Showing 1 words to 3000 words out of 62917 words

Chapter 1 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt

DIJENSY   

14 Jan 2025

5786

 🌼🌼 🌼🌼




💦 💦




*AMJAD*




💦 💦






🌼🌼 🌼🌼




*WRITTEN BY DIJENSY*


*WATTPAD:@dijensy*


*DEDICATED TO FATIMA² FWEND★*






*Assalamu Alaykum ,Alhamdullilah am back again.AMJAD is the name, yeah the story name.*


*This is a work of fiction. Names, incident in it are my imagination. Any resemblance to actual person living or dead,events is entirely coincidental.*

*The story is created to educate,enlight and entertain.Support by commenting, voting and sharing,they are the backbone of this story,your support will keep my rights up survive,without you guys i can't make tiny of it.Always want to make you happy,be with me and my stories.*





*Up up up❤ AMJAD ,let's start....💋💋Boom🎆*


*Bismillahirrahmanirrahim*


🅿 0⃣1⃣




*Canada,Mu'az resident*


Kid'a ne kawai yake tashi a gidan kai seka d'auka a club kake inba wai ka gane wa idonka ba.


Amjad! wata mace ta kira bayan data shigo d'akin wanda tana da tabbacin kid'an daga nan yake.


Saurayin data ke kiran sunan nashi ya juya baya sam ba jinta yake ba se miming wa'kar yake.Takawa tayi ta 'karasa inda yake tayi tapping kafad'arsa da 'karfi.


Da sauri ya juya tare da yin 'yar 'kara "Aww!"


"Will you please turn the music off?"


"Mom am glad you are back"Abinda ya fad'a kenan kafin ya 'karasa ya kashe kid'an.





" Amjad this is too much ".


"Mom am just having some fun,it's awesome".


" Where is Shaheed?"


"He just left"

"To?"


"I don't know".


" What about Zakia?"


"I guess she is in her room".

" Well, have you eaten?"


"No".


" Why? are you not hungry?"


"Of course I'm I just don't wanna eat"


"Is something wrong?"


"No". Ya amsa a taka'ice.


" I hope so,let me prepare omelette for you try a little son I don't want see you starving just like that".


Seda ya d'an d'age gira tukun yace "Ok".


"That's my kid".Ta fad'a tare da jan kumatunsa tana murmushi.


Shima murmushin yayi,daga haka ta fita daga d'akin shikam ya fad'a kan gado tare da d'aukan phone d'insa ya fara tapping.


D'akinta ta koma tare da rage jacket d'inta da viel d'in data yafa shima ta cire ta fito kitchen.


Cikin d'an 'kan'kanin lokaci ta kammala ,dining ta jera sannan ta hau upstairs zuwa d'akin Zakia.


" Come in"Aka fad'a bayan tayi knocking.


"Mom so you are back?"


"And you're here busy chatting"


"Ohh" Ta fad'a tare da sosa kai tana rife laptop d'in.


"Have you eaten?"


"Yes Mom"


"Ok then we enjoy our omelettes alone"


"Omelettes? that's my favorite you know"


"I make it for Amjad"


"Come on Mom Amjad is not a kid you're spoiling him much, Dad is right".Ta fad'a cikin shagwa'ba.


" Kema?"


"Nima me?" Ta tambaya cikin rashin 'kwarewar hausa".


"You're backing your dad"


"Why not ? He's right"


"Ok let's go" Ta fad'a tare da tallafo kafad'arta suka sauka 'kasa.


"Amjad! Omelettes is ready"


"Ok Mom"Ya amsa daga d'aki.


"You see"


"Zakia ?" Mom ta fad'a in between laughter.


"Ehyi he's almost 26 but yet you're treating him like a 16"


"What are you two discussing?Suka jiyo muryarsa yana sakkowa daga step.


" She.."


"Mom!" Cewar Zakia da 'karfi tana zaro ido signing take mata na tayi shiru.


"Ok ,I gerrit" Tayi alamar zipping mouth da yatsa.


"Are you guys hiding something?"Ya tambaya yana kallonsu.


" No"Suka amsa a tare.


"Lazy I hope your hands didn't touch my Omelettes?"


"What if it those?"Ta tambaya cikeda tsiwa.


" R.I.P"Ya amsa yana gyara kujerar zama.


"Really? Let.."


"Shh! Guys let eat and stop chatting" Mom ta katse su dan yanzu sesu mayar mata da table upside down halinsu neh kullum se sinyi fad'a shi tsokana ita kuma tsiwa.


"Yau wani beyi sallah na Asr ba". Zakia ta fad'a bayan sinyi nisa da cin abincin.


Karaf! Ya dire spoon dake hannunsa ,ya san inde zatai munafinci shine take jagulo hausa dukda kuwa ba 'kwarewa tayi ba amma de ta fishi dan a yanzun ma ba sosai ya fahimci abinda tace ba amma de ya ayyana dashi take.


" Zakia are you serious? " Mom ta tambaya.


"Yes Mom" Ta amsa.


"What did you mean by that?" Ya tambaya fuskarsa a d'aure.


"Amjad is that true?" Mom ta tambaya yanayin fuskarta ya sauya.


"What?"


"You didn't pray Asr" Ta amsa a takaice.


Yanzu ne ya gano gulmar data fesa mata.A fusace ya mi'ke dama Zakia tasan za'a rina, a guje ta tashi daga kujerar ta fyalle hanyar sitting room dan ba damar hawa bene.Bata san ita kanta inda zata 'boye ba,'kofar fita ta nufa.Mom na kiransa amma ko sauraranta ya'ki yi.


'Kiris be iske ta ba sega Dad ya shigo,da sauri ta la'be a bayansa.


"Dad help me!" Ta fad'a da 'karfi.


Ganin haka yasa Amjad yaci birki se huci yake.


"Amjad what's going on?" Dad ya tambaya.


Shiru yayi dan bashi da abin cewa yasan idan yaji maganar sallah ne seya santa a gun dad.


Tana daga baya amma a haka take masa gwalo.


"She took my ..my diary" Yayi 'karya.


"Diary?" Waiwayawa yai ya kalli Zakia,da sauri ta saita kanta.


"Where is it?"


"In the locker".


" Give him back ok?"


Kai ta gida'a alamar toh,daga haka ya wuce ya barsu a gun.


"I saved you"


Galla mata harara yayi tukun ya wuce ,tana bin bayansa da gwalo.


"Honey you're back". Cewar Mom lokacin daya 'karaso ta mi'ke tare da hugging d'insa.


" Uhm,mey kuke ci haka?"


"Omelettes" Ta amsa.


Amjad jin da yaren da dad yayi magana yasa yace "disgusting" ba tare da sun jiyo ba,ko takan omelettes d'in be biba ya haye sama abinsa.


"Shaheed?" Ya tambaya.


"He went out am sure he's on his way back home"


"I hope so" Ya amsa.


Spoon ya d'auka kan table d'in tare da d'iban omelettes d'in yayi tasting. "Uhhm yummy"


"Really?" Take ta hau blushing.


"Sure" Ya amsa.


Zakia dake tsaye gun ta ta'be baki tana murmushi,koyaushe haka Mom take akwai son a yaba girkinta.Sometimes takan ce dad is so lucky he has a loving and caring wife.


Ita ma d'akin nata ta koma tsokana yasa ta tsiri ci dan ba wani yunwa da take ji.


6:16pm Shaheed ya shigo lokacin kowa yana d'aki,be shiga nashi d'akin ba ya shiga na Amjad


Sallah ya tarar dashi yanayi,ko ba'a fad'a ba yasan Asr yake dan aikin kenan a haka anci sa'a be had'a da Isha'i ba.Yana zaune har ya idar tukun ya soma magana.


"Asr right?"


"Mind your own business silly boy ,where have you been?


"Do I have to explain? Look at how you're talking as if you're my dad"


"Pillow ya d'auka ya cilla masa a fuska." Get out "


"Easy,am going dude" Tashi yayi ya fita ya rabu dashi.



Nigeria, Kano.


Sauri-sauri take tafiya hannunta ri'ke da jakar makarantarta kayanta kuwa uniform d'in islammiyya ne.


"Assalamu Alaykum" Ta fad'a bayan ta 'karasa gida.


"Waalaikissalam"Aka amsa mata.


A tsakar gida ta tarar da Mahifiyarta tana gefen shinfid'ar mahaifinta daya ke kwance ana ganinsa ansan yana jin jiki.


" Sannu Baba".Ta fad'a.


Kai kawai ya iya gid'a mata dan ko magana ya kasa yi.


"Ina kika baro su Maryam d'in?


" Suna dawowa tafiyar tasu ba sauri shiyasa nayo gaba"Ta amsa.


"Laila idan kin cire uniform d'in zaki je gidan kawunki ki kar'bo ruwan rubutu za'a bawa Babanku"


"Mami wai wannan ji'ke-ji'ken baza a dena d'ura masa ba"Ta fad'a 'kasa-'kasa kar Mahaifin nata ya jiyo.


" Toh ya za'ayi"Mami ta fad'a.


Ba jimawa ta chanja cikin kayan gida tare da zira hijab ta fito.


"Na tafi".Abinda tace da ita kenan tukun ta fad'a.


Gidan kawun nata daya ke bayan layinsu ne ba dad'ewa ta dawo,a lokacin suma 'kannen nata suka dawowa.


Dama Mami ta san ba iya ruwan rubutun bane hadda sauran ji'ke-ji'ken magunguna idan ta'ki bashi kuma suce bata son d'an uwan nasa ya warke shiyasa ta dena 'kin bashi dan wasu lokutan da kansa yake zuwa ya d'ura masa.



LAILA itace d'iyar fari a gidansu se 'kannenta guda uku Maryam ,Nusaiba se auta Fauzan. Laila wannan shekarar ta kammala secondary school dan hatta jamb tayi admission take jira,tana da shekara 19 a duniya.


Mustafa Mu'az sunan mahaifin Laila ,Fatima sunan mahaifiyarta.Mahaifin Laila yana da yayyi guda biyu Yunusa Mu'az na farko da Engr.Abdallah Mu'az na biyu se shi na uku.Mahaifin Laila ba mey kud'i bane yana de d'an sana'arsa,lokaci guda rashin lafiya ya kamashi ,koda suka je asibiti aka fad'a musu ya kamu da ciwon 'koda.Duk cikin su ukun Engr.Abdallah shi yayi karatun boko mey zirfi cikin ikon Allah ya samu d'aukaka har yakai wannan matakin sanda ya kammala karatunsa a 'kasar waje ya samu aiki.


Rushda Lincoln data kasance haifarfiyar Italy business ya dawo da iyayenta Nigeria,haka yasa ta iya harshen hausa dan tun tana 'karama suka komo,Egr.Abdallah daya ta'ba yin aiki 'kasan Mahaifin ta a dalilin haka suka had'u da Rushda .Lokacin da yazo wa 'yan uwansa da maganar aurenta kowa ya'ki amincewa dan su a ganinsu ma ita Christian ce seda 'kyar suka fahimci musulma ce grandparents nata ne Christian amma iyayenta musulmai ne ,Lincoln kuwa sunan da family d'insu suke bearing ne.Bayan aurensu suka koma Canada da zama inda sukai 'ya'ya guda Uku watoh Amjad, Shaheed se Zakia.


A yanzu haka Amjad ya kammala karatunsa yana da shekara 26 ,Shaheed yana da 23yrs shima yana gab da graduating ,Zakia tana da 19yrs ita bata dad'e da fara university ba.


Engr.Abdallah lokuta-lokuta yana zuwa 'kasa Nigeria domin ziyartar 'yan uwansa dad'i da 'kari Company nasa (RAZAS),Amjad da tun befi 10 ba idan aka zo Nigeria baida buri a tafi company har yanzu sed kuma zaman Nigeria ne sam bayaso . Kusan yanzu 7yrs rabonsa da Nigeria last zuwa da akai harkar school tasa beje ba daga Mom se yaran guda biyu banda dad dayake tare dashi.

Tunda Mahaifin Laila ya kwanta rashin lafiya Dad yana tura masa kud'i na asibiti ,yanzun ko ya turo Baba seya ce Mami siyi siyayan abinci dan yana ji ajikinsa kamar baze tashi ba.Shikuwa dama Kawu Yunusa baya son zuwa asibiti haka kullum cikin had'o ji'ke-ji'ken gargajiya.Toh wannan kenan.


8:30pm


Bayan sun kammala cin tuwo suna zaune dukansu a tsakar gidan ,Mami se fifita take ma Baba abincin ma ya'ki ci se numfarfashi dayake.


"Sannu,a had'a maka shayi tunda ka kasa cin abincin"


Kai ya gurgiza mata alamar a'a.Shiru tayi daga haka ta cigaba dayi masa fiffitar.Yaran ma sinyi shiru basa ko hira,Fauzan ne ma mey yin magana shima ganin sinyi masa shiru ya dena,'kuruciya tasa baya fahimtar halin da ake ciki iya kaci yaji ance sannu Baba shima ya fad'a. A yanzu yaran nada shekara 7,Maryam nada 16 se Nusaiba 14.


9:00pm nayi kamar koyaushe lokacin baccinsu yayi dan haka suka mi'ke zuwa d'akinsu.


"Kada a mance ayi addu'a"


"Toh Mami". Suka amsa sannan suka shige d'akin.


Su duka ukun a shimfid'a d'aya suke kwana ,Fauzan daban.Basu kwanta bacci ba seda suka tabbatar sinyi addu'oinsu sannan suka kwanta,Laila da 'kyandas taji ko alamar bacci babu a tattare da ita.Ciwon Baba ba 'karamin damunta yake ba,gashi ita kanta Mami tana cikin damuwa kusan 2month ana jinya.


Da'kyar ta samu ta rufe idanunta bayan 15min bacci yayi gaba da ita.


Amjad,4:12am


Kamar ba dare ne ba,earphone ne ma'kale a kunnensa ya d'ora laptop kan gado se chat d'insa yake hankali kwance gefensa kuwa Pepsi ne yana korawa.

Kusan koyaushe haka yake baya wani isashshen bacci se kusan 4:30am ya kwanta har lokacin subh yayi be farka wa inba Mom ce ta tashesa ba itan ma setayi fama kafin ya mi'ke.Dad ya rasa yadda zeyi da irin hali na Amjad sam ya banbanta da siblings d'insa ,ga yawo shine club shine parting tare da bad guys.


Washegari,Saturday


Duka yaran suna makaranta kamar koyaushe basa d'ara 8:30am kowa take tashi daga bacci se kuma wani daren ,kowa ya shiga sabgarsa Laila kuwa tana kitchen tare da Mami suna had'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login