Showing 21001 words to 24000 words out of 62917 words

Chapter 8 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt

DIJENSY   

14 Jan 2025

5788

" Ta fad'a tana sosa kai.


"Charge?"


"Uhm"


"Find your way out"Ya nuna mata 'kofa.


Sum,sum ta fita tana rufo 'kofar tace" Karka bayar".


D'akinta ta shige disappointed, kayanta ta cire ta sauya da na bacci riga da wando wanda be kai ankle ba tayi kwanciyarta.

Washegari 10:23am


"Kin sake kiran nata a kashe?" Mami ta tambayi Maryam.


"Eh na sake kira a kashe"


"Toh ko Amjad d'in za'a kira"


"Toh ai baki da number shi"


"Semi kira Mamanshi ta turo mini ko"


"Eh"


Mom ta kira bayan sun gaisa take tambayarta ta turo mata number shi.Kiran farko data kirashi be d'aga ba se karo na biyu."Hello"


"Assalamu Alaykum" Tayi sallama.

"Waalaikissalm"


"Uh.m Mamin Laila ce" Ta fad'a.


"I..ina..yi...ina kwana" Ya fad'a da 'kyar.


"Lafiya lau,ya gida?"


"Da lafiya" Ya 'kwa'ba hausarsa.


Mami ganin ba iya Hausa yai ba yasa bata ja zancen ba ta tambayeshi Laila.D'akinta ya nufa ko knock beyi ba ya murd'a handle.Da sauri ta mi'ke daga kwancen da take "Your Mom" Ya bata wayar.


Tana rawar jiki ta kar'ba tana fara'a."Hello Mami ina kwana"


"Lafiya lau,ya gida"


"Lafiya lau,yasu fauzan?"


"Duk lafiya suke,meya sami wayarki?"


"Uhn...charge ne babu"


"Chaji? Toh ya haka?"


"Eh babu irin nawa ne"


"Kuma baki ko kira a wayar tashi ba"


"Ina son na kira ,ina su Maryam yaushe zasu zo?" Ta chanja topic.


"Tun yanzu,a'a se an d'an kwana biyu"


"Mami dan Allah suzo ko gobe ne"


" Zasu zo amma ba lalle goben ba"


"Toh shikenan"Ta fad'a a ranta bata so haka ba.


Hira kad'an sukai tukun sukai sallama,se bayan ta gama wayar ta lura ya fice.Wayar tabi da kallo kafin ta murd'a handle zata mayar ,Ring!Ring kira ya shigo.


" Baby boo❀"


"Baby boo" Ta maimaita sunan a ranta.Ganin kiran ze katse ta 'karasa 'kofar d'akinsa tana shirin murd'a handle ya riga ta bude'wa.


"Gashi" Ta mi'ka masa tayi sauri ta koma.


Ganin Rosie ce ta kira yasa ya saki murmushi ,dad'i yaji sosai dan ya tabbata ta ga sunan.




Laila sam bata ji wani haushi ba kawai de takaicinta d'aya shine zama da take haka ita d'aya wanda batasan 'karshensa ba.Kwanciyarta tayi ta rufe idanuwanta dan bacci ya fiye mata wannan zaman shirun.


β˜…β˜…β˜…


Laila tsakaninta da Amjad har yanzu kallo ne ba wani abu dake had'asu,yau aurensu kwana takwas kenan ,Amjad yaje gida so d'aya driver da Dad ya kawo masa yace baya so da kansa yake driving motarsa dukda dama ba wani fita yake ba sede restaurant wani sa'in yana zuwa ya siyi abinci.


Knock!knock! Ta jiyo tana kitchen."koh waye?"Ta tambayi kanta dan Amjad yana gida,ajje yankan carrot d'in da take yi tayi ta fita bud'ewa.


"Maryam!" Tai hugging d'insu tare da Nusaiba tana tsalle.


Lokaci guda farinciki ya dabaibayeta,ta kasa komawa kitchen d'in ma dama bata d'ora abincin ba.Ji take kamar ta cinyesu dan dad'i ,hira kawai sike ba 'ka'k'kautawa.


Se wajen 1pm ta tashi dan yi musu girki,kusan tare dasu ma aka girka abincin.Fried rice sukai mey dad'in gaske ,a plate d'aya ta zubo musu suka zauna a parlour abinsu suka ci su ukun.Har lokacin Amjad be fito ba ita bata ko damu ba dan tun jiya rabon data sashi a ido .


Suna kammala cin abincin sukai sallah su Maryam suka d'auraye kwanukan da aka 'bata."Maryam kunsan wani abu?"


"A'a sekin fad'a"


"Yanzunnan nake so ku tayani nayiwa Mami cake ku kai mata"


"Toh" Maryam ta amsa.


"Mami fa tace kar mu dad'e"Cewar Nusaiba.


" Ke dalla can seku kwana"


"Tabb bada mu ba" Maryam ta fad'a.


"Meye idan kun kwanan?eyyi?"


Shiru tayi Maryam tana munafikin murmushi tare da kad'a kai "a'a de".


" Bazaki magana ba,nace meye idan kun kwanan?"


Dariya ta shiga yi tana rufe fuska "Mtchww! Sakarya ni tashi muje kitchen d'in" Ta fad'a tana mi'kewa daga kan sofa dan ta fahimci inda ta nufa.


A hankali suna had'a abinsu har sukai baking, sosai cake d'in yayi dad'i nan ta d'ibarwa Mami mey yawa ta rage kad'an.Wajajen 5:30pm suka tafi, pictures da suka kawo mata na biki tayi ta kalla.


Amjad kuwa yana jiyo su daga d'akin yana sane ya'ki sakkowa dama ya shiga da abincin daya siya a waje d'aki harkokinsa yayi tayi a d'akinsa.


Ita kuwa da dare cake d'inta taci tasha lemo tayi kwanciyarta.


11:35pm, Knock! Knock! Tajiyo bugu tana cikin bacci, tashi tayi duk jikinta yana shaking dan bugunshi yaso ya razana ta.


"Mtchww! Ze tayar min da hankali ina bacci na" Seda ta yafa mayafi tukun ta bud'e masa.


"Let me have your phone"Abinda ya fad'a kenan banyan ta bud'e.


Seda ta d'an jinkirta kafin ta koma ta bud'e drawer ta d'akko."Gashi"Ta fad'a a ciki-ciki.


"This?" Ya wani kalli wayar tare da nuna ta da yatsa.


A wani wula'kance ya kar'beta bayan ya jujjuyata ya mi'ka mata abarta."This is useless "Ya fad'a.


" Wacce ka siyamin?"Ta fad'a a ranta.

Kamar yana so ya sake fad'ar wani abun amma de yayi shiru ya fita daga d'akin ta rifo 'kofarta.


"Allah ze sakan tashi na dakai" Ta koma ta kwanta.



***


Washegari tasha mamaki ganin ya siyo mata waya,bata yi tunanin yana da ragowar mutunci ba,IPhone 7+ silver colour.


Tunda tayi waya ta rage damuwa da rashin mutane a kusa da ita,zatai chat d'inta tayi kiranta tayi karatun novel wani lokacin tayi kwalliya tayi ta selfie d'inta.


Amjad kuwa kwana hud'u kenan da fara zuwa aiki.Ranar farko daya je company kowa kallonsa yake a iya shekarunsa a matsayinsa na chief executive officer gashi dressing yake duk wanda yaga dama har 'yar shirt me gajeren hannu ma yake saka wa ya tsuke abinsa gashin kannan yasha style.


12:14pm,taji motarsa yai parking tana daga d'aki,labulen window ta d'an bud'e tana ganin fitowarsa ta ta'be baki ta cigaba da danna wayarta.


Tana jiyo shi ya shiga d'aki,wanka kawai yayi ya sauya kaya cikin farar T-shirt da black jeans ya shirya shirts, wayarsa da key kawai ya d'auka bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito.


Knock! Knock! Taji ya bugo 'kofarta.


"Follow me" Abinda kawai ya fad'a yawuce downstairs.


"Follow you? To where?"


Komawa tayi ta zauna amma kuma ta kasa ci gaba da dannan wayar,seda tayi kusan 8min a haka tukun ta mi'ke ta yafa mayafinta kan riga da skirt na atamfa dake jikinta ,flat shoe d'inta ta zira ta ajje wayarta ta sauka 'kasa.


A living room taga bayanan,tana le'kawa waje ta ganshi ya jingina da pillar na varender.Yana jin motsinta ya waiwayo ,wata uwar harara ya watsa mata sannan ya nufi motar.


"Toh ina kuma za'a? Toh wayata kuma na d'aki"


Wata zuciyar ce tace "kika sani ko gida zey kaiki ,karki koma kuma ya fasa" A hankali ta 'karasa jikin mortar tana d'an ra'be-ra'be kanta a sunkuye.


"Get in" Ya fad'a.


Gidan gaba ta bud'e tana d'ar-d'ar ta shiga,har suka hau titi bame cewa komai tsit"Toh ina kuma zamu?"Ta fad'a ganinsa tayi ya kauce hanyar da zata sada ta da gida.


Kasa tambaya tayi ta zira ido tana ganin ikon Allah.K'aton gida taga yayi horn an bud'e masa ya shiga.Har lokacin bata gane inda aka zo ba,seda taga Shaheed yana fitowa daga ciki.


"Are you staying here forever?" Ta jiyo ya fad'a.


Da kanta ta bud'e 'kofa ta fito tana d'an taka wa a hankali so take ya shige gaba."Ina wuni"Shaheed ya fad'a lokacin da suka 'karasa


"Ina wuni" itama ta fad'a.


Handshake taga sunyi suka jero suna 'kus-'kus wanda ba ji take ba.Suna tafe tana binsu a hanya har suka 'karasa ciki,ba kowa a parlourn ta samu ta zauna a sofa,tana kallo ya nufi wani sashen Shaheed kuma ya hau sama.Not more than 3min sega Mom da Zakia sun sakko fuskarsu d'auke da fara'a suka 'karaso.


"Laila" Ta kira sunanta tana 'karasowa ta zauna daga gefenta tare da tallafo shoulder d'inta.Laila cikin jin kunya tayi 'kasa da kanta tare da du'kawa ta gaisheta.


"Get up,feel free daughter"


"Ya kike?"


"Lafiya lau" Ta daure ta 'Kalo murmushi.


"Ina yini" Cewar Zakia tana murmushi.


"Ina yini"


"My cutie sister please feel free,this is home"


Itade murmushi kawai take musu Mom tasa mey aikinsu ta kawo mata abin sha.


"Kada ki bari fa aiki yana miki yawa kiyi magana kinji se'a sami mey aiki""


Kai kawai ta kad'a ba tare da tace komai ba,tana hangoshi har ya 'karaso inda sike ko zama ya'ki yi kawai de ya gaisa da Mom ne Zakia se wani kallon gulma take masa yana harararta ji yake kamar ya mareta ganin Laila yasa ya 'kyaleta .


"Amjad talk to her to drink something" Mom tayi maganar dan ta gano ya zaman nasu yake.


"She is fasting" Taji ya fad'a.


D'ago idonta tayi har suna kallon juna yayi mata 'kiri gefen fuskarsa d'auke da murmushi.


Mom jinjina kai kawai tayi , inda Allah ya taimaki Amjad Monday ranar ta kasance.Daga bayan tashi yayi ya fita a mota ba tare da sunsan inda zashi ba,kad'an-kad'an Zakia tana janta da hira kawai amsata take dan yunwa ta gama kashe mata jiki rabonta da abinci tun 8:30am saboda yau da wuri tayi breakfast,addu'a take maghrib yayi tasan Mom zata had'a mata kayan shan ruwa har kusan maghrib Dad ya shigo suka gaisa,suna zaune Amjad ya shigo ko zama beyi ba yace ta tashi su tafi,Mom ba yadda ba tayi dashi ba ya bari tasha ruwa anan amma ya'ki dan har tasa an girka mata abinda zata ci,daga 'karshe de yace kawai tasa mata a food warmer se su tafi dashi.


"Mugu azzalimi" Ta fad'a a ranta.


Daga yadda yaga yanayinta ya gano tana cikin wani hali dan ya'ke kawai take."Let's go"Yayi mata murmushi.


Har mota suka rakasu suna tsaye suka fita daga gidan.Food warmer d'in tayi ta d'an d'agen wuya ko zata gansa d baya amma ba alamarsa,hanyar daya kamata suyi taga sun kauce.


"Where are we going to?" Ta tambaya.


"Mall,madam chef" Ya bata amsa yana murmushin mugunta.


Kai ta dafe ta kalli taga har wani duhu-duhu take gani,tana ji tana kallo yayi parking. "Let's go".


Ac dake busawa taji ta isheta,ji take kamar mey zazza'bi,yana tafe tana binsa a bayan se wani kalle-kalle yake kafin ya d'auki abu d'aya seya shafe fin 5min.


" Do you like this? " Ya d'akko wata doguwar riga iya gwiwa yana nuna mata.


"My wife is eager to go home ,but her husband is not readyyy"


Ji take kamar ta sha'keshi,haka ya gama d'age-d'agensa harda kara mata a jiki yaga wai yayi ko beba gabaki d'aya English wears yaita za'ba.8:42pm suka shiga gida ,ko kallonsa bata sake yi ba har suka shiga.kayan daya siyo leda uku ciki ya mi'ka mata ta'ki kar'ba,kan kujerar ya dire mata ya koma mota ya d'akko abincin har lokacin da ya dawo tana parlour. Yadda ya rungumo warmer d'in zaka san cewa ya taki rashin mutunci.


*Need your comment,I'm really busy but I tried hard to update coz I don't want to keep you guys waiting, I don't know If I can be able to update tomorrow, I'm really really busy.Love ur*πŸ’‹


*Dijensy*❀



🌼🌼 🌼🌼




πŸ’¦ πŸ’¦




*AMJAD*




πŸ’¦ πŸ’¦






🌼🌼 🌼🌼




*WRITTEN BY DIJENSY*


*WATTPAD:@dijensy*


πŸ…Ώ 0⃣9⃣


Binsa tayi da kallo tana jira taga mey zeyi da abincin,har kusa da ita yazo ya wuce ta gefenta yana rungume da flask d'in ya haye sama ya barta a tsaye tana had'iyar miyau.


Jitayi kamar ta bishi amma gudun karya wula'kantata ta nufi kitchen, seda ta fara had'a tea tasha tukun ta d'ora indomie sharp sharp ta gama da zafi-zafinta haka ta samu taci harda guntun hawayenta na takaici.Se bayan ta gama cin abincin ne ta tuna bata yi sallahan maghrib da isha'i ba,shima Amjad d'in tunawa tayi beyi ba."Tabb! La'ilaha illallahu maimakon yaje masallaci ,toh ko dama haka yake wasa da sallah?"Ta tambayi kanta tana mey mamakinsa dan ita shaf ta mance yunwa ta rufe mata ido batai noticing ba.


"Astaghfirillah" Abinda ta fad'a kenan ta koma d'akinta kayan kuwa ta barsu anan. Seda ta idar da sallolin da ake binta tukun ta samu nutsuwa,tana yin wanka tayi shirin kwanciyarta koh phone d'inta bata duba ba dan gajiya.


Washegari da safe kafin ta fito taji fitar Amjad, 8:20am agogon d'akin ya nuna.Inda ta bar kayan jiya anan tazo ta tarar dasu,ta'be baki tayi tai wucewarta kitchen "Ka kaiwa budurwarka ba niba"


***
Sati d'aya su Mom suka 'kara a Nigeria suka koma ,kafin su koma seda suka zo gidan Laila.Amjad ji yake kamar ya bisu ,tun lokacin da suka koma ya dena walwala ko kula Laila bayi yake ba balle magana ,kaya kuwa bata kwashesu ba se lokacin da Mami zata zo ta d'auke ta kaisu wani d'akin daban ta rife.


Saturday 8:17am,ta gama shirinta cikin lace black mey red torches,tasa sar'karta mey stones red color tayi matu'kar kyau ga d'aurinta da ya tsaru fuskarta tayi light makeup se 'kamshin turare take.Tana sauka 'kasa taga parlourn ma ba wani datti yayi ba dama jiya da yamma ta gyara shi,kitchen ta shiga dan had'a karin kumallo ,yau doya da 'kwai taji tana sha'awa ,tana d'ora doyan a pot ta nufi drawern dan d'akko bowl ,kasancewar tsahonta baya kaiwa setayi d'age tana janyo bowl d'in ya su'buce ya fad'o kan babban yatsanta na 'kafa Tass! Ya fashe pieces a wajen ,take ta saki wata 'kara dan azaba.Fuskarta tuni tayi jazir gumi yana keto mata,zaman dirshan tayi tana ri'ke da 'kafarta d'anyatsan se jini yake.


"What happ.." Be 'kare tambayar ba yayi shiru da bakinsa ganin yadda 'kafarta ke zubar jini.


Kuka ta shiga yi sharaf-sharaf hawaye yana zuba.


"Get up" Ya fad'a tare da d'ora hannu kan kafad'arta da niyyar mi'kar da ita.


"Aghhh!" Ta 'kwallo 'kara.


Jin 'karar da tayi yasa ya d'auke hannunsa,tana zaune ita bata tashi ba kuma bata dena kukan ba."Are you staying like this? "


Banza tayi dashi kamar bata jiba,yana sake d'ora hannunsa a kafad'arta ta kuma tsala ihu fin da.Ita bama iya zafin yasa ta 'karar ba ta'bata ne bata so yayi.


Tsaki yayi "It left for you" Ya fita daga kitchen d'in.Yana fita ta tashi se d'ingishi take,ganin jinin yana d'iga a 'kasa ta zauna kan wani couch a living room.Tana hangoshi ya sakko daga bene hannunsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login