Showing 42001 words to 45000 words out of 62917 words

Chapter 15 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt

DIJENSY   

14 Jan 2025

5795

"Bazan iya ci ba"


"Bazan ..iya ...ci ba" Ya maimaita abinda ta fad'a.


Tana kallo ya ciro wani d'an 'karamin note book a pocket d'insa tare da pen,gani tayi yana rubutu amma bata ga meya rubuta ba.


" Read"Ya nuna mata note d'in."Bazan iya ci ba"Taga an rubuta a jiki."I'm gonna search it's translation in English"


"Ka wahala"


Wani rubutun taga ya sake yi,exactly abinda ta gama fad'a ya rubuta.


"I think this wiil work" Ya fad'a tare da mayar dashi aljihun suit d'in.


"Let's go"


"I'm not ready"


"Then I will wait for you"


Tana jin haushi ta koma kitchen ta soya egg ta had'a da slide bread,a kitchen ma tayi breakfast d'in yana dinning yana jiranta har ta fita.Se bayan sun shiga mota ya tambayeta."Where is your niqab?"


Shaf ta mance ta baroshi kan kujera dinning aiko ta fita ta d'akko abinta,tana shigowa ta d'aura kayanta.


"You're pretty enough to cover your face right?"


"Yes" Ta amsa.


"I see"


"Mrs beautiful, pretty, cutiee, flower,diamond, gold, silver...and rest"


"Who was your first love? I asked again"


Da kamar bazatai magana ba kuma setayi."Safwan"Ta kama suna .


Be ta'ba tunanin zeji haushi ba amma jin ta fad'i suna yaji ransa ya 'bace,daurewa yayi ya cigaba da magana.


"Nice name,tell me about him,show me his picture?"


D'age niqab d'in fuskarta tayi dan ta tanadi abinda zata fad'a kuma so take yaga yanayin expression d'in fuskarta.

"He is handsome,very kind person he is so sweet, shining like a diamond". Yanda take maganar har fuskarta tana nuna farinciki.


" The first time I set my eyes on him I felt like I'm in Paradise,the first time I heard his voice ...ohh he's the beat of my heart I so much eternally love h..."Ai bebar 'karshen 'im' d'in ya fito ba yaci burki.


"Ya Allah" Ya daki steering.


"Are you alright?" Ta tambaya cikeda tsokana har tana le'ka fuskarsa.


"Yes,I'm fine ,fine!" Yayi 'ko'karin fad'a yana 'ka'kalo murmushi.


"Ok,so I should continue?"


"Laila is ok,time to stay quite, phem!" Ya had'e lips d'inshi da yatsa alamar shiru.


Kai ta kad'a tare da yin murmushi."Gobe ka sake tambayata"


Har yakaita school be sake magana ba,ita kuwa dad'i taji ta huta da tambayoyinsa.


Tana sauka ta had'u da Aliya da itama yanzun mijinta ya sauketa.


"Babyn mijinta irin wannan fresh haka" Aliya ta fad'a lokacin da Laila ta d'age niqab d'in.


"Mtchww! daga dawowa har kin fara"


"Gani nayi kinyi fresh ko kema?"


"Sede ke d'in"


"Gashi kuwa ni ina ruwana" Aliya ta fad'a.


"Tohhh sekice kece mey abu"Laila ta fad'a tana kallon cikin Aliya daya tasa.


Haka suka cigaba da hirarsu kafin a shiga lecture,a class malami yana explanation amma gaba d'aya hankalinta baya gurin.Tuna d'azu tayi -tayi tana tambayar zuciyarta koh da gasken yaji haushi har cikin ransa?


Seda Aliya ta ta'bota tukun ta dawo daga tunanin data tafi.Malamin taga yayi pointing d'in ta ,tana mi'kewa yayi mata tambaya akan abinda ake tayi tsilli-tsilli da ido se Aliya ce ta rad'a mata ta fad'a.


Da aka fito Aliya tayi ta mata tsiya wai tunanin Babynta take,lecture d'aya suka 'kara wajen 3:30pm suka tafi gida.Bata yi zaton ganin motarsa a yanzu ba dan a tunaninta se anjima ze komo gida.D'akinta ta wuce seda ta watsa ruwa ta fita 'kasa, kitchen ta shiga ta dafa couscous da miyan cabbage.Tana dinning Sega Amjad ya sakko,da beyi niyyan zuwa table d'in ba amma ganin tana wajen yaje.


" Where is mine?"Yayi nuni da abincin.


"You don't like a Nasty food"


Kamar be jita ba ya bud'e food warmer d'in ya rife tare da ta'be baki.


"It smells bad"


Dama ta 'koshi ta tattare plate d'in ta wuce kitchen.


"I heard about him but you didn't show me his picture" Tajiyo muryarsa.


Shiru tayi masa ta cigaba da d'auraye plate d'in hannunta.


"I'm talking to you"


Nan ma batace komai ba,wani takaici ne ya lilli'besa dan zuciyarsa tana fad'a masa gaskene abinda ta fad'a d'azu.'karasawa yayi har inda take bata zata ba taji d'imin mutum a bayanta.A firgice ta juya amma ko tsaiwar arzi'ki bazata iya ba dan distance d'insu kad'an ne.Zuciyarta tuni bugunta ya 'karu ,ta manne da jikin drawer d'in kamar zata shige ciki.


"Is't true what you said earlier?"


"Move back first" Tayi 'ko'karin fad'a.


"I wanna see it through your eyes" Ya sake matsawa kusa ,kallon nashi ma yanzu ta dena ta rife idanuwanta gam zuciyarta kamar zata fito,gashi ko mayafi bata yafa ba riga da skirt ne na atamfa tayi d'auri mey steps.


A hankali ya rage tsahonsa fuskarsa ba alamar wasa ya d'ora hannunsa all side na drawer d'in har yatsansa na ta'ba hannunta data dafe drawer.


*Vote*
*Comment*
*Share*



*Dijensyā¤*


























🌼🌼 🌼🌼




šŸ’¦ šŸ’¦




*AMJAD*




šŸ’¦ šŸ’¦






🌼🌼 🌼🌼




*WRITTEN BY DIJENSY*


*WATTPAD:@dijensy*





2⃣1⃣-2⃣2⃣


Tap d'in sink dake zuba ya mi'ka hannu ya kashe sannan yaja baya.Laila har lokacin idanuwanta a rufe suke zuciyarta bata fasa bugawa ba,a hankali ta rage jin d'umin mutum a jikinta,da 'kyar ta soma bud'e idanuwanta gani tayi ba kowa a kitchen d'in.Tunani ta shiga yi ko dama ba gaske bane,data dubi sink d'in taga tap d'in ya dena zuba.Da sauri-sauri ta 'karasa d'auraye plates d'in ta koma d'aki,har lokacin bata dena jin tsoro ba gani take kamar zata sake ganinsa.


Shi kuwa daya koma d'aki murmushi ya shiga yi ,be zacci tsoronta yakai haka ba shikam yanzu ya samu damar hanata fad'ar abinda ranta yaso.Phone d'insa ya d'auko yayi plugging earphone tare da turning on song(Can I have this dance:high school musical).


*šŸŽµTake my hand, take a breath*


*Pull me close and take one stepšŸŽµ*


*Keep your eyes locked to mine šŸŽµ*


*And let the music be your guide Won't you promise me? (Now won't you promise me?)šŸŽµ*


*That you'll never forget (We'll keep dancing) šŸŽµ*


*To keep dancing wherever we go nextšŸŽµ*


*It's like catching lightning The chances of finding someone like you It's one in a million,šŸŽµ*


*the chances to feeling The way we do.....šŸŽµ*


Ba'ai nisa ba ya katse wa'kar dan ta soma tuna masa da Rosie,dan itama bata da wa'ka kamarta asali ma ita tasa masa son wa'kar dan wasu lokutan tare suke jin wa'kar suna bi.


ā˜…ā˜…ā˜…


Laila har 9pm bata fito ba 'kishir ruwa take ji amma ta kasa fitowa gudun kar wani abun ya sake faruwa.Wayarta ta d'auka ta hau Instagram taga Amjad mu'az started following you,profile d'inshi ta bud'e taga post kala-kala.Wani photo data gani seda tayi tsaki ganin ko riga besa ba showing his six packs ,daga shi se ¾.


"Se kace d'an arna"Ta fad'a tana scrolling taga wani photo nashi ta gani yana yaro sosai befi 9yrs ba dariya photon ya bata yanayin yadda yayi wani kalar soko ya cakumi teddy bear.Haka tayi ta bin sauran pics d'in wasu tare da su Mom wani friends, a haka har ta soma jin bacci daga baya ta ajje wayar tayi kwanciyarta.


Washegari da wuri tayi shirin makaranta ko breakfast bata yi ba ta fice se sauri take karya fito yace ze kaita.Seda taga ta hau d'an sahu hankalinta ya kwanta,lecture biyu kad'ai sukai amma Laila ta'ki tahowa gida,2pm lokacin masjid kawai taje bayan datai sallah ta kwanta bacci ya kwasheta.


4:09pm ta farka ,mamakine ya kamata ganin har tayi bacci me tsaho haka.Tashi tayi ta d'auro alwala tayi sallah,bata ankara ba taga garin yayi duhu sakamakon hadari daya had'u.Ba shiri ta tarkata handout d'inta ta zira a jaka ta fito,sanda ta hau napep har an fara iska mey 'karfin gaske kafin ta isa gida ruwa ya sakko.Kafin ace mey nan da nan danan titi ya d'inke da abin hawa a hankali ake tu'kin ruwan se shigowa yake cikin napep d'in rabinta ta jike,ganin ta kusa 'karasawa gida kawai ta sauka ta kama tafiya sauri-sauri ,tun daga nesa ta hango wani mota a ranta ta ayyana na Amjad ne aiko tana 'karasowa ta ga shine yana ciki ya'ki fitowa gashi motar ta gagara tashi ya dad'e yana ta fama ganin ruwa ya sakko yasa ya shige ciki ya zuge glass rabi.Ta mirro d'in gaba ya hangota ,a tunaninsa ko zata tsaya amma yaga ta wuce kamar bata gane shi bane.Da kanshi ya fito daga motar dukda tsananin ruwan da ake."Laila" Ya kira sunanta.


Tana jinsa yana kiranta amma tayi burus,sema 'kara saurin tafiyarta da tayi.Da sauri yasha gabanta ya ri'ko hannunta.


"Laila I'm talking to you"


"What?"


Shiru yayi dan baida abin cewa."Get inside the car,it's raining heavily"


"No"


Tayi saurin matsar da hannunsa kan kafad'arta,sauri-sauri ta cigaba da tafiyarta.Ganin ba tsayawa zatai ba ya koma motar ya ciro umbrella ya biyota ,matsawa yayi kusa da ita ya bud'e umbrellan yayi musu rumfa.Ganin jikinta na gogar nashi ta matsa, kusan rabinta ruwa na shafa,kamar 'kiftawar ido taji ya dafa kafad'arta har tana fad'owa jikinsa."Stop misbehaving"


Ita ba abinda yake damunta kamar yadda hijab d'in ya manne a jikinta gashi rigar material ne a jikinta curve ya bayanna ,se jajjan hijab d'in take amma a banza.Suna shiga gida ta matsa daga jikinsa da sauri ta 'karasa jikin 'kofar ta ciro key ta bud'e, kafin ya shigo har ta haye sama.Tana ajje jakar ta fad'a bathroom,ruwa mey zafi tayi wanka dashi ta d'aura towel zata fito ta tuna bata shigo da wani hijab d'in ba gashi kayan data cire duk a ji'ke.Hakannan ta murd'a handle ta fito ta rufo 'kofar toilet d'in,ganin mutum a tsaye yasa ta razana.Juyawa tayi da sauri tana kici-kicin bud'e 'kofar bathroom ,kamar rufewa take sake yi 'kofa ta'ki bud'uwa,haka ta gaji ta 'kyale 'kofar amma ta'ki waigawa ta kalli inda yake.


"Mey zeyi a d'akinnan inba neman masifa ba?"Ta fad'a a ranta.


" What are you waiting for?"


Ta'kowa yayi ya 'karaso har inda take ya mi'ka mata Biro"You left it in my car?"


Ko waigowar arzi'ki ta kasa illa mi'ka hannunta da tayi ta kar'ba sede kuma bawai ya cika biro d'in bane duka, yana ri'ke da farko tana ri'ke da 'kasan biron. Tunda ga sama har 'kasa yake ta binta da kallo tana jin idonsa a kanta ta rasa inda zata saka kanta ji take kamar ta nutse a zuciyarta se zagin towel d'in take dan iya cinya yake ,biron ta sake masa ganin ya'ki cikawa shima sakinsa yayi ya fad'i 'kasa.


"Pick it up"Taji ya fad'a cikin tattausan harshe.


" Innalilahi"Ta fad'a a ranta.


"I ca.." Bata 'kare ba ta tsaya da maganar dan kar ayi irin ta jiya batasan ya za'a 'kare ba.


A sanyaye ta waiwayo tana dafe da towel d'in ta dur'kusa ta d'auka jelar gashinta dake ta kwanta gadan bayanta.Tana d'aukan biron bata ko tsaya a ko ina ba se wajen wardrobe cikin sauri ta ciro hijab ta zira,yana kallonta ta gama zire-zirenta be sake cewa komai ba ya fita daga d'akin.


"Yanzu akan biro shine za'a biyoni har d'aki mtcww!"


Tun bayan komawarsa d'akin ba abinda ke yawo a kansa irin image d'in Laila a yanayin daya ganta d'azu,da yayi 'ko'karin kauda tunaninta seya kasa ,laptop d'insa ya d'akko ya soma dann-danne amma sam hankalinsa ba anan yake ba faga baya ya d'auki waya ya soma game a thinking of Laila,pillow ya d'ora kansa ya kwanta ko zeyi bacci.Ko Rosie da take sak English wears matsastsu dasu mini skirt be ta'ba jin abu a kanta ba kamar irin Laila."She is pretty"Yaji zuciyarsa ta fad'a.


Laila kuwa bayan ta gama shirinta cikin atamfa riga da skirt ta d'aura d'ankwalinta,lokacin ruwan ma ya tsaya yamma tayi li'kis maghrib ya kusa.Windown d'akin ta bud'e tana kallon yadda flower plants sukai kore shar ga furannnin sunyi fresh sosai view d'in ya birgeta jitake kamar ta sakko sede kuma tana gudun had'uwarsu.Seda taji anyi kiran sallah ta zuge windown d'in tayo alwala itama.Bayan ta idar da sallah kuwa a jakarta ta d'akko meatpie data siya a school gida biyu ta soma ci dan yunwa ta isheta,taci abu kuma ba ruwa.


Shawara tayi-tayi daga 'karshe de ta sakko 'kasa,cikin sand'a ta shiga kitchen da sauri ta d'akko bottle d'in ruwan ta fito zata hau sama taji 'karar tsawa ,harda dur'kusawa kamar wacce za'a kama."Terrified"


Bata kalli inda take tsammanin daga nan yake ba tayi sauri ta hau sama,tana shiga d'akinta ta rufo ,ba ita ta sake fitowa ba se washegari.


Yau d'inma da sauri ta yi shirinta sede tana sakkowa 'kasa ta ganshi a dinning yana shan tea se biscuit a da'n plate.Da kamar ta koma kuma ta daure ta wuce kitchen."Morning "Taji ya fad'a.


Ko amsawa kasa yi tayi na d'aya tasan ita bata ta'ba gaisheshi ba na biyu bata sani ba ko d'aya daga cikin abunsa ne na tsokana.A kitchen d'in ma ta rasa mey zata dafa,dankali ta soya tayi 'yar chicken sauce.Sauri tayi taci gudun kar ayi ta d'ayan ranar yasa koh wanke plates d'in bata tsaya yi ba.


Tana fitowa ya bar wajen,direct ta koma d'aki ta d'akko jakarta,cikin 'kan'kanin lokaci ta fito daga gidan.Yana komawa d'aki ya d'akko key d'in motarsa,ganin bata kitchen yasan har ta fice.Ba 'bata lokaci ya fita,a hanya ya tarar da ita tana tafiya,horn yayi tayi mata amma ta'ki juyowa,sede ya fito yayi mata magana tukun ta shiga.


" Ko yaushe aka gyara motar?"Ta tambayi kanta.


"Oho" Ta fad'a.


Shiru bame cewa komai har suka isa makarantar,tana fita ta rufo 'kofar ta kama hanya ta wuce,be ja motarsa ba har seda tayi nisa yana kallonta kan daga bisani ya tafi.


Tunda ya shiga office ko aikin kiriki ya kasa banda tunanin Laila ,tun farkon aurensu zuwa wannan lokacin yayita tunawa.Shi kad'ai yana murmushi,ana knock a 'kofar office d'insa amma hankalinsa baya gun.


"Sir,sir!" Yajiyo ana kiransa.


Se lokacin ya farga ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.


2:30pm nayi ya tashi daga aiki be tsaya ko ina ba se school d'insu Laila. Da farko yayi niyyar kiranta daga baya kuma ya fasa dan yasan zata iya 'kin fitowa.Haka ya zauna a mota zaman jira kad'an-kad'an yana ganin students na fitowa amma be hangota ba ya kwashe kusan 1hr 20min kafin ya hangota tana tahowa bakin titi.Motarsa ya 'kara yin gaba da ita dede inda take a tsaye ya sauke glass d'in motar.Ta kalleshi sarai amma seta matsa gefe,tana jin wasu cikin 'yan mata a gurin suna gulmarsa.


"Yana shigowa school d'innan,ko d'azu naga motarsa".



"Wannan za'a ga kyawawan 'ya'ya"


" Kamar balarabe ne naga" D'ayar tace"A'a bature ne.


"Ke india ne bakiga irin gashinsa ba ai turawa farin gashi garesu"


Ita dariya ma suka so bata dan yadda taga hankalinsu yana kanshi se

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login