Showing 9001 words to 12000 words out of 61883 words

Chapter 4 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10806

ya falka bacci, kuma ko yanzu ma ya ga inda ta yi alwala da butar a wajen.


Sai da aka kira asuba sannan ya tashi daga kan sallayar ya tafi masallaci bai dawo ba sai da gari ya yi haske sosai ya ji damuwar ta ragu.




Da ya dawo ma bai kwanta ba sai ya ɗauki qur'ani ya shiga karantawa cikin kira'arsa ta Ahmad Sulaiman wanda tun suna islamiya ƴan ajin su suke cewa suna son kira'arsa ko malamin su idan ya zo karɓat harda sai ya yi ta saka ABBAS maimaitawa in ya gama bashi hardar ya ce ya kara maimaitawa ba don akwai kuskure a cikin karatun ba sai domin daɗin kira'arsa. Shi kuma tun yana karami Mama take kunna karatun Ahmad Sulaiman ɗin sai ya taso da son zama kamar shi, kullum in ta kunna sai ya ce.


"Mama ina son zama wannan malamin idan na girma, ina so in iya karatu irin nasa" Sai ya zamana ko surorin kasa da take koya masa sai ya ce sai ta masa kira'ar malamin haka take koya masa da kira'ar shi ma yana yi wannan ne mafarin koyon kira'ar idan yana yi tamkar Ahmad Sulaiman ɗin ne yake ga ba wa kowane harafi hakkinsa, shi dama yaro yana tashi ne da abin da ya ga mahaifiyarsa tana yi, idan mai kyau ne haka zai ke yi in akasin haka ne ma koya zai yi saboda yara sun fi ɗaukan abin da suke gani ana yi fiye da wanda ake koya musu ko ake umartarsu su yi.




Ɗumamen tuwo suka ci amma kuma sai ya ki tafiya wajen aikin kafinta ya ce zai ɗan huta zuwa kwana biyu. Ita ma Mama bata takura masa ba saboda ta san saboda damuwar da yake ciki ne kuma dama ciwo ɗan lokaci guda ne sauki sai a hankali, bare kuma cuta ta so. Da yamma ya tafi gidan nasa ɗauko kayan sawa saboda ko da ya yi wanka na jikinsa ya maimaita. Tun da mai machine ɗin ya ajiye ji a kofar gidan sai gabansa yake faɗuwa dakyar ya samu karfin gwiwar tunkarar kofar gidan ya buɗe yana ta karanto addu'a a ransa domin yana dosar cikin gidan sai ya ji komai ya dawo masa sabo fil. Tamkar ba a taɓa halittar SALIMAH ba haka ya ga gidan. Bedroom ɗin ya dosa ya shiga yana ganin kofar dirowar kayanta a buɗe ko rufewa bata yi ba jiyan duk ga kayanta nan a ciki saurin ɗauke idanunsa ya yi daga kallon kayan nata, jin wani abu ya tsarga masa a kirjinsa kan mudubin ya kalla ganin kayanta duk suna nan sai ya ji kuka yana son taso masa. Bakin gadon ya karasa ya zauna ya sunkuyar da kansa yana jin yadda sonta yake kona masa zuciya.




"Ya Allah kai ne kake jarabtar bayinka a kan komai, kai ka jarabce ni da son wannan baiwa taka wacce ita bata sona ya rabbi don tsarkin mulkinka, domin buwayarka don karfin ikon ka Allah, ka kawo mini mafita ta alkairi ka yaye mini damuwata na san babu abin da ya gagare ka, kai kake iko da kowa kai kake juya lamura ya rabb ka juya al"amurana zuwa abin da ya fi alkairi kar ka barni da son zuciyata ya Allah" Ya ce a zuciyarsa yana jin hawaye suna taruwa sai dai bai bari sun zubo masa ba ya ya ɗago tare da ɗaga hannuwansa sama ya ce.


."Rabbi inni lima anzalta ilayya min kairin fakir, la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin, subhanallahi wa bi handihi subhanallahil azim, Allah hakika baka mayar da addu'ar bayinka, ko dai ka amsa a lokacin, ko ka sanya addu'ar ta kare musu wata musiba da ta tunkarosu, ko dai ka sauya musu da abin da ya fi wanda suka nema alkairi a gare su ko ka jinkirta musu Allah ka sa jinkirin tawa addu'ar ya zama alkairi, Allah ka kawo mini ranar da zan yi farin ciki saɓanin damuwar nan da nake ciki" Ya kai karshen addu'ar bayan ya karanto sunayen Allah 99 ya shafa addu'ar tare da goge idanunsa.


Dirowar kayansa ya buɗe ya ɗauki kayan ya saka a jaka ya fito daga ɗakin da sauri tamkar wanda aka ce ya yi mantuwa a waje, cikin sauri ya fita daga gidan ya rufe kofar don ba ya so ko kaɗan wani abu ya tsikari zuciyarsa a cikin gidan game da SALIMAH.






Washe gari ABBAS jin ya kasa jure rashin SALIMAH gabaɗaya ba ya samun ishashshan bacci, ko kaɗan ba ya cikin walwala ko kafintocin ba ya iya zuwa ji yake gabaɗaya duniyar ta masa kunci. FAROUQ ya kira a waya yake faɗa masa cewa ya saki SALIMAH, maimakon da ya gama faɗa masa yadda abubuwan suka wakana sai cewa ya yi.


."Alhamdulillahi, Allah na gode maka"


"Haba FAROUQ ya ina faɗa maka ina cikin matsala amma sai ka nuna farin ciki kana hamdala".


"To ai dole na yi hamdala wannan abin a taya ka murna ne, haba ABBAS mace ka zama tamkar bawanta amma ba ta kaunarka ko kaɗan ta mayar da kai tamkar baka sam mai kake ba. Ai sakin SALIMAH shi ne kwanciyar hankalinka ka daure kawai don farko ne amma komai zai wuce tamkar ba a yi ba" Ya ce cikin halin ko in kula.


."To wallahi na san zaman da zan yi da kai"


"Yo wane zama kuwa za ka yi da ni in ba wanda ya fi na baya tsawo ba"


"Wai mai ya sa ka cika ɗaukan abu da wasa, ina faɗa maka bani da sukuni ko aiki bana iya zuwa zuciyata bata da nutsuwa ko na kawar da komai a raina sai tunaninta ya hana kwanyata sakat"


"Saboda ka sake ta ka daina zuwa wurin neman halalinka? na faɗa maka ka jure Allah zai baka wacce ta fi ta wacce za ta kaunace ka tun da ba ita kaɗai ce mai kyau ba"


"Sanin kan ka ne ba kyan SALIMAH ne ya ruɗe ni ba kawai kauna ce domin Allah da a ce SALIMAH fuskarta za ta yi dameji ta samu nakasa a jikinta wallahi daidai kwayar zarra son ta ba zai ragu a zuciyata ba".


"Wannan abu ne da ka sha biya mini shi da karatu ne ma da tuni na haddace, yanzu mai kake so in maka"


"Please FAROUQ ka zo gobe ka rakani bikonta ko Allah zai sa ta tausaya mini ta dawo" Ya ce cikin marairaicewa.


"Taɓ amma kai dai ka cika marar zuciya mace ta sa hannu ta mareka har kake marmarin dawowa da ita to ba zan maka baki ba nan gaba za ta iya saka bulala ta zane ka, kuma ina so ka sani SALIMAH ba ta tausayinka kuma ba na jin za ta taɓa tausaya maka, yadda ma take burin samun rabuwa da kai ba na jin za ta yarda ta dawo"


"Fata na gari lamiri".


"Haka ne ka jira ni gobe da bayan isha'i sai mu je ka gwada sa'arka"


"Na gode abokina".


"Tun yanzu kake gode mini ka bari sai mun dawo da ita" Ya ce cike da shekiyanci yana kyakkyalewa da dariya ya kashe wayar. Shi sosai ya ji daɗin sakin ko ba komai abokinsa zai samu nutsuwar ruhi in ta fita daga rayuwarsa. ABBAS kuwa wayar da suka yi sai ya ji nauyi ya ragu a zuciyarsa duk da ba shi da tabbacin dawowarta amma ya dace ta bibiyeta ko ba za ta dawo yanzu ba zai tsumayi zuwanta wata rana.




Ko da ya faɗawa Mama bata yi yinkurin hana shi ba, duk da ta san ba lallai ne ta dawo ba amma sai ta ga ba a kwacewa yaro garma hakan ya sa ta masa fatan nasara. Kwana ya yi yana sallah yana addu'ar Allah ya ɗora shi a kan SALIMAH da Ummarta. Ko wunin ranar ma bakinsa ba ya rabuwa da ambaton Allah har da sadaka ya yj duk na neman dacewa a wurin bikon.


Da la'asar ya yi wanka ya saka wani yadinsa fari wanda yake ga ya fi kowanne sabunta a cikin kayansa, madarar turare ya shafa ya saka hula, sai murmushi yake yana jin daɗin zai yi kwalli da wacce ya fi kauna. Duk da a gefe ɗaya yana ta jin fargaba tamkar amarya a daren farko. Hula ya saka sosai ya yi kyau kasancewarsa fari dogo mai doguwar fuska wacce ta kawatu da dogon hancinsa da yake har wajen baki, karamin pink ɗin bakinsa wanda yake tamkar ya saka jambaki, hakoransa da suke a jere reras tamkar masara gashin kansa wanda yake baki wulik a kwance tamkar na larabawa, kwancaccan gashin girarsa da zara-zaran gashin idanu, idanunsa da suke farare tas kamar madara haɗe da bakar kwayar idanun da ko kallonka yake sai ka ga tamkar kallon love yake maka,kakkarfa ne kuma fafffaɗa, ba shi da makusa ko ta ina a tare da shi ga uwa uba mahaddacin qur'ani za a iya kiransa da ya haɗa komai kuma bai rasa ba komai.




Tun da ya durkusa raka'ar karshe ta nafilar da ya yi bayan an idar da sallar ishsha'i addu'ar neman dacewa ya yi ta yi bayan kafin ya fito ya sanar da Mama a kan ta masa addu'a SALIMAH ta amince ta dawo da to ta amsa masa. Ko da ya fito daga masallacin a kofar gidan Mama ya samu machine ɗin FAROUQ roba-roba tun da dama ya faɗa masa ya kauro gidan Mama a can zai same shi. A kofar gidan suka ci karo da FAROUQ da ya fito bayan ya gaishe da Mama ta ce ya duba ABBAS ɗin a waje bai dawo daga masallaci ba.


"Kai mutumina irin wannan kyau haka kamar dai angon da zai je ɗaurin aurensa" FAROUQ ya ce cike da tsokana.


"Yo mene ne bambanci ni duba mini ma na yi kyau ko in koma in sauya kaya?".




"Eh koma ka sake har fatarka ma sai ka sake , tun da wacce za mu je wajen nata ai za ta yaba ko" FAROUQ ya ce cike da gatse.


."Ka ji ka da wani abu za ta yaba mana".


"Allah sa" Daga haka suka hau machine ɗin suka kama hanyar gidan su SALIMAH da yake unguwar badarawa. A kofar gidan suka faka machine ɗin nasu suka samu yaro domin ya kira musu ita, ABBAS ko magana ya daina sai sunayen Allah kawai yake jerowa gabansa yana faɗuwa.




"Assalamu alaikum, wai ana magana da SALIMAH" Cewar yaron da ya shigo. Maimakon Umma ta amsa masa, sai ta carara guɗa. SALIMAH da take ɗakin jin Umma tana guda sai ta bazamo da gundunta domin ta san ruwa ba ya tsami banza ma'ana Umma ba za ta yi guɗa ba sai da dalili mai karfi.




"Mene ne Umma?"


"Sai ni uwar kyakkyawa shi ya sa aka ce ƴa mace kyakkyawa jari ce, musamman kyakkyawa idan ana neman aurenta ka wanki gara idan ta yi aure ma kai ka kasa kayanka ka siyar" Umma ta ce tana darawa.


"Wallahi Umma kin kara saka ni a duhu"


"Ke goshi kika yi ƴar nan, tun baki yi idda ba har an fara zuwa zawarci kai na san dai bana kakarmu ta yanke saka"


"Wayyo daɗi Umma na kusa fara kashe kala"
.
"Ai kaloli ma za ki kashe ɗiyar nan Allah ya mini gyaɗar dogo na kusa daina zaman gaban murhu ina toya kosai da koko" Ta ce tana mikawa SALIMAH hannu suka tafa kamar wasu kawaye.


"Kula ki leka sai ki musu bayanin cewa su jira kaɗan kwanakin iddarki su cika, su zo su hau layi, don wallahi wannan karon sai kin zaɓa kin darje Allah jikan Malam wannan karon zaɓe ba nasa bane bare ya miki zaɓen tumun dare ya zaɓa miki ahlil fukara'u"


"To Umma bari na ɗakko mayafi, ai ni na matsu na gama iddar nan ko na fara wankar kuɗaɗen zawarawa in sake kayan sawa na kece raini"


"Ko ni uwaki ai sai kin sake mini sabon zubi saboda in zawarawan naki za su shigo mu gaisa kar su ganni a tsumma" Cewar Umma tana dariya.


"Ai dole ki ɗaura manyan lasa-lasai.


"Kai yaro in ji wa ko ba faɗi sunansa ba" Umma ta ce tana murmushi don kunnuwanta so suke kawai su ji an ce Alhaji wane ne, amma sai dai kash an samu akasin lissafi don cewa ya yi.


"Wai in ji ABBAS..."






Ku biyo ni don jin ya za ta kaya...😍🥹.




09013181851
[1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1






*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*






NA






MAMAN AFRAH




*GARGAGAƊI*


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️


JAN HANKALI


Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.




SADAUKARWA


Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.






PAGE 3






*SALIMAH*


Sai da ta yi sallar ishsha'i sannan batun EESHART ya faɗo mata, ta yi mamaki matuka na ganin bata kira ta ba wayar ta ɗakko ta duba bata ga miss call ba. Shiru ta yi tana ta mamaki a ranta duk tunaninta EESHART ɗin za ta yi ta kiranta suna labarta abin da ya faru tun da dai bata gama bata labari ba ta ce ta bari za su yi waya idan ta je gida. Kawar da tunanin ta yi, ta buɗe data ta hau whatsapp, sakonnin da suke ta rige-rigen shigowa ne ta jira suka gama shigowa, dubawa ta yi ko za ta ga EESHART ta mata magana amma ta ga tun maganar da suka yi lokacin tana gidan ABBAS amma ko ɗigon magana bata mata ba, bayan ta saba ko yaushe suna tare a online idan ta mata magana ta ga bata nan ta kira ta idan bata da data ta saka mata amma dai yau ta rasa dalilin hakan sai dai ta mata uzuri a kan ko wani babban dalili ne ya mantar da ita farin cikin da take, cikar burinta wato sakin da ABBAS ya mata a yau ɗin.


Ganin tana online sai ta kara shan ruwan mamaki amma bata dogara da mamakin da ta shayar da ita ba ta je ta mata magana. Hi ta ce mata amma shiru-shiru sama da minti goma bata ma buɗe sakon ba bare ta mata replay. Kara mata magana ta yi cewa kawata ya na jiki shiru, sama da minti biyar bata buɗe ba abin ya yi wa SALIMAH ciwo amma dai sai ta dake har lokacin tana jiran ta fara ji daga gare ta duk da tana ganin nata online, bayan ta saba tana hawowa wani lokacin idan ita EESHART ta bar mata sako sai ta kara cewa ina ganin ki online fa matar manya.


Basarwa ta yi ta fara scrolling ganin sakonnin group ɗin kawayen su da suka buɗe message yana ta shigowa, sai ta shiga group ɗin nan ta ga sun baja kolin hira har da EESHART ɗin yawanci hira ce ake ta zaman takewar auratayya kowacce tana bada labarin mijinta da kulawar da yake bata da yake duk yawanci matan aure ne sai ƴanmata kalilan. Taggin ɗin EESHART ta yi ta ce na ajiye miki sako a pc kawata na ga baki duba ba har yanzu. Ok kawai ta ce suka cigaba da hirarsu. Jim kaɗan ta duba amma ta ga EESHART bata duba ba har dai ta fara tunanin ko wani laifi ta mata amma iya tunaninta bata gano komai ba.


Ta kasa duba sakon kowa kawai sai dawuwuri take abin da EESHART ta mata ya tsaye mata a rai. Sunan kawarta ta kamo BASEERA wacce har ta manta rabon da su yi magana saboda ita BASEERA tana faɗa mata gaskiya tana nuna mata ta yi hakuri ta zauna a ɗakinta tun da ABBAS yana son ta kuma yana kyautata mata, shi arziki na Allah ne in da rabo wata rana sai ta ga ya yi arzikin. Wannan ne ya sa kullum suke faɗa da ita saboda tana ganin ita ma bakin cikin ta fito ta auri mai kuɗi take mata tun da ita ma BASEERA talakan take aure sai dai shi mijinta ya fi ABBAS rufin asiri.


Sallama ta mata amma sai ta ga ba ta oline datar ta kashe ta sauka ma daga whatsapp ɗin.


"Ki zubo tuwo ki ci SALIMAH, ɗazu na ce mu ci ɗazu kika ce sai an jima idan ya huce ba za ki ji daɗinsa ba" Umma ta ce tana tattare kwanuka. Da to ta amsa mata tana zuwa ta zubo kaɗan amma tana sakawa a baki sai ta ji ɗanɗanon dai sai a hankali ba kamar miyarta ba ta saka ishashshan magi duk tsiya kuma dole ABBAS ɗin ya kawo.


"Umma ki bani magi na kara lami na ji miyar"


"Haba SALIMAH to ya kike so ki ji ni da na gama ci yanzu ban ji wani lami ba, amma ga gishiri nan ki kara saboda maggi dai kin san tsada yake ni kuwa da ba wanda zai kawo mini gare ni ba komai ni nake siya da sana'ar da nake yi"


"Ai kin kusa hutawa don har mai girki zan ɗaukar miki idan na auri attajiri"


Dariya ta yi ta bata maggin guda ɗaya ta saka sannan ta ji dama-dama.




Sai da ta gama bayan sun kwanta Umma a saman gado ita tana katifa a kasa, wayar ta ɗakko ta sake hawa whatsapp amma har lokacin babu sakon EESHART. Sai dai BASEERA ta amsa mata sallama har tana tambayarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login