Showing 36001 words to 39000 words out of 66141 words

Chapter 13 - Auren Soja Book Complete Hausa Novels by Feenerh..txt

Feenerh   

17 Jan 2025

18570

beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


31&32


_muryar ta na rawa ta furta "ya kamal' Ajiyar zuciya ya sauke " na'am my wife' "ya kike ?" ta fasa mai kuka har saida ya matsar da wayar daga kunnen shi yace " shshhh "Angel me yasa kike kuka haka'?_




_ta saita kanta kadan " ya kamal kasan kukan da nakeyi ai "me ya faru? " cikin kuka "nidai kadawo kawai Allah na daina yima abinda bakaso don Allah ya kamal kadawo'_




_" Ajiyar zuciya yasauke cikin farin cikin da bazan iya misalta mukuba ya ce". Har da rowar kanki ?cikin Sauri tace eh Allah na daina. Yace "lallai matana tanason gani na to fadamin " ciwon mu ya warke ne?_




_"tace kai yaya! "Ashe batason ganina, idan har kinason in dawo kifadamin inji kin warke ko a'a? " na warke yaya Wallahi, tafada cikin saurin ta "Hmmm Asmah' kiyi hakuri kinji'_




_" nifa banason hakurin nan da kowa kebani ni kawai kai nakeson gani yaya don Allah kadawo' duk ta gama kashe mai jiki cikin kashe murya na irin shiga cikin wani yanayin "Husnah''''''''_




_" nafiki damuwa saboda nafama wa kaina wani ciwon Husnah' cikin saurin ta tace "yaya a ina kaji ciwon waye yaji maka? bata lokaci ba yace " kece Husnah da farko na d'auka idan na kusan ceki zai rage min sha'awa da kuma damuwa'_




_Amma nakara janyowa Kaina damuwa gaba daya ji nakeyi kamar inganki akusa dani ahalin yanzu "Husnah idan nadawo wace irin kulawa zaki bani?_




_" yaya komai da kakeso zanrika yimaka abinci kowane lokaci, aa Husnah ke nafi bukata fiyeda abinci idan na dawo sai kinyi hakuri dani saboda yanzu bazan iya kauda kaina akanki ba da farko ma wauta nayi da na rika kyaleki"_




_"ta rufe idanunta da tafin hannunta kamar yana ganinta tace "kai yaya' shima yace " ke Husnah''''' cikin kwaikwayon irin muryar ta "ki ajiye batun wasa agefe Husnah a gaskiya ina cikin damuwa bansan daliliba'_




_" ina rokonki da ki daure ki daina fita yawo ina kishin ki zansa samir ya kawo miki mota idan ta kama kifita banason hawa mashin kije ki koya mota a driven school "_




_" sun dauki lokaci mai tsawo yana yimata bayani da kuma irin dajin da suke a Sudan kuma shine yake jagorantar su tayi mai fatan Alkhairi dakuma Allah ya kiyaye kamar karsu ajiye waya "_




_" tayi farin cikin jin yana lafiya aranar duk yakira iyayensu ya gaishe su aranar kowa yaga sauyi har ma Gwaggo ta fara yimata tsiya "dama anason miji ake yimai yanga ita dai ranar batada ta cewa farin ciki ya cikata don har Zainab takira take fada mata yau taji muryar kamal'_






_" tace ina tayaki murna yar uwa ta Allah yadawo mana da shi lafiya ta Amsa da ameen_








_yau kusan watan ta biyu da zuwa Zaria kuma baifi sau uku tayi waya da kamal ba last kiran da yayi mata yace tayi mai hoto ta tura mai yanaso yaga yanda take kafin takai ga turawa kiran ya katse saboda rashin kyan service awurin da suke'_






_yau duk suna zaune ta mike kafa a dakin gwaggo duk su Inna na ciki tace " Inna ni fa yau faten tsaki nakeson sha agidan nan da kuma dan wake da ka lallaba'_




_gaba daya kallon ta sukeyi cike da mamaki saboda kowa yasan ba cimar ta bane duk Abubuwan da ta lissafo Gwaggo tace "Habiba to ki binciki y'ar ki Akwai magana tun watan baya nake kula da ita kamar ba ita kadai bace'_




_" kuduba y'an da take bajewa daga kasa ga nonuwanta sun cika kirji kamar zasu barke Riga gaba daya Bata fahimci komai acikin maganar Gwaggo ba ' sukuwa su Inna kowannen su kunya ta hanashi cewa komai'_




_haka taci gaba da zamanta agida gashi samir yakawo mata motar ta formatic mai kyau har hannunta yafara fadawa a tukin data ke koya Safwan ne ma ke koya mata idan yana gida saboda duk suna zuwa makarantar su'_






_yau tafito wanka adakin data mayar nata wato na kamal ta tsaya agaban madubi tana karewa kanta kallo itafa Bata ganeba ko ina nata ya habaka musamman hips dinta ga kuma kirjinta ya ciko sosai tana cikin kallon kanta ta madubin wayarta tayi kara tayi saurin dauka don jin irin ringing tone din dake fita Wanda tasaka ma kamal ne'_




_"tace "hello ya kamal"". " Husnah video call nakeso muyi Wallahi ina son ganinki kewar ki ta dameni sosai tace to yaya ta janyo hijabin ta tasaka ya kuma kiranta tayi picking taganshi akwance asaman wani dan karamin gado'_




_"ya kamal yana ganka akwance? baya ko jinta kallon fuskar ta kawai yakeyi cikin kasala yace "Asmah meye haka please kicire hijabin nan inga kyakkyawar surar matana'_




_" cikin muryar shagwaba tace "yaya wanka fa nafito towel ne ajikina kawai saida ya yi yar mika daga kwancen da yake yace" inason ganinki kicire ko inkashe wayata kuma bazan kuma kiraba saina dawo'_




_"tayi saurin zare hijabin ta dukar da kanta shi kuwa mikewa yayi da Sauri yana karewa jikinta kallo ta cikin wayar "Husnah ko idona gizo yake min naga kin ciko ne kamar bakeba ta kalli jikinta itama ta ce Wallahi yaya ni kaina nace kila banida lafiya ne'_




_" Husnah""""" yakira ta cikin sanyin murya " ki dan janye towel din ingani kadan ta zaro idanu waje cikin jin kunya tace "haba yaya towel ne fa kawai. Uhm ba kayana bane'_




_kallon ta yakeyi kamar ya janyota ya ganta kusa dashi " sai Anjima tom bari in sauka "a'a yaya ta zame towel din ta'_




_saida yaja dogon numfashi cikin sha kewar murya tareda hadiye wani irin miyau_




_" kallon kirjin kawai yakeyi kamar ya cafkesu yakeji da bakinshi yayita tsotsa "Angel kin chanja sosai me su Inna suke baki haka? Kinyi kyau sosai ga twins dina sunkara girma ganin irin kallon da yake yimata yasa ta ja towel din zuwa sama yaja numfashi'_




_" a ina ne kike yanzu? Ina dakin ka, "me kikeyi aciki? " anan nake zamana saboda inrage kewar yayana kuma mijina yayi murmushin karfin hali ya ce "Husnah kikula min da kanki sosai kinji I love you so much'_




_" yana kallon ta itama kallon shi takeyi kamar kar ya ajiye wayar gashi ya kara murdewa da kuma kyau yayi mugun burgeta haka taji kamar karsu ajiye wayar aranar suka rabu cikin dokin juna da kuma kewa'_




_jikinta yayi sanyi sosai bayan sun ajiye waya ya mugun Bata tausayi yanda ya nuna kamar ya janyota ta cikin wayar sai yanzu take kara data sanin irin jamai rai data rika yi data bashi hakkin shi da kyau may be bazai damuba irin haka'_






_wasa wasa kullum kara budewa takeyi ga dan banzan kwadayi Wanda harsu baba umaru kullum sai sun siyo mata kayan kwadayi irin na gargajiya ga cin Abinci kamar gara ranar dai Inna Habi ta cire kunya tace '_




_"y'ar nan kodai juna biyu gareki? "Inna wane irin juna biyu? " banson shirme watan ki nawa rabonki da ganin Al adarki? Sai Alokacin hankalin ta yadawo jikinta'_




_"idan Bata mantaba rabon tada Al ada tun a legos kafin tafiyar kamal tayi tsam yanzu' ana nufin ciki ne ajikin ta? tafara Addu'a Allah yasa hakan ne saboda tasan ba abinda zata farantamai dashi sama da wannan cikin'_




_Inna ta ce "yakamata gobe kije kiga likita ya dubaki tace toh saboda zataso taji sakamakon da take muradi'_






_washe gari tun da wuri ta shirya zuwa Asibiti wani private hospital dake tudun wada taje mai suna Doctor bello, gwajin farko cikin ikon Allah suka ga ciki har na kusan wata uku"_




_" likita yabata result dinta tareda tayata murna "madam congrat. Kina daukeda ciki nakusan wata uku. tayi farinciki sosai wato bugun farko har ciki ya afka tab lallai ta haduda jarumin soja'_




_" ta matsu takoma gida domin ta turamai sakon Albishir '_




_"tana zuwa gidan ta mikawa Inna result tace "yoh ni kyabani takarda karatu na iya Kayimin bayani inji tayi shiru Abinta " ganin bazata samu bayanin ba ta dauki takardar tanufi dakinsu bilal'_






_"tace kai dubamin takar dar nan kagani yayi mata bayanin meta kunsa cikin tsananin farin cikin dabazata iya nunawaba kawai tanufi cikin gida ta dauro Alwala tafara na filfili da tsakar rana saboda bawanda zata iya tunkara da labarin cewar matar kamal nada ciki'_






_"shiyasa ta nufi ubangiji tareda Addu'o'i masu yawa akan zuriar ta da kuma neman kariya ga babban danta'_






_"cikin Zainab ya kusan zuwa duniya mahaifiyar samir ta nace akan yadawo da ita gida tunda yanada sashin shi ta zauna har Allah yasauketa lafiya duk da baisoba Amma bayanda zaiyi sun kasance yara masu biyayya ga iyayensu a dole yashiryota tadawo gida Zaria "_




_" Wanda Husnah tafi kowa farin ciki kobanza zata samu abokiyar shawara saboda tana cikin damuwar rashin jin wayar kamal rabonta dashi tun ranarda sukayi video call din nan'_




_"batasan waye zata yima zancen ba kar ace batada kunya koda yaushe zancen miji Fatima ce kawai kawarsu akusa kuma tunda tadawo Fatima na school of nurse makarfi'_






_"shiyasa abin yayi mata yawa gashi ta turamai sakon samun cikinta shiru bai kiraba hankalin ta yafara tashi baitaba daukar lokaci har haka bai kirata ba'_






_ga cikinta sai motsi takeji yana yimata, Gwaggo yau ta kalleta tace Asma'u wannan kunburi da kikeyi haka ga shi Allah yabaki iyaye masu shegen kawaici waisu kunya ita Habiba anji kunyar kamal takeyi ita kuma Amarya fa keba yar fariba ina zuwa ta zari mayafi sai gidan Inna sahura wato mahaifiyar Samir "_






_" tayi mata bayanin tanaso ta tasa yarta zuwa Asibiti adubata don itadai Bata ganeba Inna sahura tayi dariya "Gwaggo ai dama dagani cikine ajikinta natanbayi Habiba tace min eh kawai na dauka kunsani'_






_" ta dauki salati Habiba sai dai ikon Allah koni da Nike tsohuwa bana Abinda takeyi Amma dai dole taga likita kunburin ta naban tsoro yarinya sai bajewa takeyi "_




_" tace. Karki damu Gwaggo insha Allahu gobe zantasata muje Asibiti aduba lafiyar ta"_




_"Zainab ta iso cikin ta yayi girma itama itama tayi mamakin ganin irin budewar da Husnah tayi tace "sister lafiya kike kuwa irin wannan bajewa kalli hips dinki'_




_" tayi murmushin karfin hali kawai har saida Zainab tace sister kirage sa damuwa a zuciyar ki domin naji cewar bake kadai bace yayan mu ya yi ajiye takarasa cikin tsokana'_




_"haka ranar suka raba dare suna hirar su irinta y'an uwa dasuka shak'u da juna_




_wannan karon adakin Inna Amarya Zainab ta baje saboda Inna Amarya tanemi da Inna sahura ta barta idan ta haihu saita koma cikin gidan su'_




_"Baba Alhaji kamar yafi kowa farin cikin jin labarin cikin Husnah Ashe da rabon zaiga Kwan kamal don gaba daya hankalin su atashe yake agidan saboda rashin jin labarin kamal suna boyewa ne kawai saboda kar Husnah taji ta tashi hankalin ta gata da ciki yashafi Abinda ke cikin ta "_




_" gashi likita yace lafiyar ta kalau kunburin ta na cikine kowa agidan yamaida hankali akanta ko Zainab da ake sa ran haihu war ta yau ko gobe Bata samun kularda akewa Husnah kowa na tausaya ma ta'_




_"yau duk suna zaune a gefen Gwaggo dukansu har su Inna baba Alhaji yashigo a sukwane bayako ganin gabansa sai salati yakeyi kanninshi na biyedashi Alhaji Suleiman sai kokarin rike shi sukeyi'_




_"yaya ka kwantar da hankalin ka don Allah Karka janyowa kanka ciwo duk matan suka mike a. tsorace saboda tsawon rayuwar su da shi basu taba ganin tashin hankalin shi ba irin wannan ko rasuwar matarshi baiyi irin hakaba"_




_"cikin kidima Gwaggo tace "ya'yan nan lafiya? Baba umaru yace" Gwaggo kamal....... ai tinkafin yakarasa Husnah ta mike cikin firgita "Baba ba abinda yasameshi ko ? don Allah me yasamu mijina? tariko babanta baba kamun bayani " kamal lafiyar shi kalau ko?'_






_"kowa tanbayar da yake aikawa kenan Inna Habi kuwa fita kawai tayi tabar dakin duk tsananin kwakwar ka bazaka gane abinda ke rantaba'_




_"Baba Alhaji yace "yanzu ake gayamun yantawaye sunkai musu hari a wurinda suke ance duk saii gawawwakin su kawai aka gani yanzu haka ankawo su gida samir yatafi yaduba'_




_Bata gama jin karshen zancen ba ta fadi a sume duk suka kwasa aguje zuwa gareta Zainab ma tuni marar ta rike tace "washhhhh tsabar tashin hankali..................✍






*AURAN SOJA kenan kullum matansu suna cikin fargaba saidai muce Allah ya kare mana su a duk inda suke jinjina gareku military wife's*
[3/22, 11:24 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨‍✈
_patients love & sacrifice_


*~Story written by~*
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


_*Allah kasa mu dace y'an uwa na ina so ku fahimci hikimar rubutu bawai anayi kawai saboda nishadi bane aa harma da fadakarwa littafi na yana nuni da karfin zumunci saboda Akwai karan cin zumunci awannan zamani saidai muce Allah kasa mudace*_


_*HAPPY BIRTHDAY 🎂to you Yaya Hayat Admin of Admins wish you many many years more Ahead. This page is for you only may Allah s.w.t bless ur new age*_


33&34


_gaba daya rushing dinsu akayi zuwa Asibiti kowannen su ana kokarin bashi taimakon gaggawa Zainab dai haihu wace zanga zanga suna isa ba dadewa ta sunkuto katuwar baby girl kyakkyawa saidai muce Allah ya raya'_






_Husnah kuwa gaba daya batasan halinda take cikiba likitocin ma duk hankalin su atashe yake bare kuma iyayen kowa damuwarshi gata da juna biyu anason tafar fado asan halinda cikin yake ciki'_




_kowa kagani sai Addu'a kawai yakeyi hankalin su yakasu kasu kashi uku ga tunanin kamal ga Husnah acikin wani hali ga Zainab ta haihu'_




_"Alhaji Mahmud ne yakira samir yayi mai bayanin halinda ake ciki yace baba ku kwantar da hankalin ku yanzu haka nakusa shigowa Zaria Awane Asibiti kuke? yafada mai suna Asibitin musulmi'_






_dakyar suka samu numfashin ta yadawo suka fara kokarin duba lafiyar cikin Allah ya taimaka ba Abinda yasameshi suka yimata Allura saboda kukan da ta bude ido dashi kar yajanyo mata matsala'_




_"gaba daya kowa fargabar farkowarta yakeyi saboda tashin hankalin ta zai iya cutar da Abinda ke cikinta Azo ayi biyu' Inna Habi ce zaune tare da ita Inna Amarya na tareda Zainab "_




_" daga baya Inna sahura ta iso Asibitin itama dakin da aka kwantar da Husnah ta nufa tareda jajantawa juna"_






_"suna zaune cirko cirko Zainab ma kukan takeyi duk su Safwan hankalin su atashe yake don suna maza ne su Alhaji Suleiman kuwa wato mahaifin kamal shinema mai kwantar ma da Alhaji babba hankali'_




_"yaya kayi hakuri komai mukaddari ne daga Allah haka Allah yaso don haka bamuda dubara saidai mubisu da Addu'a Alhaji Mahmud yace "wannan haka ne '_






_" suna zaune awurin sukaji salatin baba umaru yace "wanake gani haka Allah abin godiya dukansu suka juya zuwa wurinda yake yana nuna musu hanya'_






_" sukansu sun firgita duk suka mike tsaye bilal ne yace" ya kamal!! Allah mai iko inji Baba Alhaji har suka karaso kusa dasu suna daskare cike da mamaki'_




_"ya tsuguna Agaban su yace "baba sannun ku yamasu jikin ? " kamal' Kaine ko idanun mune kemana gizo ? Yace Baba nine Allah mai iko ya nufa na dawo lafiya batareda wata matsala ba'_






_"duk suka fara kabbara tareda hailala kafin suce wani Abu nurse ta fito tana tanbayar ina mahaifin Husnah Ibrahim baba Alhaji yace gani nan tace "doctor nasan ganinka a office'_




_" yace muje kamal' yamike yabishi yabarsu cikeda mamaki ya akayi haka tafaru tanbayoyi cike fal da cikin su Samir ma ya nufi dakinda Zainab take saboda ya kagu yaga Babyn shi'_






_"shima bai tsaya wani bayaniba ya shige ciki abinshi'_




_Doctor yafara yimusu bayani "Baba wannan mai juna biyu n a scanning da mukayi naga alamar wannan cikin yafi karfin watannin shi kuma munyi iya binciken mu ba wata matsala'_






_" nayi tunanin ko twins ne Amma scanning bai nunamin komai ba saboda cikin baiyi kwarinda zan fahimta ba saboda yanzune ma ya shiga wata na hudu'_






_gaba daya kan kamal yadaure wakeda ciki bayan samir yafada mai Zainab ta haihu jin likita na tanbayar ina megidanta ? Yasashi dawo wa cikin hankalin shi'_




_"gashi nan ai likita zaka iya yimai bayanin komai baba Alhaji yafita abinshi ya mika mai hannu "ya kamata ku kiyaye abinda zai rika daga mata hankali saboda idan takuma irin wannan faduwar zata iya rasa babynta'_






_sai yanzu ya fahimci zancen likita " Husnah ce keda cikinshi harna tsawon wata hudu'? "Allahu Akbar Allah mai kyauta da kari shine yanzu zai mallaki da nashi na kanshi kuma ta tsatson macen da yakeso kamar ranshi'_




_" cikin tsananin farin ciki yafara yima doctor godiya yafita cikin Sauri domin yanzu kam ya matsu baisata a idanunshi ba'_




_yana fitowa duk suna tsaye kowa yana mamakin abinda yake faruwa wai kamal yadawo ya akayi haka ? Meyafaru'_?






_ya gaida su Inna sahura suka farayimai barka da dawowa Amsawa kawai yakeyi Amma hankalin shi na wurin matarshi ita kawai yake muradin gani ahalin yanzu'_




_"Inna Habi kamar ruwa ya cinyeta Ajiyar zuciya kawai takeyi batareda ta furta komai ba baba Alhaji yace "kamal ga dakinta can kaje kaduba matar ka'_




_" dama a kage yake wucewa kawai yayi ya nufi cikin dakin tunda ya tura kofar yashiga yaja ya tsaya yana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya'_




_"kallon yanda take kwance tayi wata irin cika kamar ba Husnah ba gashi har cikin ya dan nuna yaja ya tsaya saida ya gama kallon ta daga nesa kafin yafara takawa cikin kasaita kamar wani sarki zuwa bakin gadon'_






_"Husnah' ya furta can kasan makoshi tareda Jan kujera yana mai kare mata kallo cikin doguwar rigar atan fa tayi kyau sosai duk da Bata San halin da take cikiba ga gashinta ya kwanta lub yasa hannunshi akan fuskar ta yafara shafawa Ahankali'_






_"matana ki tashi gani nadawo yakai idanunshi kan cikinshi hannunshi yadora akai Ahankali kamar bayason abinda zai taba mai lafiyar ciki'_






_"yana shafawa Ahankali harzuwa saman kirjinta dasuka dan fito ta cikin rigar ta suna kokarin tsole idon mai kallon su gaba daya Jinshi yakeyi awata duniyar ta daban'_






_Ahankali take motsa hannunta tareda tsirarowar wasu siraran hawaye tareda sanbatu" ya kamal karkayi min haka karka tafi kabarni nima mutuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login