Showing 39001 words to 42000 words out of 61883 words
Chapter 14 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
ambaton marayu ne, ba sai kin faɗa ba kowa ya san hakan ai amma maimaitawar bata fa wani amfani" Goggo ta katse wa Amrah zancen.
"Yo ƙarya na yi ba marayun bane Goggo kuma ai ba ni na kashe musu iyayan ba" Ta ce cike da fitsara tana shigewa ɗaki, HAWWA shiru ta yi bata ce komai ba don in da sabo ta saba ita yanzu abubuwan da aka mata bayan mutuwar iyayanta sun ƙara ankarar da ita rayuwar duniya.
"Wane mai ƙarfin halin ne ya taɓa mini mai waye ma ya shigo mini ɗaki babu izinina?" Ta fito ta tsaya riƙe da ƙugu.
"HAWWA ce ta shafa man kuma ni na ce ta shafa sannan wannan ɗakin naku ne ku biyu yanzu ita ma a ciki za take zama, kuma ba ziyara suka zo ba"
"Ah to hakan ma ya yi" Ta ce cikin gatse ta kuya ta koma ɗaki dama tun da safe ta fita wai ta tafi gidan babarta sai yanzu ta dawo babu tsiyar da take tsinanawa sai lokacin abinci ta zauna ta cika cikinta, sannan halinsu ɗaya kuma bakinsu ɗaya da Usman yayanta idan Baffa yana nan su ringa nuna su mutanen kirki ne amma idan a bayan idanunsa ne ƴan iskan kan su ne.
Ɗaki ta koma tana ji ana cewa ta fito su ci abinci da yake Goggo haɗa musu ta yi da HAWWA amma ta ce tana zuwa kuma ta ƙi fitowa. SABEER kuwa ya ce sai Baffa ya dawo za su tare.
Sai da Baffa ya masallaci aka idar da sallah ya sannan ya shigo gidan, har lokacin HAWWA tana zaune da abincin a gefe sai ma ta ɗauki murfi ta rufe tun da ita zaƙaƙura Amrah ta ƙi fitowa ita ma Goggo ya yi alwala ta shiga ɗaki ta yo sallaj ya rage sai Amrah a kan baranda sai kuma SABEER yana wasa. Jin sallamar Baffa SABEER ya tafi ta gudu tana masa oyoyo hannunsa Baffa ya riƙo suka ƙaraso cikin gidan. Amrah da take kwance tana danna waya jin shigowar Baffa sai gata ta yi wuff ta fito daga ɗakin ta zauna ko kunya tana washe baki ta ce
"Yi haƙuri ƴar ƙanwata sallah na yi kina ta jirana ko?" Ta ce tana janyo abincin ta saka a gabansu tana kallon HAWWA da murmushi a fuskarsa sosai HAWWA ta yi mutuwar zaune ganin abin da Amrah ta yi amma sai ta danne mamakinta tana sakin murmushin ita ma a zuciyarta tana mamakin irin kissa da kisisina na Amrah tana tunanin lallai idan aka ce Amrah kishiyarka ce ka shiga uku. Sosai Baffa ya ji daɗin ganin Amrah da HAWWA suna tare wannan ya ƙara sakawa ya ji daɗi a ransa.
Abincin suka shiga ci, ko nisa basu yi da fara ci ba Usman ya yi sallama ya shigo riƙe da ledar salad da ya taho fa shi, ƙurrrrr ya kafe HAWWA da idanu yana kallon yadda ta ƙara kyau da kuma girma farin fatarta ya sa ya hangi ƙanwarsa Amrah ta ƙara baƙi, dama baƙa ce sai faɗin fuskar da wani hancinta kamar gajeran wando.
Wani irin daɗi ya ji a ransa don dama sun haɗu da Baffa a waje yake sanar masa da zuwansu ya daɗe yana jin son HAWWA ransa sai dai sanin ba sa'arsa bace wato iyayanta masu akwai ne sai ya ja bakinsa ya yi shiru amma yanzu tun da dai ga ta a matsayin marainiya kuma ta zo zama sannan uwa uba Baffa ne auwalin aurenta to shi fa ya ga matar aure.
"Yaya sannu da zuwa" HAWWA ta ce ganin ya ƙura mata idanu. Amsa mata ya yi yana murmushin yaƙe don sai yanzu ya gane katoɓarar da ya yi. Amrah ganin da Baffa a zaune sai ta tashi ta karɓa salad ɗin ta je ya shiga yankawa ta saka gishiri ta wanke tas ta zuba a mataci ta tsakura musu ita da HAWWA.
"Ƴar ƙanwata kina so in zuba mana, in kuma bakya cinsa ni ma ba zan ci ba abin da kike so shi nake so" Ta ce tana murmushi dakyar HAWWA ta samu damar bata amsa saboda gabaɗaya ta shallake mata tunani.
"SABEER ko da ni za ka ci abincin ?" Usman ya tambaya.
"Ni dai da Baffa zan ci" Ya ce yana noƙe kafaɗa saboda bai manta ba lokacin suna zuwa da Ummiensa sai yake harararsa idan ba kowa a wajen ko yake zare masa idanu yana hantararsa yaro babu mantuwa.
Da daddare bayan Goggo ta ɗakkowa HAWWA katifar da za ta kwanta ta bata ta SABEER ƙarama irin ta ƴan makarantar kwana, da yake da wuri ya yi bacci sai ta kai shi ta kwantar bayan ta saka leda ta masa shimfiɗa. Sai da suka sha hira kowa ya shiga ɗaki a lokacin ne HAWWA ta ga ikon Allah don Amrah tuni ta sauya fuska ta fara mata tijara.
"Ba an lallaɓo cin arziƙi ba kar fa a zo a takurawa rayuwata, an zo kalen dangi da can baku san da Baffan ba sai da ruwa ya ƙarewa ɗan kada? Kun taɓa kun ji maraici babu daɗi ko? To bari ki ji in faɗa miki ki sani bauta kika zo yi gidan nan wankina share ɗakin nan ke komai ke za kike mini kar ki ga an haɗa mu ɗaki ɗaya ki zata ɗaya muke to ki sani baki da galihu" Ta faɗa cikin wani iko da izza. Wani ruwa ne ya taru a idanunta ganin ba a rabu da bukar ba za a haifi habu tana ganin sun baro ƙangin rayuwa a Zariya sun taho Kaduna ashe dai a nan ɗin ma ba za ta sauya zani ba. Da wutsiyar ido ta kalli inda SABEER yake a kwance tana jin tausayinta saboda muddin Amrah za ta hana ta rawar gaban hantsi to shi ma ba zai samu sakewa ba tun da ta ga hatta Goggo ma ba raga mata take yi ba sai Baffa yana nan shi kuma namiji ba ɗan zaman gidan bane koyaushe. Shirun da ta yi ta ɗan yi nazari cewa dole ta ɗauki mataki dole ta tauna tsakuwa aya ta ji tsoro dole sai ta zagine dantse za ta ƙwata musu ƴanci ita da ɗan uwanta maraici ba hauka bane ai maraya kuma yana da dama da ƴancin da zai rama koma mene ne in ba haka ba sai ya zama ahi da kashi basu da maraba wajen ƙyama.
"Amrah!!! Ina so ki sani duk wani maraya ba shi ya zaɓarwa kansa maraici ba Allah ne ya ƙaddara masa. Sannan kuma da kike batun kalen dangi ai mu munfi ƙarfin kalen dangi tun da uwa ɗaya uba ɗaya ba wasa bane mu ƴaƴan ƙanwar Baffa ne kin ga ba za a kira mu ƴan kalen dangi ba, ku da kuke ƴaƴan abokinsa ku ne za a kira da masu kalen dangi, kuma maraici tun da ku ɗin ma ubanku ya mutu su waye ku in ba marayun ba? Kuma ke baki isa in miki wanki ba ko da kuwa wankin pant ne bare na kaya, duk wani hayaƙi da kan ki yake ina so ki sani nawa ya wuta yake yi" Amrah da ta zaɓi take cin ƙaniyar Amrah a gefe a gaban su Baffa kuma ta mata walai-walai kamar yadda take wa mutane dama masu iya magana sun ce idan ka je gari ka ga kowa da jela to ko ta tsummace kaima ka ɗaura dole sai ta yi mata zabu-zabu ta yi maganin rashin mutuncin da ta mayar da shi abin yi.
Amrah sosai ta sha mamaki jin kalaman HAWWA saboda a iya saninta da HAWWA tana da haƙuri da kawar da kai kuma tana girmama na gaba ko da kuwa da kwana ɗaya tak! Ya girme ta amma yau ta shayar da ita ruwan mamaki sai dai ba za ta bada kai bori ya hau ba dole ta nunawa HAWWA cewa barazanarta babu abin da ta mata. Dakewa ta yi tana mai yin taku ɗaya biyu ta zo gaban HAWWA.
"Ke sa'ar yinki ce ni?" Ta tambaya tana sanya idanunta cikin na HAWWA amma sai ta ga ko gezau HAWWA bata yi ba, hakan ya sa ta fara tunanin to ko dai bayan mutuwar iyayanta ta samu wasu wanda suka koya mata rashin mutunci suka wanke ta. Hannu ta ɗaga don ba za ta juri raini ba wai har tana cewa su ne ƴan kalen dangi, fuskar HAWWA ta nufa ta sakar mata marin bazata, a gefen hagu kafin HAWWA ta dawo daga duniyar mamakin da ta shayar da ita ta ɗaga hannun za ta bata marin a karo na biyu.
A fusace HAWWA ta kaiwa hannun Amrah damƙa, tana mai sa ɗaya hannun ta wanke fuskarta hagu da dama da mari tare da wujijjiga ta, ta yi wurgi da ita a tsakiyar ɗaki...
*SALIMAH*
Da wani irin farinciki ta juyo tana kallonsa tamkar wanda ya mata albashir da kujerar hajj. Ta ji daɗin wannan kalami na shi don haka babu wani dogon tunani ta amince da auren a sati guda.
"Amma da sharaɗin za ka mini lefe na kece raini, lefen da za a daɗe a unguwarmu ana maganarsa domin kaya nake so na ɗaukan magana kaya wanda suka amsa sunansu kaya" Ta ce tana kallonsa wata ƴar dariya ya yi irin tasu ta mantya yana mai juyowa kocakwam yana kallonta ya ce.
"Haba gimbiya ai faɗa ma ɓata baki ne ni ganinki nake baki da bambanci da budurwa kin fi wata budurwar ma lefe zan miki na gani na faɗa kar fa ki manta da Alhaji Tahir kike magana bana tsoron kuɗi kuma bana jin komai don na kashe kuɗi dama masu iya magana sun ce da kuɗi da miciji dukakaninsu maganinsu kashewa! Bare kuma a kan tauraruwata wacce nake jin mallakarta ya fiye mini mallakar wani ƙaton zinare" Ya faɗa yana kashe mata ido, wani gingiringim kanta ya yi ya mata nauyi tamkar an ɗora mata dutse domin ya fasa mata kai sai yanzu ne take ƙara jin daɗin mutuwar aurenta ga shi tana sabuwar rayuwa bare kuma idan ta je gidansa ta zama mallakinsa tabbas wataƙila ta kan naira za take bi tana wucewa a lokacin ne za ta taka wanda take so.
"Shi ya sa nake jin ka fiye mini dubu dukkaninsu ina musu kallon taron yuyuyu, kai ne na zaɓa kuma kai zan ci gaba da zaɓa" Ta ce tana jin tamkar ta haɗiye shi saboda so don ita sai da ta ji baya jin ciwon kashe mata kuɗi ne ma ta ji tana ƙaunarsa saboda ita duk wanda zai bata kuɗi shi ne nata.
Nan suka zauna suna tsara yadda komai zai kasance daga nan suka yi sallama ta kwaso siyayyar da ya mata tana fitowa ta samu Alhaji Abdullahi tsaye a gaban motarsa.
"Big girl, sun buga sun barki babban goro sai magogin ƙarfe" Ya ce yana washe baki da ƙare mata kallo tamkar idanunsa za su fito a jikinta bayanta ta waiwaya ta ga Alhaji Tahir ya ja motarsa ya tafi sai lokacin ma ta tuna bata ɗauki kujerun ba. Juyo kallonta ta yi gare shi tana aika masa harara saboda wani message na banza da ta ga ya tura mata a waya ɗazu hakan ya nuna mata mu'amalar banza ta kawo shi gare ta ba aure ba don haka gwara ma ta auri wanda ya nuna zai aure ta kuma ta tabbata za ta samu abubuwan da take buƙata na daga dukiya da yin duk yadda ta so na facaka da kuɗi.
"Kin amincr mu tafi hotel ɗin awanni biyu sun yi yawa zan dawo da ke ba kwana za ki yi ba, na miki alƙawarin maƙudan kuɗi" Wani tsaki ta je ta masa kallon sheƙeƙe ta ce
"Allah tsari gatarina da saran shuka ka je ka nemi daidai ya kai ni kam mun yi hannun riga da zina da kuma mazinaci!. Tana faɗa ta juya ta bar shi baki sake yana mamakin ta a yadda ya santa lashe money bai taɓa zaton za ta ƙyamaci zina ba. Jiki ba ƙwari ya shiga motarsa ya bar wajen.
Tana shiga gida ta shiga labartawa Umma yadda suka yi da Alhaji Tahir sosai ta carara guɗa tana tashi tsaye ta taka rawa ta juya ta koma ta zauna ta ce.
"Kai Allah na gode maka da ka bani ƴa mai goshi mai farin jini kin ga abin da nake faɗa miki ko da yanzu kina can gidan talauci ahlil fuƙara'u Allah baku mu samu"
"Bari Ummata ta kaina yau ni ABBAS zai wa tashin balagar tsintsaye" Ta ce tana kwashe komai ta faɗa mata.
"Baƙin ciki ne yake cinsa ya gane ki sarai ko ni uwarki ba zai manta da ni ba bare ke, so ya yi ki zauna a ƙarƙashinsa baƙin talauci ya miki kanta"
Nan suka shiga tattaunawa yadda komai zai kasance don shagali za a yi. Bayan ta kwanta ta taɓo EESHART a whatsapp ta shiga labarta mata yadda suka yi da Alhaji Tahir. Sosai ta ji baƙin cikin za ta yi aure don ita a yadda ta taya ta ta kashe aurenta so ta yi ra yi ta yawo a kwararo a ƙarshe ta ƙi auruwa amma yanzum ma ta san dai ba za ta samu kamar ABBAS ba shi ne jin daɗinta. Nana ta shiga labarta mata yadda za su tsara komai. Ko RUKY da BASEERA bata kira ta faɗa musu ba dama har gwara RUKY ita BASEERA ƴar bayan a koma gidan ABBAS ce sabon auren ba zai mata daɗi ba.
Washe gari Alhaji Tahir ya kira ta ya ce su shirya su je siyan lefe waya ta yi wa EESHART dama mijinta ba ya gari ta kwaso ta taho ita ma RUKY da ta zo ta yi mamakin yadda aka yi SALIMAH ta samu miji hakan ya sa ta fara tunanin ko dai maganar SALIMAH ta tabbata da take cewa kyawawa basa kwantai.
Yana zuwa ya kwashe su da motoci biyu ya zo ɗaya direba ne kawai a ciki ɗaya shi haka suka tafi sai dare suka dawo akwati dozin kaya na gani na faɗa babu abin da babu hatta manyan sarƙar gwal da ɗankunne da warwaro set uku ne a ciki, hassada sosai EESHART ta ji a ranta amma ta danne ita ma RUKY tana jin ina ma ita ce. Tun da aka ringa shiga da akwatuna Umma take murna tana carara guɗa tana ta fama ƴarta ta yi gashi ƴarta ta kerewa sa'a ita a rayuwa ƴa ɗaya ta haifa amma ta zame mata babban jari. Sosai suka rungumi juna ita da SALIMAH suna murna kamar wasu ƙawaye, Umma bata zauce ba sai da aka fara buɗe kaya ta ga tamkar za a buɗe shago.
Da daddare ya kira ta a waya yana shawarta ta a kan cewa gidanta da ban za a ware mata ko kuwa za ta zauna da matansa.
"Haba Alhaji ai kawai ka kwatsamu tun da ka ce kowacce da ɓangarenta, in ka ware ni ai ba za su san suna da kishiya ba gwara dai in je mu jera su ga ruwan kyau yana zuba don su san cewa ni ba kishiyarsu bace shugabarsu ce saboda ba za su iya kishi da ni ba basu da abubuwan fa za su yi kishi da SALIMAH" Sosai yake yi wa maganganunta dariya daga ƙarshe ya ce babu komai kuma za a saka komai na buƙata ba sai sun kai ko da tsinke ba.
A motar EESHART da ta zo gidansu suka ɗauki katin ɗaurin aure suka yi wa kafintocin su ABBAS tsinke. Zaune yake yana danna carbi ya ga mota ta tsaya a saitinsa da yake baƙin gilashi ne kuma dai bai ɓatawa kansa lokaci wajen sanin waye mamallakin motar ba. Jim kaɗan sai aka buɗe ƙofofin biyu, ba zato ba tsammani ya ga EESHART da SALIMAH sun fito. Mamaki ya yi amma sai ya ɓoye mamakinsa suna doso inda yake bugun zuciyarsa yana ƙaruwa sai dai ambaton Allah ya sa ya ji nutsuwa ta saukar masa.
"Malam ABBAS ya kake ya ƙwale-ƙwale" SALIMAH ta ce tana wani murmushin gefen baki hakan ya tabbatar masa da wata manufa suka zo don ko ranar nan ya yi mamakin dalilin zuwanta na siyan kujera sai dai ya kasa gano dalilin da ya sa take bibiyarsa. EESHART kuwa kallo ɗaya ta masa ta kauda kai gefe tana wani yatsina da taɓe baki.
"Lafiya Alhamdulillahi, ƙwale-ƙwale ga shi nan an fito tun da shi ne hanyar cin abincin kuma bamu raina wa ubangiji hakan da ya bamu ba, a koyaushe mu masu godiya ne a gare shi dama ya ce fazkuruni azkurkum washkuruni wala takfurun, wato ku ambace ni zan ambace ku, kuma ku gode mini kada ku kafice mini"
"Allahu akbar!" EESHART ta ce .
"Yo ai ba sai ka fassara mana ayar ba mu ma ba jahilai bane" SALIMAH da ganin bai wani damu da kasancewarta a wajen ba tamkar dai ba shi ne yake cewa in babu ita ba zai iya rayuwa ba ashe dai zai rayun tun da ga shi yana lafiya babu alamar damuwa a tattare da shi harnya samu bakin magana yana faɗa musu baƙar magana wai yana godiya da matsayin da ubangiji ya ajiye shi kenan su ne basa godiya?.
"Ki bashi mu wuce" EESHART ta ce tana kallonta, jakar ta buɗe ta ɗakko katin da yake gidanda mai kwalliyar ƙyari-ƙyari ta miƙa masa. Karɓa ya yi ya fito da katin ya shiga karantawa yana murmushi har haƙoransa suka bayyana.
"Inyeee SALIMAH amarya ma sha Allah, Allah sanya albarka ya sa abokin zama ne kuma abokin arziƙin k... Ba ta jira ya ƙarasa maganar ba fuuuu ta tafi cikin baƙin ciki EESHART ta mara mata baya sun ga abin da basu yi zato ba. Shi ABBAS da ya fisu ma ko ɗago kai bai yi ba ya kafa idanu a kan katin yana murmushi a mugun guje EESHART ta ja motar don suna kallonsa ta