Showing 18001 words to 21000 words out of 62917 words
Chapter 7 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt
komawa sama sega Amjad yana shigowa.Tsayawa yayi yana kallonta itama hakan daga bisani ta soma hawa bene kanta a sunkuye.
"Hey"
Chak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.
"What is your name?"Taji ya tambaya.
"Kutt! Raini" Ta fad'a a ranta.
'Kin juyowa tayi har seda ya 'karaso inda take tukun ta juyo."I'm asking you,what is your name?"
"Laila" Ta amsa ciki-ciki ba tare da ta kalleshi ba.
"Why are you here?"Ya sake wata tambayar.
"Nima ban sani ba" Yadda tayi maganar da sauri.
Anzo wajen wannan yaren da baya son ji shi zatayi masa?
"Talk to me in English"
Yitai kamar wata kurma tana tsaye batace komai ba.
"I'am talking to you" Yanda yayi maganar cikeda 'kosawa.
Anfi 2min batace komai ba kuma bata tafi d'akin ba.
"She don't understand English? fuck up!"Yayi maganar a hankali.
Taji sarai amma tayi kamar bata fuskanci mey yake fad'a ba.
" Aiko inde turanci ne ka dena jinsa inde kana nan,Hausa ce ba fashi"Ta fad'a a ranta.
Wucewa yayi ba tare da ya sake wata maganar ba tana ji ya doko 'kofa.Itama d'akinta ta shige ta zauna wayarta dake gefe ta d'auka ta kira Mami.
"Mami ina kwana"
"Lafiya lau"
"Ina su Maryam? Anjima zasu zo?
" A'a suzo siyi miki meh? bade yanzu ba"Mami ta fad'a .
"Mami meye a ciki idan sunzo"
"Bafa zasu zo ba,ki gaida Amjad d'in ba'kina zasi tafi se anjima"
Bata kuma wani maganar ba mami ta katse wayar.Wata 'kwallar takaici ce ta zubo mata ganin ba ta ita ake ba basusan halin da take ciki bama.
Kuka ta shiga yi harda sheshshe'ka cikin 'kan'kanin lokaci tayi bacci.
Bata yi 20min da kwanciya ba taji 'karar kid'a a gigice ta farka kanta yayi mata wani mugun nauyi zuciyarta na bugu da sauri-da sauri.
Amjad da gayya ya 'kure volume d'in so yake kawai ya takura mata.
"Innalillahi wannan yana kuwa da hankali?" Ta fad'a a fili.
Baccin da batai ba kenan,tayi game har charge d'inta ya 'kare.Zama tayi-tayi har 'karfe 1pm tukun ta tashi tayi sallah,'kugin da cikinta yake ne yasa ta kasa sukuni.
Dole ta fito ta sakko 'kasa kitchen, dube-dube tayi tayi a locker bata ga komai ba har ta d'akko bread ta lura da wani corridor koda ta duba taga 'kofa tana bud'ewa taga kayan abinci taff a ciki.
Nan da nan ta d'ibo dankali ta fere a take tayi blending pepper cikin 'kan'kanin lokaci ta had'a faten dankalinta se 'kamshi yake ta cika 'kasan da 'kamshi.
Stool taja taci abinta a kitchen ta kora da juice yanzun taji normal ,'yan kwanukan datai amfani dashi ta d'auraye.Tana fitowa daga kitchen kanta a sunkuye taji tayi tuntu'be da mutum.
*Don't forget to comment,vote and share*💋
*Dijensy*❤
🌼🌼 🌼🌼
💦 💦
*AMJAD*
💦 💦
🌼🌼 🌼🌼
*WRITTEN BY DIJENSY★*
*WATTPAD:@dijensy*
🅿 0⃣7⃣
Ko bata d'ago da idonta ta kalleshi ba tasan waye dan haka ta matsa gefe ba tare da ta d'ago kai ba.
"Blind, watch out!"
Wucewa tayi ta barsa a gun a ranta tana mey jin zafin maganar da yayi mata.Shikuwa daya shiga kitchen warmer dake kan drawer ya fara gani ,ganin abinda ke ciki yasa yayi wani murmushin gefen fuska a take ya d'auka ya nufi d'akinta.
Knock! Knock!
Take hantar cikinta ta kad'a ba tare da tayi tunanin hakan ba,batasan dalilinta na tsorata ba.Tana bud'e 'kofar ta ra'be jikin 'kofar tana sunkui da kai.
"Look up,madam chef"
Tana d'agowa taga food warmer dake hannunsa."Who do you keep it for? "
Shiru ba amsa"Me?"Yayi pointing kansa.
Kai ta girgiza alamar a'a."Then who? Pets ?"
"Ni ba wanda na ajje wa"
"Oh god!"
"Look at me" Ya fad'a.
"I said look at me"Ya sake maimaitawa.
Tana d'ago da kanta ta kawar dan bazata iya had'a ido dashi ba." I.. don't.. understand... your.. language.."Yanda yayi maganar dalla-dalla.
"Nima bana gane naka" Ta turo baki.
"Ke?" Taji ya fad'a tare da nunata da d'anyatsa.
"Ashe kana ji " Ta fad'a a ranta.
Matsawa tayi daga pointing d'in da yayi mata ta kalli gefe.
Phone Ring!
"Mom" Ya gani a jikin screen.
"Hello"Ya fad'a bayan tayi picking.
"You don't even mind to call me""
"No Mom"
"How you doing?"
"I'm doing good" Ya amsa.
Ita de Laila komawa tayi kan gado ta zauna ta juya gefe ba tare da ta kalli inda yake ba,shikuwa yana tsaye har lokacin flask d'in yana hannunsa d'ayan hannunsa ya ma'kala phone a kunne.
"Laila?" Ta tambaya.
Seda ya d'au kusan 2min kafin yayi magana."She is doing ok"
Tana zaune taga an mi'ko mata waya."Mom"Ya fad'a yana binta da kallonta banza
Cikin girmamawa ta gaisheta tana gama wayar ta mi'ka masa."Gashi"Ta fad'a.
Harara ya watsa mata kafin ya fisge wayar har farcensa yana 'ko'karin cakar hannunta."'Kasami"Ta fad'a a ranta.
Kan gadon ya d'ora mata abincin "Finish it" daga haka ya fita ko 'kofar be rufe ba.
"Ca akai ma ni mayunwaciya ce?" Ta d'auki flask d'in ta dire a 'kasa bayan ta rufo 'kofarta ta koma ta cigaba da aikin zama.
Haka ta cigaba da zama har maghrib bayan tayi sallah ta tuno wayarta ba charge,drawer ta dudduba ba alamar charger nan ma hankalinta ya tashi,ita de tasan wannan mara kirkin ba sauraronta zey ba.Flask d'in data dire a kasan ta janyo ta soma ci ko chokali babu haka taci dan bason sauka 'kasa take ba, kad'an ta rage ta tashi wanke hannu daga nan ta d'auro alwalar isha'i. Tunani ta fara yi ko taje ta tambayeshi sede kuma tana tsoron wula'kanci,hakannan ta ha'kura da charge d'in wajen 9:14pm tai kwanciyarta.
*Washegari*
Da asubahr fari ta tashi bayan ta idar tayi wanka tai shirinta cikin doguwar rigar atamfa blue me ratsin pink tayi mata chif a jikinta d'ankwalin ma ba wani d'auri ta tsara ba ture kaga tsiya tayi ita kanta data kalli mudubi dariya ta shiga yi data kwance seta sake yi 'karshe de ta ha'kura ta barshi ,powder kawai ta shafa se kwalli data sa sosai tayi kyau ga humra data shafa mey 'kamshin gaske.
Phone ce yanzu matsalarta game d'in da take d'ebe mata kewa babu,8:30am ta sauka zuwa kitchen.Store d'in ta duba tana shawarar abinda zata dafa,daga 'karshe de ta fere Irish potato ta d'ora frying pan ta fara suya.Jikin window ta koma tana jira ya soyu,tana hangen waje, garden ta gano yasha flowers masu kyawu luf-luf gwanin sha'awa sam ta shagala da kallon gurin musamman da taga tsintsaye na shawagi a gun.
"Welldone madam Chef" Tajiyo muryar Amjad.
Da sauri ta juyo har mayafinta yana fad'uwa da'kyar ta samu ta tattaroshi ta rufe jikinta tana sunkuyar dakai."Can't you smell?"
Se lokacin ta gane dankali ne yake 'konewa,da sauri ta 'karasa gun tana 'ko'karin kwashewa a plate.Da sauri ya jata baya ganin mayafin ta na shirin shiga cikin man da take soya dankali "Watch out!"Ya cillar da mayafin gefe.
" Toh shine kuma seka ciren mayafi!" Ta fad'a cikin fad'a cikeda tsoro.
Sunkuyawa tayi ta d'auki mayafin ta yafa abinta ta koma gefe,dankali kuwa ya 'kone 'kurmus.
"What are you waiting for?"
Jin ya fad'i haka tayi sauri ta matso kusa ta kwashe dankalin,seda ta rage gas d'in tukun ta sake zuba wani, yana daga gefe yayi folding arms yana kallonta.
"Nasty!"
Banza tayi dashi a ranta tana fad'in"'Kwalelenka so kake kaci kuma baza ka ci ba"
Fridge ya nufa ya ciro apple guda d'aya ya samu stool ya zauna daga nesa yana kallonta.
"Why do you married me?" Ta jiyo tambayarsa.
Ko 'kala batace ba tana juya dankalinta.How old are you?"
Data gama kwashe dankalin seta tuna bata d'akko egg ba gashi yana kusa da fridge d'in amma hakannan ta daure ta 'karasa.Seda ta d'ebo guda biyu a d'an 'karamin bowl zata rife fridge d'in ya ri'ke mirfin.
"Answer me"
"Auren dole akai min"
"Damn it!" Ya buga mirfin fridge d'in tare da mi'kewa tsaye,a take ta sunkui da kai ganin tsahonsa ya kere nata tana gudun karta ji saukar mari dan har yanzu taga ganin ba sanin halinsa tayi ba.
"Look up"
"Laila I'm talking to you"Ya fad'a da 'karfi ganin ta'ki amsa sa.
A hankali ta d'ago amma har lokacin bata bari sun had'a ido ba."Speak in English"
"Ni..ban ..iya ba" Ta fad'a dalla-dalla tana kallonsa cikin ido da ido.Ita kanta batai zaton zata iya ba.
Ya d'an fahimci abinda take nufi sede be nuna ya gane ba harara kawai ya bita dashi yasa 'kafa ya fice.
"D'an wahala,Alhamdulillah gwara da Allah yasa baka ganewa nima da hausar zanke ramawa"
Nan da nan ta gama had'a breakfast d'inta, yau a dinning taci kayanta tana gamawa ta d'auraye kwanukan ta koma d'aki.
"Ni ina zan sami charger?"
Fitowa tayi ta sakko 'kasa living room ta duba ko zata samu charger nan ma babu.Ganin bata samu ba yasa ta fita ,nan taita kallon tsarin gidan,a haka har ta nufi garden data hango d'azu aiko ta samu kujera gun tayi zamanta se kalle wajen take.
Yana kwance ya zira earpiece a kunne yana sauraron wa'ka yaji kamar 'kara,da farko ya share seda yaji da gaske de 'karar ce tasa ya zare earpiece d'in tare da mi'kewa ya sakko 'kasa jin 'karar daga waje ne yasa ya fito.Yana dube-dube a harabar gidan idonsa ya sauka a kan Laila da ta d'are saman mota kanta ko d'ankwali babu a kanta gashin kanta dake parke ya ware se 'kyarma take,mayafin kuwa yana 'kasa gefen tayar motar wanda bata san inda yake ba se waige-waige take sam hankalinta baya jikinta, baback zato ba tsammani taga Amjad tsaye yana kallonta.
"Mami"Sunan da take kira kenan idanuwanta ya cika da 'kwalla.
" What is your problem? "
"Lizard" Ta ta'be baki kamar zatai kuka.
Dariya ce tazo masa amma seya basar ,ya zaci ko hausar zatai masa "So you can speak English clearly? Huh?"
Har yanzu kyarma take,ita bata san lokacin da ta fad'i lizard ba ji tayi dama batai magana ba.
Alamu yayi mata da hannu nata sakko daga kan motar amma tayi burus kamar bata gani ba.
"Hey,don't spoil my car"
"Toh matsa na sakko ,ko a kanka zan duro kana wani kallona sekace 'kadangaren" Ta fad'a a fili dan tasan ba ji zeyi ba.
Maimakon ta sakko ta saitin daya ke a'a seta sauka ta d'aya side d'in ta zagayo ta d'auki mayafin se zazzageshi take.
"Repeat what you just said in English"
Da sauri ta d'ago taganshi ya tsaya a kanta "Toh d'an garin ga'ba-ga'ba"
"Matsa min na wuce" Ta wani sha kunu.
"You're sick" Ya harareta tare da barin gun.
Tana komawa d'aki ta cire kayan jikinta ta sauya wasu dan gani take kamar zata sake ganin 'kadangaren a jikinta.
Da rana couscous tayi da miya yasha vegetables da nama tayi har dare iya cikinta .Shikuwa Amjad baya wani cin abinci mey nauyi daga madara seya d'ansha fruit ko cornflakes sam cimar ba dad'i take masa ba yayi missing girkin Mom girman kai bazesa yaci abincin Laila ba.
9:04pm taji motsin 'kofarsa alamar ya fita daga d'akin,a hankali ta bud'e 'kofarta tare da fitowa.Handle d'in 'kofarshi ta murd'a ta shiga ,fasalin d'akinsa yayi mata kyau sosai ga wallpaper dake d'akin,se frames da pictures nashi dake manne jikin bango.Ganin zata shagala da kallo ta soma neman charger, drawer take ta dubawa na mirror daga baya ta dawo na gefen gado ,ba tare da tayi tsammani ba taji an murd'a handle d'in 'kofar.Kid'imewa tayi ta rasa yanda zatai,wani idea ne ya fad'o mata tayi sauri ta bud'e clothset ta shige ta rufo murfin tana tsima.
Amjad daya shigo d'aki ganin duk abinda zeyi ya gama baze sake sauka 'kasa ba ya kulle 'kofar d'akinsa ,T-shirt d'insa ya cire ya cilla su kan couch ya zauna daga shi se 3 quater.
*Vote*
*Comment*
*Share*
*Dijensy*❤
🌼🌼 🌼🌼
💦 💦
*AMJAD*
💦 💦
🌼🌼 🌼🌼
*WRITTEN BY DIJENSY★*
*WATTPAD:@dijensy*
*Where did we stop? Laila..hihi!*
🅿0⃣8⃣
Ring! Wayarsa tayi 'kara,koda ya duba yaga."Baby boo"
Laila dake cloth set tana jiyoshi yana waya se soyayya yake sha da Rosie d'insa.An shafe kusan 40min har lokacin yana waya Laila ta soma gajiya ga bacci data fara ji.
"Goodnight sweetheart"Daga haka yayi hanging.
Wani munafikin tari ne ya turnu'ko a ma'kogoranta da sauri ta rife bakinta amma dukda haka seda ya ku'buce." Wayyo Allah"Ta fad'a a ranta.
Jira take taji an bud'ota amma taji shiru sede ma duhu data sake gani ya lullu'be hakan ya tabbatar mata da kashe light d'in d'akin yayi,haka ta cigaba da zama lokaci yana sake shigewa a yanzu har 11:46pmpm shiru Amjad tuni yayi nisa a bacci.
A tsorace ta bud'e 'kofar tana sand'a a daddafe take tafiyar dan ba gani take yi ba sosai tass! glass cup dake kan drawer hannunta ya ta'ba aiko ya fad'a 'kas.Amjad dake cikin bacci a firgice ya tashi tare da kunna light d'in d'akin.
"You? What are you doing here?"Ya fad'a cikeda mamaki.
Shiru tayi ta kasa cewa komai se waro idanuwa take gashi yana side d'in 'kofar fita.
" When did you broke in my room just like that?"
"I want to charge my phone