Showing 24001 words to 27000 words out of 61883 words
Chapter 9 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
ta ɓangarori da dama, shin an faɗa miki a banza nake son na yi aure a daula?" Ta yi maganar tana kafe ta da ido alamar tambaya.
"Sai kin faɗa na ji ai ba zan sani ba tun da ina cikin duhun kai da rashin wayewa kaina yana rufe a tukunya" Ta ce cike da gatse, amma da yake ita SALIMAH dukan iska ce bata gane magana BASEERA ta faɗa mata ba. Murmusawa ta yi ta ɗaga hannunta ta ɗora a kafaɗar BASEERA ta ce
"Yanzu da jike gani duniya ta lalace, idan kana da kuɗi kai ne mutumin kirki a idanun mutane ko da kuwa ka fi kowa rashin mutunci da halayen kyama, yanzu ba a duba wani hali kake da shi illa iyaka ana duba mai kake da shi mai ka tara? In har kana da kuɗi a gidanku kai ne babba ko da kuwa kai ne autan gidan, in kana da kuɗi ko shawara sai an jira ka zo za a yanke idan kuwa ka ce ga yadda za a yi babu mai canjawa. In aure ka je nema ko da an san duka kake wa matarka ta gidan ko kuma kana wulakantata to fa ba za a ga wannan ba ko wani ya yi yunkurin faɗar aibinka to cewa za a yi bakin ciki yake, yanzu akwai kawayenmu wanda muka taso tare tun da suka yi aure a gidan daula shikenan ko a hanya muka haɗu kallon arziki ba ma samu, a takaice ko biki kika je ko suna kina dosowa kafin ki karaso zugar matan da suke wurin za su shiga karewa suturarki kallo tun daga tsakiyar kan ki har yatsan kafarki sai an kalla daga nan za a gane wacece ke idan aka ga kin gaza ta ko ina kina karasowa idan akwai wanda kika sani za su ɗauke kai, idan kuwa sutura kika saka ta kece raini kina zuwa za a washe baki kowa yana kokarin miki magana wannan ne manyan dalilan da suke ci mini tuwo a kwarya, su ne suke sa burina yake karuwa ina so in ci mai kyau in kwanta mai kyau ni soyayya baya dame ni ba ko kasancewar miji na gari, kuma ƴaƴa ma idan suka taso suka ga talaka ka zaɓa musu sai suke ganin abubuwan more rayuwa wajen wasu amma in ka zaɓa musu attajiri ɗif za ki ji kowa yana ji da su a dangi"
Tun da ta fara dogon jawabin nan kallonta kawai take tana tunanin sabo da wannan ne ta kira ta kanta yana tukunya tabbas idan haka ne kuwa ta kama RUƁAƁƁIYAR IGIYA.
"Duk wannan ba gaskiya banr idan kuwa gaskiya ne ya keɓantu ga wanda suke da gajeran tunani da rashin tauhidi, ai zama na gari ya fi komai a rayuwa, kuɗi suna karewa talauci ya baibaye mai su sai ki ga ya zama tamkar ba shi ne mai kuɗin nan ba da yake ta facaka, shi ma talaka arziki yana zuwar masa sai ki ga Allah ya azurtashi tamar bai taɓa neman taro da kwabo ya rasa ba, ƴaƴa kuma uba na gari da shi ake ado, idan har dukiya gare shi yana da hali marar kyau wata rana sai an goranta musu wata rana sai sun tuhumi mahaifiyarsu da maganar ko tambayar da za ta nemi amsar basu ta rasa"
"Ba za ji gane ba, shi ya sa na ce a duhu kike".
"Ko kuma ke ce a duhun ba".
"Ni a haske nake kuma ni idan na tashi sai na auri mai dukiyar da koginta ba zai taɓa kafewa ba kin ga na yi ban kwana da talauci, ke ni fa saboda ba na son haihuwa gidan talauci ka taso babu ta baibayeka kai da yaran da uban ko asibiti za a kai yaro ana cewa ku je asibitin sai ki kawo katin idan na yi buga-buga na samo sai a saya maganin, in kin tambaya kuɗin cefane a ce babu a duniya na tsani kalmar babu nama kuwa daga sallar layya sai wata layyar ina dalili"
"Allah shirye ki ya ganar da ke".
"Ai kuwa ba zan gane ba, ke dai ce nake so ki gane bari sai na yi aure zan kara fahimtar da ke, shi ya sa na saka inplan a gidan ABBAS kar na haihuwa abubuwa su caɓe mutumin da ko gidan kansa ba shi da shi, sai aikin kafinta ni karatun da ya yi ma ban ga amfaninsa ba wai mai digiri amma ya ajiye takardu saboda ba aiki yana fama da kusa da katako" Ta ce tana yatsina fuska da taɓe baki.
"Allah zai bashi" Ta ce cike da takaici don ba za ta iya cigaba da tattaunawa da SALIMAH ba saboda ta yi nisa ba ta jin kira in ban da toshewar basira har ta saka inpan lallai abin mai girma ne ba karamin gaba take yi da talauci ba tana mantawa Allah ne yake azurtawa kuma shi yake talautawa. Bata wani kara jimawa ba ta mata sallama za ta tafi saboda takaici, har kofar gida ta rako ta suka yi sallama ta tafi tana shirin shiga gida sai ga RUKY tare suka shiga gidan suna tattaunawa.
"Wallahi RUKU har alla-alla nake na kammala iddar nan ko na fara tara zawara wa in ke kashe kala, don ni da na samu mai kumbar susa ba zan tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mini kafa ba"
"To ai ba a nan gizo yake sakar ba SALIMAH, zuwan zawarawa ba shi ne auren ba, bare ke da kike da kyau da kirar nan ai sai an miki layi sai dai...
"Kamar ya? Dama ai na san abu mai kyau shi yake siyar da kansa a kasuwa, amma sai dai mai?" SALIMAH ta yi saurin katse mata magana.
"Abin da nake so ki sani na gari sun yi karanci, yanzu za ki ga tarin zawarawa amma ba da aure suke zuwa ba"
"Da mai suke zuwa to?"
"Don a yi soyayya kawai"
"To ba amfanin soyayya aure ba".
"Hmmm! A baya kenan amma a wannan zamani akalar ta canja, kalilan ne masu zuwa da auren kuma wahala suke, daga namiji ya zo rimi-rimi sai ki ji ya fito fili ya faɗa miki holewa ce ta kawo shi, ku kunya ma ba sa ji ke wani fa sai ki ji ya kama miki hannu ba da izininki ba in kika masa magana zai ce ai ba komai bane, saboda yanzu zina ma ba ɗauke ta a bakin komai ba ado aka ɗauke ta duniya ta lalace kuma ta zo karshe"
.."Ikon Allah, to amma sun san matan da suke wa ko?"
"Kamar ya ai abin ya zama ruwam dare gama duniya, sai ko ga babban mutum yana baza babbar riga a girme zai haife ki amma ya zo miki da magana ta banza"
"Sai ka zaɓi wanda basu da irin halayyar nan, kin san a duniya na tsani zina na tsani mai yinta ko abin da zai kusanta ni da ita"
."To kuwa ki shirya saboda haɗuwa ɗaya biyu za ki ji ya anbata miki so yake ku keɓe, ko ya ce yana so ku je hotel ku huta".
.
"Haba dai wasa ma ai wargi yake ai bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane"
.
"SALIMAH duniyar nan fa da kika sani shekaru biyar baya kafin ki yi aure ba ita ba ce a halin yanzu, duniya ta lalace wallahi, yadda bakya zato yanzu tsawon shekara uku da aurena ya mutu ina gida amma har yau na kasa samun tsayayye, kowa ya zo ba da maganar aure zai zo ba, yanzu ƴanmata ma gasu nan duk suna zaune a gida amma miji ya kasa samuwa bare bazawara, na bari SANUSI tsohon mijina ya suɓuce mini yanzu na zo ina da na sani da son komawa gidansa amma shi kuma yanzu ba ta ni yake ba ya samu wata ya aura"
"Kowa da farin jininsa bari ki ga in yi idda zan baki mamaki"
"Hmmm! Kin kasa fahimtata ina nuna miki maza za suke miki tururuwa amma ba da aure ba ko maganar aure kika yi wa mutum sai ya janye kafarsa, idan suna zuwar miki da hulewa kika nuna ke ba haka ba da kaɗan-kaɗan za su dare su barki"
"Ki zuba ido kawai BASEERA kin san dai irin tarin farin jinin da na yi ina budurwa yanzu sai na kere" Ta ce tana wani murmushi.
."Wallahi da za ki ji shawarata da baki bari kin yi idda ba tun kina da sauran dama ki koma ɗakin ki, ba za ki gane mai nake nufi ba sai kin fara zawarcin"
"Allah mini tsari kuma za mu ɓata idan kina mini maganar komawa gidan ABBAS" Ta ce tana jan wani tsaki.
"Shikena SALIMAH tun da haka kika ce amma akwai ranar da za ki tuna da wannan tattaunawar"
"Wai ya maganar Alhaji ma'ilu naki?" Ta jefa mata maganar don son kawai da wancan maganar.
Shiru BASEERA ta yi tana tuno yadda suka rabu jiya baran-baran saboda kawai suna hira a mota sai ji ta yi ya rungume ta dakyar ta kwaci kanta, bayan shi kaɗai ne take ganin ta samu mai tsoron Allah ashe dai shi ma lumbu-lumbu ne wutar kaikayi, wannan dalilin ne ya sa ta zo don ta bayyanawa SALIMAH cewa ta rasa wanda za ta zaɓa ta aura amma ta ki fahimta ita yanzu damuwarta ta samu wanda zai aure ta amma abu ya gagara. Ga shi ita mace sai ta jira an ce ana son ta ba wai ita ce za ta je ta zaɓa ba ta ce tana so. Ita gabaɗaya sai yanzu ta gane aure ba karamar sutura ba ce ga mace sai yanzu da ta fito don takaici sai a mayar da mace kamar karya kowa ma sai ya zo ya ce yana sonta, kare da doki wani ma sa'an kanenka ne za a ce yana sallama da kai kana fita ka ga yaro a tsaye wai sonka yake tabbas akwai takaici da kalubale a rayuwar zawarci.
"Ko bai zo ba jiyan na ga muna nan a tare ya kira ki yana zuwa"
"Ya zo amma na sallame shi"
"Ke ko saboda mai bayan kin tsayar da shi"
"Saboda shi ma kamar sauran yake abin da yake kawo sauran shi ma shi ne ya kawo shi, kwantan ɓauna ya yi shi ya sa bai fahimta ba, duk na sallami kowa na rike shi ashe dai RUƁAƁƁIYAR IGIYA na kama"
"Ikon Allah to Allah kawo miki wani"
Shiru ta yi bata ce komai ba.
"Ba za ki amsa da amin ba"
"Wallahi SALIMAH na rasa wane kalar tunani zan yi, a zatona idan na yi idda ba zan wuce wata biyu ban yi aure ba, amma kin ga har shekara uku na rasa mai aurena kullum jiya i yau, ga yarana ba bar su gidan ubansu kullum idan suka zo wurina sai na zubar da hawaye saboda sun yi baki sun rame ko kaɗan ba sa cikin farin ciki ko walwala matar ubansu ta sako su a gaba basu da ƴanci uban nasu ma bai damu da su ba. Kin san mata nu ne natsalar kan mu da kan mu, idan kika samu yara gidan ubansu don kin aure shi maimakon ki rike su da amana amma sai ki ɗau tsana ki ɗora musu kike kishi da su kina gana musu azaba na yi da na sanin fitowa daga gidan aurena ga shi na yi saki na dafe a kan karamin abu na kasa hakuri har sai da na ga na kashe auren yanzu abin yana damuna na yarda duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba zai godewa azabarsa, yanzu ina so in koma in rike yarana amma bani da wannan damar"
Ajiyar zuciya SALIMAH ta sauke jin abubuwan da RUKY ta zayyano mata, duk da bata wani ji maganar ta shige ta ba amma dai ta ji babu daɗi amma tunaninta ya bata cewa RUKY don ba ta kai ta kyau da diri bane ta kasa samun tsayayye amma ita tana ganin babu mai kawo mata wargi a nata zawarcin.
09013181851
[1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 8
*ABBAS*
Ya sha yaki da zuciyarsa kafin ya samu zafin so da na rabuwa da SALIMAH ya sassautu a zuciyarsa haka ya danne ya hakura ba don ya so ba sai don haka Allah ya tsara masa kaddararsa kuma bai isa ya guje mata ba. Sai da Mama ta dage da addu'a da nasiha sannan ta samu ya dawo hayyacinsa, addu'a sallar dare da karatun qur'ani wanda ya kasance magani kuma waraka ga dukkan komai, a hankali nutsuwa ta saukar masa a ruhinsa har ma ya ji son na SALIMAH ya kwanta masa a zuciya tun da yanzu sai ya wuni ma bai fi ta faɗo masa sau ɗaya a zuciya ba kuma ko da ta faɗo masa yana kokarin kawar da tunaninta a zuciyarsa, da kuma nesanta kansa da yake sa zaman kaɗaici domin zaman kaɗaici yana sa mutum yake tafiya tunani.
Gabaɗaya kayansa na gidan ya kwashe su ya kaura gidan Mama, dama yanzu kuɗin hayar ma ya kare, ganin ya dawo daidai sai ya ɗaura ɗamarar komawa bakin aikinsa, tare da kudurtar zai yi aiki tukuru tun da yanzu babu wani mai ɗaga masa hankali ba kamar a baya ba idan zai tafi aiki ta ɗaga masa hankali haka idan ya dawo yana wurin aikin zuciyarsa bata huta ba. Sai dai kash! Duk buri da kudurin da ya ci na yin aiki sai da ya je wurin ya tarar da abin da ya karya masa zuciya, wato kayan gadon da SALIMAH ta je wurin ta siyar, da kujerun ko kallon wurin ya yi sai ya ji wani rauni a zuciyarsa, musamman idan ya kalli kujerun sai take masa gizo yana hangota zaune a kan kujera kamar yadda yake samun ta idan ya shigo gida.
Ko mudubin ya kalla hangota yake tsaye tana gyaran gashi kasancewarta ma'abociyar gyara gashinta. Da farko ya yanke shawarar canja sana'a sai da FAROUQ ya hau kansa da faɗan yana nuna masa ita tana can ta manta da shi amma shi yana nan yana wani maganar fasa sana'arsa saboda kawai ya ga kayan ɗakinta, ita kuwa dama SALIMAH da gayya ta yi hakan saboda tsabar rashin tausayi. Irin furucin da FAROUQ ya yi ta amfani da su hakan ya saka ya dake zuciyarsa sai ya zo wurin ya tafi ma amma bai ko kalli kayan ba har aka zo gaɓar da ko ya kalli kayan ba ya jin komai, har dai Allah ya kawo wanda suka siye kayan ma ko a jikinsa ma lokacin don yanzu kam ya fara aniya da ɗamarar haka rami ya binne duk wani son SALIMAH da yake addabar zuciyarsa.
Aiki yake tukuru a rana sai ya yi aikin dubu goma kasancewar yanzu ba shi da wata damuwa sai wacce ba a rasa ba, saɓanin da idan ya zo hankakinsa yana gida idan ta kira ta a waya ba za ta ɗaga ba idan ya dawo gidan ma babu kwanciyar hankali wannan dalilin ya sa yanzu ya kara gane cewa ka samu mace ta gari mai sonka wacce za ta faranta maka shi ne samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
*HAWWA*
Kwana biyu a tsakani da faruwar abin na ganin kwalabe giya a ɗakin Yaya Umar sai ga shi ya shigo gida da gabannin magrina a buge ya sha giya ya yi tatul. Sosai Hajiya ta shiga tashin hankali tana kuka wiwi kamar matar marigayi.
"Na shiga uku yanzu Umar abin naka har ya kai ga shan giya? Ni duk tunanina ɗan kodin nw kawai kake afawa ashe har da giya da kwaya wannan wace irin rayuwa ka sa kan ka?" Ta ce tana rusa kuka ganin ya kwanta male-male a tsakiyar falon yana ta wani surutai cikin muryar bugaggu ga kuma kwaya nan da tje jimke a hannunsa.
"Ke ma in za ki sha kwayar ai sai ki karɓa ni ba hana ki zan yi ba, akwai ma giyar a ɗakina a kasan gado sai ki ɗakko ko da kwalba goma kike so" Ya ce cikin muryar maye yana mika mata kwayar. Jin furucinsa na cewa akwai kwaya a gidan sai hankalinta ya kara tashi, ko ta kan kwayar da yake miko mata bata bi ba ta yi hanyar ɗakinsa a kiɗime cikin tashin hankali tana zuwa ta ga ɗakin a rufe a 360 ta dawo duk ta fita hayyacinta wannan ahi ake kira tashin hankali wanda ba a saka nasa rana da lokaci. Cikin kukan ta da ta kasa rikewa ta kama wandon Umar ɗin ta saka hannunta a aljihinsa za ta ɗakko mukullin ɗakin nasa.
"Wai waye yake saka mini hannu a aljihu zai mini sata, to wallahi zan sa kulawa(Ƴan sanda) Su kama mutum" Ya ce yana mika hannu ya dafe hannun Hajiya da yake aljihu za ta ɗakko mukulli.
"Ubanka ne, na ce ubanka ne, sakaran banza da baka san inda yake maka ciwo ba" Ta ce lokacin da ta saka ɗaya hannunta ta ɗaka masa duka a hannun da ya danne hannunta da yake cikin aljihu. Yana