Showing 3001 words to 6000 words out of 61883 words
Chapter 2 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
yi yaki da zuciyata a kan in sawwake miki ko don na ga hakan shi ne farin cikin ki, amma ba zan iya ba SALIMAH, wallahi ba zan iya rabuwa da ke ba, ba zan juri rashin ki ba rasa ki tamkar rasa duk wani walwala da farinciki na ne duk da ina tare da ke ɗin ma baki bar ni na samu hakan ba amma dai da babu gwara babu daɗi ko da a ce za kike yankar naman jikina a kullum na yarda na rayu da ke na zan iya rasa komai saboda ke na aminta a hana ni komai in za a barni da ke...
"Ai kuwa wallahi ka kama RUƁAƁƁIYAR IGIYA don wacce kake so ɗin baka gabanta kuma ni zan iya yin komai don na rabu da kai kuma tun da kai babu zuciya a kirjinka zan cigaba da zame maka ciwon ido har ranar da wa'adin aurena zai cika ka sauwake mini, duniya ban taɓa ganin marar zuciya ba sai kai ABBAS ni dai ina jin sai na fara rokon Allah ya ɗauki ranka ka mutu in auri wani...
"Zan fi so hakan ya kasance ni na fi son na mutu ke ki rayu, na fi so indai bana duniyar ki auri kowa ma na san tun da bana raye hakan ba zai yi wani sanadi a gareni ba, idan har kika haifa mini ɗa wanda zai zama na bar tsatson ki a duniya wanda zai ke mini addu'a SALIMAH burina ya cika"
"Albishinka ce goro ABBAS kalli nan" Ta ce tana ɗaga hannun rigarta farin fatar dantsen hannunta ya bayyana.
"Wannan tsinken hana haihuwa ne na saka tun ana gobe ɗaurin aurena da kai na je na saka na shekara uku! Kuma bayan wa'adin shekarun sun cika na je aka cire aka mayar mini da wani na shekara ukun yanzu shekararsa biyu yana karasa shekara ɗaya zan cire in maida wani, ko shekara dubu zan yi a gidanka sai na yi ta sakawa, ku tarayyar auratayyar ma ai ka san ba da haɗin kaina kake yi ba, kai kanka ka san wata rana maganin bacci kake zuba mini a abun sha wanda bacci mai nauyi zai ɗauke ni har ka gama uzurinka ban sani ba, saboda baka gabana uzurin auratayya da kai ma bana kaunar yi, kuma ina son ka san wani abu ni dama ba zan haifi yara a gidan talauci ba rainon madara rarrafen kafet da tiles nake so ba rainon tuwo rarrafen ledar tsakar ɗaki ba"
Tun da ta fara maganar hawaye suke ambaliya a idanunsa, wani ɗaci yake ji a zuciyarsa tabbas SALIMAH ita ce kaddararsa da Allah ya ɗora masa masifaffan sonta yana hakuri da duk abubuwa da cin kashin da take masa, sai dai an zo gaɓar da ba zai jure ba an zo wajen da bai ji zai iya ba dole ya yi hukunci dole ya ɗau mataki a kan wannan mummunan laifin da ta aikata masa tana ikirarin shi juya ne ta sanya yake bin asibitoci yana biyan kuɗin gwaji ana tabbatar masa da lafiya yake ashe dai ga miciji amma yana abin ja. Bai san lokacin da hannunsa ya ɗauki hanyar fuskar SALIMAH ba sai gani ya yi ya wanke kyakkyawar fuskarta da wani wawan marin da sai da ta ga gilmawar taurari.
MAMAN AFRAH
09013181851
[1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1
*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ka/ki ya yi daidai da labarin ki to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah ya saka da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 2
Cike da tsananin mamaki take duban ABBAS jin yatsun sa biyar a fuskarta. Bakinta take son motsawa amma ta kasa buɗewa bare har ta haɗa haruffan da za su zama kalaman da za ta furta. Shi kuma ABBAS sai a sannan ya gane katoɓarar da ya yi.
'Ai ni wallahi ba a yi ɗa namijin da zai kai hannunsa jikina ba, duk ranar da giggiwar namiji ta saka ya dake ni wallahi yana sauke hannunsa ina ɗaga nawa, kuma daga ranar ya daki aurensa wallahi don ko kai ne autan maza na bar ka bari na har abada ma kuwa' Maganar wata mata ta faɗo mata a rai wata rana a gidan biki tana tsaye take jiyo maganar wasu mata guda uku da suke jajantawa wai kawarsu mijinta ya mata shegen duka. A ranar da SALIMAH ta ji tattaunarwar su take kiyasta to ita wane tsautsayin ne zai sa namiji ya kai hannu jikinta ita bata yi kalar matan da za a duka a gidan aure ba, to kuwa tabbas shi ma da ya daki auren nasa bare kuma ita dama da take neman makala wato ABBAS lallai yau mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki.
Sai da ta shammace shi ta ɗaga nata hannun ta sauke masa a fuska. Al'ajabi ne ya hana shi yinkurin komai don bai taɓa zaton SALIMAH za ta iya dukansa ba duk da shi ne ya fara taɓa lafiyarta amma dai abin akwai mamaki.
"SALIMAH ni kika mara?"
"An mare ka who are you?" Ta ce cikin halin ko in kula.
"Kuma idan har ka haifu ɗan halal ba shege ba a cikin iyayanka to ka sawwake mini"
"Na sake ki saki ɗaya SALIMAH"
"Ayyiriri yiriiii" Karan guɗar da ta saki ne ya dawo da shi hayyacinsa tare da ankara da abin da ya yi. Sai dai kalmomin da ta yi amfani da su wajen karɓar sakin ne sun zafafa sun rura masa wuta a zuciya, sai dai ba zai ce bai shiga ruɗani da tashin hankali ba na kalmar sakin da ya furta mata wacce ta fito daga bakinsa tamkar an fisgo ta.
Yaraf ya zube a kan gwiwoyinsa don ya san SALIMAH ta suɓuce masa suɓucewa ta har abada kuwa, sai dai ya ɗauki na annabawa amma da wuya ta yarda ta dawo gare shi domin abin da take nema ne shekara da shekaru ya samu.
"Innalillahi wa inna alaihi raji'un" Ya faɗi hakan a fili sai dai kafin ya ankara har ta fita daga ɗakin ya san kuwa zancen gizo ba ya wuce na koki ma'ana zuwa za ta yi ta haɗa kayanta. Daɓas ya zauna ya haɗa kansa da gwiwa yana jin yadda gabansa yake bugawa gabaɗaya ya rasa ma wane tunani zai yi shi yunwar da yake ji ma bai san ta inda ta bi ba saboda wani ciwon ya danne wani zafin rabuwa da masoyi ya fi gaban wasa.
SALIMAH kuwa wani irin daɗi da farin ciki take ji, ji take tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha, har da wata rawa ta taka a ɗakin kayanta ta shiga haɗawa a wata babbar jaka sai da ta cika ta taf da sauran kayan amfanin da za ta bukata, kafin a zo kwasar kaya, rigar jikinta ta sauya ta yafo mayafi ta ɗakko jakar ta fito a kofar falon ta ajiye jakar ta shigo falon domin ɗaukan waya, jin shigowar ta ya tashi tamkar an tsikare shi yana jin da na sanin abin da ya yi. Cajar wayarta ta ɗauka da kuma wayarta kallo ɗaya ya mata ya gane tsantsar farin cikin da take ciki.
"ABBAS saduwar alkairi Allah haɗa kowa da rabonsa yau ka biya ni" Ba ta jira cewarsa ba ta bankaɗa labulen ta fita ta ɗauki jakar sai ga shi kamar an watso shi duk ya firgice sai ma ta so ta ji tausayinsa amma dai ganin bahaushe ya ce so, so ne amma son kai ya fi sai ta ji ta fi tausayawa kanta a kan shi.
"SALIMAH don girman Allah ki yi hakuri"
"Wa? Ai in ka ganni a lahira kai ni aka yi" Daga haka bata jira cewarsa na ta juya ta fice, zaunawa ya yi a kasa yana jin zuciyarsa tana suya tabbas in akwai abin da yake kaddararsa kuma jarabawarsa to bai wuce son SALIMAH ba, akwai lokacin da ta yi yaji ta ki dawowa ba tare da wani dalili ba dama mahaifiyarta ma ba kaunar auren take ba Babanta ne mai son auren kuma ya mutu. Tsawon sati biyu ta yi bata gidan amma sai da ya kwanta jinya hatta aikin kafinta ba ya fita, wata rana idan ya je gidansu SALIMAH aka ki kula shi kan maganar bikon sai ya zauna a kofar gidan ya wuni sallah ce kawai take tashin sa daga wurin idan ya yi ya dawo saboda kawai jurewa ya yi ta yi amma ya san ya azabtu da rashinta. Wasu hawaye ne masu zafi suke masa ambaliya a fuska tabbas ba kowa zai gane irin hali da raɗaɗin da yake ciki ba sai wanda yake cikin halin da yake ko wanda ya taɓa shiga irin halin.
'A kullum addu'a ta shi ne in rayu a duniya ɗaya da SALIMAH duk duniyar da babu SALIMAH sai in ji tamkar dai makabarta ce, amma yau kaddara ta gifta kaddara wacce take rubutacciya don in ba kaddara ba ba na jin akwai ranar da ni da bakina zan furta kalmar saki ga SALIMAH amma rubutacciyar kaddara wacce ba ta goguwa domin irin wannan kaddarar ita ce ake kira kaddara wacce ta riga fata, na san wasu za su ji haushina wani ya ji kamar ya hau ni da duka wani kuwa zai ga ai so ba hauka bane sai dai kash! Bai san irin ɗinbin so da kaunar SALIMAH da suke dankare a tawa zuciyar ba ni ban taɓa cin karo da irin son da nake yi wa SALIMAH ba, ko da kuwa a labari ne son da nake mata ya fita da ban ya fi karfin zuciyata, da ce SALIMAH za ta bukaci in ɗaye fatar jikina in bata babu wani dalili da zai sa in kasa ko da za a saka bakin bindiga a kaina a ce in sake ta ko a harbe ni, to tabbas ba zan furta mata kalmar saki ba amma yau tsautsayi wanda ba ya wuce ranar sa ya sa giyar fusata da gajen hakurin ɓacin rai da kasa jure kalamanta uwa uba shaiɗan mai amfani da dama idan mutum na cikin ɓacin rai ya ci galaba a kaina' Ya furta a zuciyarsa yana haɗa kai da gwiwa ji yake duniya ta masa kunci tabbas yana cikin matsatsi.
"Don Allah ki dawo gare ni SALIMAH" Ya furta a fili da karfi har jijiyar wuyansa tana bayyana raɗo-raɗo, yana mai fashewa da kukan tausayin kansa.
*SALIMAH*
Cikin wani farin ciki ta fito daga gidan kofar gidan ma a buɗe ta bar ta ko darajar rufewa bata samu ba, ji take tamkar ta taka rawa ji take rabon da ta ji ta cikin annashuwa tun ranar da aka ɗaura mata aure da ABBAS, tun daga wannan rana ta tsinci kanta cikin wani yanayi tun daga wannan rana wani abu ya tokare mata makoshi abin nan da ya tokare ta bata taɓa jin ya gushe daga wurin ba sai yau da ABBAS ya furta mata kalmar saki abin dai tana jin sa kamar almara sannan kuma sai take jin tamkar a mafarki.
Duk da soyayya suka yi da ABBAS ɗin sai dai ita ta kauna ce shi ne saboda kyau da yake da shi duk cikin maneman ta babu wanda yake da kyansa, kuma babu wanda ya haɗa duk abin da take bukata daga ɗa namiji kamar ABBAS su dai sauran kuɗi da manyan motoci da gidaje za su faɗa masa shi kuma Allah ya mallaka masa komai da mace za ta so ga ɗa namiji matsalarsa ɗaya cikas ɗinsa ɗaya mugun talaucin da ya kanannaɗe shi ya masa dabaibayi. Manyan alhazan da take kulawa masu hannu da shuni suna kashe mata kuɗaɗe jikinta suke so, don sun sha zuwa mata da kalmar ɓatanci amma ta ki bada haɗin kai, shi kuma ABBAS kaunarta yake da gaskiya wannan dalilin ganin yana jumuri da jure duk wani abu da za ta masa kuma nutsatstsan matashi mai girmama na gaba, uwa uba ibada da tarbiya hakan ya sa mahaifinta ya dakatar da kowa daga zuwa wurinta ya ce ABBAS zai aura mata. Ta yi kukan bakin ciki tun daga ranar ta ji ta tsani ABBAS kyansa da take gani ya koma mata muni domin ta fi kaunar kuɗi da morewar rayuwar duniya a kansa.
Kamar kumbo kamar katanta yadda abin nan yake a wajen SALIMAH haka yake a wajen mahaifiyarta, bakin su ɗaya ita ma duniyar ce a gabanta, don duk abin da mahaifin SALIMAH zai faɗa mata a kan rayuwar duniya da bin duniya a sannu da dai nasihu masu bin sassan jiki da shiga zuciya, yana tufka ne mahaifiyarta tana warwara abin da zai faɗa mata da ban wanda za ta faɗa mata da ban, idan ya biya mata karatun ta nutsu sai mahaifiyarta ta goge hardar. Har ya bar duniya bayan auren da watanni uku a sannan ne ruwa ya karewa ɗan kada domin kuwa sun bi duk hanyar da za su bi wulakanci kala-kala a kan ABBAS ya sake ta amma ya ki yau dai ga shi buri ya cika.
Tafiya ta fara yi tana rike niki-niki da jakar kayanta, sai murmushi take, sai sannan kiran kawarta EESHART ya faɗo mata da sauri ta kamo sunanta ta danna mata kira ringin ɗaya biyu wayar ta yi ta ɗauka.
"Hlo kawata...
"Albishirinki ce goro" Ta katse mata maganar tana dariya.
"Goro fari tassss" Ta ce cikin zakuwa da son sanin dalilin shigar kawar tata cikin wannan farin ciki, saboda bata yi wani tunanin komai ba.
"ABBAS ya rangaɗa mini saki EESHART yau ya warware wannan doguwar igiyar kaddarar da tsofaffin nan da shedu suka taru suka talaulaye ni da ita" Ta ce hakoranta talatin da biyu a waje.
Alhaji ALI da suka shawo kwanar layin yana waya, da ita ya fara tozali ganin dariyarta sai ya saka shi cikin wani yanayi har ya shagala da kallonta har suka zo saitin ta yana kare mata kallo tabbas ya shaidata ita ce dai ta safen nan da ya gani lokacin da suka fita.
"Eh, dariya, kyakkyawa" Ya ce a wayar saboda gabaɗaya ya ma sha'afa da abin da suke magana a kai. Daga ɗaya ɓangaren aka katse shi da mai yake nufi sai sannan ya dawo hayyacinsa don hatta direban sai da ya gane cewa Alhajin ya yi suɓutar baki, dariya ce ta so kwace masa amma gudun yi laifi sai ya danne, don ya lura da wacce yake kallo yana ganinsa ta madubi.
"Ke SALIMAH bana son wasa wallahi ai ko za ki yi wasa da komai ban da wasa da sakin ABBAS don na san wannan ɗan a nace ɗin ba zai sake ki ba"
"Wallahi kawata da gaske nake da bakinsa ya furta kin ganni har na haɗo kayana na baro masa agwajan gidansa, kin ga shi ma ya huta da da biyan kuɗin haya"
Wani ihu EESHART ta saka don ta rasa ma ina za ta ajiye wanna magana mai daɗi.
."Barka kawata na taya ki murna Allah mana tsari da auren masu dattin hula ƴaƴan malam shehu to ina dalilin auren talaka "
."Wallahi kuwa ai yanzu sai na zaɓa na darje"
"Hahaha wallahi kuwa kawata kina lokaci" Ta ce tare daɗa fashewa da dariya.
"Bari in na je gida ma yi waya so nake in je in yi wa Umma albishir ita ma ta ɗanɗani wannan farin ciki" Da to ta amsa mata tana mai kashe wayar sosai take ji da EESHART yadda take kaunarta tana bata shawarwarin yadda za ta kuɓuta daga auren ABBAS ta yi auren da za ta ji daɗi ta huta, sai dai bata san cewa ba turba mai kyau ba ce haka ba kuma hanya mai ɓullewa ba ce illa iyaka RUƁAƁƁIYAR IGIYA ce.
Alhaji ALI kashe wayar ma ya yi don ba ya so yake kwariɓi a waya, sai ya ga gwara ya bari idan ya zauna ya nutsu ya yi wayar. Raja'a ya yi da kallon SALIMAH da take waya har aka buɗe get ɗin bai sani ba sai da direban ya durfafi cikin gidan sannan ya dawo hayyacinsa. Ganinta yake tamkar ba bahaushiya ba sai ka ce wacce take ɗaya daga cikin ukun nan, larabawa turawa ko indiyawa saboda yanayin farin fatarta kamar ba na africa ba.
Napep ta hanga ta ɗaga masa hannu tahowa ya yi sai da ya zo saitin ta ya ja birki.
Jakar ta saka a cikin napep ɗin, tana shirin shiga kamar an ce ta ɗago kanta ai kuwa ta hango ABBAS ya fito daga gidan tamkar zararre kafarsa ko takalmi babu uwa uba fuskarsa da hawaye, da sauri ta yi saurin shigewa napep ɗin.
"Malam ja da sauri mu tafi kar wancan ya karaso na ga ya yi kama da mahaukaci kar ya warce ni ya mini duka" Ta ce tana hango yadda ABBAS ɗin ya rugo da gudu zai zo wajensu ganin da ya yi ta shige. So yake ya zo ya gwada sa'arsa ko za a dace duk da ya san da wuya wai gurguwa da auren nesa.
Mai napep kuwa kallon tsoro ya jefi ABBAS ɗin da shi