Showing 48001 words to 51000 words out of 62917 words
Chapter 17 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt
iya tashi yin sallahr asr dan tsabar hankalinta ya kasa kwanciya se recalling take.Yunwa take ji amma ta kasa sakkowa kitchen, har bayan maghrib se shawara take daga 'karshe de ha'kura tayi ta kwanta a haka yunwa na addabarta.
Washegari 8:12am ya gama shirin office saboda makarar da yayi ko tunanin breakfast ma beba ,koda ya sakko 'kasa yaga be ganta ba.Haka ya hau bene yayi knocking d'akinta,tana zaune dama ba zuwa zatai ba yau.
"Laila" Ya kirata.
Da farko 'kin amsawa tayi se a karo na biyu ta amsa .
"Are you not going to school today?"
"Yes" Ta amsa daga ciki ta'ki tasowa ma daga kan gadon balle ta bud'e 'kofa.
Jin haka yasa ya kama hanya ya sauka,yau duk seya ji ba dad'i fitar kasancewar ba ita.Yana driving kusan rabin hankalinsa baya gurin,ya hau gadar sama yana driving be lura ba da wuri sega mey d'an sahu ya biyo one way garin kaucewa mey napep d'in motarsa ta daki gefen gadar ta fad'a 'kasa,upside down ta sauka ,tayi mugun chanja kamanni,mey d'an sahu ya daki gini, lokaci guda jama'a aka hau salati a take waje ya d'inke da mutane.
*Shocked?? Don't forget to comment.*
*Dijensyβ€*
πΌπΌ πΌπΌ
π¦ π¦
*AMJAD*
π¦ π¦
πΌπΌ πΌπΌ
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
*Thank you for your warm support sister,Amjad fans kuma ina godiya ,ana tare*
2β£5β£-2β£6β£
Mey d'an sahun da aka yi 'ko'karin ciro shi daga d'an sahun aka ga ko numfashi bayayi ,kwance aka ajje shi gefe,daga 'kasan gada kuwa mutane uku ne suka shiga kici kicin bud'e 'kofar motar amma abu ya gagara ,seda ambulance suka 'karaso suka ciro Amjad da 'kyar sakamakon belt dake ma'kale a jikinsa, jini ya wanke fuskarsa haka aka sanya shi a mota a sheme.
β
β
β
2hrs later,tana d'aki tana duba handout wayarta tayi ringing,ganin Canada jikin screen ta'ki picking.Sau biyu ana kira bata d'aga ba se ana uku."Hello".Cikeda 'kosawa.
Jin murya daban bana Amjad ba yasa ta gyara zama.Tana jin abinda aka fad'a ta d'ayan 'bangaren ta saki wayar kan gado.
Ta rasa abinda zatai,wayar ta d'auka ta sake kallan call d'in."Amjad "Ta furta a tsorace.Tafi 10min kafin daga baya ta d'au waya ta kira Mami.
" Innalilahi wa innailaihirraji'un"Mami ta fad'a.
"Kina asibitin?" Mami ta tambaya cikin rud'ani.
"A'a"Ta amsa feeling guilty.
" Mey kika zauna yi da baza ki tafi ba?"
"Zan tafi yanzu" Ta fad'a.
"Toh nima ina tahowa".
Mami kafin ta tafi seda taje gidan Kawu Yunus ta fad'a masa halin da ake ciki,tare suka tafi asibitin kusan tare suka isa da Laila, Kawu Yunus ne ya kira Dad ya sanar masa.A gabansu aka shiga dashi theatre room hankalinsu yayi mugun tashi dan yanayin da suka tsince shi.8:15pm aka fito dashi daga nan aka kaishi d'akin kwanciya,suna kan bench ko d'akin basu samu shiga se bayan doctor ya fita daga d'akin,Mami da Kawu suka shiga abin tausayi hannunsa yasha plaster sakamakon karaya se kanshi an zagaye masa da bandage, ga 'karin jini da ake masa.
" Allah ya baka lafiya"
"Ameen" Mami ta amsa cikin nuna jimami.
Kawu Yunus se can dare ya tafi ya bar Mami da Laila data kasa shigowa tana waje kan bench itama daga baya Mami fitowa tayi ta zauna kan bench d'in.
Mom kuwa basu san mey ake ciki ba se ji sukai Dad yasa su shirin tahowa Nigeria da suka tambayesa dalili ya'ki fad'a musu.Koda ta kira Amjad d'in ma ta fad'a masa suna zuwa taji wayar a kashe.
Washegari 9pm suna Nigeria, Mom tunda taga an shigo asibiti jikinta yayi sanyi."Tell me what's going on?"
"It's Amjad..."
"Mey ya sameshi ? What happened to my son?"
"He had an accident"
Dukansu ba wanda be firgita ba,cikin rashin ha'kuri driver na parking ta fita a motar Dad yana kiranta amma ta'ki tsayawa,da 'kyar ya samu ta tsaya ganin ba sanin d'akin tai ba.Seda suka kira Mami ta fad'a musu numbern room d'in.Cikin rud'ani suka 'karasa ,Laila tana zaune kan bench tagansu tsidik cikin hanzari suka shiga ita de ta bisu da kallo dan har lokacin ta'ki shiga d'akin.
Har yanzu yana kwance same position ko motsi beyi ba,Mami da Zakia tuni suka fara tsiyayar hawaye.
"Amjad" Ta 'karasa gefen gadon.
Hannunta ta d'ora kan gashin kansa tana shafawa.
"My child"
Suna tsaye a kansa Mami ta shigo d'akin,bayan sun gaisa suka jajantawa juna Mami se bawa Mom ha'kuri take amma ta'ki dena sharar hawaye.
"Ina Laila" Mom tayi 'ko'karin tambaya.
"Ta'ki shigowa tana waje" Mami ta amsa.
Mom da kanta ta fita wajenta ta tararda ita ta jingina da alama tayi nisa cikin tunani."Laila"Ta kira sunanta.
Da sauri ta dawo daga tunanin data tsillima."Mom,Ina yini"Ta gaisheta tana sunkui dakai.
Hannu tasa ta d'ora a kafad'arta."Kiyi ha'kuri kinji,pray for him ze zamu sau'ki"
Kai kawai ta kad'a ba tare da ta d'ago ba,bata ankara ba taji Mom ta jawota jikinta kamar 'yar baby tana shafa bayanta se bata ha'kuri take.Itade Laila tayi lif ita kad'ai tasan abinda take ji a ranta.
Sun dad'e a asibitin kamar baza su tafi ba Dad ya tashesu suka tafi,aka bar Mom se Laila Mami ma gida ta koma. Mom bata da buri irin taga ya farka,tafi 1hr tana zaune gefen gadon tana kallonsa.Laila data shigo d'akin ma daga can baya ta ta tsaya kamar bodyguard ta'ki zama.
Seda dare ya nisa ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun d'akin,a hankali gyangyad'i ya fara d'aukanta daga bisani tayi bacci.Mom data kalleta du setaji tausayinta ya kamata.
β
β
β
Kullum se su Dad sunzo asibitin ,yawanci su suke kawo musu abinci sometimes Mami ,har anyi kwana shida amma Amjad be farka ba abin har ya soma damin Mom ko tashi ta shiga bathroom ba son yi take ba dan gani take kamar idan ta dawo bazata ganshi ba.Laila dan ma Allah yasa yawancin coaurses d'in duk anyi covering ba zuwa school take ba.
Yau ne ma da Aliya ta kirata take fad'a mata za'ai test shine taje school d'in tana yi ta komo asibitin.Ganin Dad ,Shaheed Zakia da Kawu duk suna d'akin yasa ta fito ta samu bench tayi zamanta,sun jima kafin su fito tayi bacci kan bench d'in lokacin 10pm yayi.
β
β
β
Gidansu Amjad taf yake da mutane,tana shigowa taga su Mami suna zaune kan carpet da sauran mutanen da ba sanin fuskokinsu tayi ba,Mom ta hanga daga kan step d'in bene gefenta Zakia se kuka take tana wata magana da baji take ba.Gwiwa a sanyaye ta 'karasa inda suke bata yi musu magana ba ta haye saman ,'kofa ta gani daga gefen side d'inta a bud'e tana shiga taga gawa a kan makara cikin likafani ba kowa d'akin a tsorace ta 'karasa tana zuwa taga fuskar a bud'e ganin Amjad ta saka ihu.
"Amjad!"Ta mi'ke firgit se zufa take ,asibitin yayi shiru se yanzu ta gane mafarki take,zuciyarta se dukan uku-uku take da sauri ta tashi ta bud'e 'kofar d'akin ta shiga.
Mom ta gani tana bacci a zaune kan kujera,1:28pm agogon d'akin ya nuna.A hankali ta 'karasa gadon tana kallonsa ko 'kifta ido ta'kiyi,gefen gadon ta zauna tana 'kare masa kallo mafarkin datai yana dawo mata ,zuciyarta ce ta raya mata what if da gaske mutuwa yayi.Tsoro ne ya hauta lokaci guda, hannunsa ta d'ago ta d'ora a tafin hannunta 'kwallar dake ma'kale a idanuwanta ta zubo kuka sosai ta shiga yi mara sauti.Mom dede lokacin ta bud'e idanuwanta ta d'ora su kan Laila dake zaune gefen gadon ri'ke da hannunsa, ganin haka setayi murmurshi ta maida idanuwanta ta rife a zuciyarta tana mey jin dad'i ta wani 'bangaren tana jin tausayin halin da Laila ta shiga.Tafi 20min a haka har lolacin bata sake masa hannunsa ba sede yanzu ta dena kukan,kamar gangan taji motsin yatsansa d'aya a hannunta.Tana kalla taga ba gangan bane ,a sanyaye ta mayar da hannunsa ta ajje ta mi'ke daga kan gadon zuciyarta kuwa wani irin farinciki mara misaltuwa ne ya ziyarce ta.Gefe ta samu wani kujerar ta zauna cikin 'kan'kanin lokaci bacci ya saceta.
Yau ma da safe akai mata waya ake fad'a mata za'ai test dan haka ta shirya ta tafi school,har se to 12pm akai musu test d'in bayan nan kuma aka shiga lecture,hakannan ta samu ta zauna se 4pm tukun ta komo asibitin.Tana shiga ta tsaya daga 'kofa ganin mutum ido biyu tayi yana magana da Mom amma bata san mey yake cewa ba.Ba wanda ya lura da shigowarta se Zakia ta kira sunanta,se lokacin kallo ya komo kanta Amjad yana daga kwance ya kallota a wahale idanunsa sun 'kan'kance fuskarsa ta nuna alamar ramewa.
"Laila,I'm glad you're back" Mom ta fad'a tana kallonta sannan ta komar da kallonta kan Amjad irin alamar ya farka d'innan take nuna mata.Kallo d'aya ta sake yi masa ta kawar da kanta,duk wani move datake yana kallonta gashi ko magana yaga ta'ki yi ,su Mom kuwa basu ma lura da hakan ba.Mami da sukai waya da Mom take sanar mata ya farfad'o tare da kawu suka zo suka duba shi daga nan ta sake tahowa da Laila wasu kayan nata.Se 9:30pm suka bar asibitin aka bar Mom da Laila,gabaki d'aya ta kasa sake wa fiye da da.
"Amjad you need to eat" Mom ta fad'a dan tun d'azu da rana dayaci chicken spaghetti be kuma cin wani abu ba.
"No I'm ok"
Fruit salad d'in ta samu ya sha kad'an,ita de Laila kallonsu kawai take duk abinda suke,jinta take a takure dama ta koma gida da yafi mata take fad'a a zuciyarta.Bayan yasha magani ya kwanta bacci daga baya Mom itama tayi,Laila 'karshe se tunanin yadda zata 'kare wannan zaman take.
Washegari 5:40am Mom ta tashi bayan tayi sallah Amjad ya farka ta taimaka masa yayi taimama yayi sallah,Laila dama bayin sallah zatai ba amma dukda haka takan tashi sede kuma yau baccinta tayi har se wajen 7:30am ta farka.Tana bud'e ido taga Mom tana gefen d'anta tasa abinci a gaba tana bashi yana ci da 'kyar,duk kunya taji ta isheta tashar'bi bacci surukarta na kallo abin kunya tayi tunani a ranta.Kamar ko yaushe cikin rissinawa ta gaisheda Mom ganin ido yasa shima ta gaishehi harda tambayarsa ya jiki, shikuwa ya'ki amsawa yayi kamar beji ba.
Bayan awanni kad'an sega su Zakia sunzo asibitin,dama haka take so tana ganinsu tayi fitowarta ta fita can waje ta samu bench ta zauna tana kallon shuke-shuke.
"Mom are you staying here until..." Shaheed be 'kare magana ba Mom tace."No..no I'm not going to stay here beside I' m going back home today"
"What? Are you leaving me like this?"
"Amjad ,Laila is here and I think is ok like that"
"Yes!" Zakia da ba da ita ake ba ta tsomo baki.
Kallonta kawai yayi ya kawar da kai ba tare da yace komai ba dan yanzu ba lokacin wannan bane.
"Your wife is here,I'm sure she will take good care of you I knew it"
"But.."
"Do you want me to tell you something you don't know?"Ta tambaya bayan data ga yaran hankalinsu baya gun.
"What?"Ya tambaya.
" The time when you was unconscious I saw Laila holding your hands crying, tears flowing down her cheeks,you know why? Because she cares about you she don't wanna lose you "
Kallanta ha tsaya yi saroro yana tunanin anya kuwa Laila ce zatai haka.
"Didn't you believed me?"
"I do 100% remember I trust you Mom" Ya fad'a yana murmushi har cikin ransa ,farinciki ya mamayeshi.
"Laila cried for me ,does this means she loved me?" Abinda ya shiga tambayar zuciyarsa kenan yana mamaki.Ya 'kosa yaganta a halin yanzu amma ya neme ta a d'akin ya rasa ko ina tayi?
Laila seda ta gaji da zaman wajen ta komo ciki,abinda take gudun shi ta sake tararwa watoh kallon da yake mata,ko abinci ta'ki sakewa taci Zakia tana mata hira kad'an-kad'an tana amsawa,suna zaune har Dad yazo bayan 'yan awanni suka tashi tafiya jin Mom tace tafiya zatai itama Laila hankalinta ya d'aga.Kamar ta tsuguna ta ro'keta ta zauna haka taji,tana kallo ta tattara inata-inata suka tafi tare aiko Laila harda biyo bayansu irin rakiyarnan zatai suna tafiya ta zauna kan bench ta'ki komawa d'akin,ta gwammace ta zauna a waje data shiga.Ko wayarta bata fito da ita ba ,zaman wajen kuma yanzu taji ya gundireta 7:40pm ta tashi ta komo d'akin kamar wacca "kwai ga fashe mata a ciki.Ta shiga ta rufo 'kofar ko kallonsa ta'ki shikuwa tana shigowa ya sauke idanunsa a kanta kallo bama na wasa ba...
*Dijensyβ€*
πΌπΌ πΌπΌ
π¦ π¦
*AMJAD*
π¦ π¦
πΌπΌ πΌπΌ
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
2β£7β£-2β£8β£
Kan kujera ta samu ta zauna tana sake gyara zaman mayafinta data yafa kanta.
"I thought you run away" Taji ya fad'a.
Shiru tayi bata ce komai ba tana hangen handbag d'inta dake kan drawer,mi'kewa tayi daga zaune ta taka inda jakar take ta ciro wayarta ta dawo ta zauna.
"Where is my phone?" Ya tambaya ganin ta ciro tata wayar a jaka.
Tuna inda ta jefa wayar ta shiga yi dan tun sanda aka dam'kamata a hannunta sanda tazo asibitin.Mi'kewa tayi daga zaune ta shiga duba akwatin kayansu ta bud'e can ta bud'e nan can ta gano ta 'kasan akwatin.Tana ri'ke da wayar ta 'karasa gadon ta mi'ka masa."Thank you".Ya furta.
Suna zaune d'akin shiru bame magana nurse ta shigo,kai tsaye ta wuce inda yake ba tare da ta lura da Laila ba.
"Amjad Mu'az,sannu koh"
Alluransa da ake masa ta had'a ta bud'e carnula ta tsiyaya,se magani data mi'ka masa bottle of water data gani kan drawer side na gadon ta d'auka ta tsiyaya a cup a mi'ka masa se wani 'kwar'kwasa take."
Se lokacin ta waiwayo ta kalli Laila dake latsa wayarta."Ke ki biyo ni ki kar'bi wasu magunguna nashi"Ta wani kalleta a wula'kance.
Laila tajita sarai amma jin tace 'ke' yasa ko d'ago kanta batayi ba balle ta kalleta.
"Baki ji bane" Ta matso inda take.
"Ke naji kin anbata kuma a nan d'akin ba mey suna ke" Laila ta fad'a bayan ta komo da kallonta kanta.
"Ba irinku ya dace kuke jinyan mutum ba dan baku san darajar wanda kuke jiyyar ba," Tana gama fad'ar haka ta fita ta bar Laila.