Showing 45001 words to 48000 words out of 62917 words
Chapter 16 - AMJAD COMPLETED Complete Hausa Novels by DIJENSY.txt
kallon motar suke kamar saje su shiga.
Basu suka rud'e ba seda suka ga ya fito,basu kad'ai ba hatta wasu mata dake gefe seda suka kalleshi.Tana ganin tahowarsa ta gefen ido ta'ki juyo wa."Laila come on get into the car"Taji ya fad'a cikin tattausan harshe.
Gefen fuskarta ta waigo tayi masa wani kallon banza,ita bata so taga yana shishshige mata"Nina ce kazo d'aukana"Ta fad'a 'kasa-'kasa dan beji mey tace ba.
Badan kar ta yarfa shi cikin mutane ba da bazata bishi ba,a hankali ta taka wajen motar.Kallo suka bita dashi suna mamaki."Wace wannan d'in?"
"Matarsa..."
"A'ina d'in"
"Matar aure ce ai" Wata daga cikinsu ta fad'a.
Da ido suka bi motar da kallo har suka bar gun suna mamaki.
"How was the lectures?"
Banza tayi dashi bata amsa ba kamar bata ji ba tama kawar dakai tana kallon window.
"Are you hungry?" Ya sake mata wata tambayar.
"A'a" Ta bashi amsa a ciki ciki.
Ganin ba son magana take ba shima yai shiru a tunaninsa ko stress ne.Suna komawa gida ya sake fita cikin 'yan mintina se gashi ya dawo da leda a hannunsa.
"Knock! Knock! Taji an bugo 'kofar d'akinta ko wankan ma bata shiga ba,hijab d'inta ta zira tukun ta bud'e.Ledar ya mi'ka mata fuskarsa a sake ita kuwa ko d'an sakin fuskar ta'ki yi,hannu tasa ta kar'ba batace komai ba ta koma ciki ta ajje kan drawer, da ya tsaya kamar zeyi wata maganar se kuma yayi shiru ya tafi d'akinsa.
" Better "Ta fad'a.
Se bayan ta fito daga bathroom ta duba ledar,burger ne da baguettes se sauce da tana bud'ewa ta ta'be baki "'Karni ma take Allah kad'ai yasan wacce ta dafa,Allah yasa ba miyar 'kwad'o bace dan shima baze rasa ci ba ko kuma ma tsutsa"
Koda ta gama shirinta bata kalli abincin ba dan a 'koshe take ,haka ta 'karachi zamanta har se bayan isha'i ta janyo ledar ,burger d'in kawai taci ta ajje saura baguettes d'in kuma ta sauka 'kasa a kitchen ta ajje, miyar kuma ta ajje a fridge.Cock da bottle of water ta d'auka ta komo ,tana hawa bene shikuma yana sakkowa daga d'aki sukai karo har kayan hannunta suna fad'uwa,kusan shine sila tunda shine da sauri-sauri yake sakkowa.
*Don't forget to vote, comment and share.love ur๐*
*Dijensyโค*
๐ผ๐ผ ๐ผ๐ผ
๐ฆ ๐ฆ
*AMJAD*
๐ฆ ๐ฆ
๐ผ๐ผ ๐ผ๐ผ
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
2โฃ3โฃ-2โฃ4โฃ
Nan take ta dur'kusa tana dafe 'kafarta,ha'kuri ya shiga bata "I'm sorry ,I'm so sorry Laila".
" Ba wani sorry kana sani"Ta fad'a tana ri'ke da 'kafar.
Cock d'in ta kalla daya gangara 'kasa dan shi take tunanin ya fad'o mata a 'kafar.Mi'kewa tayi tsaye ta fara tafiya amma ta 'kasa take 'kafar se d'ingisawa take."Let me help you"Ya taho da shirin ri'ke hannunta ya d'ora a kafad'a aiko tayi saurin matsawa garin haka ta take 'kafar."Aghh!"Ta tsala 'kara.
Bata ankare ba taji an raba ta da 'kasa anyi mata d'aukan amarya, tuni ta shiga wutsul -wutsul tana d'uma masa duka a kafad'a."Mami!"Ta hau kiran sunan Mami.
Har seda ya kaita d'akinta sannan ya direta kan gadon."Stubborn ".Ya fad'a.
"Nan da nan idanuwanta sun cika da 'kwalla seda taga ya sauketa a d'akinta ta d'an nutsu." You can leave now"
"You're sending me away,what did you think I'm doing? Sometimes you're crazy"
Fita yayi daga d'akin bayan 'yan minti kad'an ya dawo da man zafi a hannunsa.Jira take taga abinda yake 'ko'karin yi,tana gani ya zauna gefen gadon tare da ri'ke 'kafar ta matsar da 'kafar."Na iya shafawa"
Duk da be fahimci abinda ta fad'a ba ganin ta matsar da 'kafarta ya mi'ka mata man "Rub it".
Kar'ba tayi cikin sanyin jiki ta bud'e man ta soma shafawa a 'kafar a hankali sekace mey tallan mai.Ta sakankance taga ya wafce man ya soma shafa mata yana matsa 'kafar,hannunsa tasa tana 'ko'karin janye nasa hannu amma ta kasa sema ri'ke hannayenta biyu da yayi waje guda ta kasa ku'bucewa ,haka tayi ta raki har seda ya gama.
" Toh sake min hannun tunda ka gama"
"Mey kika fad'a?" Taji yayi magana.
"Tunda ka iya yaran ai zaka sani"
"I can speak hausa for the whole entire day"Yadda yayi pronouncing d'in hausar kamar like " Hosa"
"Ok,start"
"Ok,yanzu" Ya fad'a yana murmushi.
Itama murmushin tayi tana kallon arm d'insa data buga d'azu har wajen yayi ja kasancewar singlet ce a jikinsa.Shikuwa murmushin datai ne yasa ya kasa dena kallonta dan ba 'karamin kyau tayi ba.Saurin kawar da ido tayi ganin ita yake kallo,wayarta dake gefe ta d'auka ta hau dubawa dukda ba abinda take da ita.
"Na fita?"Taji ya tambaya.
"Eh"Ta amsa kanta a sunkuye.
" Ok,I'm going but you have to answer my questions "
"Questions".
"Yes".
Kai kawai ta girgiza tana tunanin irin tambayar da zeyi mata."Do you have feelings on me ? don't lie"
Sam batayi tunanin wannan tambayar zeyi mata ba duk da bata rasa amsar fad'a masa ba sede kuma tana mamakin dalilinsa na tambayar.Ya tsireta da ido kawai jiran amsarta yake.
"No" Ta amsa ba tare da ta bari sun had'a ido ba.
"No" Ya maimaita abinda ta fad'a.
"Ok,let's assume I love you? Will you love me back?"
"No"
"Why?"
"Because I don't love you"
"Your heart is for only one person?"
"I want to sleep" Ta fad'a tana janyo blanket d'in.
"Are yo sleeping like this?"Ganin ba sleeping dress bane a jikinta.
" Uhm"Ta rufe kanta.
Tashi yayi yazo fita ya kashe wutar d'akin sannan yaja 'kofar,tana jin fitarsa ta bud'e kanta, tambayoyin da yayi mata ta shiga yi ,seda ta jima kafin bacci ya d'auketa.
12:13am ya farka daga bacci ,da tunanin Laila a ransa ya farka.Drawer side lamp ya kunna ya tashi zaune agogon d'akin ya kalla yaga 12am,mi'kewa yayi tsaye ya bud'e 'kofarsa ya fita zuwa d'akinta,yana murd'a handle d'in yaga a bud'e 'kofar ma take.Tana ta baccinta yau ma tafin hannunta na kan fuskarta kamar rannan hakan yasa shi yin murmushi yanzu ya fahimci d'abi'arta ce haka.A hankali ya d'akko stool d'in mirrorn d'akin ya ajje opposite da ita ya zauna se 'kare mata kallo yake,tuna ko pic d'inta bashida yasa ya koma d'akinsa ya d'akko wayarsa ya komo ,hannun data kare fuskarta dashi ya matsar yadda fuskarta zata fito,pictures kala-kala yayi ta d'auka har kusan 12:40am tukun ya koma d'akinsa.
โ
โ
โ
Kwanaki suna sake yin nisa ,Laila lecture d'insu yayi nisa kullum Amjad ne yake kaita school baya ta'ba bari ta tafi da kanta,hatta dawowa gida wasu lokutan shi yake d'akkota hatta saba ma yanzu ta dena gudun.Haka ta 'bangaren abinci ma inde tayi girki zeci inba wai yaga besan irin abincin ba.A kullum Laila sake shiga ransa take duk wani abu da tayi birgeshi take haka idan yana office yata kallon photos nata kenan ,tunanin ta ba 'karamin d'auke masa hankula yake ba daga al'amuransa na yau da kullum ana meeting seya tsinci kanshi yana tunaninta wanin sa'in harse P.A d'insa ya masa magana.
Yau ma bayan ya tashi daga aiki ya biya mall 'yan siyayya,wani henna ya gani wanda ya tuna masa da 'kunshin da Laila tayi kwanakin baya,jiyai yanaso yaga ta sake yi dan haka ya siya mata.
Yana zuwa school d'insu tana fitowa,suna tafiya yana mata tambayoyi da suka shafi school d'inta rabi maganar da yaran hausa yake dan yanzu ya fara iya hausa sosai sede wajen pronouncing ne ake samun kura-kurai , kad'an -kad'an take bashi amsa dan ita har yanzu ta'ki sakin jiki dashi.Seda suka isa gida tazo fita ya kira sunanta."Laila"
Tana juyowa taga ya mi'ko mata package na henna d'in.Seda ta 'karewa lallen kallo sannan ta dawo da kallonta kansa daga bisani kuma ta kar'ba ba ko godiya tayi ficewarta.
Tana shiga d'aki ta bud'e drawer ta ajje ciki ta rufe ta wuce bathroom tana fitowa bayan ta shirya tayi sallahr asr.
Knock!Knock! Taji bugun 'kofarta.Dama hijab d'in ta na jikinta ta tashi ta bud'e,yana tsaye bakin 'kofar fuskarsa d'auke da murmushi.
"I just wanna inform you that I will take a trip tomorrow morning"
Kai kawai ta kad'a a ranta dad'i kamar ta ziba ruwa a 'kasa tasha.
"Alhamdulillah " Ta fad'a a ranta.
Dama gobe Saturday bikin Bahijja 'kawarta,tasan idan yana nan ba yadda za'ai ta kwana a gida yanzu kuwa setai amfani da wannan damar.
Yayi tunanin zega ta damu amma yaga sa'banin hakan ,du seyaji jikinsa yayi sanyi,gwiwa ba 'kwari ya koma d'akinsa.
Laila da farinciki ta kwana a ranta da sassafe ta soma had'a kayanta,dan tsabar farinciki kota kan breakfast bata biba,se wajen 9:30am ta sakko 'kasa a kan dinning ta hangi wata takarda dake ninke.Har zata shige ta ta dawo, tana bud'ewa taga short note.
I'm sorry for leaving without saying goodbye, I don't wanna wake you up.
Amjad
Duk da ba wani damuwa tayi ba amma seda taji wani iri dan tayi tunanin yana d'aki,ninke ta tayi ta ajje kan table d'in sannan ta shiga kitchen had'a breakfast.
Cikin azar'ba'bi tayi sauri tayi breakfast tana kammalawa ta koma d'aki ta shirya,kit d'in data sa kayanta ta d'auka ta fito daga gidan ,a hanya ta kira Maryam ta fad'a mata tana tahowa.Laila tana isa gida ta tafi gidan 'kunshi aka tsantsara mata ta dawo gida.
"Gan d'oki" Mami ta fad'a.
"Nice fa babbar 'kawa Mami"
"Da haka nan aka ce kiyi 'kunshi da tuni kina nan kina zun'buro baki amma dayake kin sa kanki har rawar jiki kike"
"Kwana nawa zeyi?"
"Sati d'aya" Tayi 'karya.
"Abin nema ya samu"
Kallon Mami kawai tayi a ranta ta san 'karya take.Wajajen 4:30pm ta tsantsara kwalliyarta ta rangad'a d'auri ta yafa gyale d'an 'karami ta fito.
"Inde a haka zakije kuwa sede bazaki fita ba,haka kike fita mijin naki ya barki?"
"Mami biki ne fa?"
"Koh meye zaki wani d'ora mayafi a wuya ke bakisan babbancinki da 'yan mata ba?"
Bata fita ba seda ta koma ta sauya mayafin ,ita kad'ai ko 'yan rakiya ma bata d'auka ba.
7:30pm ta komo gida Mami kam tayi ta mata fad'a tana kallo Amjad yana kiranta a waya amma ta'ki d'auka,daga baya taga text nashi.
Hi,how was the day? Hope you're doing good.
"Ina ruwanka?" Ta fad'a a fili tayi cilli da wayar.
"Komai ace aure..aure "
Tunda ta cillar da wayar bata sake dubata ba tayi baccinta,Amjad kuwa baida tunanin daya wuce nata ya matsu yaji muryarta yana ta jiran reply amma shiru.Ko washegari ma beyi zuciya ba da safe seda ya kirawo ganin bata d'aga ba yayi mata message.
Morning hope you're doing good?
Laila ba ita taga message d'in ba se to 10am shima 'kin reply tayi ta maida wayar ta ajje.Dan saboda Mami ta barta taje yinin bikin seta d'auki Fauzan suka je tare da ita aka kai amarya sannan ta komo gida.
Messages da missed call ba adadi ta tarar a wayarta banyan ta komo gida.
"D'azu kuwa Amjad ya kirani " Taji Mami ta fad'a.
"D'azu" Ta maimata tana zare ido a ranta tana fad'in Allah yasa Mami bata gani 'karya nayi ba.
"Mami se kuka gaisa?" Ta tambaya tana neman 'karin bayani.
"Ehyi naji yanzu ma ai Hausa ta shiga bakinsa ba kamar da ba"
"Uhm" Ta fad'a zuciyarta na raya nata Mami batasan komai akai ba.
"Ashe ma gobe ze dawo" Taji Mami ta fad'a.
Ita a tunaninta ze iya yin sati d'aya ,nan take murnarta ta koma ciki.
"Uhm" Ta fad'a a ciki.
"Toh gobe seki koma da safe aiko"
Nan ma ta amsa da "Uhm".
Haka ta kwanta tana jin haushi plan d'inta ya rushe kwana biyun datai d'in ma bata gode ba.Washegari da safe tayi ta la'kai-la'kai ta gaji da baccin safen ma amma ta'ki tashi seda taga dama kafin tayi wankan ma tayi ta la'kai-la'kai haka breakfast ma, ba ita ta tafi ba se wajen 1pm,tan d'an sahu taji shigowar text.
I'm on my way back home
" Naji"Ta fad'a.
Tana shiga gida tayi zamanta a d'aki ko kitchen bata kalla ba balle tayi tunanin wani abu shi girki.Tana yin sallah ta kwanta bacci, bama baccin take ji ba ta dole kawai tayi forcing kanta tayi baccin.
3:30pm 'karar doorbell ya tasheta daga bacci,seda ta d'auka mayafi ta yafa dan ta ayyana shine ya dawo.Fuakarsa d'auke da murmushi yake kallonta amma ita kuwa...
Bata tsaya ya shigo ba ta komo ciki."Laila, you don't like me here?"Ya fad'a bayan ya shigo.
Shiru tayi bata amsa ba kuma bata cigaba da tafiyar ba haka bata juyo ba.
"Are you mad at me?"
"No I'm not" Ta amsa sannan ta hau sama.
Shide ya rasa gane kanta the more yana showing mata kindness the more tana gudun sa besan dalili ba.Hakannan ya wuce d'akinsa ya watsa ruwa ,daga shi se singlet ya sakko 'kasa neman abinda zeci dan yunwa yake ji.
Babu wani alamar girki daya gani,'karshe se 'bigewa yayi da shan cornflakes,ya fito daga kitchen d'in ya had'u da Laila.Yanzu ba mayafin daga ita se doguwar riga na material red colour,'kunshin hannunta ya yi rad'au a fatarta,idanunsa basu sauka a ko ina ba se hannunta.Ba 'karamin dad'i yaji ba ganin tayi 'kunshi,a hankali ya taka zuwa inda take.
"Beautiful, I like it" Ya fad'a lokacin ya dawo da kallonsa kan Laila.
Hannayen nata ta 'boye a bayanta tana sunkui da kai.Batayi aune ba taji ya ri'ko hannayenta biyu kamar yarinya,duka biyun ya d'ago dasu kusa da face d'inshi ta rasa ma abinda zatai illa tsayawa kallan ikon Allah.
"Your hands always look good" Kamar 'kiftawar ido taga yayi kissing hannayen ta tsaya uwa gunki,seda hankalinta ya dawo jikinta tayi saurin 'kwatar hannun ta koma d'aki da sauri ta barshi a tsaye ya rasa ma mey zeyi sam ya kasa controlling kansa shikansa besan yadda akai haka ta faru ba.
Tana shiga d'aki tasa key ta rufe,hannayen nata tayi ta kallo tana tinawa.
Da'kyar ta