ta kulle da mukullin tana jin yadda yake dukan ƙofar, ita kanta ta fara zargin ko dai kafin ya fita ɗaurin auren ya sha ƙwayar ko dai akwai wata a jikinsa wacce bata sake shi ba don lamarin abin mamaki ne da al'ajabi. Tana fitowa za ta nufi ɓangarenta ta samu samarin nan biyu da suka taimakawa mai gadi da direba aka shigo da Umar suna tsaye. Hatara ta wurga musu ta ce
'Tsayuwar mai kuke ko ganin ƙwaƙwaf?"
"Sallama muke jira"
"Sallamar uban me, saboda kun kamo Umar ɗin ne har sai an biya ku? Sai ka ce wanda kuka kamo raƙumi ko doki?" Sumi-sumi suka fice suna jan Allah ya isa a zukatansu su dama sun ɗauka za a basu wani abu shi ya sa suka zage suna zabgar gudu har aka ci nasarar kamo shi aka kawo shi gida.
Falo ta koma duk tanta a jagule maƙociyar tata ce take bata baki, waya ta ɗauka ta dokawa direban nan ta ce ya zo ba a ɗauki minti uku ba sai ga shi ya shigo.
"Wai Alhaji a masallacin can wajen ɗaurin auren kuka baro shi? Ina ta kiran wayarsa a kashe"
"Alhaji fa yana asibiti...
"Yanzu fisabilillahi maimakon ya zo gida ana buƙayarsa ya wuce dubiya asibiti" Ta katse shi ba tare da ya kai aya ba.
"Jiki ya yanke ya faɗi a wajen ɗaurin auren fa aka kwashe shi aka tafi da shi asibiti bai san ma a wanda yake kanshi ba, shi ne taron ya watse ba a ɗaura auren ba"
"Ya faɗai innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu tsakani da Allah ka san Alhaji yana can asibitin amma baka faɗa mini ba ka barni gaho a nan ina aikin banza da wofi har da wani cewa aka kwashe shi ba za ka ce aka taimaka masa ba" Ta ce lokacin da ta miƙe tsaye daga zaunen da take tamkar ta kai masa duka shi da ba shi ya kai zomon ba rataya aka bashi.
"To fa! Iko sai rabbani su Baba ko dai lokaci ya yi" Lawisa ta ce cikin halin ko in kula. Wani dundu Hajiya ta sakar mata a baya har sai da ta gantsare.
"Shegiya marar tarbiyaina zaman zamana za ki jaza mini takaba to a bakin ki" Ta ce tana nufar hanyar fita ɗankwali yana neman faɗuwa duk ta rikice.
Ita da maƙociyar tata suka shiga motar direban ya ja suka nufi asibitin don Lawisa ko a jikinta wai an tsikari kakkausa sai ma haushin dukan da Hajiya ta mata tana jin ba don ba don ba da sai ta rama dukan amma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe!.
A harabar asibitin ya tsayar da motar tun kafin ya gama fakin Hajiya ta fito hankali tashe maƙociyarta ta bi bayanta hango wasu abokan Alhajin a tsaye cirko-cirko daga can ɗan nesa da su wurinsu ta nufa hankali tashe tana tambayar ya jikin nasa ko dai mutuwa ya yi nan suka shiga bata haƙuri da kwantar mata da hankali a kan cewa yana nan da rai kawai dai ruɗani ne ya saka ya suma amma basu san ruɗanin mene ne yana waya dai ya yanke jiki ya faɗi. Ganin tana kuka wiwi hankalinta a tashe likita ya bata damar ta shiga ta gan shi ko hankalinta ya kwanta ganin tana nuna ko dai mutuwa ya yi aka ɓoye mata. Ita kaɗai likitan ya ba umarni ta shiga ita maƙociyarta sai ta tsaya, shi dama direban yana can gefe don dama a wajen ɗaurin auren ya ji suna faɗar sunan asibitin da za a kai Alhaji.
A rikice ta shiga ɗakin da yake tana ta faman share hawaye, Baba da ya ji shigowarta idanu ya ƙyallara ya ga ita kaɗai ce amma bai buɗe ba saboda kar ya je wani ya biyo bayanta a gane gafar zaren da ya shirya. Tana zuwa ta dafa jikinsa tana kuka.
"Hajiya!" Ya kira sunanta a hankali yana buɗe idanunsa tarwai mamki take ganinsa raɗai tamkar dai lafiyarsa ƙalau.
"Ki kwantar da hankalinki lafiyata ƙalau na yi haka ne don a fasa ɗaura auren kin san in ban yi wannan dabarar ba babu wanda zai fahimce ni idan na ce kar a ɗaura auren" Ya ce cikin raɗa-raɗa yana sakar mata murmushi, ido ta ƙyafita masa tana sakin nata murmushin tare da ɗaga hannunta tana jinjina masa da babban ɗan yatsanta ganin abin bajintar da ya yi. A hakan likitan ya ƙwanƙwasa ƙofa ƙofa da sauri Alhaji ya koma ya kwanta lifet tare da rufe idanu ita kuma ta ba likitan umarnin shigowa tare da cigaba da ɗan share hawayen munafurci!.
*HAWWA*
Bayan sun gama tattaunawa da Baffa suka shiga hirar yaushe gamo tana ta bashi labarin irin halin da suka kasance na rayuwa a gidan ƙanin mahaifinsu, sosai ya tausaya musu yana Allah wadarai da halin wasu mutanen da suke gallazawa maraya, bayan sun san cewa duk wanda ya raini maraya ya faranta masa zai zauna a aljanna da ma'aikin Allah kafaɗa da kafaɗa yadda manzo S.A.W ya kwatanta kusancinsa da shi, kamar kusancin yatsun hannu. Amma shi wannan ga cin amanar marayu ga kuma cin amanar zumunci duk yadda aka yi ta nuna girman zumunci da lada da matsayin da wanda ya sada shi yake da shi amma shi ya yi watsi da hakan. Goggo Salame ruwan wanka ta haɗa ta yi wa SABEER wanka ta shafa masa mai sai ta bashi kayansa ya mayar. Sannan ta haɗawa HAWWA ma ta ce ta yi wankan, kafin HAWWA ta fito ta shiga ɗakin Amrah ta ɗakko wata doguwar riga ta atamfa ta ajiyewa HAWWA da yake kusan sa'annu suke sai dai Amrah ta girmi HAWWA amma da kaɗan.
Bayan ta fito Goggo Salame ta bita ɗakin ta nuna mata rigar.
"Ki saka rigar nan kin ga sai ku zauna a nan ɗakin ke da ƴar uwarki Amrah" Gaban HAWWA ne ya bada sautin didim jin sunan da Goggo ta ambata saboda ta san basa ga miciji da Amrah gabaɗaya ma bata san mai ta mata ba ta tsaneta tun lokacin Ummie tana raye idan suka zo sai Amrah ta yi ta harararta ko take faɗa mata magana bare kuma yanzu a ce ta saka rigarta ba ma wannan ne damuwarta ba wai da aka ce su zauna a ɗaki ɗaya.
"To Goggo amma da kin bar mata kayanta sai na mayar da ma jikina tun da Baffa ya ce za a siyo mana kaya" HAWWA ta ce cikin sanyin murya don ta san muddin ta saka kayan sai Amrah ta mata wulaƙanci idan ta zo ita kuma duk abin da za a wulaƙan tata ko mene ne gwara ta haƙura da shi.
"To shikenan " Goggo ta ce ita ma dama ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama domin ta san Amrah bata da kunya ko kaɗan ita ma ba raga mata take yi ba dama an ce riƙon ɗan wani sai mai haƙuri, ko kaɗan Amrah ba ta ganin maraicinta kuma bata ɗaukan Baffa da Goggo da muhimmanci da kuma godewa ɗawainiya da su da suke yi duk da suna yi domin Allah na sai dai wani lokacin sai take ganin kamar ita mahaifiyar su Amrah ɗin ce take zuga su da yake ita tana raye tana aure a wani gidan bayan mutuwar mahaifinsu.
Fita Goggo ta yi daga ɗakin ita kuma ta shafa mai ta mayar da kayanta ta fito,, lokacin Baffa ya fita, nan ta karɓi girkin da Goggo take ta ƙarasa dafawa dama wake da shinkafa ne bayan ta tace ta mayar da shi ruwan ya tsotse sai ta ɗora miyar tana gamawa tana cikin kashe wutar sai ga Amrah ta shigo gidan da sallama tana wani shan ƙamshi, HAWWA ce ta amsa mata da kallo ta bi HAWWA daƙyar ta gane ta saboda kayan jikinta da suke ƙasƙantattu sannan lokacin a sunkuye take tana kashe wuta.
"Sannu da ƙoƙari Hauwa'u Allah ya baki masu yi miki" Goggo ta ce tana kallon HAWWA tabbas HAWWA ta samu tarbiya ta san girman na gaba da tausayawa komai nata a nutse tabbas Goggo ta san tarbiya ce kawai iyaye za su ba ƴaƴansu ita ce har bayan ransu ba za su taɓe ba domin tarbiya ita ce mutum.
"To in ji mai tallar totuwa yau kuma marayu ne suka kawo mana ziyara wato an tuna da dangi an zo kenan...
"Amrah ke mai ya sa har kullum tunaninki na ƙananan yara ne yanzu mene ne na