Showing 12001 words to 15000 words out of 61883 words

Chapter 5 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10808

lafiyarta.


"BASEERA yau dai ABBAS ya yanke igiyar aurenmu na huta da alakakai"


"Subahanallah! Yanzu sai da kika yi yadda kika yi kika kashe aurenki, darajarki da kimarki ɗakin mijinki, wannan rayuwar da ake ciki a irin dagulallan zamanin mai cike da ruɗu samun miji managarci ma wahala yake, maimakon ki rufawa kan ki asiri ki rabu da tunanin ruɗin duniya mijin ki yana son ki yana kyautata miki sai abin da kike so yake yi ki juya shi kamar waina a tanda, mai mace take nema da ya wuce abin da kika samu? Wasu fa malamai da bokaye suke bi don su samu waɗannan abubuwan amma ke ba boka ba malam Allah ya mallaka miki, amma shi ne kika yi watsi da ni'imar Allah, kina bin gurguwar shawarar zuciyarki da ta kawaye suna ɗora ki a keken ɓera, ke baki san RUƁAƁƁIYAR IGIYA kike kamawa ba...


"Dakata! BASEERA wai ce miki na yi na gama aure a duniya ne? ".


"Baki ce mini ba amma dai ai auren mai kuɗi ne da kike kwaɗayin yi ya sa kika raina naki mijin, shin wai ke baki san cewa kuɗi ba su ne rayuwa ba, kuɗi ba su ne farin ciki ba, to wallahi mafi yawan wanda suke cikin daula wasu basu da kwanciyar hankali, ga komai sun samu gida mai kyau mota su hau wacce suke so kuɗin su yi facaka, ga sutura sai wacce suke so ga ƴan aiki nan bila adadin suna musu hidima su ci mai kyau su kwanta mai kyau, amma da za ki duba rayuwar gidan cike take da tarin matsaloli da kalubale, wata da za a bata zaɓi in dai za ta auri talakan da za ta samu kwanciyar hankali to ta gwammace ta bar daular da take ciki. Wata mijin ma ba shi da lokacin ta wata ta yi hannun riga da farin ciki abubuwa dai barkatai ga su nan ke idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, amma ke ki raina taki ni'imar kike hangen na sama da ke? Idan mutum yana son ya gane ni'imar da Allah ya masa to kar ya dubi na sama da shi ya dubi na kasa da shi, shi inda mutum yake buri da kwaɗayin samu ai hangen dala ba shiga birni bane, akwai abubuwa barkatai da baki ba zai iya faɗinsu ba" Gabaɗaya ran SALIMAH ya gama ɓaci kwata-kwata wannan dogon lissafin da BASEERA take mata shi ne ya sa take raba hanya da ita, shi ne dalilin da ya sa ko magana bata san faɗa mata ita kullum nasiha tamkar malamin da ya hau minbarin wa,azi sai ka ce ita ce mikiya mai hangen nesa.


"Fakyakul kairan auli yasmut" Shi ne abin da SALIMAH ta tura mata bayan ta gama jin dogon voice ɗin.




Haushi ma ya sa ta kashe datar ta sauka, tun da har lokacin ita EESHART bata mata replay ba, dama a rashin uwa ne ake uwar ɗaki, da a ce EESHART ta mata magana sun cigaba da tattaunawa da babu abin da zai sa ta taɓo ustaziyar wannan wato BASEERA dama EESHART ɗin ce tasu ta zo ɗaya don ko wasu daga cikin kawayenta haushin ta suke ji a kan yadda ta auri kyakkyawan miji managarci mai cikar haiba da kamala yake son ta da nuna kulawarsa a gare ta wannan ya sa wasu duk suka janye jiki daga gare ta don kowacce so take dama a ce ita ce ta samu wannan damar. Suna ganin sun auri ɗan dukununu ga baki ga bakar zuciya amma ita ta samu fari mai farar aniya da kyakkyawar zuciya.




*WASHE GARI*




Tun da asuba da Umma ta idar da sallah ta hura wuta ta ɗora katuwar tukunyar ruwan koko. Ita kuma SALIMAH tana idar da sallah ta koma ta kwanta.


"Ke SALIMAH tashi kike iza wutar kokon nan idan ya tafasa ki dama, zan tafi in kai markaɗen kosan nan" Umma ta ce tana ɗaɗa mata duka a kafa. Ɗif ta yi tana jin wani ɓacin rai in akwai abin da ta tsana a duniya bai wuce a ce an hana ta bacci ba, da a gidanta ne idan ta kwanta ko mene ne sai dai ABBAS ya hakura da tambaya saboda kar ya tashe ta sai ta yi bacci son ranta take tashi amma ga shi tun da farar safiya Umma za ta ɗaga mata hankalo. Wani dukan ta sakar mata a kafa tana cewa.


"Wallahi kar fa in tafi ki koma bacci, ki tashi gari ya waye tangararai ana jimawa masu siyan kokon za su fara zuwa" Ba don ta so ba ta tashi tana murtsuke ido ta fito tsakar gidan ta wanke fuskarta, kujera ta ɗakko ta zauna tana iza wutar ga uban hayaki duk ya turnuke da yake iccen ɗanye ne. Haka ta cigaba da fifitawa idanunta yana ruwa, ita rabon da ta fifita wuta ma ta manta tun yajin da ta yi ta zo gida sai ko idan ta zo gida Umma ta ce ta iza wuta, duk talaucin ABBAS da take gani amma da gawayi take girki bai taɓa siyan ita ce ba, sai dai da sallar layya in ya saya ma kuwa shi yake suyar don cewa take ita bata son zuwa wurin hayaki.


Sai da ta dama kokon ya sha iska ta masa gasara sannan Umma ta shigo lokacin har an fara shigowa siyan koko, ita ta zauna tana zuba musu kokon tana ɗaura sugar, ita kuma Umma ta ɗora kasko ta fara soya kosan.


Sai da kokon ya kare ta ɗauki wanda ta zuba a karamin kofi ta sa sugar ta zuba kosan a plate, ɗaki ta shiga tana ci. Bayan ta gama ta share gidan ta hau wanke-wanke wanda a gidanta duk da ba wasu kwanuka ba ne sai da ta matsawa ABBAS ya ɗauka mata mai shara da wanke -wanke.




Da yamma ta shirya ta yi wa Umma sallama a kan za ta je gidan EESHART.


"Ni ban ji kuna waya ba ma tun da kika zo, ku da kun saba kamar saurayi da budurwa ko yaushe kuna waya"


"Ba ta jin daɗi ne wayar ma bata fiya amfani da ita ba" SALIMAH ta samu kanta da sharara karya.


"Subhanallah, Allah sawake ki ce ina mata sannu" Umma ta ce tana jimantawa. Da to ta amsa ta fito ta kama hanyar gidan EESHART a kafa ga shi da nisa sai dai bata da kuɗin hawa napep kuma ba ta son tambayar Umma don yanzu za ta fara mata lissafi, kuma ma da ta san bata da kuɗi ai sai ta bata ba sai ta tambaya ba tun da jiyan ma ta san da ta zo a wajenta ta karɓi kuɗin napep ɗin. Tun da take tafiya ake mata magana amma sai ta ce tana da aure ganin bata gama idda ba kuma ma dai masu tsayar da ita ɗin dai dama a mota suke tsayawa ita kuma duka motocin burinta ya fi karfin su, dama da a ce ta samu wanda ya mallaki tsadaddiyar mota da ta sanar da shi auranta ya mutu sai ta bashi lambar wayarta idan ta yi idda sai ya shiga sahu.




A gajiye tikis ta karasa gidan EESHART saboda sanin da da mai gadin ya yi bata wani sha wahala wajen shiga gidan ba. Ƴar aikin EESHART ɗin ce ta mata iso zuwa falon ta kawo mata lemo da ruwa da kofi, bayan ta sanar da EESHART ɗin zuwan SALIMAH. Shiru-shiru tana zaune sama da minti ashirin amma babu alamar EESHART ɗin za ta fito.


"Kin ce mata ni ce kuwa?" SALIMAH ta tambayi ƴar aikin tana kallonta.


."Eh na faɗa mata"


"Ko wani abun take yi?"


"A kwance take tana danna waya" Sosai mamaki ya cika SALIMAH sai ta ma rasa wane kalar tunani za ta yi, tana ta tunanin manufar kawar tata amma bata gane komai ba.


"Je ki kara tuna mata ce ina jiranta" Ta kara faɗa mata ganin zamanta ma wajen sau huɗu ta kira ta amma bata ɗauka ba.




Da to ta amsa mata ta koma ɗakin sai ga ta ta fito jikinta sanyi kalau, da alama amsar da aka bata ce bata mata daɗi ba da alama ma ko koro ta EESHART ɗin ta yi amma kuma sai ta kirkiri murmushin yake ta ce mata tana zuwa ta fita daga falon. Sai da aka ɗauki kimanin minti biyar sai ga EESHART ɗin ta fito sanye take cikin dakakkiyar shadda da alama ma yau ta fara saka shaddar ta sha ɗaukin ɗankwali ta fito tana wani takun kasaita. Ko irin murnar da take nunawa idan ta zo gidanta yau bata nuna ba, zama ta yi tana mata magana ba yabo ba fallasa.




"Haba EESHART wai mai yake damunki ne, tun jiya nake miki magana a whtsapp amma shiru har a group na sanar miki na ajiye miki sako amma baki buɗe ba bare ki mini replay".




"Ayya kin ga mantawa na yi ya kike ina Umma, don ba a ce miki ina mijinki ABBAS ba tun da yanzu bazawara ce ke baki da aure" Sasai ta yi mamakin kalamanta jin kamar ma har da gori take mata wai ta zama bazawara duk da ba son ABBAS take ba amma sai ta ji wani iri wani banbarakwai wai namiji da suna hajara.


"Haba EESHART mu da dama burinmu kenan samun sakin to don ya sake ni na zama bazawara ai ba wani aibu bane, ba ma wannan ba duk kiran da na miki yanzu amma baki ɗaga ba zamana a nan ma kusan minti talatin amma kin yi ɓatan dabo a cikin gidan"




"Ayya sorry fa ina can tare da baby nah ya saka ina masa tausa, kin san matar aure" Ta ce tana mata wani kallo mai haɗe da murmushin da ta kasa gane inda ya dosa ko dalilin yin sa.


Ɗan jim kaɗan ta yi tana nazarin maganganunta, da kuma maganganun ƴar aikin EESHART ɗin da ta ce tana kwance tana danna waya kuma ita kuma ta ce tana wurin miji har da faɗa mata abin da take yi a wajen miji.




"Kai kawata kina wuta wallahi" Ta ce tana dariya don kawar da maganar da EESHART ɗin ta yi da wacce ƴar aikin ta yi don kar ta ba kanta wahala, tun da ma ba daga ɗakin mijin ta fito ba.




"Ke ko" Ta ce tana ɗan darawa.


"Wai ni ko maganar sakin da aka yi mini jiya baki mini ba, kuma ko ki tuntuɓe ni"


"Ki mini uzuri abubuwa ne suka sha min...


"Aysha wai mai ya sa bakya jin magana ne, ba na ce in na ajiye abu a daina canja mini waje ba? amma saboda raini sai an taɓa" Mijin EESHART Alhaji Yusuf da ya sakko daga saman bene bai gama sakkowa ba ya faɗa cikin hargowa. Ɗan diriricewa ta yi saboda ganin SALIMAH tun da bata fiya zuwa gidan idan mijinta yana nan ba idan kuma ta same shi ma to wata rana har ta tafi bai fito ba.


Maimakon ta bashi amsa jiki yana rawa kamar yadda ta saba, sai ta tashi cikin kissa da kisisina tana son ta tabbatarwa SALIMAH irin abubuwan da take faɗa mata na tattalinta da mijin nata yake yi, don tana nuna cewa ita ta haɗa komai ga miji mai kuɗi ga kulawar miji. Tana ɗan wani murmusawa ta fara hawa step ɗin shi kuma gabaɗaya ya kufula da abin da ta yi saboda dama ransa a ɓace karuwarsa ta gama masa rashin mutunci kuma ya je ɗaukan agogonsa ya ga agogunan basa lokar agogunan.




"Baby n... Maganar tata ta katse ne sanadin marin da ya ɗauke ta da shi, a fusace ya shiga nuna ta da yatsa.


"Mahaukaciyar banza da wofi, ina miki magana kika watsa yin maganata kamar wani sa'anki" Ya ce a fusace yana nuna ta da yatsa. Sosai abin ya ba wa SALIMAH mamaki sannan ta shiga ruɗani ganin marin da aka ɗauke da kawarta ba da wani kwakkwaran dalili ba, sannan aka bi ta da bakaken maganganu. A take maganganun da BASEERA ta mata jiya suka faɗo mata, ta shiga jimanta wa a ranta ashe dai wasu masu kuɗin suna shuka rashin mutunci, tun da ga shi dai EESHART ɗin bata rasa komai ba na morewar rayuwa ita za ta tabbatar da hakan don ko cima sai abin da take so take ci haka za ta tura mata hoton abinci kala-kala sannan suturarta ma in ka gani tamkar za ta buɗe shago komai wadatacce amma kuma ga wani abu da ban wanda iya zamansu da shakuwarsu da EESHART bata taɓa faɗa mata hakan ba, sai ta nuna bata da matsalar komai.




Yanayin yadda ta yi lokacin da ya mare ta ɗin alamu sun nuna cewar ba wannan bane karo na farko. Ita kuwa ABBAS in ban da jiya ko yatsa bai taɓa kaiwa jikinta ba, jiyan ma ta san tsinken hana haihuwar da ta saka ne ya kona masa rai tun da ta san yadda yake da son yara, sai kuma maganganun da ta fusata shi da su amma in ban da wannan tsawon shekara biyar ABBAS ko harararta bai taɓa yi ba duk abin ta masa shanyewa yake ya nuna komai ba komai bane.




EESHART kuwa dama ta saba idan da sabo sai dai yau bata ji daɗin hakan ba da aka mata a gaban SALIMAH shi dama mijin nata babu abin da ya dame shi a gaban ƴan aiki na sai ya kai mata hannu shi dama wuyarta abu ya bashi haushi yanzu zai ɗauke mutum da mari.




"Ka yi hakuri Alhaji ɗaya lokar na saka maka" Ta ce cikin sanyin murya idanunta yana cikowa da kwallar zafin marin.


"Hakurinki na banza da wofi, uban wa ya ce ki canja mini ma'ajji? Sakarar banza da wofi" Ya ce yana doka tsaki ya haye saman ya bar ta rike da kumatu. Jiki ba kwari ta dawo tana wayancewa, duk da ta ji haushi kuma ya tsinka ta amma hakan ba zai sa ta rasa abin faɗa ba.




" SALIMAH kin ga baby ko da alama ransa ɓace yake yau amma ba komai na san ana jimawa zai durkusa ya bani hakuri" Ta ce tana sakin murmushin yake tare da danne ɓacin ranta duk da dama mari ba wani bakon abu bane a wurinta.


"Durkusawa fa kika ce EESHART? To ko jiya gama baki labari ne ban yi ba ni da ABBAS ya tsinke ni da mari a take na ɗaga hannu na rama, sannan na bishi da bakaken maganganun da suka fusata shi ya sawwake mini amma ke ba wani babban abu ba ya mare ki amma kin kasa kataɓus, dama haka masu kuɗin suke?" Diriricewa ta yi ta ma rasa abin cewa nan ta kawar da maganar tare da shigo da hirar babban rashin da ABBAS ya yi da ya da ya rabu da ita tabbas za ta auri attajiri nan ta ci gaba da ɗota ta a RUƁAƁƁIYAR IGIYA ita kuma tana hawa. Sai da ta yi magriba sannan suka ci abinci don ko da Alhaji Yusuf ɗin mijin EESHART ya sakko zai fita sai buɗaɗa kamshi yake watakila ita dai SALIMAH ba ta raba ɗayan biyu zance zai je duba da yanayin shigar da ya yi. Ko da SALIMAH ta gaishe shi a ciki ya amsa ita kuma EESHART cikin kalmashe murya ta ce masa.


"A dawo lafiya" Amma ya ba bango ajiyarta.


Sallama ta mata ta bata kama hanyar gida, da ta saba in ta zo tana bata dubu biyu ta ce ta hau napep amma yau ko naira biyar bata ba ta ba, tana zuwa gida ta yi sallar isha'i ta kwanta tana ɗan charting yau dai EESHART ta kula ta sun yi magana ba kamar jiya ba amma da alama har yanzu tana jin kunyar abin da ya faru.






Wannan karon mmn afrah ba dariya za ta baku ba, labarin yana ɗauke da sarkakiya, cin amana, butulci soyayya mai zafin maraici labari ne da zai taɓo mana ɓangarori da dama. Ba zan warware muku komai na labarin ba ku dai ku yi jumurin bina har karshe mu warware tufkar a tare a nan ne za ku gane mai ya sa aka sanyawa labarin RUƁAƁƁIYAR IGIYA.


09013181851




*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*






NA




MAMAN AFRAH




*GARGAGAƊI*


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️


JAN HANKALI


Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.




SADAUKARWA


Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.






PAGE 5




"ABBAS" Suka haɗa baki wajen faɗa cike da mamaki, wani takaici ne ya turnuke SALIMAH ita a halin da ake ciki ko sunansa bata so ta ji an ambata.


"Umma kin ga ɗan nacin nan ya zo ko? Har kina cewa tun da ya ji ciwon abin da na masa har ya iya furta sakin ya rabu da ni kenan, ina ganin na yadda kwallon mangwaro kuda ya daina addabata ashe dai na fahimci abin a baibai" SALIMAH ta ce tamkar ta yi kuka. Shi yaro yana gama faɗa musu sunan mai kiran ya juya ya tafi ya je ya cewa su ABBAS ɗin tana zuwa.


"SALIMAH idan baki yi da gaske ba wannan ɗan anacen sai ya hana ki rawar gaban hantsi, domin zai hana ki cin duniyarki da tsinken tsire, dole ki tashi haikan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login