Showing 3001 words to 6000 words out of 66141 words
Chapter 2 - Auren Soja Book Complete Hausa Novels by Feenerh..txt
Alokacin kamal ya dago kanshi jin wata irin murya mai dad'in sauraro yakai idonshi cikin nata saida gabanta ya wani irin faduwa_
_saurin dauke kanshi yayi Samir kuwa duk ya rude ganin wa innan kyawawan yan matan don ko Zainab ba bayaba fagen kyau_
_suka shige cikin gidan yana biye dasu tareda tanbayar su ya karatu? Part din goggo suka fara wucewa saboda sunriga da sun saba sai sun gaisheta idan suka dawo kafin suwuce nasu part din_
_"cikin tsokana Zainab ta fada mata kan jiki "ta tureta tareda cewa " karasa jikin girman zakiyi Husnah tace "sannu gwaggo' tace kema sannu miskila kinfi ma haukaci ban haushi_
_sunan da take kiranta dashi kenan Samir dake biye da su yace " uwar gida sannu da hutawa, ta washe baki "a'a na karfen ina na roban yake?_
_" yana waje jama'ar shi na wurin, tasa dariya "wannan sarauta ta zama ta dole kenan, " wallahi sun manna mai dole_
_cikin ran Husnah ta ce sune yake wani burgesu da ma sarautar samir suka ba ma da yafi Amma wannan sai zurfin rai da uban Jan aji kamar tsohuwar karuwa,_
_dayar ta mike tace " muje ingaida su inna in wuce gida magrib na yi "Fatima zaki wuce ? Tace eh gwaggo dare nayi kar mama tamun fada,_
_suka mike duka suka shige ciki Samir na binsu da kallo, saida ta gaisheda su inna ta wuce gidan su dake kusa da nasu tayi tayi sutaka mata Husnah taki saboda samarin dake wajen_
*karfe takwas na dare*
_Duk sun gama taruwa adakin Baba Alhaji iyayen harma da Gwaggo tana gefe yace " Alhamdulillah naji dadin wannan taruwa ta mu a yau_
_Gwaggo bayan na dawo Amarya ta sameni da maganar danta cewar yasamu mata Acan wurin aikin shi to duk kan mu nan Abinda muke fata kenan ya Ajiye iyalin kanshi kuma dama naso inyi mai maganar to sai gashi tazomin da zancen,_
_don haka zansa ayimin bincike akanta Akwai wani abokina yana aiki tareda su zansa yamin binciken_
_Gwaggo tace " hakan yayi Allah yayi muku Albarka daku da ya'yan Ku duk suka Amsa tare Baba Alhaji yace Suleiman bakuce komai ba akai,_
_"a'a yaya wannan ai zancenku ne kaida d'an ka saikuma Umaru ko yanada tacewa, shima Alhaji umar din yace " yaya duk abinda kayi akanmu ko ya'ya n mu duk dai dai ne_
_yaji dadi sosai "yace Allah ya kara hada kanmu, Gwaggo harda kwalla tana tasa Albarka,_
_haka suke gudanarda rayuwar su akoda yaushe cikin girma ma juna da hadin kai,_
_kwanansu uku suka juya wurin aikinsu , kuma duk tsawon kwana kin nan Husnah Bata kuma y'ar da sun hadu da kamal ba har ya koma, ko Samir duk nacin shi saida ya hakura_
_ahankali kwanaki ke Dada shurawa har zuwa lokacinda su Husnah suka fara shirye shiryen fara rubuta Exam gaba daya Kansu ya dauki zafi kullum suna cikin karatu don ma sun gama da catering school_
_suna zaune adakin inna Habi dukansu har inna Amarya " nidai yaran nan Kuyi Ku gama wannan jarabawa ko kwayi jiki duk kunbi kun rame saboda karatu,_
_inna Amarya tace" yaya kenan Safwan dake jarabawa a Jami a bai rame ba sai su, to ni akansu nafara ganin salo kala kala agidan nan da ace bamuda yan bokon tun farko da munga salo_
_tace " ai suna kokari kedai kyalemin yara na Zainab "tace wallahi inna karatu Akwai wahala na matsu mu gama muhuta_
_bayan tafiyar su kamal Baba Alhaji yasa aka yimai bincike Yarinyar da kamal yace zai Aura Amma baice komai ba akai yana jiran dawo war kamal din_
_su Husnah sun gama exam lafiya yanzu sai zaman gida iyakarsu zuwa hadda burin Husnah bai wuce jarabawar su tafito ba yanzu ta ganta a jami'a_
_yauma duk suna zaune a gefen gwaggo harda su Safwan anata hira Husnah tace " zee nifa nafison inje kadpoly,_
Bilal yai carab yace _first in history kenan anan gidan yarinya, "waye kika taba gani mace da Baba yabari taje jami'a, ko Aunty murja Agidanta tayi hakama Aunty karima,_
_inna Amarya tace kyale ma haukaciya zamu gani inkunfi kowane anan gidan_
_inna Habi tace da izinin ubangiji zatayi tunda suna so kuma nida Kaina zanyima yaya magana, ai tabuga wani irin tsalle ta makale inna tareda cewa " I love you so much my inna_
_Gwaggo tayi dariya naji nagani ke kuma fa, Zainab tace "nikam baruwana wallahi bansa ma araina ba_
_aiko inna saida tasamu Baba Alhaji tace mai " yaya nazo da magana ne akan Yata tace tana bukatar taci gaba da karatun ta idan jarabawa tafito,_
_yanisa tareda gyaran murya "Habiba karki damu ina jiran yayan su yazo sai yaje ya nema musu don yafini hanya yanzu,_
_itakanta tayi mamakin saurin Amincewar shi tasamu su Husnah da labari mai dad'i aranar kamar tasa ruwa akasa tasha_
_Zainab ma tayi farin ciki da Amincewar Baba Alhajin_
_kwana ki nata tafiya wannan karon kamal yadauki kusan wata shida bai shigo Zaria ba saidai waya kullum da iyayen shi_
_yau Garin yatashi da ni ima irin Yanayin da Husnah ke bala in so wato lokacin damuna don tun tana karama tanason wasa da ruwa don haka ko yanzu suna zaune tace_
_Allah yakawo ruwa yau inyi wanka, inna Habi tace " kiwa Allah y'ar nan karkice zaki shiga cikin ruwan nan kinsan Bakida jumurin ciwo kizo ki hanamu rintsawa_
_ai saidai ke ta hanaki yaya badai niba tunda yarinyace kamar y'ar ruwa, "waini yaya haka take kwana da hijabi ta wuni kuma dashi?_
_saikace konanniya lallai Akwai aiki, inna Habi tace " indai wannan hijabin ne nayi fama har na gaji, ke Anyi lokacin zafi saina bari tafara bacci infara kokarin cirema Amma sai kiga tarike shi carab_
_Zainab ta tuntsire da dariya Wallahi inna koni Bata barina ina ganin jikinta ko Riga zata canja saita cikin hijabin_
_ta zabga mata harara "karki wani harareta yaya da bamusan yanda halittar take ba danace tanada nak'asu, " to ya isheku haka keda y'ar ki gwara tarika boye jikinta gudun mayu karsu kama min ita_
_"farar fatar da ta sata zasu lasa kome; " tunda mayu basu yi komai daniba mezasuyi da ita ko kafata takama ne Allah natuba yaya inbanda girma ai jiya ba yauba_
"Ke Amarya inake ina Yata kedai kiyi shiru kawai kinji,
_itadai tanajin su kuma bakomai ke hanata cire hijabi ba sai kunya takeji aga nonuwanta don ita gaskiya bazata iya sa bra ba kuma inata zauna Ahaka zasuna ganin kansu_
_Bata taba mantawa mutum daya ne yataba ganinta ba Riga tun shekaru biyu da suka wuce lokacin da tafara k'irgan dangi lokacin yazo Hutu tafito wanka a dakin Gwaggo tana cire zaninta yana shigowa_
_tayi wani uban k'ara ta dunkule wuri daya shi gaba daya Alokacin ya dauka wani Abu tagani yatsorata ta saida ya lura da yanda take ta dunkulewa wuri daya yaga no ta_
_aikuwa cikin hasala ya fisgo ta " ke uwar me kike boyewa anan yafara kokarin dagota tafara kuka " don Allah ya kamal Karka kalleni wallahi ba kaya ajikinta_
_dariyama taso Tabashi y'an da ta keta wani kare kirjinta bayan yana ganin dan k'urjin datake boyewa saida ya saketa yafita tayita jeramai Allah ya isa kuma tundaga ranar take boye jikinta_
_Bata fatan kowa yakuma kalle mata jiki da ko ita kanta yanzu idan takalla kunya takeji yanda komai nata yacika some time ma matsesu takeyi da best kafin tasa Riga_
_sanadin tsanar shi kenan take mai kallon dan iska tama tsani taji sunan shi Akwai lokacin da ya aiko kaya da Salla aka rarrabawa kowa da har ta dauki wani material dayamata kyau_
_Tanajin labarin kamal ne yakawo tawurgar Allah yasa inna Amaryace kawai da Gwaggo awurin tace "kayan dan iska Allah ya kiyaye ta sa Ajikinta_
_aiko inna takaimata gwabza abaki tace " Ashe kuwa har Abincin gidan nan zaki daina ci saboda ko tsintsiyar gidan da zufanshi ake siya_
_kukanta yajanyo hankalin Inna Habi tazo tana tanbayar lafiya " waye yataba min ya? Gwaggo tace y'ar ki ko shakiyiya wai batason wa innan kayan suka rufe zancen kara irinta Matar nan ita tasiya mata wasu kayan_
*cigaba*
_kafin dare ruwan sama ya sakko wanda ya sanya kowa yanatsu acikin dakinshi suma su Husnah suna kwance akan gadon Inna Habi tana faman naci_
_innan mu indan shiga ruwan nan kadan, tace " a'a bazaki shi gaba ki kwanta kiyi bacci kamar yadda y'ar Uwarki tayi tabude baki zatayi magana sukaji sallamar shi_
_"Inna ta bude kofar tareda cewa" lafiya da Daren nan kuma cikin ruwa? "Wallahi munzo wani couse ne a jaji nida abokaina ne naga inna tayi bacci shiyasa nazo nan muna bukatar Abinci_
_tace " to bari ingani suna cin tuwo ko? Donshi mukayi yau agidan yace zasuci ai hausawa ne duka bari inje Aba yaran nan su kawo mana...............β
*Bear with me fan's I have just started*
[3/8, 8:38 AM] Feenat Marubuciya: πΈπΈπΈπΌπΈπΈπΈ
*AURAN SOJA*π¨ββ
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
ββββββ
Golden pen writers Association.
ββββββ
βWe are bearers of Sooo golden a pen we write assiduously percieven no pain so magical our creative golden pen be hold our words A product of our pen savour our words for it will couse you no pain.β
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7&8
_tun lokacin da Husnah taji muryar kamal ta lafe kamar mai yin bacci, jin yana maganar akai mai Abinci harda bada umarnin a aiki yara tasan idan ta motsa karshen ta ita zata kaishi_
_yana ko tafiya inna tace " Husnah " tayi shiru takuma tab'ata "ke" Husnah " tashi ki kaima yayanki Abinci yazo da baki,_
_taleko da kanta tace "wallahi tsoro nakeji innan mu darefa yayi" tace "nasani daure karya kuma dawon daki kinji"_
_tasan da nauyi ta kuma musu da mahaifiyar shi yasa batada zabi sai na dole ta mike tana tura baki tareda gunguni " mutum kamar maye zai wani biyo dare dama yan fashi sun tare mugayen a hanya kowa ya huta_
_inna kam tayi gaba wajen hada musu komai a tray na silver harda zobo da su kunun zak'i ta fito da zunbulelen hijab inna ta mika mata " muje inraka ki kimika musu mudawo_
_taji dad'i suka fito har kofar dakinshi tayi sallama cikin zazzakar muryarta kafin ta shigo yayi saurin tasowa ya tareta cikin zafin nama ya karbi trayn_
_duk da cikin duhu ne bai hana shi ganin fuskarta ba acikin hasken fitilar dake cikin dakinshi gashi har zuwa lokacin ana dan yayyafi_
_yadan kalleta cikin muryarta kamar anayimata dole tafurta " sannu da zuwa ya kamal " saida ya amshi tray din kafin ya amsa can kasan halshe "Yauwa_
_"kikoma ciki' wani kallo tayimai Azuciyarta tace " ai kobakace ba malam ta juya Abinta batareda ta kuma cemai komai ba tasamu inna suka wuce Abinsu_
_inna tace " yi hakuri Yata kinji zamu hadu da safe zanja mai kunne karya kuma damun mu da dare yaje ya damu uwar shi, itadai gado kawai ta haye sai bacci_
_da gari ya waye suna yin sallar Asuba inna ta aiki Zainab tace " jeki samu Amarya kifada mata d'an ta ya shigo da dare, Zainab tayi tsalle "yehhhh ya kamal? tace " shi wuce kitafi_
_ana fada mata ta mike cike da d'oki tace bataga ta zama ba " koma ki kira y'ar uwarki Ku zo mu yimai Abun k'ari, tasamu Husnah akan sallaya ta na lazimi " kizo muyiwa yaya Abin k'ari inji Inna Amarya"_
_tace "kuth jiya ya hanani bacci yanzu kuma bazankoma baccin ba, inna Habi dake shigowa tace " ke wuce kubarmin y'ah ta huta hakanan Zainab tace " innace tace tazo fa_
_muje muyi aikin barta ta huta Zainab ta kalle ta " y'ar gatan inna kwanta mu bari muje aikin" tayi mata gwalo ta haye gado Abinta_
_aiko inna Amarya naji tafara fada " eh lallai yaya wato daure mata kikayi karta moru to shi kenan saboda Allah ga yar uwarta anan ita ta yi kwanciyar ta adaki_
_"jiya ya hanata bacci yanzu kuma ya hanata" idan sun tashi ta gyara musu dakin kuwa zamu gani_
Kafin gari yayi haske har sun gama shirya musu Abun k'ari irin na gargajiya kunun tsamiya da kuma kosai gefe ga ruwan zafi Wanda yaji kayan kamshi
_ana gama hadawa inna Amarya ta tasota " fito ki kaimu su Abin cin kuma ki tabbata kin gyara musu daki' kafin kidawo ta turo baki gashi ba inna Adakin dole tamike_
_" haka zakije da wannan hijabin kamar Matar liman tace "inna don Allah kibarni inje haka " Allah ya kiyaye wuce kiban wuri haka ta wuce ba don ranta na soba_
_ta Dade atsaye tana tunanin yazata tayi ta shiga ciki ga tray dinda ta dakko da nauyi cikin dauriya ta yi sallama, jin shiru yasa tasan basa ciki tasa kanta kawai_
Saida ta karewa dakin kallo rabonta da shi tun lokacinda su kayi mai bincike ita da Zainab taga komai ya canja harda sababbin kujeru katifar shi katuwa
_gudun karsu dawo su sameta yasa tayi saurin Ajiye tray akan dan center table dinshi tafara Kaye Kaye ganin hijabin na hanata Sauri tayi saurin cireshi dama wani dogon wando ne kawai da wata yar shimi ajikinta wandon ya kamata tam_
_ga shimin ma tayi mata dab ajiki kana ganin komai nata cikin Sauri take aikin ta don tasan masallaci suka je tayi tana gab da gama wa tafara gyara katifar kamal ya sawo kai cikin dakin_
_da Sauri ya koma baya yace ma Abokan nashi suje dakin baba Alhaji kawai bari Agyara musu nan, daya daga cikin su yace " bari indauki system dina'_
_no "bari indakko maka " wai meye haka ne Don saikace mai boyon wani Abun aciki da batare muka kwana ba zance Akwai wata acikine kake boye mana_
_"eh naji kujirani anan kawai cikin matse fuska duk suka bishida kallon mamaki kamar wani mai juju, yana shiga tana janyo hijabin ta juyowarda zatayi sai ganin ganin mutum kawai tayi_
Kasa motsi tayi har hijabin ya fadi daga hannunta shi kuwa tunda yashigo ba abinda yakeyi sai Aukin kallonta tundaga kasa har zuwa samanta ya tsayarda idanun shi cikin nata da sukayi kwalkwal da ruwa
_ya tattaro dauriya cikin wata irin murya mai bala in taushi yace " me kikeyi anan? Saita fara inda inda ganin irin kallonda yake aika mata yasa ta kalli jikinta kamar ta kurma ihu tsabar jin haushi tayi saurin daukar hijab din ta zura shi ta baibai_
_kafin cikin rawar murya tace Abinci na kawo muku ga shinan tafara shirin fita still kallon ta kawai ya keyi harzata rabashi tafita yaji muryar Abokinshi yana cewa Don kabani mana ko inshigone?_
_ya wani irin fisgota " stay hare " karki fita" ya shige ciki ya dakko laptop din yasakai yace gashi maye saika wuce ko " idan tayi wari maji ai " a'a idan ta tafasa ne dan iska,_
_yasa dariya ya wuce saida yaga yashige part din Baba Alhaji yakoma ciki " ki wuce cikin gidan' dama a matse take tafita da saurin ta tana famar tsine mai " d'an iska kawai karo na biyu kenan Allah ya isana ya tsaya kamar wani maye yana kallon mutum_
_tana fita saida ya fada akan gadon ta baya ya runtse ida nunshi yana maida numfashi ya dauki lokaci ahakan kafin ya mike ya fita dakinsu bilal ya nufa suna ganinshi suka Mike "sannu da zuwa yaya" cikin dakewa yace Akwai Abinci a dakina Ku kaimun dakin Baba na_
_yajuya abinshi Safwan yace " yafazo gayen nan bari inyi inbar gidan nan kawai bilal yasa dariya yace " bari nidai inkaimai nasan inada na pocket anjima_
_duk suna zaune adakin baban harma dasu baba ummaru yace " ina fatan lafiya ko da kuka shigo da dare? Cikin girma mawarda yasaba "eh baba wani course zamuyi na sati biyu a jaji kuma jiya jumu'a yakamata mu isa jajin ruwa ya hanamu yanzu sai ranar Monday zamu fara_
_" Toto to Allah ya taimaka "wa innan duk tare kuke aikin Acan? " eh baba yanuna mai laptop baba wannan sunan shi Abubakar, sai wannan kuma Ibrahim sai kuma Nasir_
_Baba yamusu nasiha mai shiga jiki sukansu sun yaba da mutum cin iyayen na kamal bayan sunyi wanka suka shiga ciki domin su gaisa da iyayen su mata_
_sasan Inna Amarya kawai yakai su domin yasan yaran nan na dakin Inna Habi suka gaisa cikin mutunci suka ajiyemata bandir din kudade suka nufi sasan Gwaggo_
_saida gabanshi yafadi ganin su acikin dakin dukansu harsu Safwan tana tsaye da guntun hijabi iya gwiwarta tayi ado cikin Riga da zani na atanfa six piece's tayi wani irin kyau_
_sai tsiya Safwan keyimata "kanwata dama haka kikeda kyau kullum kina cikin katon hijabi, ta murguda mai baki " ai dama ya Safwan kasan nafi budurwarka kyau yadan matso kusa da ita cikeda tsokana " ke ni Nafasa ma dake za ayi Amma kidan cire hijabin nan kisaka gyale muje ma ni zanraka ki_
_Zainab ta kwashe da dariya " ya Safwan Ashe bazakujeba indai saita sa gyale ne kasan ma irin famar danayi ta yadda tasa wannan hijab din_
_Gwaggo tace "ai kedai mijinki Nada aiki wallahi Safwan yace " nine nan mijinta baruwanku muje ki sa gyalen kinji my fiancΓ©_
_ta kwabe fuska cikin sonyin kuka " Allah duk saina hadaku da Inna ta juya cikin Sauri Safwan yariko hannunta daidai da Shigowar su cikin dakin ya wani daka mai tsawa " kai meye haka?_
_"yaya hadani zatayi da Inna ai jin muryar shi yasa duk suka natsu Abubakar tunda yadora idonshi akan Husnah yake furta masha Allah,_
_Babyn badai haduwaba kamar wata bala rabiya, dama abinda yake gudu kenan don yasan halin Abokanshi Akwai son matan tsiya kuma shibaima ba Masan dalili ba da Sam bayaso su ganta gashi ta wani sa karamin hijab_
_tajuyo ganinda tayi mai harda Abokanshi masu irin fuskarshi dole ta gaishesu suka amsa cikin Sakin fuska tace zee muje rana nayi please_
"Zainab ma ta gaishesu Gwaggo tace " Ku shigo mazaje na Ku daina kallon wa innan kyau ya wa nafisu wayewa, duk sukasa dariya banda kamal,
_suna fita su Safwan suka bisu abaya jiyayi gaba daya baida natsuwa kawai mikewa yayi yafita waje sai kaiwa da komawa yakeyi ga direbansu da sojojin dake kula dasu suka taso " do u need something sir? Yace "no Emanuel_
_yana wurin suka fito still suna tareda Safwan Amma Bata canja hijabin ba yayi saurin taresu " kai ina zakuje ne wai? Zainab ce tayi