Showing 30001 words to 33000 words out of 62917 words
Chapter 11 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt
"Speak in English"
"I'm hungry"Taji ya fad'a.
"Bring me water"
Tana turo baki ta tafi kitchen, dankalin data soya ta zibo masa tare da soya masa egg ta kawo,se bottle of water da cup ta jero a plate.Tana direwa tasa 'kafa zata fita."Laila"Ya kira sunanta daga kwance.
"Where are you going?"
"School" Ta amsa.
Kai kawai ya girgiza bece komai ba ya d'ora d'aya hannunsa a kai se squeezing yake.
Tana sauri haka ta fice koh a jikinta ciwonsa be d'aga mata hankali ba.Yauma bayan sun fito daga lecture na farko ita da Aliya suna zaune kan bench suna duba wani aiki.
Ring!Ring!Taji kira ya shigo wayarta,unknown number ta gani seda ya kusan katsewa tayi picking.
"Hello"
"Laila come back home" Taji an fad'a daga d'aya 'bangaren.
"Who am I talking to?"
"It's me Amjad"
"Why do I have to come back"
"I'm dying Laila, I totally can't breath"
"Then take your medicine"
"I can't"
"Naji gani" Ta fad'a tare da katsewa.
"Mtchww!" Bata san tayi tsaki bama.
"Tohh,keda wa?" Aliya ta tambaya.
"Uhnm,tafiya zanyi" Ta fad'a rai a d'an 'bace.
"Tafiya kuma? Sauran lectures fah?"
"Ya zanyi? Wata'kila na dawo".
" Ok,Allah yasa lafiya"
"Hmm" Abinda ta fad'a kenan ta tashi
Ita de Aliya kallo ta bita dashi dan har yanzu ta rasa gane kanta.
10:45am ta koma gida,seda ta shiga d'akinta ta ajje jakar tukun tai knocking d'akinsa."Come in"Ya fad'a.
Lokacin data shiga ma yana zaune ita sam bata ga alamar wani tsananin ciwo ba,basarwa yayi kamar ba shine wanda ya kirata ba."Why are you here? "
"You called me"
"I'm fine,you can go coz I don't need you now"
"Tabd'ijan,wannan yana haukane?" Ta fad'a cinkin ranta.
"'Kazami kawai" Tayi 'kun'kuni ta fita daga d'akin.
Abincin data kawo masa ma be bud'e ba se yanzu,loman farko yayi ya ajje fork d'in bayaso yaci abincinta sam amma dad'in dayaji yayi yasa ya cigaba da ci.Kad'an ya rage badan ba dad'i ba sedan ya 'koshi,da'kyar ya samu yasha magani tukun ya kwanta.
12:30pm haka ta tashi ta koma makaranta,lecture d'aya suka 'kara yi ta komo gida duk a gajiye dan ma seda taci abinci ta taho.Tana watsa ruwa ta kwanta bacci,se kusan maghrib ta tashi.Tunda ta sakko 'kasa d'aukan ruwa bata sake fitowa ba se wata washegarin.
Yana 'kudundune cikin blanket yau ma da zazza'bin ya tashi da 'kyar a daddafe yayi sallah.Tana shiryawa wayarta tayi 'kara koda ta duba taga number da Amjad ya kirata jiya ne.
"Hello" Ta amsa.
"Make me ginger tea"
"Uhum" Ta fad'a ciki bata bari ya sake wata maganar ba ta kashe.
Seda ta gama abinda zatai tukun ta sauka zuwa kitchen,fara had'a nata breakfast d'in tayi kafin daga bisani ta had'a masa tea d'in."Come in"Ya fad'a bayan tayi knocking.
Kan drawer na gefen gado ta d'ire masa,bako sannu tayi fitowarta.Komawa tayi dinning tayi breakfast d'inta tukun ta dawo d'aki ta d'auki handbag d'inta tayi tafiyarta.
Shikad'ai yayi ta fama da ciwonsa,yanzu daya ji wuya ya kashe Ac d'aki kuwa yana nan yadda yake kaca-kaca.
★★★★
Yau ta samu lecturen farko ba kamar jiya ba,seda sukai lecture biyu 12:15pm suka tafi cafeteria.Suna fitowa ne wani saurayi dake ciki ya soma biyo bayansu,yana daga side d'in Laila.
"Assalamu Alaykum"
Kamar bazata amsa ba ,ta amsa da "waalaikassalm" amma bata kallon inda yake.
"Baiwar Allah ko zan iya jin sunan?" Ya tambaya yana murmushi.
Banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta, Aliya se bugin hannunta take "Ke baki ji ? Ki sallameshi ya dena bunmu"
"Please ko zan iya samun number ki?" Ya sake wata tambaya.
"Bawan Allah kai baka san matar aure bane" Laila ta fad'a rai a 'bace.
"Ayi min afuwa amma dake matar aure ce nima zan gane hakan,dan Allah ki taimaka ko numbern ki ne ki bani".
" Mtchww!"Taja tsuka tayi gaba tabar Aliya anan.
Kai ta girgiza ta bita a bayan dan ita a tunaninta ta fad'i haka ne saboda ya rabu da ita.Ita kanta Laila mamaki ta shiga yi na 'bacin ranta bata zaci haka ba.
"Haba Laila, shine kike yin 'karya da aure akan bakyaso ki kula wani?"
"'Karya? akan mey zanyi 'karya shi baida tunani ze tare ni..." Laila bata 'kare maganar ba se ji tayi kuka ya ku'buce mata ,Aliya dake tsaye ta ri'ko kafad'arta ta zaunar kan bench.
"Abin yakai ga haka?"
"Aliya baza ki gane ba" Ta fad'a tana 'ko'karin share hawayenta da tissue.
Shiru sukai na d'an lokaci kafin Aliya ta sake wata maganar."Laila na tambayeki?"
Kai ta kad'a alamar "Eh".
"Da gaske ne abinda kike fad'a ,kina da aure?"
"Ina da aure Aliya.."
"Kina nufin kice jiya wayar da kikai da mijinki kikai?"
"Uhmm"
"Amma shine kike magana haka? Laila sekace a 'kauye"
"Please mu bar maganar nan"
"Keko dan Allah tun yaushe kikai aure?"
"4month,ki tashi mu tafi ko an shiga lecture" Tayi 'ko'karin kawar da zancen.
"Idan kince yanzu mu bar maganar ai gobe ma rana ce,idan kikai wasa ma har gidan naki zanzo"
"Jibeki ni tashi kin fiya manyancen tsiya"
"Naji,ke kuma babba dake amm..."
"Amma mey?"
"Abar kaza cikin gashinta" Tayi dariya tare da mi'kewa.
"Oho miki" Suka jera suna tafiya.
Lecture da aka shiga yasa basi samu lokacin sake magana ba,ana fitowa kowa ya tafi gida.
Tana shiga gida taga kiran su Aunty bilki ,nan take fad'a mata suna hanyar zuwa gidanta ita da sauran sisters d'in Mami.
*Short and boring chappy I know,don't forget to comment,share and vote. Love ur❤*
*Dijensy❤*
🌼🌼 🌼🌼
💦 💦
*AMJAD*
💦 💦
🌼🌼 🌼🌼
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
1⃣3⃣ - 1⃣4⃣
Lokaci guda cikinta ya d'uru ruwa,ba shiri ta fito daga d'akinta ta sakko laundry room anan ta d'akko broom stick tare da mop.Tunanin yanda zatai masa bayani ta shiga yi kafin tayi knocking tafi 4min,jin shiru yasa ta murd'a handle d'in 'kofar ta shiga.Gani tayi baya ciki kuma ba alamar yana bathroom ,hakan ba 'karamin dad'i yayi mata ba.Cikin sauri ta fara gyaran d'akin tana yi tana masif-masife."K'azami kawai ,dubi kan katifa mtchww!"ba dan Allah ba haka ta gyara d'akin tass bathroom d'in ma haka ta gyaresa.Tana goge kan mirror ne taga wani d'an 'karamin doki da aka sassa'ka da katako,d'auka tayi tana ta kallansa ta juya can ta juya nan garin haka ya su'buce ya fad'i,aiko tana dubawa taga kansa ya gutsire,salallami ta hau yi tana tarkatoshi.
D'akinta ta koma ta d'akko wani super glue ta shiga mannawa a wuyan, daya jonu seya 'bintire har ta 'karar da glue d'in gashi duk ta 'bata dokin yayi fari-fari a brown colour d'in
Amjad kuwa jin zaman d'akin ya isheshi yasa ya fice waje garden yayi zamansa,seda ya shafe 'yan mintina ya komo.
"What is she doing?" Ya fad'a a ransa ganinta bakin mirror ta juya baya.
"What are you doing in my room?"
Nan da nan ta soma mutsu-mustsu ,da sauri ta 'boye dokin a bayanta,gashi yau ba gyale a jikinta doguwar rigar atamfa ce da d'ankwali.
"You're hiding something" Ya 'karaso inda take a fusace ya mi'ka mata hannu ta fito da abunda take 'boyewa.
"Let me see"
"Ni babu abinda na d'auka" Ta turo baki.
Ganin zata 'bata masa lokaci ya mi'ka hannu bayanta ze kar'be abinda take 'boyewa,da sauri ta juya bayanta gam ta ri'ke dokin kamar nata.Kici-kici suka shigayi yana murd'e mata hannu tana ihu amma ta'ki saki,jin nauyinsa gabaki d'aya a bayanta yasa tayi saurin saki da 'karfi ya wafce body d'in dokin. Ba shiri taja jiki ta matsa gefe du se taji wani irin dama bata ri'ke ba.
Ganin tsurar doki ba kai yasa Amjad ya waigo ya dubeta."You broke it "
Shiru tayi bata ce komai ba kan dokin na hannunta na hagu ta dam'ke.
"Give me the other part" Ya mi'ka mata hannu.
Tana so ta bashi kuma tana tsoro kar yayi mata wani abun dan ta kula ta irin expression d'in fuskarsa d'auke da guntun murmushi mey manufofin.
A sanyaye ta bud'e ta mi'ka masa daga nesa -nesa,ganin hannunta be kai ba ta d'an matsa aiko abinda take tunanin shiya faru.Hannunta ya janyo har kan dokin ya fad'i 'kas ita kuma ta fad'o jikinsa.
"Can't you apologize?"
"Ka cika ni,kai kayi min godiya?"
Ta kasa ku'bucewa sam se raba idanuwa take."Shut up!"
"Toh ka cikani"
"Keep your mouth shut"
Ya sake matso da fuskarsa har numfashinsu na had'uwa.Tsoro ne ya fara kamata dan haka tayi shiru mutsunma ta dena idanunta a rufe.
Door bell rang qlin! Jin haka yasa ya cika mata hannu har tana shirin fad'uwa da'kyar ta iya balancing kanta,a kunyace tayi sauri ta fita daga d'akin.
"Aunty" Ta furta lokacin data bud'e 'kofar.
"Sannunku da zuwa" Ta fad'a tana bud'e musu 'kofar widely.
Waje suka samu suka zauna su hud'un ,bayan data gaishesu ta kawo musu drinks."D'ayan d'an kunnen fad'uwa yayi?"Wata daga Cikin 'kannan Mami ta tambayeta.
Se lokacin ta shafa kunnenta taji ba d'an kunne d'aya,zuciyarta ce ta bata a d'akin Amjad ta yar.
Amjad bayan fitarta ya lura da d'an kunnen ma'kale a jikin shirt d'inshi,kallo d'aya yayi mishi ya bud'e drawer ya cillar a ciki coz yana expecting zata zo kar'ba.
Hira suka shiga yi irin ta 'yan uwa har wajen maghrib tukun suka tafi.Suna tafiya ta koma d'aki ta d'akko mayafi ta yafa ,d'akkunen kuwa ta cire ta sauya wani dan bata jin zata iya komawa ta d'akko kayanta.
★★★
Tun abinda ya faru Laila bata sake yarda ta shiga d'akinsa ba ,Amjad ya samu sau'ki har ya koma aikinsa.Aliya a makaranta daga tayi mata maganar aurenta seta share zancen gashi lecture tayi nisa yanzu har sun fara test,tana dad'ewa ma bata sakko 'kasa ba rabon data had'u dashi tun da safe yanzu har 10:23pm gashi an shigo watan azumi gajiya take sata kwanciya da wuri.
Amjad ma yanzu da wuri yake barin wajen aiki kuma yaci abincin ta ya'ki ko tayi dayawa sede ta bawa mey gadi da yazo kwanannan,wani lokacin fita yake restaurant ko ya siyo ya taho dashi kullum a wahale.
Aliya haka tayi ta 'ko'karin turo mata video girke-girke iri-iri idan taga dama tayi wani kuma ta share musamman idan taga mey wuya ne.
Yau ba school,tunda ta tashi take jin alamar ciwon mara kad'an-kad'an aikuwa wajen 11:30am azuminta ya karye,dan haka ta shiga kitchen dan had'a abinda zata ci indomie kawai ta dafa bayan taci tasha magani ta komo d'aki tayi kwanciyarta.
Amjad shaf ya mance be tafi da key ba,2:30pm ya dawo a gajiye.Qlin!Qlin ya danna door bell shiru, har ya soma gajiya da tsaiwa.Laila kuwa baccinta take ta shara bata san yana yi ba.Gwada kiranta yayi a waya amma switchoff tana charge.
Ransa ba 'karamin 'baci yayi ba gashi ko mey gadi baida key d'insu na ciki,cikin mota ya koma ya kunna Ac.Se wajen 3:45pm ya koma ya sake ringing,dede lokacin ta sakko 'kasa ita a tunaninta ma ko ba'ki tayi.Yana tsaye fuskarsa ba annuri kamar ya sha'keta haka yaji, gefe ta matsa ya shigo tukun ta rufe 'kofar.
"I spent more than 1hr waiting for you to open this fucking door"
"Ni na hanaka fita da key"
"You..." Ya nuna ta da yatsa.
Matsawa tayi daga pointing d'inta da yayi ta waiga gefe."You're disrespecting me"
"Nasan matsalarka ,yunwa" Ta fad'a a ranta.
Ring! Ring! Wayarsa tayi 'kara, Dad ya gani jikin screen.Be sake wata maganar ba ya bar gun.Gwalo ta bishi dashi ba tare da yasan tana yi ba.
Da lokacin shan ruwa doya da 'kwai kawai tayi ta d'ibawa mey gadi saura data ci ta ajje,Amjad yau ko fita ya siyo abincin beba koda aka sha ruwa iya fruits yasha da. dabino.Seda ya dawo daga masjid ya lura da flask d'in da ta ajje doya da 'kwan,d'aya ya d'auka yasa a baki yana feeling taste d'in.
"Not bad" Ya fad'a kafin ya sake d'aukan wata ya lun'kume a wasa awasa har ya kusan cinyewa.
Washegari da safe bayan ta gama shirinta tayi toasting bread da d'an yawa saboda zata je school dashi.Tana cikin yin breakfast Amjad ya shigo,jitai kunya ta kama ta lomar dake bakinta ta had'iye da 'kyar ,saboda gudun karya ganta yasa bata ci a dinning ba amma duk da haka seda ya ganta.
"Are you suppose to eat? You don't even feel guilty of what you're doing"Ya 'karaso yana janye plate d'in gefe ,kuma ya gane amma jan magana yasa shi yin haka.
" Meya shafe ka?"
"Repeat what you said, I can understand little of it"
Jin ya fad'i haka tayi shiru bata kuma wata maganar ba.
"Yarinya I'm soon living you here alone"
D'agowa tayi ta kalleshi jin ya anbaci yarinya"Toh a ina ya fara koyan wannan?"
"Surprised koh?"Murmushi kawai yayi ya fita daga kitchen d'in, abincinta ta cigaba da ci tana tunanin yadda ya fara iya Hausa.
Tunda aka fara azumi sau d'aya ta sake zuwa gida yanzu har za'a 'kar'kare.Tana d'aki bayan ansha ruwa yazo yace mata ta shirya su fita,seda suka tsaya a mall tasan inda zasu.Siyayyar kayan sallah suka yi,daga nan suka komo gida ,su Maryam da suka zo ta basu suka kai mata d'inki,ranar sallah ji take kamar ba sallah ba ita kad'ai sede idan kunna chat tayi,jitai tayi missing tuwon Mami na sallah ,kira tayi a ways race su kawo mata ko abincinta 'kinci tayi tana jira anjima su Nusaiba su kawo mata tuwo.
Basu suka zo ba se 4pm,ganin 'kunshinsu datai taji ya birgeta jitai dama itama taje anyi mata ,Aliya seda tayi ta fad'a mata amma ta'ki.
Biyu ga sallah ta shirya zata gida,Amjad ne ya d'auketa badan yaga dama ba saboda Mom tace yaje.Suna tafiya a hanya ta ciro mirror d'in powdernta tana kallan fuskarta." You better stop it ,you're not even beautiful "Taji ya fad'a.
Har