Showing 6001 words to 9000 words out of 61883 words
Chapter 3 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
duk da bai masa kama da mahaukaci ba ko ta yanayin shigarsa, sai dai dole ya bi umarninta tun da aikin kuɗi zai yi. A guje ya fisgi napep ɗin suka tafi. Cak! ABBAS ya tsaya bai san ma ya ɗaga hannaye biyu ya ɗora a kansa ba tamkar wanda aka yi wa mutuwa.
SALIMAH wata ajiyar zuciya ta sauke ganin bai cim musu ba domin ita a halin da ake ciki yanzu ko hanya ba ta son haɗawa da ABBAS ɗin don an yi mai gabaɗaya haihuwa har hanji.
A kofar gidansu aka ajiye ta, gidan kasa ne aka shafe shi da jar kasa, cewa ta yi ya jira ta ta ɗauki jakar ta shige cikin gida.
Umma da take zaune a kan kujera tana goga ɗanyar kuɓewa ganin shigowar SALIMAH da sallama tana rike da jaka riki-riki bata san lokacin da ta cillar da magogin kuɓewar ba, tare da kuɓewa guda ɗaya da take rike a hannunta tana gogawa tsaye ta mike tana kallon fuskar SALIMAH mai cike da alamar farin ciki hakan ne ma ya sa ko sallama ta kasa amsawa.
"Allah ubangiji ya sa ba ya ji bane" Ta faɗa tana kallonta don ta tsani yaji ma ta fi son ta ji kalmar saki duk da ta san mawuyaci ne a yi sakin amma dai ganin yanayin SALIMAH ya sa ta ji tana son jin karin bayani. Cilli SALIMAH ta yi da jakar hannunta, ta karasa da gudu ta kankame Umma cike da farin ciki.
."Umma ABBAS ya sake ni" Ta ce tana kara kankame mahaifiyar tata da karfi.
"Ke SALIMAH kin san dai bana wasa da ke" Ta ce lokacin da ta ciro SALIMAH daga jikinta tana kallonta ido cikin ido.
"Wallahi Umma ya sake ni saki ɗaya" Ta ce tana ta murna da nuna farin ciki..
"Ayyyyyiririr yiriiiiii" Umma ta rike hanci tare da kwarara guɗa.
"SALIMAH anya yana cikin hankalinsa kuwa ya sake ki, ko dai wani abu kika bashi ya sha ya bugu kika tambaye shi sakin?" Umma ta ce tana jinjina yadda aka yi hakan ya afku.
"Rass yake babu wani buguwa dawowarsa kenan ma daga...
."Assalamu alaikum" Wani yaro ya shigo da sallam. Amsa masa Umma ta yi tana masa kallon rashin sani.
"Wai in ji mai adaidaita sahu a bashi kuɗinsa" Ya ce yana ja ya tsaya.
"Lah ka ga na manta ma da shi, Umma kawo ɗari huɗu a bashi" Cewar SALIMAH.
"To zo ka karɓa" Ta ce tana mika masa ya karɓa ta fita.
"Oh wai kuɗin adaidaita ma sai kin zo gida baki da kuɗi, yau dai Allah ya yanke miki wannan wahala, mai za a yi da wahala na san yanzu manyan mutane masu faɗa a ji sai kin zaɓa kin darje" Umma ta ce tana dafa kafaɗar SALIMAH.
"Wallahi kuwa Umma na san layi za suke yi da motoci a kofar gidan nan kowa yana burin ya mallake ni" Ta ce tana rungume Umma tana jin wani daɗi domin ta rasa gurbin da za ta ajiye farin cikin da take ciki. Saboda har ta fara hango ta a kayataccen gida na alfarma tana cin duniyarta da tsinke.
"Ai babu wanda zai yi tozali da wannan kyakkyawar halittar taki, ya yarda ki suɓuce masa, shi ya sa nake jin takaici da mahaifinki ya aura miki fukara'u bayan na san na haifi babban jari farar mace alkyabbar mata" Umma ta ce, dariya suka saki a tare.
*ABBAS*
Tamkar mahaukaci sabon kamu haka ya juyo ya dawo gidan, yana shigowa ya ji wani kunci a ransa kamar zararre haka yake jin sa sai ya ji ba zai iya jure zama a cikin gidan ba, ganin SALIMAH bata nan kuma ya san cewa ba wai unguwa ta je ba gidansu ta tafi a matsayin ya sake ta. Bedroom ɗin ya shiga da niyyar ya sauya kayan jikinsa amma da ya shiga sai ma ya rasa mai zai yi a cikin ɗakin, fitowa ya yi ya shiga falon ya ɗakko mukulli ya kama hanyar waje sai a sannan ya tuna babu takalmi a kafarsa, dawowa ya yi ya saka takalman ya fita ya rufe gidan. Tafiya ya fara yi amma sai yake ji tamkar kafafunsa ba za su yi jumurin ɗaukan gangar jikinsa ba, saboda yadda kafafun nasa suka yi sanyi ba ma kafafun ba hatta jikin nasa ma sanyi karai ya yi kawai dai yana saka kafafun ne ba tare da sanin ina ma yake jefa su ba, ga wata juwa da take faman ɗaukansa. Machine ya tsayar ya faɗa masa inda zai kai shi a daidai kofar gidan da ya masa nuni ya ajiye shi ya bashi kuɗinsa.
Da sallama ya shiga gidan Mama da fitowarta kenan daga banɗaki tana rike da buta ta ga ABBAS ya shigo da sallama amsa masa ta cikin sanyin murya, ganinsa ba yadda yake, idanunsa jajur kai gabaɗaya a matsayinta na uwa mahaifiya a gare shi tana ganinsa ta san yana cikin matukar damuwa tana ganinsa ta san gabaɗaya ba ya cikin hayyacinsa. Butar hannunta ta ajiye tana nutar falo ya bi bayanta zaunawa ta yi a kujera yana shigowa ɗakin wani kukan ya taho masa irin kukan da mai yinsa yake yi idan ya ga mai rarrashin sa. Da sauri ya karasa gabanta ya durkusa gwiyoyinsa a kasa tare da kifa kansa a kan cinyarta ya fashe da kuka.
09013181851
[1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 4
*ABBAS*
Dakatawa Mama ta yi bata hana shi kukan ba, duk da sautin kukan nasa yana taɓa mata zuciya, ta san cewa ba karamin abu bane zai sa ABBAS ɗin kuka haka ba kamar wani mace, kasancewarsa mai hakuri da juriya haɗe da kawar da kai sai dai ta san kukan nasa ba ya rasa nasaba da SALIMAH domin ta san ita kaɗai ce matsalarsa, ita kaɗai ce damuwarsa, ya ɗauki son wacce ba ta son shi ya saka a ransa ko kaɗan SALIMAH ba ta tausayinsa bare ta ji tausayin halin da yake ciki na soyayyarta burinsa kullum ya faranta mata, amma bata gani ta raina duk kokarinsa a kanta shi kuma kullum faɗi tashin sa SALIMAH ce duk da Mama ta san yana matukar kokarin ganin ya kyautata wa Mamar matsayinta na mahaifiya a gare shi sai dai ganin irin jarabawar da ya haɗu da ita na matar da ya aura sai take yafe wasu abubuwan tun da bata rasa komai ba kanin mahaifin ABBAS ɗin bai rage ta da komai ba tun bayan mutuwar mahaifin ABBAS yake ɗawainiya da su har yau bai daina ba kuma bai gajiya ba.
Sai da ta ji kukan nashi ya tsagaita, ta tabbatar ko ma mene ne yanzu zuciyarsa ta yi sanyi, saboda duk idanun da suka zubar da hawaye to mai idanun yana samun salama a zuciyarsa. Jin yana ajiyar zuciyar sai ta saka hannunta wanda tun da ya kifa kansa a cinyarta ta ɗora hannun a bayansa, fara buga masa bayan ta shiga yi a hankali sai da ta tabbatar ya samu nutsuwa daga ɗimuwar da ta gan shi a ciki sannan ta saka hannun ta duka biyu ta ɗago shi. Sosai ta ji rauni a zuciyarta ganin yadda idanunsa suka yi wani irin ja hatta fuskarsa da saman hancinsa duk sun yi ja saboda kukan da ya yi, kasancewarsa mai farar fata. Ba ma wannan ne ya ɗaga mata hankali ba sai ganin ya yi wani irin zuru-zuru idanun duk sun faɗa, kuma ko jiya ya je gidan nata domin rana bata taɓa fitowa ta faɗa bai je ya ga Mama ba yana kaunar mahaifiyarsa ita ma tana kaunarsa kasancewar sa ɗa ɗaya tilo a wajenta.
"ABBAS mene ne?" Ta tambaye shi cikin sanyi da tausasa murya. Idanunsa ya runtse wasu hawayen suka zubo sosai ta ji hakan ya taɓa ta, ta rasa SALIMAH wace irin mace ce da bata tausayin mijinta kullum yana cikin damuwa sai dai ta ɗauki hakan a matsayin jarabawar da Allah ya jarabci ABBAS ɗin da ita tana masa fatan Allah ya bashi ikon cin jarabawar.
Idanunsa take kallo wanda ya rufe su hawayen suna surnanowa.
"Na sha faɗa maka kake rike sirrinka, su iyali da kake gani sirri ne, daɗi ko wuya ba a son a ke jin kansu sai in abin ne ya yi yawa sai a faɗa domin sulhu da kawo maslaha" Ta ce cikin murya mai kama tana masa nasiha, duk da ta san ABBAS yana da dauriya da zurfin ciki sai dai wani lokacin kasancewar ta na mahaifiya gare shi ba sai ya furta cewa yana cikin damuwa ba kallo ɗaya take masa ta fahimci halin da yake ciki, duk da cewar halin da gidan ABBAS ɗin yake ciki abu ne bayyananne wanda kowa ma ya sani sai dai wanda bai taɓa taka kafarsa a gidan ABBAS ɗin ba.
"Ka cigaba da hakuri wata rana sai labari, wata rana masu bada labarin ma babu kowa, shi zaman duniya ɗan hakuri ne duk abin da aka yi hakuri da shi zai wuce wata rana kamar ba a yi ba"
"Mama" Ya ce bakinsa yana rawa don har ya fara jin sanyi alamar zazzaɓi zai rufe shi, ga shi yana so ya faɗa mata cewa ya saki SALIMAH amma kuma bakin nasa ya masa nauyi.
"Na'am ABBAS"
"Na, na, na" Ya ce yana ta faman maimaitawa tamkar wani mai in'inna.
"Mai ka yi ABBAS? Ni mahaifiyarka ce da baka da kamata a faɗin duniya ina so ka sani da a ce SALIMAH ce take maka wannan kaunar da kake mata, ai dai ka san kana matukar kaunarta, kaunar da kai kan ka baka san iyakarta ba to da ita ce take maka kauna ko da ta fi wacce kake mata to ina so ka sani da bata kai ni kaunarka ba" Idanunsa da suke rufe ya buɗe har sai da gaban Mama ya faɗi ganin irin mugun jan da suka yi.
."Tabbas da bata kai ni kaunarka ba, ai a duniya babu wanda ya kai uwa kaunar ɗanta, na maka misali da kaunar da kake mata ne don ka gane, uwa-uwa ce kaunar uwa da ban take, shi ya sa ma aka ce a yi wa uwa biyayya sai da aka nanata sau uku sannan aka ce a bi uba amma sau ɗaya aka ambaci uba. Saboda kaunar uwa da ban take ɗanta tun yana cikinta bata gan shi ba take kaunarsa, jin sa take har cikin ranta, yadda take shan wahala rainon cikin da haihuwar da kuma shayarwa rainon yaro har ya girma shi ya sa ubangaji maɗaukakin sarki ya ambata a littafinsa mai tsarki, cewa wahala ce a kan wahala. Shi ya sa uwa kaunar ɗanta bata taɓa gushewa a zuciyarta sai dai ta ki wani hali nasa in yana aikatawa sannan kuma kullum a yaro yake a wurinta bata ganin girmansa"
"Haka ne Mama" ABBAS ya ce cikin sanyin murya yana jaddada cewa in har duk wannan kaunar da yake yi wa SALIMAH yana jin zai iya sadaukar da komai ita ta samu zai iya sadaukar da numfashin sa ita ta rayu, amma kuma Mama ta ce ko dai kaunar ta fi haka to kaunar uwa ta wuce nan wannan ya sa ya ji jikinsa ya yi sanyi.
."Faɗa mini mene ne ka yi?"
"Na saki SALIMAH" Ya ce wani kuka yana taho masa sai da ya dantse bakinsa ne kuka mai sauti bai fito ba sai hawaye kawai. Wani irin bugawa da karfi zuciyar Mama ta yi. Sosai ta ji tashin hankali tun da ta san tabbas zai shiga matukar damuwa da rashin SALIMAH abu ne mawuyaci SALIMAH ta karɓi bikonsa ba ta ma jin hakan zai iyu musamman da yake daga mahaifiyar SALIMAH har SALIMAH burinsu bai wuce karɓar takardar sakin ba, dama mahaifinta ne zai iya yin komai to shi kuma mai yanke kauna ta ɗauke shi wato mutuwa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!" Ta shiga maimaitawa har sau uku, shi dai yana ambata mata ya yi sakin sai ya yi saurin maida kansa ya kifa a cinyarta, ita ma ganin zai kifa kan nasa sai ta sake shi daga rikon da ta masa tun lokacin da ta ɗago shi.
Shiru ta yi na ɗan lokaci gabaɗaya tausayinsa ya mamaye mata zuciya, da a ce tana da ikon cire masa son SALIMAH daga zuciyarsa da tuni ta cire masa ya huta.
"ABBAS garin yaya haka ta faru? Baka san cewa saki shi ne halataccen abun da ubangaji ba ya so ba? Baka san cewa a duk lokacin da aka yi saki sai al'arshin ubangiji ya girgiza ba? Mai ya sa ka yi wannan ɗanyan aikin bayan ka san kai ne za ka cutu ba ita ba, ita dama wannan damar take nema kuma ita ce cikar burinsu ita da mahaifiyarta. Sau nawa suna tako gidan nan su mini ɗiban albarka da cin mutunci a kan sai na saka ka sake ta, amma saboda son da na san kana mata nake shanyewa in jure, mai ya sa ka yi haka babu shawarata?"
"Mama, ni ma ban san na furta ba zuciya ce ta ɗauke ni da ɓacin rai, haushi da takaici sai da na furta kalmar sakin sannan na gane wautar da na yi"
"To ai dama shi shaiɗan har abada burinsa kenan burinsa ya shiga tsakanin ma'aurata burinsa ba ya cika sai ya ga ya raba aure, kai shi fa duk wani abu mai kyau gaba yake da shi"
. "Haka Allah, ya kaddara dama can rubutacciyar kaddara ce, a rubuce yake cewa a wannan rana igiyar aurenku za ta datse, a wannan rana zamanta a gidanka zai yanke sai dai wani rabon kuma in akwai shi za ta dawo" Mama ta ce bayan ya gama faɗa mata yadda abin ya faru.
"Ba za ta taɓa dawowa ba Mama ni na sani" Ya ce har lokacin kansa kife a cinyarta.
"Ka kwantar da hankalinka ka yi addu'a ni ma in taya ka Allah zaɓa abin da ya fi alkairi" Ta ce tana ɗago fuskarsa ta share masa hayawayen, tare da masa faɗa sosai a kan sanyawa mace hannu sosai ta nuna masa illar yin hakan ta umarce shi da duk runtsi duk wuya kar ya kara dukan mace, sannan ta masa nasiha mai ratsa jiki a kan yadda da kaddara kyakkyawa da kuma mummuna. Har sai da aka kira magriba tana ta masa nasihar sai da ta ga ya samu nutsuwa, ta saka masa albarka da fatan wanyewa lafiya, sannan ta ce ya je ya tafi masallaci ita ma ta yi alwala ta yi tata sallar.
Sai da ya yi sallar ishsha'i ya dawo gidan, nan ta zuba masa abinci amma ya ki ci duk da akwai yunwa a tare da shi amma shi ba ya jin yunwar zafin rashin SALIMAH ya danne komai. A tsakiya Mama ta saka abincin ta ɗauka a cokali ta nufi bakinsa tare da ce masa ya yi Bismillah, Bismillar ya yi ta shiga bashi a baki, sai ya samu kansa da kin mata musu haka take bashi abincin a baki ita ma tana ci har suka cinye ta karo musu, suka kara cinyewa sannan ta mika masa ruwa shi ma a baki.
"Haba Mama aikin ai ya miki yawa ruwan ma sai kin bani a baki" Ya ce yana dariya har hakoransa suka bayyana. Ita ma dariyar ta yi ta ce
"Ai gwara in karasa laifina, na bada abinci ma bare ruwa" Haka ya buɗe baki suna rike da kofin a tare har sai da ya ɗago kansa alamar ya koshi sannan ta shanye sauran.
"Mama saura nawan kika shanye?"
"Ai uwa ba ta jin tsantsanin ɗanta" Sosai suka ringa hira cikin farin ciki tana ta jan shi da hira tana bashi labarai don ta kawar masa da damuwa, domin ya ce ba zai koma gidansa ba a nan zai kwana. Ɗakinsa na da ta shiga ta share masa, katifarsa ce a ciki sai sallaya da qur'ani. Tana dawowa ta ga ya yi nisa a cikin tunani da haka ta ce ya tafi ɗakin ya kwanta, a can ma zuwa ta yi ta zauna har sai da ta ji ya yi ɗiff alamar bacci ya ɗauke shi ta fito ta tafi nata ɗakin.
ABBAS kuwa dama ba bacci ya yi ba ya yi hakan ne don ta je ta kwanta ta huta kuma idan ta ga ya yi baccin za ta rage damuwa amma idanunsa biyu. Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kamo sunan SALIMAH "Duniyata" Shi ne sunan da ya yi saved da ɗaya lambarta, ya daɗe yana kallon sunan amma sai ya kasa kira domin tsoron abin da zai biyo baya, watakila ta ki ɗauka ko kuma ta ɗauka ta faɗa masa maganar da za ta tada masa mikin damuwar da ya ji ya kwanta masa.
Har wajen karfe biyun dare idanunsa biyu, fitowa ta yi ya yi alwala domin zuwa ya yi nafila haske ya hango a ɗakin Mama ya san ita ma kuma sallar take don tun yana yaro haka ya ga suna tashi da Babansa suna nafilar dare idan