Showing 33001 words to 36000 words out of 62917 words

Chapter 12 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt

DIJENSY   

14 Jan 2025

5791

cikin ranta taji haushi" Banyi dan kace nayi kyau ba"Tayi maganar a fili.


"I can understand all you're saying better watch your tongue"


Baki ta zun'buro ta mayar da mirror d'in, sam bata lura dashi ba yana ta satar kallonta,kayan jikinta ya amsheta sosai.Lace tasa maroon da torches golden se sar'karta ma golden data kwanta a wuyanta,fuskarta ma tayi makeup dede ,lipstick maroon tasa da eye liner kwalli ya fito tar a idonta.Mayafinta ma golden ne tayi d'aurin....(guess).


Zaman kurame sukayi har suka isa gidan Mami,ta bud'e 'kofar zata fita ya tsayar da ita."Don't expect me to take you back home ".


" Better "Ta fita.


Se bayan ta shiga ya shiga gidan ,yana gaisawa da Mami ya fita daya had'u da Fauzan a 'kofar gida ya bashi 10k 'yan 500 sabbi.


" Ashe de da sauran mutunci"Laila ta fad'a sanda Fauzan ya shigo yana nunawa su Mami.


"D'azu nayi waya da Maman shi take fad'a min Amjad d'in zeje can Canada d'in" Mami ta fad'a.


"Uhm..eh" Ta fad'a a ranta kuwa tunani ta shiga yi,da gaske yake ashe.


"Mami yaya gida zata dawo ko?Nusaiba ta tambaya.


"Eh toh.."


"Ehmana nan zan komo" Laila tayi saurin fad'a.


Dad'i taji sosai dama exam zasu fara ba dad'ewa ,a ranta tana fad'in"Na huta yaje can ya 'karata da ba'kin halinsa".


Laila bayan ta 'kare wuninta a gida wajen 5 :30pm ta tashi tafiya dan tasan ba zuwa ze d'aukanta ba.Lokacin da ta koma gida ta tarar yana gida,d'akinta tayi wucewarta.


Haka ta 'kare sallah ba inda ta sake zuwa,bayan 1week suka koma school,yanzu shirye-shiryen exam suke ba dad'ewa suke ba 12pm wani sa'in ta komo gida,ita jira take taji yayi mata maganar tafiyarsa amma shiru beyi ba.


8:05am ta sakko 'kasa,'karamar trolley dake girke a living room ta tsaya kallo bata gama sa'ke-sa'ke ba sega Amjad yana sakkowa daga steps. Yau ana ganinsa za'a san yana cikin farinciki,specs dake idansa ya zare.


"Home alone" Taji ya fad'a.


"Ni nace maka anan zan zauna?"


"You can speak the way you like to but you can't change it ,I'm leaving now".Yaja trolley ze fita Laila tace." I'm not staying here alone "


"That is none of my business, the decision is yours" Yayi mata waving bye cikin rainin hankali.


Tana gani driver ya amshi trolleyn yasa a bayan mota ,Amjad ya shige baya abinsa driver ya jasu suka fice. Bata 'kara ko minti d'aya ba tayi sauri-sauri ta haye sama.Nan take ta soma had'a nata kayan duk wani school things ta d'auka tazo duba phone d'inta kan drawer ta lura da kud'ad'e kan drawer d'in 50k ta gani.Handbag d'inta kuwa ta d'auka ta zira a ciki tasa wayarta key d'in gidan ta d'auka ta sakko bayan data kulle d'akinta,sauran doors na 'kasa ma ta rife tukun exit door taja akwatinta ,mey gadi ne ya samar mata Napep ta tafi.


Tun a hanya ta kira Mami take fad'a mata tana hanya.Tana shiga gida ta ajje akwatinta a d'aki ,se murna take."Se yaushe ze dawo?"Mami ta tambaya.


"Uhnmm.uh..3weeks" Ta kintata ta fad'a.


"Allah ya kaimu"


"Ameen" Ta amsa.


"Mami wainar gero nake son ci" Laila ta fad'a.


"Toh ta rashin ta idon zaki min" Cewar Mami.


Ita kwata-kwata Laila bata zaci za'a d'auki hakan da wani manufa ba da bata fad'a ba,kawai de ta dad'e bata ci bane shiyasa taji sha'awa.


"Kai mami nifa.."


"A'a kina sani kawai de tareraya irin ta yaran zamani"


Tashi tayi ta koma d'aki ta d'auko handout d'inta ta soma duba kayanta tunda su Maryam basa nan gidan shiru,wainar ma fasa siyowa tayi.


β˜…β˜…β˜…


Amjad kuwa koda ya isa be damu da kiranta ba ,shi sam hankalinsa ba anan yake ba baida buri irin ya had'u da Rosie.


Mom ,Zakia da Shaheed ne suka taro shi a airport,Dad yayi tafiya,Mom ce first d'in ganinsa cikin sauri ta 'karasa tayi hugging d'insa tightly."My baby ,missed you so much"


"Missed you too"


Jitai kamar karta cika shi,su Zakia ma sukai hug lastly Shaheed, brother's hug


Tunda suka taho a mota zuwa gida Mom hirar Nigeria take masa tana tambayarsa amma yana amsa mata kad'an -kad'an wani abun ma 'karya yake mata idan yaga ta isheshi.


"Laila told me she's staying there with her Mom" Yaji Mom ta fad'a.


"Uhmm" Ya kawar da maganar amma a ransa yayi 'kwafa dan shi bece mata ta tafi ba.

Dinner na musamman aka shirya masa, se ji dashi Mom take zakia har tana tsokanarsa momy's bae amma wannan karan be taya ta ba.Sam ranar be samu chance ba balle yaje wajen Rosie, se washegari da safe 10am bayan sunyi breakfast yace zeje wajen Sam abokinsa duk da kuwa Mom jikinta ya bata wajen Rosie zeje.Be tashi zuwa ba seda ya siya mata flowers da bracelet mey tsadan gaske,har wani rawar jiki yake.


"Angel I'm on my way to your house"Ya tura mata text.


Few minutes later ya isa gidan,3missed call yayi mata bata d'aga ba,yasan wani lokacin tana yin haka idan tana so tayi surprising d'inshi sometimes seya shiga gidan.'Karasawa yayi hannunsa ri'ke da flowers d'in se bracelet d'in a aljihunsa ,knock! knock! Yai knocking ba'a bud'e ba.Handle d'in ya murd'a ya Shiga.

" Hello"


"Hello"Ya 'karasa living room." Hel...."


'Karashen lo d'inne ya ma'kale a ma'kogoro dan tsananin tashin hankali ,jiyai kunnensa ya dena jin sound tsaiwar ma da'kyar yake.Irin yanayin da ya tsinceta yasa ya kasa magana,a zuciyarsa yana 'kokonto anya Rosie d'insa ce.Tana zaune a cinyar wani guy da besan waye ba suna kissing passionately ,tana sanye da wani fitinannun sleeping dress wanda dashi da babu duk d'aya.Guy d'inne ya fara lura da Amjad dake tsaye kamar gunki,ganin guy d'in ya dakata yasa ta d'ago tana kallon direction da yake kalla."Amjad "Ta fad'a a hankali cikeda mamaki....




*Duba da yanayin lokaci azumi na tahowa ,shiyasa na maidashi page 2 in 1,and na 'kara tsahon page d'in,hope hakan yayi muku.Don't forget to vote.*



*Dijensy❀*















































🌼🌼 🌼🌼




πŸ’¦ πŸ’¦




*AMJAD*




πŸ’¦ πŸ’¦






🌼🌼 🌼🌼




*WRITTEN BY DIJENSY*


*WATTPAD:@dijensy*






*Sorry for the late update*




1⃣5⃣ - 1⃣6⃣




A inde yake tsaye ya yasar da flowers d'in ba tare da ya san yayi hakan ba ,kamar 'kiftawar ido ya fita daga gidan. Da fitarsa da shiga mota be wuci 'yan sakanni ba,tu'ki yake amma besan inda zashi ba,seda ya tabbata yayi nisa da area d'in ya samu yayi parking can bayan gari."No!"Ya daki steering d'in motar ya zira yatsansa cikin sumarshi se mutstsukawa yake kamar ze cire gashin kansa."It can't be,No! Rose why? why?"be ankara ba yaji idanuwansa na tsiyayar hawaye,feeling his heart broken into pieces.
Tunanin rayuwarsu da suka shafe tare ya shiga yi,ko a mafarki idan aka ce Rosie zata ci amanarsa baze yarda ba amman yau ya gani da idansa.


Yafi 20 min yana abu d'aya wayarsa da tayi ringing yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.


"Mom" Ya gani a jikin screen.


Ta kira har sau uku amma ya'ki d'agawa,lokaci guda yaji ciwon kai ya kamashi.Da 'kyar ya samu ya iya komawa gida, image d'inta ya'ki gushewa daga idansa.


Mom ganinsa ya shigo gida tayi sauri ta 'karasa inda yake."Son, where have you been? are you ok?"


Kai kawai ya kad'a yana 'ko'karin cire jacket d'inshi.


"Amjad, you're looking sick" Ta fad'a tana dafa kafad'arsa fuskarta d'auke da damuwa.


"Mom ,I just need to rest"Yayi 'ko'karin fad'a.


"Ok ,go to your room I will prepare your a meal immediately you woke up"


Yana shiga d'akinsa ya rufo 'kofar,yana ciro wayarsa daga aljihu sega kiran Rosie.


"Baby boo" Ya bayyana a screen.


Gabaki d'aya wayar yayi switching off ya cilla gefe,ya fad'a kan gadon ya rufe idansa trying to force him self to sleep.


An hours later,2:30pm ya farka har lokacin kanshi be dena ciwon ba,tashi yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa yayo alwala ya tada sallah.


Knock! Knock! Mom tayi knocking ,ganin be bud'e ba ta murd'a handle ta shiga,sallah ta tarar yana yi haka yasa ta koma.Chicken Spaghetti ta dafa mashi tayi arranging,tana gamawa ta koma sama ta kirashi.


Ga abincin yasa a gaba amma ya kasa ci ,Mom data san Chicken spaghetti ne favorite d'insa tayi mamaki ganin ko fork d'in be d'aga ba.


"Amjad, don't you wanna eat?"


"I lost my appetite"Yana fad'ar haka ya mi'ke ya bar wajen.


" Am.."Bata 'kare ba taga har ya 'bace mata daga gani.


β˜…β˜…β˜…


Laila


7:12pm suna d'aki ita dasu Maryam se hirarsu suke ta mance da wani Amjad,idan Mami ta tambayeta suna waya da Amjad setace eh,wani lokacin har alarm take sawa idan yayi ringing setai pretending kamar kiran waya ne.


Amjad kuwa cikin dare 11:00pm sam ya kasa bacci kawai juye-juye yake akan gado daga ya rufe ido Rosie yake gani da wannan guy d'in,tashi yayi ya d'auko wani box a 'kar'kashin gado.Hotuna ne ciki na Rosie harda wanda sukai tare dashi tun suna teens daga gefe kuwa teddy ne 'karami mey heart a cikinsa wanda Rosie ce ta bashi wani lokaci da yayi birthday. D'aukansu yayi ya tarkata duka ya fita can backyard ya cinna musu wuta yana kallo har suka 'kone ya watsa tokar a dustbin.Hatta phone d'insa babu wani abu na Rosie daya bari pictures nata na musamman daya tanada musu folder seda yayi deleting,seda ya tabbata ba abinda ya ragu nata a wayarsa ya iya samun yin bacci.Amjad sam be iya so ba haka be iya tsana ba,ya tsani yaudara mutum ne mey zafin kishi ko Zakia idan ya ganta da wani classmate bama boyfriend ba seya ji haushi.


"I hate you like hell"


"I hate you forever,I never wanna see your face again"


Idansa a rufe yake fad'ar haka ,firgit! Ya farka ,se lokacin ya lura 5:54am yayi,nan ya tashi yayi sallah.Yana idarwa ya sauka 'kasa "Morning"


"Morning" Mom ta amsa.

Da 'kyar ya samu ya iya yin breakfast d'in, data tambayeshi meyake damunsa ya'ki fad'a.


β˜…β˜…β˜…


Amjad ko kwana uku beyi ba ya koma Nigeria dan ji yake kamar a kan 'kaya yake a Canada,sede ba wanda yasan Nigeria ya koma 'karya yayi musu yace Ethiopia yaje daga can ze wuce Nigeria.


Yana komawa Nigeria ya cigaba da zuwa aikinsa dan so yake ya mance da komai har 'karawa kansa lokaci yake kafin ya tashi se wajen 5:30pm,daya koma gida ma baya hutawa wani aikin ze tsiri yi yaita dube-dube a system, a 'yan kwanakin da akai har ya rame da an ganshi za'a san yana da damuwa.


Laila kuwa cikin kwanciyar hankali take exam d'inta,ji take kamar ta komo gida kenan dan ko maganar komawa bata yi.Seda suka kwashe 2weeks da 'yan kwanaki suna exam,yanzu anyi hutu na 'yan weeks kad'an.Yanzu ta komo hawa online sosai ba kamar sanda suna exam ba idan ba abu daya shafi karatu ba bata bud'e data.


Yau bayan sun gama cin abincin dare,su Maryam suna parlor suna kallo ita kuwa tana d'aki se chat d'inta take hankali kwance.


9:45pm,yana d'aki be jima da dawowa ba daga restaurant kullum seya je yaci abinci acan,yana watsa ruwa ya d'auka waya ya hau whatapp chat ,abinda ya dad'e beyi ba.Contact ya shiga yana ta duba numbers ,yazo N letter idansa ya sauka kan Nigeria,daya duba kuwa yaga tana online. Profile d'inta ya shiga viewing inda yaga profile picture d'inta dake d'auke da photo d'inta tayi rolling da red mayafi kuma fuskarta tasha make-up sede ba duka ta d'ago fuskar ba ta d'an sunkuya inba wanda yasanta ba baze gane itace ba.


"Hi" Yayi sending da 'kyar dan ya dad'e kafin ya iya turawa.


Tana cikin chat taga "hi" data dubi number d'in taga na Amjad ne ,tafi 10min kafin tayi reply da .


"Hello" Tayi reply.


"Why are you chatting at this time, aren't you suppose to be reading ?"


"Exam is over ,hutawa zanyi"


"What did you mean by those last words?"


"You don't need to know"


"Ok,can you please change that profile pic with something better? coz you're looking ugly"


"I choosed it myself and I like how I'm looking"


Murmurshi abinda ta fad'a yasa shi."But I don't like it"


"I don't care"


"Ok,where are you now?"


"Home"


"You're Lying, Mom told me everything"


"Your house is not my home, I'm referring to Mami's house"


"Good for you,you're soon coming back"


"No"


"You must"


Laila: "When are you coming back?"


Amjad:" Do you care?"


Laila: "No"


Amjad: "Then why did you ask?"


Laila: "Just wannan know"


Amjad: "I knew you missed me"


"Wallahi a'a"


Amjad:"Lier"


Laila:"I'm not"


Amjad:"You are!"


Daga haka bata sake tura wani abu ba tayi banza dashi ta cigaba da sauran chat d'inta. Amjad kuwa da tun tini dama da ita yake chat in banda it a ba kowa,ganin shiru ya sake yi mata magana.


Amjad:"Laila"


Laila:"Mene?"


Amjad:What is your problem?

Amjad: What is the meaning of "mene" ?


Laila :"It means "what"


Amjad: What of "why" Ya sake tambaya dukda kuwa ya san ma'anar kawai jan magana be.


Laila: "Meyasa"


Amjad:I gerrit,what of "Ni nace" You often say the words.


Laila:I'm not a teacher, I'm going to bed"


Amjad:😏 who care to learn your language? disgusting!


Laila:Eh d'in chat d'in ma baza a sake yi dakai ba"


Amjad:Rubbish!


Sauka tayi daga chat d'in ta zira charger a wayarta tayi shirin kwanciya,tana kwance chat d'in da sukai yana ta dawo mata wani abun ya bata dariya wani ya bata haushi.Se to 11:30pm tayi bacci.


Ta 'bangaren Amjad kuwa ganin ta sauka ya koma Instagram,"Lai-mus" sunan da take amfani dashi a insta.526 followers,jiyai ya damu da yaga followers d'in kad'an-kad'an yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login