Showing 39001 words to 42000 words out of 62917 words
Chapter 14 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt
d'akinsa ,dan haka ta zauna kan gado aikin zama.
1hr later,Knock! Knock! Taji bugu,tana daga shingid'e tayi saurin mi'kewa zaune zuciyarta na dukan uku-uku.
"Laila" Ya kira sunanta.
'Kin amsawa tayi se wararo idanuwa take wata zuciyar tana ce mata ta bud'e 'kofar bathroom immediately ta bud'e masa 'kofar seta shige bathroom,haka tayi ta sa'ke-sa'kenta.
"Laila open this door"
Hijab d'inta ta d'auka ta zurma ta ma'kale shi a jikinta, a hankali ta bud'e 'kofar ta ra'be daga baya-baya.Tsayawa yayi daga bakin 'kofar bema shigo ba,wani card dake hannunsa ya mi'ke mata,a tsorace tasa hannu ta 'kar'ba ba tare da ta d'ago sun had'a ido ba.
Anniversary Invitation ne wanda taga yau ne ranar zuwan 8:00pm aka rubuta a jiki,bata gane nasu waye ba ita de ta karanta.Tana d'ago da kai taga har yana komawa d'aki dan haka ta shigo ta rufo 'kofarta.
"Ni naje nayi mey acan? wa na sani a wajen? Tare zamu?" Ta jero wa kanta tambayoyi.
Har bayan maghrib bata soma shiryawa ba seda taga ya turo mata text."Are you ready?"
"No" Tayi reply.
"What are you waiting for?"
Bata sake wani reply d'in ba ta tashi ,wardrobe ta bud'e ta soma duba kayan da zata saka,ganin zata 'bata lokaci ta ciro wani ba'kin abaya me golden duwatsu,nan da nan ta saka.Powder ,lipstick da kwalli kawai ta sa ta fesa turare mey taushin 'kamshi,red mayafi tayi rolling dashi.
Wayarta kawai ta d'auka ta zira takalmi mey matsakaicin tudu golden ta samu waje ta zauna.7:41 knock! Knock!
Tsaye ta ganshi yayi shigarsa cikin dark blue suit ciki white shirt da ba'kin jeans ,gashin kanshi yasha gyara se shining yake,turarensa mey 'kamshin gaske se dukan hancinta ake.
"Ready?"
"Uhm" Ta amsa ciki-ciki.
"Let's go" Yayi nuni da hannu.
'Kofar d'akin ta rufo tabi bayansa dan ta'ki bari su jera ,a haka har suka sauka 'kasa.A mota shiru ba mey magana,laila ita tama kau da kai can tana kallon waje.Suna isa gurin mutane an hallara ,ita de kallo take binsu dashi dan ba wanda ta sani,se gaisawa yake da mutane wanda yawanci duk abokanan business ne.Wani table suka zauna kafin daga bisani ya tashi amsa kira,bayan 'kan'kanin lokaci sega iyayen taro sun shigo wajen tare da baby d'insu wanda bata wuce 3yrs ba sunsha 'kwalliya gwanin sha'awa,ana ta gaggaisawa dasu tana gani Amjad yaje suka gaisa bata ankara ba taga sun nufo inda take.
"Wayyo ni Laila" Ta fad'a a fili.
Matar cikin fara'a ta soma mata magana Laila ma 'karfin hali tayi suka gaisa tayi musu fatan alkairi,sede taga Nigerians ne kuma hausawa "how come's Amjad ya sansu?" Abinda ta tambayi kanta kenan dan a iya saninta dashi baida wani abokai.
"Laila ko?" Macen ta fad'a.
"Eh" Ta amsa.
"Ni kuma Aisha,yau Allah yasa min had'u de"
"Gaskiya kam" Cewar Laila.
Sauran ba'ki da suka zo gaisawa da Aishan yasa suka katse hirar da suke,Amjad d'in ma se hangoshi tayi daga nesa yana gaisawa da mutane.
Farouq d'an abokin Dad ne yawanci inde suka zo Nigeria suna zuwa gidansu,shekararsu hud'u kenan da yin aure ,duk a Nigeria shikad'ai ne wanda Amjad zece suna abota ,bayan shi baida wasu abokai.
Laila Tana zaune Aisha tazo "Nan hayaniya,taso mije ciki" Ta taso laila dan ta lura kamar laila bata son hayaniya.
Cikin gidan nasu ta shiga da laila ta kaita wani parlour."Bari gani zuwa".Ta fad'a tare da barin parlourn.
Kitchen ta shiga d'aya daga cikin masu aikinta tasa ta kawowa Laila abinci,kiran waya da akai mata yasa ta fita zuwa wajen ba'kin .Ita kuwa mey aikin ganin aiki ya mata yawa yasa tasa wata 'yar uwarta da tazo daga 'kauye ta zibawa Laila.
Kai tsaye ta bud'e wani plate dake kan drawer ganin friedrice tasha chicken akai ga kayan had'i burjik ,dama ma'kuiyaciyace yasa kawai tasa spoon ta d'ora plate d'in a tray tare da d'ora robar ruwa da orange juice ta kaiwa Laila.
Laila dama tun yamma take jin yunwa,ba 'bata lokaci ta bud'e plate ta soma ci,sede taji abincin taste d'in ba dad'i cabbage d'in yayi wani iri gashi ba zafi ita a tunaninta ko hucewa yayi.Haka ta lalla'ba taci, naman ma ba sosai ta iya ci ba,rabi taci ta rife plate d'in.Leman ne ma tasha da yawa ta kora da ruwa.
Wayarta ta kunna Tana d'an duddubawa a haka lokaci naja har taci fin 30min.Sede kuma tun bayan cin abincin ta fara jin suka a cikinta kad'an-kad'an yana murd'awa.
*Let's stop here,yau na fita hakannan na daure nayi typing coz bana so na barku kuna jira.Don't forget to comment,vote and share.Love u all๐*
*Dijensyโค*
๐ผ๐ผ ๐ผ๐ผ
๐ฆ ๐ฆ
*AMJAD*
๐ฆ ๐ฆ
๐ผ๐ผ ๐ผ๐ผ
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
1โฃ9โฃ-2โฃ0โฃ
Wani irin murd'awa cikinta ya hau yi,nan take gumi ya soma keto mata ta rasa abinda ke mata dad'i wayar ma ajje ta tayi gefe.Tashi tayi a rud'e ta nufi inda taga mey aikin ta shiga,a kitchen ta tarar da ita tana wanke-wanke.Laila tambayarta tayi toilet tana ta zufa.D'aki ta rakata wanda yake d'auke da toilet a ciki,da sauri-sauri laila ta fad'a ciki.
Minutes later ta dawo parlour gwiwoyinta sun fara sanyi gashi cikin har yanzu be dena hautsinawa ba,wayarta ta duba taga 3missed na Amjad. Bata ko zauna ba ta fita,a chan farfajiyar gidan ta hangeshi yana zaune a table shi kad'ai jama'ar wajen ma sun fara raguwa.A hankali ta taka zuwa inda yake,sede ta 'karaso ya kula da ita.
"Where have you been?"
"Gani na fito ai"Ta fad'a.
Mi'kewa yayi tsaye ya fara tafiya tana biye a bayansa Farouq da Aisha suka 'karaso inda suke.
" Tafiya?"Ta tambayi Laila.
Laila cikin ya'ke ta amsa da "Eh"
"Toh bari na kar'bi numbernki".
Numbernta ta fad'a mata a take tayi flashing itama Laila tayi saving, har waje suka rakosu ita de Laila kawai basarwa take cikinta ba abinda yake se hautsunawa ta 'kagu su koma gida.
Tunda ta shiga mota bata ce 'kala ba,gani take kamar ba tu'ki yake ba har wani le'kawa take tana ganin speed d'in."Mtchww" Tayi tsaki ba tare da ta sani ba.
"Are you alright?" Ya tambaya.
Kai ta kad'a alamar "eh" se kad'a 'kafa take tana tapping cinyarta."Innalilahi wainna ilaihirraji'un"Ta fad'a a ranta ganin traffic light ya tsayar dasu.
Da 'kyar ta samu ta iya jurewa har suka koma gida,cikin sauri ta fad'a toilet ko 'kofar d'akin yau bata rufe ba.Daga dawowarsu zuwa yanzu Laila ta shiga toilet yafi sau uku,gwiwoyinta gabad'aya sunyi sanyi da'kyar take takawa.Gashi batasan inda zata sami magani ba,lokaci guda tayi zuru-zuru jinta take kamar kara dan tsabar rashin 'kwarin jiki.
11:29pm Ring!Ring! wayar ta tayi 'kara lokacin tana toilet har 3 missed call batai picking ba.
Amjad yana d'akinsa dede lokacin yake shirin kwanciya wayarsa tayi 'kara,koda ya duba yaga Farouq.
Knock! Knock! Ya 'kwan'kwasa 'kofar d'akinta shiru,handle d'in ya murd'a ya shiga beganta ba.
"Laila" Ya kira sunanta.
Tana shirin fitowa taji ya kira sunanta ,zaro ido tayi ido tana mamakin jinsa a d'akinta a irin wannan lokacin.
"Laila ,come on open the door"
Tsit kake ji ko motsi ta'ki yi gashi tsaiwar ta isheta,kan bathtub ta samu ta zauna ta dafe cikinta.
"Laila,can't you hear me? open the door now stop pretending I know everything"
"Mey? Waya fad'a masa? Yasan..." Ta dafe kai shikenan tonon silili.
"Laila don't let me open it myself, you know I have a spare key right?"
"Innalillah" Jiki ba 'kwari ta mi'ke tsaya a daddafe ta 'karasa jikin 'kofar gashi jikinta kayan bacci ne riga da wando kusan ยพ,inda Allah ya taimaka ma rigar ta hauro kusan cinya,d'an'kwalin kanta ta ware yadda ze sakko 'kasa , a sanyaye ta bud'e 'kofar kanta a 'kasa.
"Laila" Ya kira sunanta.
A hankali ta d'ago da kanta kallo d'aya tayi masa ta maida kanta 'kasa,se jan mayafin take tana kare 'kirjinta.
"Uh...you need to see a doctor"
"I'm fine" Ta fad'a murya 'kasa-'kasa.
"You're not,you better stop pretending I know you're not ok they explained everything to me, you ate a spoiled food"
Shiru tayi bata musa masa ba,ta kasa d'ago da kai dan tsabar kunya a ranta tana da tasanin cin abincin.
"We need to go now".
Tana jin kunya ta wuce zuwa wardrobe ta ciro hijab d'inta ta zira, wata doguwar riga ta d'auka tana so tasa gashi yana tsaya a d'akin se so take ya fita amma yayi burus sema folding arms da yayi yana kallonta.'Karfin hali tayi ta ri'ko doguwar rigar a hannu ta wuce bathroom yana kallonta.
Tana fitowa ya tafi d'akinsa ya d'auka key ya fito,a sitting room ya taradda ita zaune kan sofa dan ko tsaiwa ta kasa.
Ganin ya sakko ta mi'ke a kasalance ,suna fita kafin ta shiga mota kawai amai ya tunkaro ta kafin ta koma ciki ta she'kashi a cikin flowers.Kafin aje asibiti ta sake galabaita ,suna zuwa aka sa mata drip,tana kwance se kallon carnula d'in dake hannunta take,hijab d'in ta cire se mayafin kanta ta yafa.Amjad yana daga zaune kan kujera daga gefenta.Gashi ta manta wayarta ba dama ta kira Mami,ga abinci daya siyo mata ta kasa ci maganin ma da'kyar tasha.
"You need to eat"
"Na 'koshi" Ta fad'a a ciki.
Be sake ce mata komai ba ya cigaba da tapping wayarsa.
โ
โ
โ
5:06am ,ta bud'e idonta hannunta ta d'aga ganin carnula ta mayar,a kan kujera ta kalleshi ya jingina se baccinsa yake.Data kalli ledar ruwan taga ya kusa 'karewa,tunanin yadda za'ai ta tashesa ta fad'a masa ta shiga yi.Pillow ta d'auka ta d'an buga 'karshen gadon amma kamar bayi take ba,haka tayi -tayi harta gaji,daga baya kawai ta cilla masa pillow d'in aiko ya sauka kan fuskarsa.Yana bud'e ido ta sunkui da kai kamar ba ita tayi ba.
Pillow d'in ya kalla kan cinyarsa ya dawo da kallonsa kanta,ganin ba pillow kan gadon yasa ya gano abinda tayi."What do you want?" Ya tambaya.
Drip d'in ta kalla tayi masa nuni dashi yanda tayi da bakinta ne yaso bashi dariya har ma da birgeshi,cikeda shagwa'ba ta ta'be bakinta.
Da kanshi ya cire mata ,bayan ya kira nurse kuma ta cire carnula d'in.Cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga toilet ta d'auro alwala,shima masjid ya fita sallah.Bayan ya dawo daga masjid ya siya mata abinci,dama yunwa take ji tana ci tasha magani.Wajajen 8:30am akai discharging d'insu suka koma gida,se bayan sun dawo ta tuna da office d'insa,tana so ta tambayesa zeje amma ta kasa."Toh zaman mey kake ai na warke"Ta fad'a a ranta.
"How are you feeling now?" Ya tambayeta.
"I'm fine" Ta amsa kamar bata so.
Daga yadda ta amsa ya gano bata son maganar."Any story? tell me about it how does it started? "
Tasan dama za'a rina,bade yaga taji sau'ki ba.Sake murtuke fuska tayi ta kauda kai.
"Come on,it started with stomach ache followed by...." Be 'kare ba yayi shiru yana murmushi.
Ring!Ring! Wayarta tayi 'kara 'Aisha'Ta gani a screen.
"Hello"
"Hello Laila,ya jikinki?"
"Da sau'ki"
"Ayya ,kiyi ha'kuri shirmen mey aiki ne bata duba ba ta baki lalataccen abinci"
"Karki damu ba komai na samu sau'ki"
"Aha,Allah ya 'kara sau'ki se munzo"
"Nagode" Daga haka sukai sallama.
Suna gama wayar tayi dialing number Mami har lokacin Amjad be fita ba,ita kuwa tayi hakane dan karya dameta.Bayan ta gaisa da Mami ta shiga labarta mata abinda ya faru harda 'kara langa'be murya."Mami ruwa leda 2 fa aka 'kara min"
"Toh Allah ya sawwa'ke"
"Mami su Maryam suzo"
"Har sai kin ro'ka? sarkin raki anjima sazo amma karki zaunar dasu".
" Toh Mami ,mami dan Allah kiyi min tuwo"
"Tuwo? toh shikenan se sunzo" Daga haka sukai sallama.
Tana had'a ido dashi taga ya ta'be baki kamar yadda tayi.Dariya da kunya taji ta kawar da kanta.
"Mami,Mami ruwa..bla..bla" Ya kasa 'karasa 'karshen dan sunyi skipping daga kansa.
"Bade zaka fahimta ba" Ta fad'a a fili.
"Bade mey ba?" Taji ya fad'a.
Yadda ya iya had'a sentence d'inne yasa tayi mamaki ta d'ago tana kallonsa.
"Surprised?"
"I saved each an every word you're saying"
"Toh ina ruwana"
"Zaki ga" Wani mamakinne ya sake kamata tana kallonsa sa'kalo.
Daga haka bata sake magana ba dan yanzu kuma ta soma shakkar fad'ar abinda ranta yaso.
Pillow ta janyo ta gyara kwanciyarta ta rufe idonta,so take taga ya fita.
"Sleep tight" Yana fad'ar haka ya fita yaja mata 'kofar.
Yana fita ta bud'e idonta,wayarta ta d'akko ta shiga chat.
Su Maryam se wajen 2:30 pm suka zo,tana ganinsu ta mi'ke kamar ba itace mey shamo-shamo ba.Tuwon da suka kawo ta zuba a plate taci kayanta sauran ta ajje na dare.
Yau 'yan mutucine akan Amjad ,dasu Maryam zasi tafi da kansa ya kaisu harda tsayawa a mall yayi musu 'yan siyayyar biscuits da chocolates.
โ
โ
โ
A kwana a tashi Laila har sun koma school, yau zata koma , 7:25am ta gama shirinta breakfast zatai ta tafi. Ta gama had'a sandwich d'inta da tea ga pancake d'inta tayi dede bakinta ,a tray ta jero ta kawo kan table ta ajje,tuna bata d'akko bag d'in ta ba ta hau sama.
Few minutes later ta dawo dinning d'in ganin mutum ya hakimce yana sambad'ar abinci yasa ta tsaya kallo.Ko a jikinsa hankali kwance yana ta enjoying breakfast d'insa,tana kallonsa yana kallonta bako kunya.
"What?" Ya tambayeta bayan ya dire cup d'in shayin.
Kallan abincin tayi sanna ta komo kansa."My meal"
"Yours? Where is mine?"
"I didn't cook for you"
"Why?"
"Because I always prepare a Nasty food"
"Exactly,you gerrit,that's why I wanna show you how to make your food yummy"Yana maganar ya goge bakinsa da tissue ya tashi.
" Oh I remembered, I will drive you to school you need to hurry up I'm almost late"
"Ni bazaka kaini ba,sena ma yi abinci"
"Who will eat the rest of this?" Yayi nuni da pan cake a plate.
"Left over d'in zanci?"
"What wrong with that?"