Showing 1 words to 3000 words out of 66141 words
Chapter 1 - Auren Soja Book Complete Hausa Novels by Feenerh..txt
ο»ΏCompiled By Umar Dalha Funtua.
Copied By Feenerh.
πΈπΈπΈπΌπΈπΈπΈ
*AURAN SOJA*π¨ββ
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
*Am back Fan's duk kan yabo da godiya ya tabbata ga Allah ubangijin kowa da komai da yabani ikon dawowa Acikin sabon littafi na ina fatan Allah kasa A amfana da shi kuskuren dake ciki Allah ya yafemin*
_jinjina gareku_
βGolden pen writers Association.
_ina Alfahari daku Mun Amsa sunan, ZAMANA AMANA Allah yakara mana kaunar juna_
1&2
_A kofar gidan na hango motoci Ajere kamar wani sarki ne ko ince gwamna Amma abin mamakin Samarine matasa reras Akofar gidan_
_Koda na matsa domin in dakko muku labarin Abinda ke faruwa sai naga Abin mamaki_
_matashin saurayi ne Azaune kyakkyawa Ajin farko wato (first class) duk inda kuke tunanin shi ya kai,_
_bawai fari bane a'a chocolate colour ne kala mai tsada, ga cikar zati da kuma haiba,_
_gadai samari masuji da jini Ajika Amma duk cikar wurin ba kamar shi,_
_mamaki na to wai waye wannan da samari suka za ga ye shi haka?_
*KAMAL*
_Lieutenant colonel kamal Ibrahim kenan (the youngest colonel)_
_gaba daya matasan suna zagaye dashi, shi kuwa ba abinda yakeyi sai faman danna tsadaddiyar wayar dake hannun,_
_ya wani kishin gida kamar wani sarki, kana ganinshi kaga miskilin soja ga wani irin kalai laita kamar wata mace,_
_hirarsu kawai sukeyi atsakanin su Amma shi hankali shi na kan wayar shi,
_can naga wani matashi Wanda bazasu wuce sa o 'I da kamal din ba ya karaso kusa da shi,_
_ya duka saitin kunnen shi " Don' yakamata kayi wani Abu gayun nan su watse kasan Alhaji na jiran isowarka ko_
_cikin ginshira kamar kuma bayaso yayi maganar, "do something'_
_gayen yayi murmushi tareda girgiza kai ya Ciro wasu bandir na y'an one one thousand ya mikawa daya daga cikin su,_
" Kuyi hakuri da wannan kafin ya gama ganawa da mahaifin shi zuwa gobe,
_cikin tsananin farin ciki samarin suka fara yimai godiya da kirari "Allah yayima General shugaban matasa kafin su watse,_
Yarage daga shi sai wannan gayen da naji wani ya kirashi da Samir,
_"Don yanzu zaka iya Ajiye wannan wayar mu shiga daga ciki ko kuwa ya fada cikin kuluwa_
_mikewa kawai yayi cikin kuzarin su na sojoji ya kama hanyar shiga cikin gidan,_
_Hmm Ajiyar zuciya na sauke domin yanzu ne na kare mai kallo da kyau dogone sosai Wanda ya Amsa sunan shi namiji_
_Allah yayi mai k'ira irinta jaruman sojoji Masha Allah,_
_Abin mamakin shine nasan sojoji basa mu amala da manyan kaya Amma shi gashi harda hula ga lafiyayyan Agogon Rolex takalminshi wow_
(He is damn handsome Fan's)
_Sun nufi cikin gidan kai tsaye, direct wani part naga sun shiga saboda na lura gidane mai dauke da parts da d'ama,_
_wani dattijo na hango kishin gide acikin wani ma dai daicin falo w'anda akalla zaiyi sittin ko fiye da hakan,_
_Yanada cikar zati irin na girma da kuma haiba, ganin irin littafan dake cikin falon ya tabbatar min da cewar malamine_
_sukayi saurin karasawa kusa dashi bayan sunyi sallama, kamal yayi saurin cire hularda ke kanshi cikin girma mawa ya duka Agaban dattijon_
_baba munsameku lafiya? Cikin tsananin farin ciki ya amsa " sannu kamalu' kun samu shigowa; ai tun dazu nakeso infita saboda kafadamin zaka iso na tsaya jiranka_
Samir ma ya gaishe shi,
_"Allah yayi muku Albarka ya kuma kareku daga dukkan nin sharri_
Suka Amsa da Ameen cikin girma mawa
" nasan mutanen Ku na jiranku don haka zaku iya tafiya idan kun huta sai muyi magana,
Cikin tsantsar lad'abi yace "Baba ai mun sallame su, a'a duk da haka Ku shiga daga ciki Ku gaida sauran mutanen gidan ko,
Suka mike cikin natsuwa tareda yima tsohon godiya yana binsu da kyawawan Addu'o'i,
*Alhaji Ibrahim Khalil* malamine Wanda yasan Abinda yaka mata,
_Suna zaune ne Acikin Garin Zaria Acikin unguwar ban zazzau, gidan da yake ba shi kadai bane, yana tareda kanninshi_
_Alhaji Ibrahim shine babba sai kuma mai binshi wato Alhaji Suleiman sai kuma Autansu Alhaji umar,_
_Kowannen su yana zaune da iyalinshi acikin wannan gidan dake cikin ban zazzau,_
_part hudune agidan part na farko shine na Alhaji Ibrahim sai kuma na Alhaji umar na Alhaji Suleiman ne na uku sai part din karshe na mahaifiyar su,_
_wato tsohuwa mai ran karfe, hajiya Rabi'a wadda suke kira da gwaggo,_
_bawai gidane irin na masu Arzikiba a'a sunada rufin Asirin su ba Abinda ya fi karfin su Arayuwa tun ma kafin yaransu su girma suzama wani Abu_
_gidane mai cike da had in kai da kuma zumunci sunada iyali ba laifi Amma bazaka taba gane waye ya haifi waniba saboda tsabar hadin kai da zumunci_
_Duk kaninsu sunada mata Amma Banda Alhaji Ibrahim tunda matarshi ta rasu shekaru biyu da suka wuce kuma duk tsawon zamansu Allah bai basu haihu wa ba harta koma ga Allah_
Y'an uwan shi sunyi ta fama dashi yayi Aure Amma yaki yace "ya'yan su sun isheshi Arayuwa,
_idan ba Anfada maka ba bazaka taba sanin bai haihuba Agidan saboda komai na yaran gidan shi ya dauke tun daga karatunsu har hidimomin su,
Musamman Dan gatanshi wato kamal ga badaya yaron yatashi Agabanshi ne, shikan shi kamal din saida ga baya yasan basune suka haifeshiba,
_Kamal D'ane ga Alhaji Suleiman wato mai bin Alhaji Ibrahim su hudune Adakin su shine babba duk agidan sai safwan bilal sai Autar su Zainab_
_Alhaji umar kuwa yaranshi uku duka mata duk biyun sunyi Aure sai Autar su wadda take sa ar Zainab ce wato Asma'u Wanda suke kira da *HUSNAH*_
Atakaice gidane bawai mai yawan cikar ya'ya ba
*KAMAL*
_Wato Don yanda Abokansu suke kiranshi yasamu shiga aikin soja ne saboda tsananin kaunar da yakewa aikin tun taso war shi_
Bayan kammala diploma dinshi yasamu shiga makarantar horodadda sojoji dake cikin Garin Kaduna wato N.D.A Wanda yafito da babban matsayi,
_gashi yanzu harya kai ga matsa yin lieutenant colonel Acikin shekara talatin da y'an kai_
_Akwai girman kai Wanda bawai kanninshi mata kawai ke shakkar shi ba har ma da kanninshi mazan y'an Jami'a_
_Zainab da Husna sun ma tsani ace yau ya shigo Garin baya duka baya zagin su Amma kallo kawai ya ishe su_
*Husnah*
Tafi kowa tsanar lamarin shi saboda tafi kowa sanin wanene shi tun taso warta, acewarta yanada Fuska biyu Annabi a fuska firauna A zuciya.................β
*taba ka lashe yanzu nafara acigaba da gashi my fan's*πππππππ
[3/8, 8:37 AM] Feenat Marubuciya: πΈπΈπΈπΌπΈπΈπΈ
*AURAN SOJA*π¨ββ
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3&4
_Samir shine Abokinshi tun suna kuruciya tare suka taso unguwar su daya har zuwa lokacin da suka fara aiki shima sojan ne Amma kowa yana serving awuri daban_
_Akwai zumunci mai karfi atsakanin iyayen su kasan cewar su a unguwa guda kuma dukansu malamai yasa Amintar su ta core_
_Alhaji Ibrahim baida wani Amini da ya wuce mahaifin Samir saboda kaunar dake tsakanin ya'ya n su,_
_Husnah da Zainab sun taso cikin kaunar junan su kamar ciki daya suka fito saboda suntaso sunga kan iyayen su ma duk Ahade ba wani mai nuna ma wani banbanci_
_gaba daya rayuwar su sunayinta ne A part din inna Habi wato mahaifiyar su Kamal dasu Zainab_
_lokacin da margayi ya na Raye wato uwar gidan Alhaji Ibrahim gaba daya ita take kula da yaran gidan tarikeso kamar ya'yan cikinta_
_bayan rasuwarta kamal ya koma gefen inna Amarya wato mahaifiyar su Husnah kasan cewar Sam baya samun kulawa daga mahaifiyar su irin kunyar nan ta y'an fari_
_sanin da sukayi baida wurin zaman da yawuce can yasa sukafi mu amala da dakin inna habi gefen gwaggo wato tsohuwa kakarsu ma sai idan baya garin_
_ita Zainab tana son Dan uwanta sosai saidai tana bin ra ayin kawarta kuma yar uwarta don komai nasu tare sukeyi gida da waje y'an biyu ake kiransu komai nasu iri daya ne_
_A halin yanzu suna matakin k'arshe a secondary, shekarun su baza su wuce shatakwas ba don kana ganin su kasan Akwai kuru ciya atare dasu_
_kuma sunyi saukar Alqur ani mai girma sun sami ilimi da tarbiya sosai Awurin iyayen su Amma dai Akwai rawar kai da kuma tsiwa_
_ban taba mantawa lokacin suna j.s.s sun zo kamal ya zo pass Aka sasu su gyara mai dakinshi dake cikin part din Baba Alhaji yanda suke kiran Alhaji Ibrahim_
_sun samu kayan shi a acikin Akwatin shi suda aka aikesu su gyara mai daki suka buge da bude mai kaya suna mai Searching_
_Wanda suna cikin yimai binciken ne ya shigo dakin, kuma yayi dai dai da lokacin Husnah nafito da wata zungure riyar kwalba_
_Da ya daka musu wata irin tsawa ai tuni tayi wurgi da kwalbar suka cure guri guda tsabar tsoro da kuma firgita, cikin husky voice dinshi_
_Dan ubanku Abinda aka aike Ku kenan Kuyi; wayace Ku taba min kaya ai jikinsu ba Abinda yakeyi sai rawa suka fara rokonshi "ya kamal don Allah kayi hakuri'_
_Yace su wuce su samo bulala kowacce dai dai da tsawon ta, ai suna samun tazare suka ruga da gudu dakin inna Habi don sun San zasu tsira_
_tana sauraron labaru agidan redio suka fado da gudu har saida ta tsorata tayi wurgi da redion tareda dafe kirjinta_
_"kai waya koroku haka? Cikin kidima Zainab tace " ya kamal ne zai doke mu" ta hade fuska me kuka yimai da zai tabamin ku?_
_Husnah cikin rashin gaskiya tace "wai kawai don mun gyara mai daki baiyi da kyau ba, ita kanta Zainab tasan karya ne ta kalli Husnah kafin tayi magana inna Habi ta hau fada_
_akan me zai firgita min Ku haka; ina zuwa ta mike tareda nufar sasan inna Amarya itama har ta mike zata nufa cikin sasan inna Habin don taji gudun su sai sukaci karo tace_
_" yaya lafiya naji hayaniya? Tace ba dole kiji haya niyaba d'an ki ya firgita min yara, tace Safwan? dan nasan shine me shiga sabgarsu ko bilal,_
_"wannan yaron dai na awurin ki, inna Amarya takwashe da dariya don taganota wato kamal don ita akwaita da bwarkwanci_
_"Yaya indai D'ana ne sunyi mai laifine kema kinsan halin ya'yanki mu samman me idon nan A tsaye, ba Abinda Yata takeyi, suna haka ya nufo sasan yasamesu atsaye_
_"Yawwa kar ka sake katabamin yara inba hakaba ranka zai baci ya dukar da kai cikin ladabi yace " kiyi hakuri innan mu_
_"Aida Sauri tabar wurin tareda cewa saika nemi uwarka, ba Abinda inna Amarya takeyi sai dariya don don lamarin na su Abin dariya ne,_
_"shima da gan gan yayi don yasan ta tsani ya nuna itace uwarshi saboda tsananin kunya da k'ara irin ta ta_
_inna Amarya ta tanbayeshi me sukayi yayi mata bayani tace" nasan halinsu ai musamman Husnah kabarni da su, ka je ka ba yaya hakuri,_
_Haka yasameta har dakinta yabata hakuri takuma jamai kunne"kar ka sake inji ka taba min yara idan ba haka ba ranka zai baci, shidai yana duke ba Abinda yakeyi sai Bata hakuri,_
_saboda haka Sam baruwanshi da lamarin su saboda gudun Bata ma mahaifiyar shi rai Safwan ne shi kam ba ruwan shi yanzu yakai duka bare kuma bilal da baya basu iska,_
_koda yashiga soja ma basuda wani wayo Amma saboda yawan zuwan da yakeyi gida yasa suka wa ye shi da kyau Kasan cewar tunda yafara aiki ya daukewa iyayen su nauyin komai_
_tundaga hidimar Abinci har zuwa kan su tura da kuma karatun kanninshi, shi ya dauki nauyin Auradda kanninshi, wato yayyin Husnah murjanatu da karima,_
_shiya hana Alhaji Ibrahim aiki yace yanzu ya huta shi zai rika yin komai tunda yanada karfin yi Baba Alhaji yaji dad'i sosai kuma yasan bazai taba kukan rashin haihu wa ba Arayuwa,_
_kamal yazama abin Alfaharin shi yasan bazai taba daya sanin rashin haihu wa ba saboda ga yaran y'an uwan shi kuma ba mai yanke wani hukunci agidan sai Abinda ya zartar,_
_duk da kasan cewar part dinsu arabe baisa sun raba tukunya ba komai nasu yana hade a babban kicin tare sukeyin komai agidan tun margayi ya na Raye,_
_har zuwa yanzu haka suke tafiyar da gidan su, Ata k'aice gidane mai cikeda hadin kai da kuma fahimtar juna,_
*Cigaban labari*
_dakin mahaifiyar shi yafara nufa Samir na dariya don yasan mezai iya faruwa yanzu, cikin zolaya yace yanzu za akoromu,_
_shi kanshi kamal din saida yayi wani irin murmushi mai tsada irin na miskilayen maza kafin suka shiga daga cikin falonta da yadanji gyara ba laifi_
_jin sallamar su abakin kofar yasa tayi saurin dago kanta ganin su yasa ta kawar da kai tareda Amsawa cikin basarwa,_
_dukawa sukayi cikin ladabi kamal yafara gaisheta inna ina wuni ta dankalli gefen Samir da yake cemata inna munsameku lafiya?_
_ta amsa shi da sannu ya aiki; yace Alhamdulillah inna yana tafiya cikin Amincin ubangiji tareda Addu'o'in Ku agaremu, tace Allah yasa Albarka kuje innarku naciki,_
_suka mike atare Samir yaciro kudi ya ajiye mata yace inna asamana Albarka, tace " kai dannan zoka dauki kudin Ku mezanyi da kudi har haka bayan kun dauke mana lalurorin komai_
_yace Kuyi mana Addu'a kawai inna, banga k'anni na ba yau ma basa gidan ne? Tace " basu dawoba suna zuwa wurin koyan girki Yama kuke kiranshi?_
_yayi dariya yace catering school Ashe sun girma yanzu don yafi shekara biyu rabon da mu hadu dasu fa,_
_kamal yayi gaba don shi Yama manta da wasu yara agidan iyakarshi duk karshen wata yaturo ma da Baba Alhaji kudi domin hidimomin su_
_,wucewa yayi abinshi yabar Samir don shi tsabar naci yasa inna take kula shi dole,_
_gefen inna Amarya suka nufa ta taresu cikin farin ciki "maraba da ya'ya na ta kakkabe musu kujerar dake cikin falon jikinta narawa Ku iso Ku zauna sannunku da zuwa,_
_cikin tsananin girma mawa suka tsuguna a gabanta " inna sannunku mun sameku lafiya? Ta amsa da fara arta Allah yayi muku Albarka yasa Ku gama da duniya lafiya_
_"Y'an da kuke mana Allah yabaku masu yimuKu kuma Allah ya kare Ku daga duk kanin makiya dakuma ma hassada,_
_kamal nason Addu'o'in da iyayensu keyimasu don yasan Addu a Bata faduwa kasa banza da izinin ubangiji,_
_kafin kace me ta cika musu gabansu da kayan abinci irin na gargajiya irin cimar da tasan sunfi kauna suka mimmike akasa suka fara dibar girki,_
_sunci sunyi nak kafin tafara yimusu magana "naji dad'in zuwanku lokaci daya wannan karon Saboda muyi magana,_
_gaba daya suka bada hankalin su gareta " Samir Sahura tayimin maganar ka akan ta nema maka mata kace bakaso sai Abokinka yatashi zaku nema tare,_
_har zuwa yaushe ne iyayen Ku zasu cigaba da yimuku k'ara; ni nasan yaya kallonku kawai yakeyi idan yatashi yanke muku hukunci bazaiyi muku dadi ba,_
_don haka tun wuri Kuyi kokarin fitoda matan Aure, cikin sunkuyar da kai kamal yace inna Kuyi hakuri dama ni Abinda yakawoni kenan, nasamu mata mungama dai dai tawa da ita Abokiyar aiki nace,_
_inna tayi shiru.......kafin tace "kana nufin soja ce itama? Yace" eh inna, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya Hmmm, "to ba komai yanzu kabari zanyima yaya bayani Anjima_
_to kai kuma fa Samir; shi yanzu ya shirya Saura kai kuma, ya Sosa kai " inna zankawo tawa insha Allah, tace Allah yanuna mana yakuma Baku mata na gari_
_inna har yanzu banga su Husnah ba, sai yaushe suke tasowa ne? Tace ai wa innan sai karfe shida suda gidannan yaran nan Sam basa hutawa ko ranar sati,_
_daga sun dawo boko sun fita wurin koyan girki daga can su nufi hadda kuma ai yanzu sun natsu angirma tafada tana metuna kuruciyar su,_
_shi kanshi Samir yakan tuno kuruciyar yaran musamman Husnah, sundade kafin sufita gidan su samir suka isa inna Saura tanata farin ciki "lale da mutanen ikko Kamal take nufi da yake shi Acan yake serving,_
_sun gaisheta cikin girma tasamu su Albarka tareda Addu'o'i masu ratsa zuciya hade da nasi hohi ta Dora da nata fadan rashin Auren duk suka yi shiru,_
_" nasan Hajara ta cika muku ciki ai , Samir yace eh mun koshi inna ina bana yake? "Ai tare suka fita da Alhaji babba wurin daurin Aure,_
_daga nan dakin kamal suka koma domin Sudan wata ruwa,
karfe shida da kusan rabi kofar gidan takuma cika dankam da matasa
_na hango wasu y'an mata guda uku kyawa wa ajin farko musamman ta tsakiyar su duk suna sanye da hijabai dogaye har kasa har ma da safa kowacce na dauke da jakar hannu,_
_Wanda kana gani kasan ta debo takaddu Aciki daka ga yanayinsu kasan sun gaji, taku suke cike da natsuwa suna kuma yar hira atsakanin su_
_kofar gidan naga sunnufo gaba daya hankalin samarin yakoma Kansu ba abinda suke sai tasbihi saboda hango tsantsar haduwar su duk da suna cikin hijab_
_ta tsakiyar tafi kowa tafiya da hankalin su Samir kanshi kallon su yakeyi don bai gane kosuwaye ba saida suukazo dab dasu,_
_sukam tundaga nesa sun San ko waye yau agarin don haka Husnah tace " yau Akwai kulle adaki,Zainab tace saboda me? Bakya ganin mala ika jibirilu ya sakko yau,_
_dayar dake gefe tace waye mala ika kuma sarkin yan sharri tace "ya kamal mana shine ya iso daga ganin gidan nan yau_
_abinka da dan uwa Zainab sai murna wayyo yau zabga ya kamal " sis kusan shekara biyu bamu ganshi bafa bakya missing dinshi_
_tace Allah ya kiyaye ta dan matse fuska meyayi miki haka sis tace haka kawai ni na tsani SOJA,_
_dayar danake tunanin kawar suce tace wow soja ne nikam ina son *AURAN SOJA*..............somin tabi me my fans muje zuwa_βππππππππ
_need comment_
07062906225
[3/8, 8:37 AM] Feenat Marubuciya: πΈπΈπΈπΌπΈπΈπΈ
*AURAN SOJA*
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
β
Golden pen writers Association.
βwe bearers of Sooo golden we write assiduously percieven no pain so magical, our creative golden pen be our words A product of our pen savour our words for it couse you no painβ
5&6
_gaba daya idanun gayun nakansu amma banda kamal da kanshi ke kan wayar shi yana faman dannawa saida su ka iso gab dasu Zainab da dayar suka gaishe su_
ya Samir sannunku da zuwa, Zainab tafada cikin fara a da kuma murna
Ya washe baki shima "Husnah'ko? Tace" a'a Zainab, ga Husnah nan, ta nuna ta
_yakalli Husnah tareda tasbihi cikin zuciyarshi wow "kan wata ba gaisuwa ne? cikin basarwa tace " ina wuni ya Samir'_
_sai