Showing 6001 words to 9000 words out of 66141 words

Chapter 3 - Auren Soja Book Complete Hausa Novels by Feenerh..txt

Feenerh   

17 Jan 2025

18536

magana " yaya Auren wata kawar mu za ayi shine zamuje mufara shiri_








_Dama yawo kuke zuwa ko? tayi saurin cewa " aa yaya yaune kawai kuma best friend din Husnah ce" wani irin kallo ya aikamata yana mamakin meyasa Yarinyar takeda shariya ne_






_shine kuke yawo da kana nan hijab bakuda manya ne? Husnah tayi carab" ba a dinka mana ba' ya girgiza Kai " OK kubari idan andinka muku sai kufita yanzu Ku koma gida_







_tsabar girman kai kawai ta juya kuwa Zainab ma tabita Safwan kuwa aiya sulale tuni gefen inna Habi suka wuce cikin fushi " kinga bakar maganar ki ta janyo mana ko! Yanzu me zaki fadawa ihsan din idan Bata ganmu ba?_yafita _Inna tayi ta tanbayar su Husnah tayi shiru saida Zainab tayi magana aiko ta hau fada takira bilal " jeka kiramun shi" bilal da tsokana yace " Inna waye? Tace kanin ubanka umaru' duk sukasa dariya yafita Amma har sun fita abinsu cikin gari_




" Inna yaya yafita fa' tace kutashi kutafi abinku kunji Inna Amarya taleko " kai yaya salon kijamai raini yace karsuyi Kice sai sunyi nidai gaskiya aa kuma wallahi kufita kuga ikon Allah




_tace to shikenan zai dawo zamu hadu dashi ne ai, kamal kuwa tunda suka fita Abokanshi ke damunshi "Don irin wannan kyawawan yan mata haka"_




_" gaskiya nidai inason wannan farar sosai" yayi saurin kallon Abubakar din " tanada Wanda take so saika yi hakuri' gaskiya bazan iyaba"_






_cikin zafi yace " look Sadiq na fadama tanada Wanda takeso" so leave my sister Alone, "mamaki abin yabashi sosai saboda baiga Abinda zaisa yaji haushi ba kawai don ya ce kawai yanason sistern shi_






_haka suka dawo yanata faman cin magani yana shigowa suka ci karoda Inna Habi ta balbaleshi baice komai ba sai hakuri dayake Bata ya mika mata ledar da yashigo da ita " Inna kibama yaranki wannan "_






_" takarba tareda godiya ta wuce ta mika masu " gashi inji yayanku" Zainab takarba cikin doki tabude ledar hijabaine dogaye sunkai kala goma hade da nikab dasu sock's_






_inna tace yakarama kananzir fetur kenan itako Zainab sai murna takeyi itakuwa tana tsarama kanta daga yau zata fara saka gyale tunda ba abinda yadameshi da sa hijabin ta bayan yagama kalleta,_






_Samir yakira shi yana fadamai bikin wani Abokin su gobe ya dafe kai " I totally forget wallahi "OK zanshigo da wuri duk kuna tareda su Sadiq ne? Yace yeah saika iso_






_suntashi dawuri suka nufi wurin telansu kafin lokacin bikin yayi bayan sunkarbo tace " muje mu gyara kai yau a saloon,Zainab ta waro ido tareda taba kanta_






_"sis lafiya kalau kike kuwa? Tacire hannunta " lafiya na kalau, yau ina ra ayin hakan ne, haka sukaje aka gyara musu kai tareda yar yada musu design na sajen Abinka da farar fata sukayi wani irin kyau_




_tunbasuyi kwalliya ba yan matan sun fito kamar wasu many an yan matan jami'a koda suka koma gida sai tsiya bilal keyi musu " wannan ai saiku tashi taron don kuna shiga anga kauyawa " hala yau kyauye day zasuyi?_




Ai sai tsalle suna buga kafa yana ganin sun nufi sasan Inna ya ware don yasan sauran,






_karfe hudu suka shirya zuwa wurin partyn da aka hada a Faisal co, center dake cikin Zaria cikin wani irin pink material sunyi kyau kamar ka sacesu ka gudu,_




Zainab tace sis yau meke faruwa ne haka zakije ina hijabin yau cikin tsokana "haka zantafi ko mai bazan yafa ba ina gwaggwaro na yake?




_gaba daya takasa ganema yar uwarta saikace mai Aljanu haka suka gama shirya wa dinkin ya karbi jikinta komai yafito das Inna sai masha Allah kawai takeyi ganin yan matanta sun fito tace " yaudai Yata ba hijabi ko,_






_" eh Inna gyale zamu yafa itadai dadi kawai takeji ta Ciro kudi gashi Ku rike ahannunku kwayi liki, suka amsa suna godiya Allah yabar mana ke innan mu,_






_sunfito kenan suka haduda Samir zai wuce Zainab cikin murna tace " ya Salim ina wuni' shima ganinsu saida yakusa Sakin key din dake. Hannunshi " kanne na ne haka? Gaskiya kun hadu Amma ina zakuje haka?_






_Zainab tace Faisal co zamuje Auren kawar mu ne yace " wow nima can zanje Auren Abokin mu ne Husnah ta yi saurin cewa " SOJA ne shima?_






Ya kalleta sister " kebakyason SOJA ne tace um gaskiya banason AURAN SOJA.




_"why? Just like that. Yayi dariya yace Ku shiga mutafi driver yataso da gudu wani kurtun soja ne yace " no am going with my sisters stay hare_






Zainab ta shige gaba ita kuma Abaya " sis ke kinason AURAN SOJA? Tace nidai suna birgeni sosai wallahi, yace harda ni? Ta sunkuyarda kai kasa cikin jin kunya,




_"look Zainab let be serious, " will you Mary me? Tayi saurin dago idanunta tanaso ta gazgata zancen shi yace yeah Am serious,_






_Husnah na baya tayi kamar Bata jisuba saida yakuma cewa " bani numbern ki saimuyi magana inkin yi tunani" tace bamuda waya dama baba Alhaji yace zai siya mana idan munci jarabawa,_






_OK ni zansiya muku dakaina suna tafe yana janta da hira har suka isa wurin duk suna tsaye awurin ana jiran isowar ango da Amarya ganin motar da ta tsaya duk sai hankalin mutane yadawo Kansu harma dasu kamal dake tsaye da sauran Abokansu ,_






_ganin Motar Samir yasa kamal yasaki murmushi yafara takowa zuwa wurin su saiyaga Zainab na fitowa ta gaban mota saida gabanshi yabuga fatan shi daya Ace Husnah Bata zonan wurin da irin wannan dressing din ba_





_baigama tunaniba tabude kofar tasako kafarta waje tafito zata kulle muffin motar gyalenta ya makale ajikin kofar yafita daga jikinta gaba daya_








_numfashin shi saida ya tsaya kafin yakarasa cikin Sauri yasha gabanta kawai ganinshi tayi a gabanta cikin fushin da Bata taba gani yayiba " koma cikin motar yafurta cikin fushi_








_duk kallon shi sukeyi cike da mamaki samir ne kawai yayi murmushi tareda mikamai key_






Yafada tareda fisgar motar yabar wuri n da d'an ban zan gudu hanya r gida yanufa






_suna tsaya wa ya hango iyayen shi duka maza harma da baban su Samir.......✍_




*What is going to happened fan's? More patients please*
[3/8, 8:39 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*
_patients love &Sacrifice_




✍
Golden pen writers Association.


❄we are bearers of Sooo golden pen we write assiduously percieven no pain so magical our creative golden pen be hold our words A product of our pen savour our words for it will couse you no pain.❄




*godiya nake maman Aisha da tukwicin katin da kika turomin Allah yabar kauna Husnah da kamal suna yinki nima ina yinki dozen*




*tareda ke mom sayyed &noor Ina jin dadin comment dinku dake Ummu nawax Allah yakara dankon zumunci*


9&10


_Bude motar kawai yayi yanufi wurin iyayen na su ya durkusa tareda gaisuwa duk suka Amsa cikin farin ciki tareda sa Albarka, itama tabude motar ganin yafita ta gyara gelenta da kyau ta karasa wurin su ta gai shesu cikin girma da kuma ladabi_






_sai fara'a Baba Alhaji keyi ta wuce zuwa cikin gida shima ya mike tareda binta cikin Sauri yakarasa cikin zauren ya fisgota saida ta tsorata_




_bai kyaletaba saida yakaita cikin dakinshi ya kalleta cikin fushi " ubanwa yace kifita Ahaka? Ta marai raice idanunta suka kawo ruwa_




_"ya kamal Zainab ma fa tasa gyalen. Yadaka mata tsawa "just shut the hell off, sai jikinta yafara rawa don ta mugun tsorata da shi sai hawaye_




_har yabude baki zaiyi mata magana yaga tana zubarda hawaye yaja da baya ya zauna bai kuma ce mata komai ba ta tsaya hartagaji tanemi wuri ta zauna_




_yana kallonta ta wutsiyar ido har tafara gyngyadi awurin, ya juyo tareda saita wayar shi yafara daukarta_







_saida yaga zata buge da center table ya yi saurin tareta jin hannun mutum yasa tayi zunbur ta mike tareda zaro idanu cikin mamaki me yake shirin yimata?_






_ganin irin kallon da take mishi yasa yace mata " ki wuce ciki" ai dama kamar tana kan kaya ta wuce da Sauri tana me faman Tara Tara da gyalen tana rufe jikinta har tafita yana binta da kallo,_






_tana fita yayi baya akan katifar shi yana me rufe idanunshi wurin partyn da bai koma ba kenan yana faman tunani afili ya furta "Ya Allah help me,_






_ita kuwa da kuka takarasa cikin dakin Inna Habi tayi saurin tarota" lafiya kika shigo da kuka? Me ya faru dake? Ina y'ar uwarki take? Me yasa kika dawo yanzu Angama ne? Duk ta jero mata tanbayoyin Amma bawanda ta Amsa tana ta rusa kukanta,_






_saida Inna ta gaji tayi shiru dan kanta tace " ya kamal ne ya hana ni zuwa party ya dawo dani." Saboda me? tamike afusace sai gefen gwaggo tasamu harda Inna Amarya tana wurin_






_"Gwaggo k'ara nakawo, tace toh karar waye kuma? " dan gidan Amarya. "Ai nasani wai ke yaya don Allah me Dana yayi miki haka ne? Nasan bai wuce zancen wannan y'ar taki mai ido tsakar ka,_






_"yanzu Gwaggo saboda Allah yarinya ta fita wurin biki ya dawo da ita yabar yar uwarta inba tsana ba me...._






_" kishinta yakeyi ba tsanarta yake ba. Sukaji muryar Baba Alhaji dake shigowa tareda Aminin shi Alhaji Mahmud, wato mahaifin Samir,_






_tayi saurin matsawa daga ciki tareda gyara mayafin jikinta " sannunku da shigowa yaya" suka Amsa " Yauwa Habiba inna Amarya ma ta gaishe su,_






_Alhaji Mahmud yafara gaida Gwaggo kafin baba Alhaji suka samu wuri suka zauna, su Inna sunmike zasu fita yace "kudawo " maganar ya'yan Ku ne_






_Duk suka samu wuri suka zauna " Gwaggo tace " na am Allah yasa muji Alheri. "Alheri ne ma insha Allahu, " mungama yanke hukunci nida Amini na akan hada yaran mu Aure,_




_"nasa anyi min bincike akan wannan yarinya da ya kawo Amma hankali na bai kwanta da lamarin ba a gaskiya shiyasa mukayi shawara nida Alhaji zamu hada Samir da Zainab Husnah da kamal._






_Alhamdulillahi" nagode Allah da yanuna min wannan rana Allah yasa ayi a sa'a yakuma sa Albarka. Yakara hada kawunan ku, duk suka Amsa da Ameen_






_"Inna Habi duk jikinta yayi sanyi don tasan Husnah bazata so wannan hadin ba Amma tafi kowa farinciki zuciyar ta_









_Kamal Abokanshi sai faman kiranshi sukeyi yaki daga wayar har zuwa dare lokacin da su Zainab suka dawo gida tareda Fatima suna ta tanbayar ta me ya faru?_






_tayi musu shiru har Fatima tawuce gidan su Bata kula suba don tsabar haushin da take ji gaba daya takara tsanar shi a zuciyarta Bata ko son koda hanya ta hadasu dashi_








_Baba Alhaji ya tarasu su hudu tunda taji Baba na kiransu gabanta ya mugun faduwa "me ya faru aka tarasu harda Wannan mugun mutumin?_




_Baba ya gyara murya tareda cewa ina fatar Kunsan dalilin taraku anan "kamal da"Samir, mun gama yanke shawara akan zancen Auran naku zuwa karshen wannan watan insha Allah,_






_gabanta ya wani mugun bugawa " Aure? Ita da kamal Baba yake nufi kome? Tayi nisa tana yima kanta tanbayoyi Baba yakira ta "Husnah' tace " na'am Baba._




_"kinji Abinda nake fada Auren Ku keda ya'yan ki Zainab da Samir. Ina fatan zakuyi min biyayya kamar yadda kuka saba, tunda yafara magana yake kallon ta ta gefen ido,_








_yana so yaga reaction dinta Amma bai fahimci komai ba har Baba ya sallame su suka shige cikin gidan Zainab kam tana cikin farinciki, domin tasan Allah ne ya Bata miji na nuna ma sa'a,












_"Husnah kam gefen gwaggo ta wuce tana shiga ta rushe da kuka mai uban karfi Wanda duk ya firgitasu,"Allah ya rabamu da kuka mudai inji Gwaggo,_






_Inna Habi ta taso da saurin ta " me yafaru? tsabar haushi inna Amarya tace " wallahi kina cewa tak saina sabautaki_




_saboda tasan da lilin kukan nata kuma tasan idan Bata kwabeta ba fada zatayi kuma ai ana barin halas kodan kunya,_




_Inna sai faman lallashi n ta keyi Amma ina sai famar ajiyar zuciya ta ke tsabar bakin ciki yasa Inna Amarya barin wurin ta nufi nata gefen yar karamar wayarta ta dauka takira yaranta mata dake Aure,_




_tareda yimusu bayanin komai ta Dora da cewa " Ku kwabi y'ar uwarku tun Bata jamin abin kunya ba nasan yau idan mahaifin ta yaji sai ya kusan yi mata baki_




_sun tausa mahaifiyar tasu kafin suzo gidan ita kuwa Inna Habi mijinta tanema tayimai bayanin cewar za ashigar mata hakkin y'ah don Bata so, Yace "Habiba' " idan har kika ga ba ayi wannan Auren ba to bana Raye,_




_"banga dan da zamu Haifa ya kasa yimana biyayya ba kuma shima kamal din na fada mai wallahi ko bayan baraina ya sabawa zancen dan uwa na ban yafe mai ba,_






_dole tayi shiru don batada tacewa abinka da mace ta gari sai tafara lallashinta hadi da nasihohi"kiyi hakuri Husnah da yardar Allah bazaki tabe ba bazan taba yarda dan gidan Amarya ya cuceki ba kinji kiyi shiru Abunki,_




_gaba daya tasan Bata kyauta ba yanda take nuna ma Inna Habi Bata kaunar danta kuma gashi tana kan lallashi n ta_






_Amma ya zatayi har cikin ranta Bata kaunar kamal ta tsaneshi......✍




*Happy for the next level Fan's*πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ


*Congratulations Baba buhari tukwici gareku masoyan APC*




*muhadu a next level*πŸ’ƒ
[3/8, 8:40 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*πŸ‘¨β€βœˆ
_patients love & sacrifice_




✍
Golden pen writers Association.




❄we are bearers of Sooo golden a pen we write assiduously percieven no pain so magical our creative golden pen be hold our words A product of our pen savour our words for it will couse you no pain❄




*Welcoming to the next level fans Zinariya wannan nakine Alherin Allah yakai miki a duk inda kike. Page din sai yanda kikayi dashi ina Alfahari dake*




11&12


_kamal sun shirya tafiya washe gari suna zaune da samir yace " Don' yakamata Ku gana da yarin yar nan tun kafin A daura Auren ko._




_Ajiyar zuciya ya sauke " Samir kana ganin zan iya yimata magana ne? Yana maganar kamar bayaso, kasan sunada raini ne yaran kar taga kamar wai nadamu da ita ne._






_"kadamu da ita mana, da baka damuba da baka dakko ta jiya Awurin biki ba kuma nasan saboda kishinta da kake yine yasa hakan,_






_kallonshi yayi irin kallon bakada hankali " Samir remember she is my sister I must protect her no matter what, ya kwashe da dariya " ita kadai ce sister dinka? Me yasa kabar Zainab ka dakko ta ita?_




_"look Don nasanka tun muna yara nasan Abinda kakeso I no your hidden secret kana tunanin bansan meke faruwa ba ne? Ya kalleshi yace "u don't no anything,_






_" haka kace OK ni bari infada maka Abinda yake raina,"I love Husnah" yawani irin juyo wa "what? Matar taw.... Saikuma yayi shiru Samir ya kwashe da dariya sannan yace_






_" to be sincere I love Husnah. ya wani hade girar sama data kasa " not any more, tun lokacin Dana fahimce ka nakuma ga secret dinka a diary na cireta A zuciyata_






_"kamal koda ace ni nafara son Husnah zan iya hakura da ita inbar maka saboda nasan saboda ita ka kasa yin Aure duk tsawon rayuwar nan,_




_"nikuma na tsaya biye maka but am still happy saboda nima nayi sa ar mata and I promise you zankula da ita kamar raina ko ba komai kunfito ciki daya don haka Dole inso jininka_




_yayi Ajiyar zuciya "tank you frnd, cikin sanyin jiki, Yacigaba da cewa " yanzu inkirata ne Kuyi magana? " no. " but why? " bcos she doesn't love me impact she hate me,_






_"cikin wata irin murya mai ban tausayi, shi kan shi Samir he feels bad yasan Abokinshi yana bukatar kulawar ta don yayi dakon so shekara da shekaru shi kadai batareda yafada ma kowaba'_






_"zankirata inji ra ayinta kafin mu tafi' suna cikin maganar suka fito tareda Zainab dama suna zaune ne a kofar gidan nasu yau ba fadawan kuma Abokanshi su sunwuce Kaduna,_




_har su odilin shi duk suntafi kafin yazo Samir na ganin su yamike don sun bala in burgeshi cikin wata blue atanfa Riga da sket hijab dinsu tree quarter sunfito sunyi bala in kyau kamar wasu taurari_




_shi kanshi ogan yakasa daurewa kallonta yakeyi, ita kuwa tunda tafito ta gansu ta daure fuska kamar Anyi mata mutuwa Samir ya matsa kusa da su " gimbiya ta ina zuwa da safen nan ne ?_






_"zamuje tudun wada gidan Aunty kareema' tafada cikin fara a tareda kuma kunya Husnah kuwa ko gaisuwar ma basu samu ba tawani dauke kai zata wuce"_




_"haba Amaryar mu irin wannan dauke kai? Da girman kujerar ki uwar gidan colonel kamal Ibrahim, ji tayi kamar ta tsala ihu batasan lokacin da tawani zabgawa Samir din harara ba"_






_daga nesa yana ganin ta saida yaji wani iri har cikin ranshi "bari inkai Ku ko, Samir yafada, sanin Husnah bazata yarda ba yasa tace mungode ya Samir zamu biya nan gidan su Fatima ne mutafi tare,_






_" OK karku hau mashin to yaciro rafar yan Dari biyu yamika mata Ku hau napep da wannan ta sunne kanta Aa ya samir inna ta bamu na mota ai"_




_ya karbi yar karamar Jakarta ya bude ya saka mata yace banson musu kuje kawai tayi godiya tawuce saboda Husnah harta shige gidan su Fatima_






_yana dawowa kusa da Kamal yace "kaga irin rainin ko? " Hmm zata daina Kaine zaka saukar da kanka komai zai daidaita'_






_" zata raina ni kawai idan taso ayi zaman lafiya za ayi idan kuma taki ita zataji jiki, kar ayi haka Don karamar yarinyace fa yanzu suke eighteen_








_" sai kuma ta raina ni? Karshen raini kuda zakuyi Aure har gadon baccin ka saita gani girman naka ma ai nata ne yace " Allah ya kiyaye ya zatayi dani?_








_" y'an da kowace mace keyi da mijinta kabar raina Allura karfe ce" yace " mubar zancen kawai"_






_sun isa gidan Aunty Kareema tace " aini nasan badon Inna ta aiko kuba bazuwa zakuyi ba bilal ma da yake namiji yafiku ziyarar y'an uwa suka fara dariya tace " kaga Amaren nan da sati hudu. Ai tuni Husnah ta Bata rai"_




_"waike dama da gaske kikeyi bakyason Auren? " "Husnah meye illar yayan mu Allah yabaki miji na kyace raini Amma kinason kiyima kanki bakin ciki ga yar uwarki ta karbi nata hannu bibbiyu Allah ya shirye ki_






_"dama naso inzo gobe don haka bazan zoba sai zuwa jibi idan na gama hado muku kayan gyaran jiki don gyaraku zanyi tsab zankira murja ma inyimata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login