Showing 21001 words to 24000 words out of 61883 words
Chapter 8 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
an yi zancen matacce? Ai arahar kunu ta banza ce idan babu gaya a ciki, yanzu baku da gata da galihu don haka abin da kuka yi a gidan nan mai kyau shi zai sa ku samu abinci saboda abubuwan da iyayanku suka yi na kyautatawa ya wuce babu shi mun ɗakko ku ne gidan nan ku yi mana hidima ku samu abinci, in kun yi da kyau za ku ga da kyau! Kuma ko Umar da yake cewa zai aure ki ba wai ƴanci za ki samu ba illa iyaka bauta ce da musgunawa ki zama
baiwarsa.
Kanta ta sunkuyar ta ci gaba da zuba musu abincin hawaye suna sintiri a kumatun ta, a duniya ta tsani ta ji ana faɗawa iyayanta maganganu, sannan ta ki jinin ta ji ana cewa za a aura mata Yaya Umar mutumin da bai san komai ba sai shaye-shaye kullum ya zo gida idanunsa jawur in ya dawo da dare a buge amma saboda ita ba su suka haife ta ba sai a aura mata shi, ita yanzu aure ma ba ya gabanta karatu take so amma tun da ta kammala karatun ga takardun sakandiren nan amma kuma an ki a sama mata adimishan ta cigaba da karatu in ta yi magana a ce wai ta gama karatu iya sakandiren ma ya isa saboda ba sa kaunar ta yi zurfi a karatu har ta zo ta samu aiki ta zama wani abu shi ya sa don su dakusar da rayuwarta za su aura mata Yaya Umar wanda shi ko secondryn bai gama ba ya watsar da karatun wai dama ana karatu ne don a samu aiki ana yin aiki ne don a samu kuɗi to su kuma dukiya gata nan har sun ci sun tada kai. Sallah wannan bai damu ya yi ba shin ta aure shi ta ce ta auri wa?"
Fitowa ta yi bayan ta gama haɗa musu ta nufi wajen Baba Sadiya ta karɓo abincin SABEER wanda koko ne da kosai.
"SABEER ba ya son kokon nan ya fi son shayi kullum in na masa dole ya sha sai ya yi amansa" Hawwa ta ce cikin sanyin murya.
"Ki yi hakuri Hauwa'u da a ce da yadda za a yi in ke zuba masa shayin da ko na iya lipton ne da na zuba masa, to bani da wannan damar, da ina da ita hatta dankalin turawan nan da wainar kwai sai na zuba masa Hauwa'u to kin san dai tsari da dokar gidan nan matsawar aka yi hakan ko a ɓoye ne sai ka fuskanci hukunci ko ka rasa aikin ma baki ɗaya'
"Na sani Baba Sadiya abubuwan ne suke damuna, ni na san babu na san hakuri amma SABEER yaro ne kullum sai ya yi mitar abinci sai ya yi mitar makaranta da zuwa makaranta a kafa sai ya yi mitar kwanciya a kasa a ɗakin wancan kuma in dai zai yi sai ya sako maganar su Ummie a ciki sai ya tuno cewa da a gidanmu ne da an yi kaza da kaza ya kasa mantawa ni kuma hakan yana tada mini mikin damuwar da muke ciki yana tada mini rashin da muka yi wanda ba za mu mayar da gurbin ba har abada!"
"Ita dama rayuwa tana canjawa mutum a lokacin da bai yi zato ba, to ya za a yi da lamarin ubangiji haka Allah ya tsara, wata rana sai labari duk abin da mutum ya yi hakuri wata ran zai zama tarihi"
"Haka ne" Hawwa ta faɗa tana danne kukanta.
"Ki yi hakuri ke ma girma ne ya same ki wanda baki yi zato ba, haka za ji bi komai a sannu su kuma Allah ganar da su".
"Amin Baba na gode da kulawarki gare mu"..
"Babu komai Hauwa'u karamcin mahaifiyarki gare ni ba zan taɓa mantawa ba mace mai kirki da girmama ɗan adam kowa nata ne abin hannunta bai rufe mata ido ba, ɗimbin dukiyar da suke da shi bai saka nata girman kai ko kyamatar talaka ba, ki je ki bashi abincin ku tafi ungo wannan ɗari biyun ko hau adaidaita sahu, idan kin kai shi sai ki dawo a kafa, wannan kuma man shafawar ne na lakuta muku kuke shafawa in aka biya mu kuɗin aiki zan saya muku naku tun da nakun ya kare" Hannu biyu ta saka ta karɓa tana godiya yanzu duk duniya Baba Sadiya ce kaɗai mai kaunarsu mai taimaka musu duk da taimakon ma a ɓoye ake yi saboda kar masu gidan su ankara wani abu ya biyo baya.
Dakyar ta samu ya kukkurɓi kokon jin ya ce zai yi amai ta kyale shi kosan ya ci kaɗan yana ta cewa da a gidansu ne da an yi kaza da Ummie ta haɗa masa kaza ita dai tana ta cewa sun kusa dawowa.
"Aunty Hawwa kullum fa sai Hajiya ta ce sun tafi kenan"
"Wasa take yi" Ta ce tana jin zafin furucin da Hajiyar take musu tun da ga shi ya shiga kwakwalwar yaron ya zauna daram.
Hannunsa ta kamo suka fito suna zuwa get ɗin ga motoci nan guda shida a ajiye ga direbobi nan zaune suna jiran umarni.
"Aunty Hawwa ki ce direba ya kai mu mun makarafa"
"SABEER, SABEER, SABEER sau nawa na kira ka?"
"Uku to ka daina cewa mu hau motacin nan daga su Ummie sun dawo za mu koma gidanmu sai mun zaɓi wacce za mu hau" Ta ce tana sakar masa murmushi tare da lakato hancinsa dariya ya kyalkyale yana kankame ta suka cigaba da da hira suna darawa su kaɗai ne farin cikin junansu. Har suka samu napep ɗin ɗan arziki a ɗari da hamsin ya kai su sai ta siya masa biskit na hamsin ɗin yana ta murna. A da SABEER bai damu da biskit ba saboda gasu nan kala-kala- da wafera da cakulet lemuka iri -iri a store in aka saka masa cikin
lunch box ɗinsa wata rana ma haka zai dawo bai ci ba, amma rayuwa kenan yanzu sai ya yi wata ma bai ci ba.
Tana dawowa Hajiya ta tisa ta da masifa wai ta je ta daɗe ko yawon banza take tafiya, haka ta yi ta gasa mata maganganu ta shiga aiyukan gidan duk da akwai isassun masu aiki amma don a musguna mata ita ake sakawa rabi da kwatar aikin gidan.
"Ki je ki gyara ɗakin Umar saboda raini kullum sai ki gyara ko ina ban da ɗakinsa ki gyarawa kowa nasa ɗakin amma ban da shi" Hajiya da take zaune a kan kujera ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya ta ce tana aika mata harara. Da to ta amsa tana daukan kayan gyaran ta nufi ɗakin nasa ta tsani zuwa ɗakin Yaya Umar kasancewar shi namiji kuma mashayi. Tana tura kofar wari ya mata sallama wannan warin da take ji gwara warin kashi a kansa.
Kolon amai ne ya sa ta fitowa daga ɗakin tana danne bakinta da tafin hannunta Hajiya da take zaune ganin wulgawarta da ta fito daga part ɗin Umar sai kuwa ta taso cike da masifa son a zaton ta gyaran ne ta yi ha,inci bai gyaru ba ta fito. Duk kiran da take mata bata amsa ba kasancewar aman ya taho can ciki ta wuce ɓangarensu na ma'aikata ta je makwarara ta ringa kela amai cikinta yana kullewa kasancewar babu wani abinci a cikin sai da gama ta wanke fuskarta ta gyara wajen ta dawo nan ta samu Hajiya ko ta bakinta ba ta saurara ba illa iyaka ta ce ta raina mata wayo tana ji tana kiranta ta kyale ta sai yanzu ta zo a shelake.
Hakuri ta shiga bata duk da bata san takamaiman laifinta ba amma haka ta kama kunnenta ta murɗe sai da ta kusa sakin fitsari sannan ta kyale ta ganin ta jigata. Umarni ta mata a kan ta koma ta kara gyara ɗakin Umar ɗin ira Hawwa bata samu damar cewa komai ba tun da ba saurarenta za a yi ba. Ɗankwalinta ta since ta ɗaure hancinta ta shiga ɗakin duk kayansa a kasa haka ta tattare ta kintsa su a waje guda hango wasu kwalabe reras a kasan gadon karambani ya sa ta yin kallon kwakwaf ai kuwa ta yi tozali da kwalaben giya. Sosai jikinta ya shiga karkarwa tana mamakin shi dai Yaya Umar duk wani abu na saɓo yana yi bayan shan kwaya, yana shan giya ga neman mata wace mace ce za ta yarda ta aure shi? In ba wacce bata san ciwon kanta ba, ko iyayanta mararsa sanin darajar ƴar su ba, amma ita saboda maraici da rashin sanin ya kamata da kuma rashin tsoron Allah za a aura mata ɗan shaye-shaye.
Da a ce ƴar su ce ba za su taɓa yarda su aura mata shi ba.
09013181851
[1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 7
*SALIMAH*
Kwance take a barandar kofar ɗaki tana charting da EESHART yanzu kam ta sakar suna hulɗarsu kamar da, sai dai ita a ɓangaren EESHART dama abij da ya da ta fara yi wa SALIMAH wulakanci lokacin da aka yi sakin saboda kuduri da burinta ne ya cika a fili tana kaunar SALIMAH kamar me amma a zuciyarta ta tsane ta hassada take mata musanman da take zaune a gidan aurenta lafiya bata san matsaloli da kalubaken da mata suke fuskanta a gidanjen aurensu ba. Duk da dama aure ɗan hakuri kuma hanya ce ta samu aljanna ita kuma aljanna ba za a same ta a haka ba dama an kewaye aljanna da abubuwan da zuciya bata so, kuma an lulluɓe wuta da abin da zuciya take so. Ma'ana duk wani abu wanda yake saɓon Allah ne sai aka ce sai mutum ya bar shi zai shiga aljanna, haka ma duk wani abu da zuciya take so sai aka hani mutum aikatawa sai hakan ya zama mukullin shiga aljanna. Misali idan mace ta yi hakuri ta jure a gidan aure ta yi biyayya ga mijinta to za ta shiga aljanna sai dai wannan biyayyar ita ce mai wahala wata tana gani mijim ya tauye ta ne bayan kuma Allah ne ya yi umarni da hakan. Idan kuma ta bijire hakan zai sa ta shiga wuta Allah kiyaye.
Har sai da ta ga ta kashe mata auren sannan hankalinta ya kwanta ko kyautata mata da take yi a gidan auren, saka kati da data bata kuɗi da sauransu din ta kara saka mata kwaɗayi da burin auren mai kuɗi ne ta kashe auren saboda ta san da wahala ta samu miji mai hakuri mai sonta wanda ya haɗa komai kamar ABBAS. Ganin kar SALIMAH ta yi saurin harbo jirginta tun lokaci bai kure mata ba ta koma gidan ABBAS ɗin shi ya sa ta sauya shawara a kan bin komai a sannu har sai ta yi wani auren duk da ta san yanzu burin auren mai kuɗin ya zauna a zuciyarta daram ta yadda duk runtsi duk wuya ba za ta koma gidan ABBAS ɗin ba.
Sallamar BASEERA ce ta katse mata dariyar da take kyalkyalawa, EESHART tana bata labarin wani littafi mai ban dariya da ta karanta na maman afrah mai suna ƳAN ADAIDAITA SAHU har tana ce mata tsabar dariya sai da ta tuntsuro daga kan kujera, tamkar ita take karantawa haka ta ji labarin ya bata dariya tana cikin wannan halin ne BASEERA ta yi sallama. Amsa mata ta yi tana mai haɗe rai tamkar ba ita ce take dariya yanzu ba.
Karasowa ta yi ta zauna tana murmushi dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya.
"Hajiya SALIMAH ikon Allah kamar kin ga makiyiyarki?" Ta ce tana murmushi har lokaci.
"Mai kika gani?"
"Mene ne ma ban gani ba, kin ga yadda kika ɓara rai?" Majewa ta yi ba tare da ta amsa mata ba.
"Ina wuni, ni in gaishe ki tun da ni ban samu arzikin a gaishe ni ba"
"Yo katin gayyata na aika miki da zan gaishe ki? Ke babu mai yin magana da ke cikin daɗin rai sai ki hau wa'azi tamkar ke kika fi kowa sanin dai dai da sanin ya kamata"
"Allah sarki kawata, ita dama ai gaskiya ciwi ne da ita kuma tana da ɗaci amma ki saki ranki yau ba wannan ne ya kawo ni ba dama na ga na miki magana saman whatsapp baki buɗe ba na kira ki ya fi a kirga bakya ɗaukan kirana, sgi ne na ce bati na zo in ji laifina tun da ni ba za a je inda nake ba"
Sakin fuskarta ta yi, ta ce
"To ai ke ɗin ce daga nasiha sai wa'azi kin ga kuwa ai ba kullum akw kwana a gado ba"
"Haka ne"
"Yanzu ya kike, kuma ina kika baro mini baby da babanta?"
"Ina lafiya, baby tana gidanmu a can take yau tun safe, shi kuma Habib kalbi yanzu ya ajiye ni"
"Inyeee ka ga tattabaru masoyan asali in ka ga wata ka ga zarah ni na kasa sanin yaushe ne soyayyar nan za ta tsufa don kullum sai hauhawa take tamkar an zubaaa fulawa yis" Ta ce tana dariya.
"Ke ko, wa ya faɗa miki soyayya tana tsufa ai sai dai masu yin ta su tsufa, kuma a gidan aure in dai miji zai samu abin da yake so daga gare ki, na daga biyayya kuma kina girmama shi, sanna uwa uba tsafta da kwalliya gyara jikin ki matsayinki na ƴa mace idan na ce gyara kowace macs ta san mai nake nufi to matsawar kika kiyaye wannan duk taurin kan namiji za ki samu salama da sasaauci za ki samu zaman lafiya shi namiji yana da son girma da son a girmama shi, sannan gyaran jikin ki ko yaushe ya jiki yadda ya kamata domin mu'amalar auratayya ita ce aure duk wanda ba ya samun biyan bukata kuwa wannan ne mafarin gurɓacewar zaman lafiyarsa a tare da abokin zamansa, wai ina Umma kin sa sai zuba nake ban tambaye ta ba".
"Ta je asibiti dubiya, kuma wannan dogon jawabin naki zai fi kyau ga wanda yake tare da mijin da yake so yake kauna, idan fa aka ce babu so to babu magana duk wani abu ba zai samu ba, idan na yi sabon aure na auri zaɓina zan zo kike biya mini karatuttukan nan" Ta ce tana dariya, ita ma dariyar ta yi shiru ya ɗan biyo baya.
"Ga ruwa" Ta ce lokacin da ta ɗakko mata pure water ta mika mata, karɓa ta yi tana fasawa ta sha kaɗan ta ajiye.
"Ni yanzu na matsu in gama idda ko na fara famtamawa na zaɓa na darje" Ta ce tana kallon BASEERA. Murmushi mg ciwo BASEERA ta yi tana kallonta da tausayawa ta san SALIMAH ta yi rashin miji mai kaunarta da gaskiya kauna wacce babu algus duk da bata mata fatan wani abun a nan gama amma dai ta san ba za ta taɓa samun kamar ABBAS ba sai dai wani lulluɓi mai cike da duhu ya mata shamaki da ganin hakan, duniyar ce w gabanta tana mamakin ma yadda ita ko mutuwa ba ta wani damuwa da tunaninta ko a cikin zance da wuya ki ji ta sako mutuwa.
"Zaɓa da darjewa ai ba shi ne nagartar ba, wani zaɓin ba ka gane zaɓen tumun dare ka yi sai in ka je cikin gidan auren"
"Ban gane ba mai kike so ki ce mini?"
"Hmmm! SALIMAH kenan, shi fa samun nagartaccen miji dace ne kin san shi namiji ba kamar kwarya bane da za ki ce sai kin kwankwasa kin gane shi, kuma baka gane waye mutum har sai ka zauna da shi ko da kuwa cikin kawaye ne zama ne yake sa ka fahimci halayyar mutum idan zama ya yi zama, kin san hangen dala ba shiga birni ne ba bari na yi shiru kar na cika ki da surutu tun da kin ce ni wa'azi da nasihata sun yi yawa"
"A'a ni fa a kan ABBAS ne bana son ki dame ni amma in dai a kan zawarawa ne idan akwai hanyoyin da zan gane wa zan aura ki fahimtar da ni duk da ni ban damu da kasancewar mutum na kirki ba bukatata in samu inda zan huta in ci uban naira har ta yi kukan dole"
"To ai tun da tunanin da burinki ya sha bamban ba sai na mata lokacina ba, in dai mai kuɗi ne ai ana iya gane shi a kallon farko dama nagarta ce nake magana ke kuma ba ita bace a tsarinki, kenan ke ko buri da fatan ki zaɓawa yaranki uba nagari bakya yi sai mai kuɗi kawai?"
Sosai SALIMAH ta kyalkyale da dariya, hae tana rike ciki, mamaki BASEERA take yi don a cikin maganganunta ba ta ga wanda ta yi da har zai bada dariya kamar yadda ta ga tana yi ba. Kallonta take har sai da ta tsagaita sannan ta ce
"Wai don Allah BASEERA sai yaushe za ki waye? Har yanzu idan kika yi wani furucin sai in ji tamkar a cikin tukunyar yake, baki san yanzu ka ya waye ba an samu cigaba