Showing 24001 words to 27000 words out of 62917 words
Chapter 9 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt
ya ri'ko first aid.
"Cabb! Zaka ga first aid"
Bata ankare ba taga yaja wani guntun table ya zauna opposite da ita."Let me see"
"Kaga mey? kai likita ne?"
Ko bin ta tata beyi ba ya kama 'kafar se fisgewa take amma ta kasa "Aghh!"Se 'kara take yayi banza da ita yana goge jinin se kuka take, seda ya gama ya rife ciwon da bandage tukun ya sake mata 'kafa.
" Allah ya isa"Ta fad'a a fili tana share hawaye.
"You have to be careful"
"Ni matsa min na tashi" Ta fad'a tana 'ko'karin mi'kewa.
Maimakon taga ya tashi seyai zamansa yana kallonta.
Kasa balancing tsaiwarta tayi ta fad'a kan couch d'in.Ganin ya sake matso da kujerar yasa hantar cikinta ya soma kad'awa,ta sunkui da kai tana jin idonsa a kanta.
"I need to know why,why did you agreed to married me?"
Shiru tayi ta kasa cewa komai tana murza yatsa."I'm asking"Ya sake matsowa har takai baza ta iya mi'kewa tsaye ba."Please let me go"
"Until you answer my question"
"I never married you because I love you,they..they forced me to"Ta fad'a da 'kyar.
"Wow! I hope what you're saying is true"
"Now what is your plan? Run away?"
"Please!".Ta ro'keshi data bata sake.
Tashi yayi tsaye ya d'auke first aid d'in ya haye sama,tana gani ya tafi tayi sauri ta bar wajen ta koma kitchen tana d'ingisawa,wajen daya 'baci da jinin ta gyara a daddafe ta 'karasa had'a breakfast d'in taci kayanta.
Tunda ta koma bata sake fitowa ba se bayan zuhr,tana ganinsa a parlour yana kallo tai 'kasa da kai bata so ta had'a ido dashi.Shiko be sake yi mata maganar 'kafar ba balle yai mata sannu.
Laila da daddare ta kira Mami tana ta shagwa'ba ita a lalle taji ciwo Nusaiba tazo.Washegari Mami ta turosu Nusaiba harda Fauzan amma basu kwana ba.
Tun bayan tafiyarsu Laila ta soma jin sauyi game da ita,kad'an-kad'an mararta ta soma ciwo tun bey takura mata ba har ta kasa jurewa.Ta kwanta se mutsutstsuka 'kafafuwa take tana dafe ciki,tunani ne ya fara zuwan mata na MP date nata data lissafa taga lokaci yayi." Tir'kashi!"
"Ya zanyi?"Tana ta sa'ke-sa'ke a zuciyarta ko zata samu mafita,8:18pm taga agogo ya nuna juyi kawai take ta rasa inda zata saka kanta gashi idan a gida ne magani take sha wani sa'in Mami ta had'a mata black tea ta kur'ba amma yanzu ba d'aya.Hawaye ne kawai yake tsiyaya daga idanunta tana tausayin kanta na halin rayuwar data shiga.9:03pm a daddafe ta tashi ta sauka 'kasa ,a kitchen ta had'a tea kad'an ta samu ta daure ta kukkur'ba ga yunwa data ke ji amma bata jin zata iya cin komai.D'akinta ta koma ta cigaba da aikin juye-juye,gashi tana tsoron gobe monday tasan da wuri zey fita,idan kuwa ta bari ya fita tana cikin matsala dan bata da ko sisi balle tace zata fita suyo wani Pad dan duk 'Yan kud'ad'enta ta 'karar wajen saka credit last siyan ma shine dasu Fauzan suka zo ta aikesu suka suyo mata na 500 d'in.Se can bayan 30min bacci ya kwasheta da ciwon ya lafa.
5:46am ta farka taga har subh tayi,da 'kyar ta iya tashi dan a halin data tsinci kanta mey faruwa ta faru bata san kuma ya zatai ba yau.Wata zuciyar ce ta bata shawara ta fad'awa Amjad,tana jin kunya haka tayi knocking 'kofarsa lokacin 6am.
Tafi 6min kafin ya bud'e mata ,daga ganinsa ta gane lokacin ya tashi daga bacci.
"Morning" Yaune lokaci na farko data ta'ba gaisheshi.
Da'kyar yake bud'e idanuwansa "What?"
Wayar hannunta ta mi'ka masa bayan data gama danne-danne a cikin.
Kamar baze kar'ba ba yasa hannunsa ya kar'ba"Read"Ta fad'a tana kallon gefe.
"I want to use pad" Yaga ta rubuta ta note app.
"So?"Ya fad'a ba tare da ya nuna damuwa ba.
Hannunta ta mi'ka alamar ya bata wayarta a lokacin kuwa idanuwanta sun cika da 'kwalla jira take kawai ta bar wajen.
"Check in what you have thrown away the other day"Abinda ya fad'a kenan ya mi'ka mata dan yasan bata duba kayan ba dan da ta duba da bazata tambdaya ba.
Tana gama karancewa ta tuna da inda ta ajje kayan,kunyace ta lullu'beta tana da tasani duk da ba haka ba.A kunyace ta juya zuwa d'akin data yasar da kayan.
Tana dubawa tagani kuwa se lokacin taji relief,da sauri ta komo zuwa d'akinta da pad pack d'in a hannunta ,mamaki ne da kunya ya sake lullu'beta lokacin da taga yana tsaye har lokacin a 'kofar d'akin kamar jiranta yake.Basar wa tayi ta wuce a hannun hagu ta ri'ke yadda baze gani ba tai sauri ta shiga.Shi dariya ma ta bashi (Gani na yaushe kuma).Tana shigewa shima ya rufo 'kofarshi,se lokacin yaje ya d'auro alwala dan yin sallah.
โ
โ
โ
A kwana a tashi har sun shafe kusan 4month,sun saba da irin zamansu yanzu kowa baya damuwa da kowa wannan itace rayuwar da suka za'barwa junansu.Laila har ta samu admission a BUK ,kafin ta fad'a masa seda aka kwana biyu taci sa'a bece komai akai ba kud'i kawai ya bata na registration shi a yanzu besan ma lokacin da zata fara zuwa ba be tambaya ba kuma bata fad'a masa ba.Ita kuwa ta 'bangaren ta ranar Monday kawai take jira dan shine sanda zata fara shiga lectures ita har ta 'kagu lokacin yayi ta huta da zama shiru.Mom lokaci-lokaci suna waya da ita ,shima ta 'bangaren Rosie ba abinda ya chanja har yanzu bata san wani abu game da auren Amjad ba.
***
Monday
Da asubar fari ta farka saboda d'okin makaranta,tana idar da sallah tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na material purple colour,powder kawai ta shafa se lip gloss ta shafa turare mey taushin 'kamshi.
Hijab d'inta da tasa aka kawo mata daga gida ta d'akko d'aya daga cikin kalar kayanta ,zira abinta tayi se niqab d'in kuma ta ri'ke a hannunsa had'e da handbag d'in ta saki ta kalmi ta sauka 'kasa.
Ba wani breakfast mey d'aukan lokaci ta had'a ba ,tea kawai tasha da toasted bread.Tana fitowa daga kitchen d'in ta d'aura niqab d'inta dede lokacin Amjad yake sakkowa daga bene cikin shirinsa na Blue suit ciki kuma white shirt se black jeans ya rife idonsa da specs.
*Short chapyy and boring I think.Akwai d'aya daga cikin littafina wanda shine na farko da na fara rubutawa sede Allah besa na kammala ba,a bisa complain da nake samu game da rashin 'karasawa inshaAllahu bayan na kammala wannnan zan cigaba da HASHIM ABDALLAH amma bata blog ba zan dawo dashi wattpad ina tunanin hakan zefi sau'ki.Masu son d'ayan littafin mey suna SON ZUCIYA zaku iya samunsa ta wannanan khadijasko.blogspot. com*
*Dijensyโค*
๐ผ๐ผ ๐ผ๐ผ
๐ฆ ๐ฆ
*AMJAD*
๐ฆ ๐ฆ
๐ผ๐ผ ๐ผ๐ผ
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
Ina godiya Amjad fans ,musamman 'yan whatapp ,one luv๐
๐
ฟ 1โฃ0โฃ
Tana kallonshi ta cikin niqab d'in ta sunkui da kai,tana jinsa tsaye yana kallonta."Where are you going to?"
"School" Ta amsa a ta'kaice.
"Why did you dress this way?" Ya fad'a tare da nunata da yatsa daga sama har 'kasa.
Shiru tayi bata amsa shi ba har lokacin bata d'ago da kanta ba."Are you a terrorist? "
Jin abinda ya fad'a yasa tayi saurin d'ago da kanta tana kallonsa "Kana musulmi kake irin wannan maganar" Ta fad'a cikin ranta.
"I'm asking you?"
"Muslims are not terrorist" Ta fad'a tare da kawar da kanta gefe.
"Whoa! so Amjad is not a Muslim, may be I'm Christ or jews right?"
Ganin zey 'bata mata lokaci ta gyara handbag d'inta ta wuce."Do I ask you to go?"Taji ya fad'a.
'Karasowa yayi inda take ya zagaya yanda zata ga fuskarsa dan ko juyowa batai ba."Answer me"
"No"
"Then why did you?"
"Because I have to"
"Now,did I ask you to stop"
"Rainin hankali" Ta fad'a a ranta.
Be sake wata maganar ba ya wuceta ya fita tana tsaye."Mtchww!"Taja tsa'ki itama ta nufi wajen bata ko kalli inda yake ba ta nufi bakin gate tayi ficewarta.Ba abinda ya 'kona masa rai irin yadda ta fita bata ko damu ta rufe 'kofa ba.Da kanshi ya koma ya rufe 'kofar tukun ya shiga motarsa ya fice.
Tana tafiyarta taji horn mey uban takura ba 'ka'k'kautawa tana juyawa taga motarsa ce,seda yazo daf da ita kamar zey bigeta ya zuge glass d'in motar.Cikin suit d'insa ya zira hannu ya zaro 2k 'yan d'ari biyar ya mi'ko mata da hannun hagu a wani wula'kance.
Ranta inyayi dubu ya 'baci,kawar da kanta tayi ta cigaba da tafiyarta ita kad'ai tasan mey take ji a ranta.Tana cikin wannan halin ne bata ankara ba taji an fisgo hannunta.
"How dare you shun me like that?" Ya fad'a ransa a 'bace.
A 'kufule ta d'ago da idanunta ta kalleshi cikin glasses d'insa suka had'a ido."Kai wawan ina ne ,ka sake min hannu! "Ta tsawata tana 'ko'karin fisgewa.
" Come on fight back"
Ri'kon da yayi mata ba 'karamin zafi yayi mata ba kuka ne yake son ku'buce mata amma hakannan ta daure dan a ganinta babbar asara ce yaga hawayenta.
"Let me go"
"Make me"
Doke kafad'arshi ta shiga yi ba 'ka'k'kautawa tana fisge-fisge,da 'kyar ta samu ya cikata .Bata ko tsaya ba tayi sauri ta tari wani Napep dake shigowa street d'in,ta gwammace an bi da ita ta wani titin data bi ta hanyar da zata sake ganinsa.
Tana barin gun ya koma motarsa cikin zafin rai ya fizgi motar ya bar wajen.Laila a d'an sahu bata ankara ba taji hawaye na bin 'kuncinta,kuka mara sauti ta shiga yi har ta kusa isa school tukun ta d'akko tissue a jakarta ta goge fuskarta,3k da sukai saura na registration d'inta a ciki ta d'auka N500 ta bawa mey d'an sahu ya mi'ka mata chanji ta wuce.Tana shiga school d'in daga kan wani bench ta zauna,tunanin irin abinda yayi mata ta shiga yi ji take kamar daga makarantar ta gudu gida,a ranta tana tunanin Baba ,da ace be rasu ba da tuni tana gidansu.
"Assalamu Alaykum" Taji muryar mace.
Tana d'ago da kanta taga ba'kuwar fuska"Waalaikissalm"Ta amsa tare da yin guntun murmushi.
"Baiwar Allah kema sabuwar d'aliba ce?" Ta tambayeta.
"Eh" Laila ta amsa muryarta kusan a dashe.
"Wani course?"
"Microbiology" Ta amsa.
"Ashe course d'in namu d'aya"
"Allah ya bamu sa'a" Laila ta fad'a.
"Ga nan ki zauna" Laila ta matsa mata.
"Ya sunanki?"
"Laila" Ta amsa.
"Ni kuma Aliya ta fad'a.
Daga haka duka su biyun sukai shirun dan Aliya taga kamar Laila bame son surutu bace,ita kuwa Laila ba kasafai take sakin jiki da ba'kin fuska ba inba wai ta zauna ta fahimci halayyarka ba.
An d'auki kusan 1ยฝhr a haka kowa d'an danne-dannen wayarsa yake a hankali wasu students d'in na zuwa lokacin suka had'u da course mate d'insu.
10:30am suka shiga first lecture, kowa yana jin ba'kunta class yayi shiru ana sauraron lecture Aliya tana kusa da Laila.Seda aka kwashe kusan 1โ
suka fito daga class,tana jin yunwa amma sam bata jin zata iya cin abinci.
Basu suka sake shiga wani lecture d'in b se bayan zuhr,se 4pm ta komo gida."Tir'kashi!"Ta fad'a ganin 'kofa a kulle,ita sam ta manta da batun wani key na gida balle har tayi tunanin fita dashi.Ga yunwa tana ji banda gajiyar data kwaso,kan steps na bakin 'kofa ta zauna tana addu'a Allah yasa ya dawo yanzu duk da kuwa ba son ganinsa take ba.Zama tayi-tayi shiru har ta gaji,se to 5:45pm ya shigo gidan ,tunda ta hangoshi ta kawar da kanta gefe tare da sakin niqab d'inta ta rufe fuskarsa ko idanunta baza a gani ba.
Cikeda ta'kama ya 'karaso yiyai kamar be ga mutum ba.Gefe ta matsa masa karya bangaje ta,tana jin ya bud'e 'kofar ta mi'ke har ya shiga yana 'ko'karin rufewa ta ri'ke handle d'in.Ba tare da yace komai ba ya wuce ta shigo sannan ta rife ,ko d'aki bata je ba ta shiga kitchen.Wani ragowar donot da tayi tun shekaran jiya ta d'auko ta had'a da orange juice taci sannan ta koma d'aki.Seda tayi sallahr maghrib tukun ta watsa ruwa ta zira doguwar riga mara nauyi na material ta koma kitchen ,jollof d'in macaroni kawai tayi kad'an taci ta koma d'aki.
Washegari ma da wuri ta tashi ta had'a breakfast mey nauyi-nauyi bayan data d'anyi gyara-gyaranta tai shirinta yauma bayan ta zira hijab ta d'aura niqab d'inta, tana rufo 'kofar d'akinta shima yana fitowa,waya ce ma'kale a kunnansa yayi shirinsa cikin black T-shirt da jeans ba'ki fuskarsa yau ba specs."Bye Darling "Ya fad'a ganin Laila tana kallonsa yana sane ya tsiri kiss ,wayar ya kara a bakinsa yanda Rosie zata ji sautin kiss d'in,(Irin kiss da shaheed kapoor ya kewa Sonakshi a R..rajkumar ,lol). through phone.
Kanta ta kawar ba tare da ta kallesa dukda kuwa taji shi,dama tasan da biyu yayi hakan kuma ko a jikinta." Jealous"Taji ya fad'a.
Key taga ya mi'ko mata ta gefe,hannu tasa ta kar'ba ba tare da ta d'ago ba tayi wucewarta.Yau ma kamar jiya tana tafiya taji wucewar motarsa ,seda ta jima kafin ta samu d'an sahu dan sanda ta isa school ma har an shiga lecture,inda Allah ya taimaka ma Aliya ta samar mata seat.seda sukai 2hrs lecture cir suka fito ,ko 10min basi ba suka sake shiga wani lecture d'in se 12pm suka fito daga nan suka wuce cafeteria cin abinci. Kad'an-kad'an suna hira da Aliya,suna haka ne wayar Aliya tayi 'kara cikin fara'a ta amsa kiran.Ta d'au lokaci tana wayar kafin daga bisani ta katse."Sorry na zaunar dake"Aliya ta fad'a.
"Babu komai" Laila tayi murmushi.
"Ke gwara ke daga kin koma gida hutawa zaki,ni kuwa senayi girki" Aliya ta fad'a.
"Uhnn..kina da aure?" Laila ta tambaya.
"Au ban fad'a maki ba ko? Wata shida kenan" Ta amsa.
Jinjina kai kawai Laila tayi tana mamakin hakan dan ta zaci Aliya budurwa ce ,dan ko a fuska tafi nuna yarinta a kan Laila.
"Lalle kam hakane" Abinda ta fad'a kenan ta kawar da zancen.
Lecture d'aya suka 'karayi suka tafi,yau bata bi takan abinci ba wanka kawai tayi ta zauna tana hutawa abinta.
Laila seda ta jera sati biyu tana zuwa school ba tare da ta nemi kud'i gunsa ba,a 'karshen satin seda ta koma tafiya da abinci school dan kud'inta yayi 'kasa,gobe Monday 50 Naira ce kawai ta rage bata san kuma ya za'ai ba.
9:39pm,ta sakko 'kasa shan ruwa tana shiga kitchen d'in ta ganshi zaune kan stool yasa fruit salad a gaba yana sha,d'ayan