Showing 60001 words to 62917 words out of 62917 words

Chapter 21 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt

DIJENSY   

14 Jan 2025

5801

bisani ta soma gyangyad'i cikin lokaci 'kalilan bacci ya saceta ta saki handout d'in a 'kasa.Koda ya d'ago kansa yaga tayi bacci,ganin haka ya mi'ke tsaye ya 'karaso inda take ya d'auketa ya kwantar kan gadon tare da rufa mata blanket daga gefenta ya kwanta bayan ya kashe light d'in d'akin yana ri'ke da hannunta yana murzawa softly " I love you "Yayi kissing d'inta a forehead ,shima cikin lokaci 'kalilan bacci ya d'aukesa.


★★★


Washegari da asubah ta farka,d'akin hasken wata ne kasancewar light a kashe yake ,cikin sauri ta mi'ke ganinta kan hannunsa.Zata sauka daga gadon kuma seta dawo tana 'kare ma fuskarsa kallo ,cikin kwanciyar hankali yake baccinsa.Gashin kansa ta shiga kalla tana ganin irin cikar sumarshi da 'kyalli da take kamar yanzu aka shafa mai,a hankali ta mi'ka hannunta kai tana so taji yanayin laushinta." Very silk"Zuciyarta ta fad'a.Ta shagala sosai daga baya ta sakko kan girarsa tana so tayi comparing da tata,idan ta shafa tata seta shafa tashi ,gashin kanta ta shiga shafawa shima tana so taga na waye yafi laushi,data sake shafa nashi taji nashi ya d'ara nata."Ai de kad'anne,nima nawan da laushin"Ta fad'a tana guntun murmushi.


Ganin zatai late ta mi'ke ta shiga bathroom, tana shiga ya bud'e idanunsa fuskarsa ya saki 'kayataccen murmushi dan tun d'azu duk abinda take yana jinta.


"Laila" Ya fad'i sunanta cikin sanyayyar murya.


Koda ta fito ta ganshi zaune bata wani yi mamaki ba dan tayi tunanin ko 'kofar data buga ne sanda ta fito ya firgita dan tana sani tayi hakan.Jira take taga ze shiga bathroom d'in aiko bata gama sa'ke-sa'ken ba ya shiga."Da gaske yake wannan"Tayi maganar a ranta.


Ganin yana shirin siyi sallah bayan ya fito tace"Wai kai baka zuwa masallaci?"


"If that is what you want then I will go"


"Eh,ka tafi" Ta fad'a tana waigar da fuska.


Hakan kuwa akai tana tsaya ya fita."Mutum kullum sallah a gida sekace munafiki,hala a can Canadan baya zuwa"


Sanda ya dawo ta koma bacci,gefen gadon ya zauna yana 'kare mata kallo blanket d'in yaja mata tare da kissing cheeks nata ya fita daga d'aki,a d'akinsa kuwa laptop d'insa ya d'auka ya shiga dube-dube.




*Dijensy❤*









🌼🌼 🌼🌼




💦 💦




*AMJAD*




💦 💦






🌼🌼 🌼🌼




*WRITTEN BY DIJENSY*


*WATTPAD:@dijensy*


*Wannan page naku be AMJAD fans*


*Last page*




3⃣7⃣-3⃣8⃣


Laila sai 9:04am ta farka daga bacci,bathroom ta fad'a tayi wanka bayan ta fito tayi shirinta cikin riga da wando Pakistan red se d'an 'karamin gyale tayi yafe dashi ba abinda ta shafa a fuskarta illa spray data fesa ta sauka 'kasa.A kitchen d'in ta tarar dashi ko meyake sha ma oho tade ga bowl a gabansa yana zaune kan stool ,yitai kamar ba mutum a kitchen d'in,bama tasan mey zata girka ba dube-dube ta shiga yi du abinda take yana kallonta.Mi'kewa yayi daga zaunen ya 'karasa inda take "Laila relax,I know you're here to see me stop pretending and wait for my hello"


Fuska a tamke ta juyo ta kalleshi,kamar zatai magana kuma setai shiru ta bud'e fridge ta d'akko 'kwai indomie da kwai kawai ta shiga preparing yana daga gefe ya wani sunkuye se magana yake mata baya ko gajiya ita kuwa ta'ki fad'in 'kala."Heartbeat please talk to me"


Tana gama had'in da zatai ta nufi gas cooker ta barshi anan yayi yun'kurin sake matsawa gunta kuma ya fasa yayi hanyar fita a dede bakin 'kofa ya tsaya hannunsa na dama ya d'ora a dede saitin zuciyarsa ya dur'kusa ya soma mur'kususu yana hakin 'karya.Laila da hankalinta dama yana gun da sauri ta ajje frying pan dake ri'ke hannunta ta 'karasa inda yake cikin rikicewa ta tallafoshi hannunta ta d'ora kan 'kirjinsa tasa kuka."Amjad! Please "


"My heart ...it's ..paining" Yayi maganar da 'kyar.




"Please don't leave me I love you wlhy i'm here for you"Tayi maganar cikin kuka da rud'ani ganin yadda face d'inshi yayi ga jijiyoyinsa sun tashi kamar gaske.


Ta rasa wane taimakon zatai masa daga bisani ta mi'ke ta tafi d'akko waya.Bayan 2min ta dawo kitchen d'in tana searching numbern da zata kira idanta na sauka bakin 'kofar taga empty place daga gefe taga mutum a tsaye ya jingina da bango hannu d'aya yayi folding a 'kirji d'ayan kuwa yasa alawa a hannun yana 'barewa da baki." You.."Ta 'karasa inda yake ta d'uma masa dundu a 'kirji."Ahhg!"Yayi 'kara.


"You wanna kill me?" Ya ri'ke hannunta.


"Let me go" Ta fad'a tana kici-kici.


"I love you wlhy please don't leave me" Ya 'kwai'kwayi abinda ta fad'a d'azu.


A hankali ta kai masa wani dukan fuskarta d'auke da murmurshi,yana dariya yayi hugging d'inta itama hugging back d'in tayi tana murmushi.




★★★


Yanzu soyayya suke nuna wa junansu sosai a kodayaushe inde suna gida to fah suna tare,Laila yanzu ma ta koma d'akinsa no more 'buya again.


3 years later


7:09am,Amjad yana kwance bacci yake cikin kwanciyar hankali,beyi aune ba yaji saukan remote control a kansa.Da sauri ya mi'ke yasa hannu ya ri'ke"Stop!"Ya tsawata.


Wata iriyar 'kara yaran dake zaune kan gadon ya tsala nan take ya fara shararar hawaye kamar fanfo.Cikin kid'imewa Amjad ya mi'ke shhh! ya d'aukesa ya d'ora a cinya se faman lallashinsa yake amma kamar zugashi yake,hannu yasa ya toshe bakin duk dan ya dena amma mey makon hakan se cizo daya gasa masa a hannu.


"Laila!" Ya 'kwala mata kira.


Tana d'aki tana shirya 'yar baby dake hannunta wacca bata fi 5month ba,jin yadda ya kira ta tasan ba 'kalau ba,ko riga bata sa mata ba daga wando se band tsabar rikicewa ta tashi zuwa d'akinsu.


"Mene kuma?" Tayi maganar tana daga bakin 'kofa.


"Look" Ya mi'ke daga zaunen ya 'karasa inda take ya mi'ka mata hannun da aka ciza.


"Toh nina yi?" Ta fad'a kamar zatai dariya.


"Allah ya sake sena rama"


Yanzu kwa dariya take sosai "Adil d'in zaka ciza,gaka gashi wlhy da anyi cije-cije har ha'koransa nawa just 8 ko twelve fa kai mey thirty two tabb!


Adil dayai cizon ya tsiresu da ido kukan ma ya dena ya kalleta ya kalli Amjad d'in haka yayi tayi."Zo "Ta mi'ka masa hannu.


Ba musu ya sakko daga kan gadon ya 'karaso inda take" Mummi ,daddy"Yayi maganar yana nuna Amjad.


"Ya matse ma baki ko,next time ma ya sake cizon zefi haka" Taja hannunsa suka fita.


'Kofar yayi banging ya koma kan gadon jiya be samu yayi isashshen bacci ba dan tsabar kukan "Ashalina" baby girl d'insu ,ba yadda beyi da laila ba kan take sata nata d'akin amma fafur ta'ki ita seda ita zasi bacci ko Adil seda yayi 10month ta ware masa d'akinsa.


Adil(Mustafa;sunan baba) 1½year kawai ya bawa Ashalina shiyasa komai ya cakud'ewa Laila dan ma Allah yasa ta kammala school wannan year d'in yanzu ta samu relief.




Se 9:30am Amjad ya sakko 'kasa a dinning ya tarar dasu Adil yana kujerar gefe,kusan shine yayo kamar Amjad sak Ashalina da Mumminta take kama.


"Morning heartbeat" Ya fad'a tare da manna mata kiss a kumatu."Morning Hayati"Ta amsa fuskarta d'auke da murmushi.


Plate dake gaban Adil ya d'auke cancaras ,a take ya kurma ihu kamar wanda ake cirewa ido,ba shiri ya mayar masa tare da dungure masa kai."Shut up!"


"Nide ya zama fat ba ruwana na dena d'aukansa na fad'a miki ki dena bashi abinci mey irin wannan." Cheese, chocolates duk shi kad'ai".Ya 'kare maganar tare da zama kan kujera opposite dasu.


"What of my sweetheart(Ashalina)?"Ya tambaya.


"Sleeping" Ta amsa.


"And you let her?"


"Uhm"


"I'm gonna wake her as soon as I'm done with my meal"


"Ka barta mana she's too young"


"An'ki d'in sanda mike bacci ta dame ni da safe tayi nata no way itama yanzu bazatai ba"


Haka suna yi suna hira bayan sun gama ta mi'ke tattare kwanukan se lokacin ya lura da dress datai,leggings black ne a jikinta se yellow shirt paralyzed hand tayi parking gashinta jelar ta zubo a bayanta. "Looking. se....." Had'a ido da Adil da yayi yasa ya'ki 'karasawa.


Mi'kewa yayi daga dinning d'in slide cucumber dake plate d'insa ya caka ya danna wa Adil a baki,ba shiri ya tofar dashi ya d'auke tissue yayi wiping bakinsa kamar yadda yaga anayi.Cije lips Amjad yayi tare da barin dinning d'in ya nufi kitchen .


Tana tsaye jikin drawer taji hug ta baya."Heartbeat you don't even care about me now"Yayi maganar a han ankali.


Juyowa tayi tare da zagaye hannayenta a wuyansa"After all why am I here,isn't it all because of you ? Because of you I decided to came in here wait for my man.."


Shigowar Adeel yasa tayi shiru,gira ya d'aga mata alamar "what?"


Hannunta tayi pointing inda Adil yake,yana tsaye ya tsiresu da ido ko 'kiftawa ya'kiyi."Ya Allah "Amjad ya furta tare da furzar da iska daga bakinsa." Wannan wannan inde muka je Canada baze dawo ba ,kajini you are staying with Mom "Yayi pointing d'insa.


Laila 'karasawa tayi inda yake ta tsuguna dede tsahonsa." My boy mey kake so uhm? Chocolate? "


Kai ya girgiza alamar "a'a".Nan ta sake tambaysrsa " Cake?"


"No,Apple"Ya amsa.


Apple d'in ta d'akko masa a fridge ta mi'ka masa, haka yasa hannu ya kar'ba ya tafi se waige-waige yake." Ohni"Ta fad'a.


"I'm serious a Canada za'a barshi kina gani ya takura mini" Yayi maganar fuskarsa ba dariya.


"Oh hayati ,calm down"


"A hakan? Bama shi ba Ashalina now maganarta ,you refused to .."


"Zan maida ita d'akinta nan da few months"


"Months? Geez!"


Ring! Ring! Wayarshi tayi 'kara haka yasa be sake wata maganar ba ya fita,kallo ta bishi dashi tana murmushi.


★★★


Haka ranar Ashalina ta wuni tana bacci da daddare kuwa ido 'kiri ta'ki ko gyangyad'i,Laila data gaji ta sata tsakiyarsu itama tayi kwanciyarta ,ko minti 5 ba'ai ba ta fara ihu kamar daga sama yaji 'kararta aiko a kid'ime ya farka,gefe ya kalla yaga Laila ta rufe ido tana kwance aiko a hankali ya mi'ke ya d'auke pillow d'insa ya nufi bakin 'kofa ze fita yajiyo muryarta."Where are you going? "


Yana shafa 'keya ya waigo"Don't worry I'm soon coming back I want to see Adil and come back"


"Dawo,dawo he is sleeping comfortable I just came back from his room come back"


"Laila" Yayi maganar kalar tausayi.


Mi'kewa zaunen tayi tare da d'aukan Ashalina dake kuka ta 'karasa inda yake tsaye ta mi'ka masa ita." Wait for me here"Ta bud'e 'kofar ta fita.


Ya rasa inda zeyi da ita ya jijjigata ya d'agata ganin zata shid'e ba shiri ya fito daga d'akin,baki ya saki ganin Laila kwance a parlour se sharar baccinta take,'kararta yasa ta mi'ke tsaye.Girgiza kai kawai tayi cikeda takaici ta kar'beta tana kar'barta tayi shiru dan dama ba yunwa take ji ba,da niyyarsa ya koma ya kwanta sekuma yaji ba dad'i dole ya ha'kura ya zauna dasu ,da 'kyar suka samu tayi bacci seda ya kwanta rigingine a sofa ya d'orata kan 'kirjinsa yayita jijjigata a haka tayi bacci shima baccin ya d'auke sa Laila tana d'ayan kujerar itama tayi bacci.


6:30am ,hasken daya kwallare mata ido yasa ta farka da sauri,6am taga agogon ya nuna.A kasalance ta mi'ke kanta yayi mata nauyi ta aza idonta kan Amjad dake ta bacci Ashalina a kan 'kirjinsa itama baccin take,'karasawa tayi inda suke tasa hannu ta d'auketa dede lokacin ya bud'e ido.Ganin ya makara yayi saurin mi'kewa shima a gajiyan yake haka suka koma sama,nan yayi shirin office d'insa Laila kuma ta sakko shirin breakfast,Amjad a tsattsaye yayi breakfast ya wuce office dan ya makara sosai ita kuma ta kama aikin gida tayi wannan tayi wancan kan ace mey lokaci yaja mutuniyar kuwa se 9am ta farka 12 bayan anyi mata wanka ta koma bacci (Mata muna aiki😓).



Ko 2 weeks ba'ai ba suka tafi Canada dan tunda aka haifi Adil basi je ba rabon da suje tun da cikinsa,Mom se nan -nan ake dasu 'yan jikokinta Adil da Ashalina kamar ta lashe su.Adil ta'bara se abinda ya 'karu abinda yake so shi Mom suke masa.Duka familyn suka ware rana suka je park ranar sun wataya pictures ba adadi kamar karsu koma,Laila seda sukai 3 weeks cir suka komo gida.


2 days da dawowarsu, furnitures na d'akinsu yau suke sakewa Laila tana kwashe kayan drawer taga picture na Amjad tare da wata baturiya ya dafe kafad'arta su biyun duk sunyi dariya a photo d'in data kalli date taga kusan 6 years da d'aukan picture d'in.Wani irin kishi taji ya tokareta hoton ta yasar ta tashi aikin ma ta fasa,Amjad ta gani tsaye bayanta picture d'in ya kalla sannan ya kalleta."My heartbeat "Ya 'karasa inda take.


Gefe ta kauda kanta ta tamke fuska tare da nad'e hannu a 'kirji.


" This "Ya sunkuya ya d'akko picture d'in,hannu biyu yasa ya yaga into pieces yasa a shara tana kallo." Shikenan?"Ya tambayeta.


Kallo d'aya tayi masa ta fita dukda taji relief.Wajejn 8pm ya dawo daga masjid dede lokacin ta gama waya da Mami, tana ganin shigowarsa d'akin ta soma d'aga yatsun hannunuta se wasa take dasu sunsha 'kunshi red."Wow! heartbeat I love this "Ya 'karaso ze ri'ke hannun ta d'auke.


" What?"Ta tamke fuska.


"Laila henna"Yayi maganar yana zama kusa da ita.


" Ok listen to me"Ta gyara zama ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya.


"I'm all ears"


"Amjad,I ..I " Ta'ki 'karasawa tana kallon reaction d'insa a yanzu. Sosai ya bada attention a abinda zata fad'a."I'm pregnant "Tayi maganar a ta'kaice.


A razane ya zaro ido kamar zeyi kuka" Laila you're p..."


Dariyar data shiga yi ne ya tsayar dashi,harda ri'ke ciki tana nuna shi."Ka fiya tsoro"


"Kansa ya waigar yasha kunu " You scared me"


"Ooh come on my man I'm just joking" Ta dafe kafad'arsa.


Juyowa yayi har lokacin fuskarsa a tamke seda tasa hannu biyu ta kama kunnenta ya saki fuskarsa."Let me see this"Ya ri'ko hannunta.


Waje guda ya had'a hannayen nata ya manna musu kiss."Looking pretty always "


Murmushi ta shiga yi tana kallonsa bata ce komai ba,d'agowa yayi yana kallonta daga baya ya jata jikinsa yana shafa bayanta."I love you heartbeat "


"I love you too Hayati".


*Alhamdulillah*


*Anan na kawo 'karshen littafina mai sunaAmjad,abinda na rubuta ba dede ba Allah ya yafemin.Ina fatan an amfana da abinda ke ciki,readers, fans ina godiya sosai da goyon bayanku without you I can't make it,thanks a lot.Wannan azumin dake tahowa Allah yasa a fara damu kuma a gama Ameen,se min sake had'uwa a cikin wani sabon littafin nawa mey suna.....se bayan sallah😘 ana tare✌*




*Dijensy❤*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login