Showing 51001 words to 54000 words out of 62917 words

Chapter 18 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt

DIJENSY   

14 Jan 2025

5796

Ranta in yayi dubu ya 'baci ,duk wannan uban zaman da take sha a asibitin nan shine zata fad'a mata 'bakar magana.


"What did she said?" Ya tambayi Laila.


"Nothing" Ta amsa bata ko kalleshi ba.


Gida'a kai yayi dukda be aminta da abinda ta fad'a ba dan yaga sauyin yanayin fuskarta fiye da da.Wayar ma ajjeta tayi dan tsabar takaici ta kasa yin abinda zatai.


"Laila I'm hungry" Taji yayi magana.


D'agowa tayi ta kallesa nan Mom tace yaci abinci amma ya'ki shine yanzu zece mata wani zeci abinci.A hankali ta tako zuwa inda warmer d'in yake ta samu plate ta ziba masa pasta had'e da sweet creamy potato sauce ta samu spoon ta d'ora ta mi'ka masa, ganin be kar'ba ba ta ajje masa kan gefen gadon ta koma ta zauna.


"Laila can't you see ? I can't use my hand to eat"


Se lokacin ta d'ago ta kalli hannunsa na dama dake nad'e a plaster."Kaci da hannun hagun".


"Laila it's not good to eat with left hand"


Sekace ba shine mey cin abinci da hannun hagun ba wata rana."Laila I'm starving "


Cikin sanyin jiki irin nata ta 'karasa,a gaskiya bazata iya zama gefensa ba kamar yadda taga Mom nayi, tsayawa tayi ta d'auki plate d'in a tsayen ta d'ibo a spoon ta mi'ka masa.


"I can't take this while you're standing"


"It's ok for me"


"But it's not ok for me,sit"Ya fad'a.


A raku'be ta zauna daga gefensa dan wajen ba wani space ne dashi ba duk yadda takai ga no'kewa seda ta ra'bi jikinsa abinda bataso kenan.Bata bari sun had'a ido ba ta mi'ka masa, yana sane ya 'bata lokaci kafin ya kar'ba har hannunta ya gaji.Dayaga ya kusa 'koshi inde ta d'ibi abincin seyace lomar tayi masa girma har seta rage zeci.Tana gama bashi ta mi'ke da sauri.


"Water" Ya tuna mata.

Shima ruwan seda ta tsiyaya a cup ta bashi ,yana sha yana kallonta.Laila a yadda ta kula ruwan ya isheshi amma da gayya take sake d'ura masa seda yayi mata alama da hannu ta maida cup ta ajje.


Tana komawa kan kujerarta ta gado ta jingina ta rufe idanunta."Are you comfortable there?"


"Uhm" Ta amsa.


Yana kallonta se motsi take dan ba bacci take ba."Laila come over here"


"Wa ? Cinyarka kake so na kwanta? you're sick" Ta fad'a a ranta.


Haka yayi tayi mata magana har ya gaji bata ko bud'e ido ba.


β˜…β˜…β˜…


Tun 5:00am ya tashi daga bacci,kwanciyar du ta isheshi ya juya nan ya juya can,Laila kuwa se sharar bacci take.


6:30am ta farka daga bacci, tana maida kallonta kan gadon nashi ta lura da nurse dake tsaye a bakin gadon sede kuma bata jiya bace.


"Your sister?" Ta tambayi Amjad lokacin data ga Laila ta tashi daga zaune.


"No,my wife" Ya amsata yana kallon Laila fuskarsa d'auke da murmushi.


"Married at young age"Nurse ta fad'a tana kallon Laila.


" Your wife is pretty but she don't smile"Nurse d'in tayi dariya,Amjad ma dariya yayi yana kallon Laila data sunkui dakai tana guntse dariyarta dan ita kanta Nurse d'in ta bata dariya musamman yadda tayi maganar dan ba bahaushiya bace.


"Ehnn...amma ita ba Nigerian bane?,yayi kamanni irin na bature mijinka" Ta tambayi Laila cikin gur'batacciyar Hausa.


"Nigerian ne mana" Laila ta amsa.


"Ehenn ban yarda ba,baka so nace mijinka yafika kyo"


Itade Laila dariya tayi ta rabu da ita da surutunta har ta fita.


"Morning" Taji ya fad'a.


Shiru tayi batace komai ba ,akwatin ta zuge ta ciro kayanta ta shiga bathroom.10min later ta fito cikin shirinta na atamfa doguwar riga ta yafa mayafi.


"Can you please help me sit up?"


Basarwa tayi kamar bata ji ba."Laila I'm talking to you,why are you shunning me as if you're not the one crying for me..."Ya 'kare maganar a hankali.


'Kiri tayi da ido tana mamakin yanda akai ya sani."Taya ya sani,ko dama yana jina lokacin? "


"I'm gonna call Mami to tell her how you're treating me,you don't show any respect to your husband"Ya mi'ka hannu ya d'auki wayarsa.


Ganin haka tayi sauri ta 'karaso inda yake,pillow daya d'ora kansa tasa hannunta zata zame." Laila ,do you wanna break my neck?"Ya 'kwantar da murya.


D'an d'ago da kanshi yayi yana jiran nata taimakon ,rufe ido kawai tayi ta zagaye hannunta a bayansa da taimakon ta ya mi'ke zaune ta sanya masa pillown a baya yanda zeji comfortable.


"Thanks dear" Ya fad'a yana murmushi.

Suna zaune aka kawo musu breakfast,Laila tana kallon abincin amma ta'ki ko ci balle ta bashi shima,shiru yayi beyi mata magana ba.


"Laila" Ya kirata .


"Why are you always mad at me ,is't because of..." Se kuma yayi shiru.


"Because I'm not suppose to be with you here but your girlfriend."Ita kanta bata zaci haka ba daga bakinta.


Ya dad'e kafin ya sake wata maganar." Laila I know I was wrong to treated you like that,I'm sorry for hurting you..."Be 'kare maganar ba aka turo 'kofar d'akin.


"Assalamu Alaykum"Mom ta tayi sallama.


" Waalaikissalam"Suka amsa.

Cikin rissinawa ta gaisheda Mom."Laila, how you? "


"I'm fine" Ta amsa.


"Mom I'm the patient not Laila?"Ya fad'a.


" You're jealous "Cewar Mom tana dariya.


"Have you eating?"


"No" Ya amsa yana kallon Laila tare da yin makirin murmushi.


"Why?"


"He refused to eat" Laila tayi saurin fad'a.


Waro ido yayi yana kallonta ashe itama ta iya sharri."Mom I ..."


"You what? You have nothing to say,now that i'm here I will force you to eat"


Abincin data taho musu dashi ta d'akko.Baguette da liver sauce se sandwich.A plate ta jera komai ta zauna ta soma bashi.Laila haka kawai taji 'bacin rai ganin Mom ke bashi,ita kanta batasan dalilin fushin ba(Jealous).


Komawa tayi gefe ta zauna dan ta huce takaici seta d'auki wayarta tana dubawa.


"Laila,are you not gonna eat?"Mom ta tambayeta


"Ita ai taci d'azu" Amjad ya fad'a.


Shima ya rama,suna had'a ido yayi murmurshi ita kuwa ta murgud'a masa baki tare da watsa masa harara.Kamar wani dolo haka ya saki baki ya bita da kallon dan be ta'ba gani tayi masa irin abinda tayi yau ba,ba 'karamin birgeshi tayi ba yaji dama tana kusa dashi.


Mom duk wannan dramar da ake bata kula ba ,haka Laila ta zauna bata ci abinci ba wajen 12pm Mom ta tafi ta barsu da halinsu.


"Why did you lied?"


"Toh ai kaima ka rama"


"Wannan is a little thing,when the time you will see"


"Allah ya nuna mana"


"I know you will cry"


"Cry? Tabb god forbid"


"Hmm" Yayi murmushin mugunta.


Ganin haka kuma seta ji jikinta yayi sanyi lokaci guda 'kwa'kwalwarta ta fara ganar da ita mey hakan yake nufi.


"I'm hungry"Ya fad'a.


" D'azu kaci abinci fa"


"Yes I want more"


Tana jin haushi ta mi'ke ta ajje wayar dake hannunta,yau ma ra'ku'bawa tayi a gefensa lomar farko data mi'ka masa yasa hannunsa na hagu kan nata hannun ya mayar da spoon d'in saitin bakinta."Eat,I know you're hungry".


"No I'm not"


"You're"


Tana bud'e baki zatai magana ya saka mata,ba yadda ta iya ta had'iye.Plate d'in ta maida kan drawer ta mi'ke zata bar wajen yasa hannu ya ri'ko hannunta bata ankara ba ta fad'o jikinsa.


"Auch!" Yayi 'yar 'kara.


"Sannu ,I'm sorry" Ta rikice se duban hannun take ta d'auka ko bigeshi tayi.


"Relax" Ya fad'a hankali kwance.


Ganin fuskarsa ta gane ba abinda tayi masa ma yana sane,tayi 'ko'karin tashi daga kanshi ya sake janyota ta zauna kan cinyarsa.


"Ka sake ni"Ta shiga mutsu-mutsu amma ko jinta ya'ki yi.


" You care,you care about me Laila I knew it"


"No" Ta harareshi.


"I like the way you glared at me,you look beautiful doing it"


Jin haka yasa bata sake hararar ba balla murgud'a baki.Muryarsa a raunane ya soma fad'in;

"Laila I gave up ,I have no choice my heart choosed you,I fall for you Laila why can't you understand?I'm thinking of no one but you it's always you Laila I mean it"


"I don't care,you love her not me"Ta fad'a zata tashi ya sake ri'keta gam.Hannunsa mey plaster ta kalla." You're hurting your self"


"Anything that happen to me is you, it's because of you Laila, I no more love her again I was wronged to love her when I have someone like you ,I have regretted everything I have done,I was so stupid to turned my back on you,Laila I'm begging you to forgive me I'm very sorry"





*Dijensy❀*



































🌼🌼 🌼🌼




πŸ’¦ πŸ’¦




*AMJAD*




πŸ’¦ πŸ’¦






🌼🌼 🌼🌼




*WRITTEN BY DIJENSY*


*WATTPAD:@dijensy*





2⃣9⃣-3⃣0⃣




Alamun murya taji a waje wanda yake tabbatarwa d'akin za'a shigo."Dan Allah ka sakeni,please let me go"


"You have to repeat what I will say before I let You go"


"My husband, please let me go" Ya fad'a.


Ganin ba mafita ta maimata"My husband please let me go ".Tana fad'a ya saketa yana murmushi.


Da sauri ta mi'ke ta bar gurin tayi chan nesa dashi " Mugu"Tayi maganar a ciki.


"Assalamu Alaykum" Akai sallama bayan an turo 'kofar d'akin.Laila tana d'agowa ta had'a ido da Aisha ri'ke da 'yarsu se Farouq a bayansu.


"Waalaikumussalam" Ta amsa fuskarta a sake.


Da yake Aisha irin mutanennance masu saurin sabo kamar ta dad'e da sanin Laila haka suka gaisa ,dukda yarinyarsu mey 'kwiyace da Laila ta kirata bata 'ki zuwa ba.


"Fad'a min sunanki?"Ta tambaya tana d'orata kan cinyarta.

"Minal" Ta amsata tana wasa da takalmin 'kafarta.


Amjad dake hira da abokinsa Farouq rabin hankalinsa na kanta ,seyaga tayi 'kyau da kid a hannunta.Zuwan Aisha ya d'ebe mata kewa taji dama karta tafi,lokacin da zasu tafi har rakasu waje tayi bayan sun tafi maimakon ta dawo setai zamanta a waje kan bench.


Amjad jin shiru bata dawo ba ya kirata a waya sejin ringing d'in wayarta yayi a d'akin,yasan dama so take ta samu damar da zata fita shiyasa tayi rakiyar.


Seda taji zaman wajen ya gundireta tukun ta komo ciki.


"Meyasa baki zauna chan ba?" Taji ya fad'a.


"Ai yanzu zan koma" Ta fad'a stubbornly.


"Zan gani taya zaki fita"


"Taya za'a iya ,mutum a kwance"Tayi maganar a hankali.


"Haka kika fad'a koh?"Ya kad'a kai.


Jin haka yasa bata 'kara fad'ar 'kala ba se wayarta data d'akko ta soma dubawa.


β˜…β˜…β˜…


Haka suka cigaba da zaman asibiti koyaushe rikici na yau daban na gobe daban ,wani sa'in ko ze iya yin abu da kansa seyace baze iya be setayi masa ,seda suka kwashe sati biyu cir aka yi discharging d'insu daga asibitin lokacin ya samu sau'ki sosai dan a yanzu an cire masa plastern hannunsa an sauya masa da arm sling,bandage dake zagaye a kansa shima an cire iya bandage d'an 'karami be ya rage gefen eyebrow d'insa na hagu.Mom kuwa kwanansu biyu da komawa Canada,Laila jefi-jefi tana shiga school yanzu ma exam zasu fara result nasu na wancen semester ya fito ta samu sakamako mey kyau.


First day da suka komo gida,tunda ta shiga d'akinta kuma shikenan ko le'kowa ta'ki yi 7:30pm se addu'a take karya kirata dan tana expecting hakan.


Ring! Ring! Wayarta tayi 'kara ,har cikin zuciyarta taji kiran."Canada"


"Mutum sekace tsoho"Ta d'aga kiran.

" Laila where are you?"


Bata amsa ba ta katse kiran ,mayafinta ta sura ta yafa ta fita zuwa d'akinsa.Tana shiga ta tsaya daga bakin 'kofa tana kallan gefe.Yana zaune yayi d'are- d'are kan mirror drawer.


"Laila you left me alone,I'm hungry"

Juya tayi zata fita ya tsayar da ita"You didn't ask me what I wanna eat"


"What is your favorite?" Ya tambayeta.


"D'an wake" Ta amsa dukda kuwa ba shine fav d'inta ba.


Kasa repeating d'in abinda ta fad'a yayi dan haka ya gid'a kai kawai.


"OK,make me your favorite".


" Uhum"Ta fita.


"Zaka ga favorite sekayi regretting cin d'an wake,bade kai d'an takura ba" Ta fad'a tana d'akko bowl zata had'a d'anwaken.Cikin 'kan'kanin lokaci ta gama kwa'bawa ruwan data d'ora ya tafasa nan ta soma sakin d'anwakenta kai kace d'an 'karamin ball ne dan girma,tana gamawa after few minutes ta sauke.Plate ta cika taf ta ziba manja ko soyawa batai ba danma ba'a daskare yake ba,Maggie ta 'bare ta barbad'a ta d'ibi yaji tea spoon hud'u ta ziba akai ta ko ina,ta d'akko fork ta d'ora.


Dayake tasan mey ta shirya se gimtse dariyarta take ta shiga d'akin,daga drawer side na bango ta ajje plate d'in dake a rufe. Ganin haka Amjad ya sakko daga kan mirror drawern ya 'karaso inda take.


"Sit" Ya fad'a yana d'aukan plate d'in.


Tana tsaye kawai jira take taga ya bud'e taga irin reaction d'insa,d'an basarwa yayi ya kalli kalar d'an waken ya d'anyi guntun murmushi. "Feed me" Ya mi'ka mata plate d'in. Daga gefen gadon ta zauna opposite dashi,'kwaya d'aya ta soka wanda yaji yake mamaye a kai ta mi'ka masa saitin bakinsa.Amjad yana kallonta ya mi'ka baki ya kar'ba ,tashin farko yaji uban yaji gashi ya shika masa bakinsa ko taunawa da'kyar yake,kamar ma'kogoronsa ze fashe haka ya had'iye.Kafin ya dawo cikin nutsuwa tasake sokar wani ta mi'ka masa, kamar wanda aka dannewa baki ya kasa maganar,haka ya bud'e bakinsa ta sake zirawa.Ma'kwat! kuke ji take bakinsa ya d'ad'e shhh! Ya fara.


Tana sake mi'ko wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login