Showing 60001 words to 63000 words out of 66141 words

Chapter 21 - Auren Soja Book Complete Hausa Novels by Feenerh..txt

Feenerh   

17 Jan 2025

18580

mijin shi " ya waro idanu "cikeda jin dadi " Allah matana? Oya zo inkara yi tunda kin sallama "_






_" Ai da gudu ta fita yafara dariya " tayi sa'a sun shiga daga ciki domin anfara kiran Salla "wanka tayi ta gyara jikinta sannan tayi shiga mai sauki cikin wata irin doguwar Riga mai guntun hannu tareda dan karamin mayafin ta"_








_"ta leka su Gwaggo ta gaishe su " sukace " ina yaran? Suna wurin baban su suna bacci bari inkawo muku su"_




_"Aa kyale su yagana da Abinshi shida zai tafi yabar su "_




_ta samu ta sulale ta koma wurin mijinta" Tasame shi akan dadduma yana lazimi" saida ya idar ta gai sheshi"_


_"Yace inajin yunwa madam kinki bani Abinci " ta jefeshi da wani irin kallo " da shi kadai yasan ma'anar shi "_






_" Ta riko hannunshi yamike ta taimaka mai ya cire jallabiyar jikinshi ta nade Salla yar Sannan tajashi har zuwa wajen data jeramai kayan Abincin "_






_" Ta bude kulolin tafara zubamai white rice data dafata da kayan lanbu tayi wani irin kyau saboda su green Bean's din data zuba akai" ta bude Kumar stew dinda taji namomin kaji ta zubamai akai"_






_"Ai tuni miyan shi ya tsinke" wannan girkin matana ne wow? This is delicious ""_




_" yadauki spoon domin yanzu ne yunwa ta dawo sabuwa yafara aika girki yana Bata labarin aikinshi dakuma zancen komawar shi legos "_




_"gaba daya jikinta yayi sanyi" domin jitake kamar su dawwama a haka kullum suna tare gashi yanzu yara har uku Bata ba zancen bin miji ta ina zata fara"?_




_"Saida yadafa ta " me kike tunani haka?"batareda tunanin komai ba ta ce" banaso kana tafiya ko ina " takarasa tareda zurarowar hawaye "_




_" Ya Ajiye spoon dinda ke hannunshi yajanyota zuwa jikinshi" haba matar soja yakamata ace yanzu' kin zama jaruma kin saba da yanayin aikin mijinki "_




_"Ta share hawayenta tareda cewa" zaka rika zuwa koda yaushe? Tafada cikin sigar shagwaba "_




_" Wani irin murmushi yayi mai dan sauti" Husnah " kina tunanin Kinfi ni son mu kasan ce a tare? Ko y'an zu nasan idan ma nace zamu tafi tare gida baza a bariba da kafata kafar iyalina "_






_" Ya kalli yaranshi dake ta faman bacci a cikin gadon su " inason kasan cewa daku Husnah akoda yaushe nima bada son raina nake tafiyar ba_
[4/20, 9:29 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨‍✈
_patients love & sacrifice_


*~Story written by~*
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


62&63


_"Ya dauki lokaci yana lallashin ta tare da kwantar mata da hankali'_




_"Saida ya tafi sallar isha ta samu ta sulale ta koma dakinta bayan ta kwashe yaranta "_




_" Ya dawo yaga wayam shida yasa ran zai kwana ajikinta " har ya kwanta yaji Sam bazai iya kwanciya shi kadai ba bayan yasan yana kusa da matar shi"_




_"Dakinta ya nufa shanye da jallabiyar shi yayi sa a dakin na bude ya tura a hankali " ya shiga tsaya yawa kawai yayi yana kallon su "_




_" Gashi tana bacci ga yaran nata cilla kafa sama Alamar sun tashi Abulkhairi ne ke baccin shi"_




_"Karasowa yayi dauke da kyakkyawan murmushi a fuskar shi" ya samu gefen su ya daukesu duka biyun a cinyar shi yafara yimusu wasa saida dayar tafara tura hannu a baki alamar yunwa takeji ya kalli Husnah daketa baccinta hankali kwance "_




_" Ya janye Abulkhairi a kusa da ita ya kwantar da ita da kanshi ya Ciro mata nonon ya saka mata abaki Saida ta koshi ya saka ma dayar Sannan ta fara motsawa"_




_"Kamar a mafarki takejin ana tsotsar ta tareda kuma shafata da Sauri ya janye y'ar shi tareda riketa ganin tana juyi zata danne mai yarinya "_




_" Ta bude idanunta ta zuba a kan fuskar shi ya sakar mata murmushi " sory muntashe ki ko " yunwa mukeji shiyasa"_




_"Amma meyasa kike kwanciya tareda su? " yanzu da kin danne min yarinya da bana kusa' tunda suna da gadon su ki rika kwantar dasu idan sun farka ki basu nono"_




_"Tace" OK sir Amma mekazo yi a nan ? Bai Bata Amsa ba saida ya kwashe yaran ya mayar a kan gadon su Sannan ya dawo kusa da ita ya zame jallabiyar shi yarage dagashi sai short nicker kawai ya raba gefen ta ya kwanta"_




_"Tareda rungumota zuwa kirjinshi " ta zaro ido " Abban yara me zakayi? Umman yara bacci zamuyi kawai ba abinda zanyi miki "_




_" Ya zan kwana nikadai kamar wani gouro " ya cumuimuyeta a kirjinshi tun tana tsoro harta saki jikinta ta koma baccin ta"_




_"A ranar shi yayita jigilar yaran idan sun farka batareda ya damu Maman su ba haka ya kwana sintirin kula da y'an uku n shi har zuwa Asuba lokacin da suka koma baccin su shi kuma ya mike ya dauro Alwala yafara tayarda Salla "_




_" Yana kan sallaya har saida gari yafara haske Sannan ya koma dakinshi "_






_" A haka Kamal yayi kusan sati daya a Zaria kullum yana kula da iyalin shi kamar kar yatafi " Amma ya zatayi AUREN SOJA N kenan"_


_"yafara shirin komawa legos gaba daya hankalin ta ya tashi " ita gaskiya Bata tunanin zata iya sabawa "_


_" Yana kula da y'anda take ta faman daure fuska tana shirya mai kayan shi " matsawa yayi gaf da ita batareda ya cemata komai ba ya rungumota "_




_" A kunne yake rada mata " Madam karki damu na samo miki Abinda zai rika debe miki kewa ta" da kinyi Arba' in zaki fara zuwa A.b.u "_




_" Wani uban tsalle ta buga tareda rungumo shi sosai tafara manna mai kiss ta ko ina tana godiya domin babban burinta zai cika na ganin ta zurfafa iliminta"_




_"Nagode Ruhina Allah ya barmin kai yakareka daga dukkan nin sharri ka gama min komai yayana kuma mijina uban yarana"_




_"Aa duk ni kadai madam wannan irin matsayi? Kamafi haka a wurina my Ruhi "_




_" Sun rabu cikin farin ciki batareda yabarta cikin fushi ba " saida ya biya gida duk da kusan kullum sai yaje unguwar su kuma sun San da tafiyar shi "_




_" Saida yaje ya musu Alkhairi kamar ko wane lokaci idan zai tafi Sannan ya wuce "_






_" A sannu komai ketafiya Husnah tayi Ar'ba in ga yaranta sunyi wayon su sun ciko bul bul kamar ba y'an uku ba saboda suna samun Abinci mai kyau da kuma lafiyayyan ruwan nono"_




_"Cikin ikon Allah Kamal ya cika mata Alkawari n ta tafara zuwa makarantar ta cikin kwanciyar hankali yaran kullum a gida take barin su wurin masu kula da su "_


_" Gwaggo Rabi ta koma gidanta sunayin Arba in yarage sai tsofaffin nan guda biyu wurin su take barinsu har ta dawo daga school "_




_"Kamal kuwa tunda yaji tayi Ar'bain yake so yazo Zaria Amma aiki ya rikeshi kusan kullum sai ya mata zancen shifa yafara gajiya Allah zai gudo ko kwana daya ne yayi ya koma"_




_" Ta kan kwantar mai da hankali " Tace yayi hakuri har yasamu isasshen lokaci domin ita bataso yazo yayi kwana daya yatafi"_




_" kusan kullum zancen kenan kuma shi gaskiya yana Azabtuwa gashi yanzu girkima dole yakeyi da kanshi domin Maman sudais suma sunyi posting zuwa makurdi"_






_"Yauma yadawo aikinshi yana kokarin neman Abinda zaici yaji an bude kofar an shigo " yasan bamai shigomai gida sai yaranshi kuma sai yakira su ,ya fito domin ganin waye"_






_"Tsaya wa kawai yayi ya matse fuska " ganin wadda ke tsaye cikin matsattstsun kaya tana wani kara'i raya da jikinta"_




_"Lateefa what are you doing in my house? A hankali take takowa cikeda yanga tana karkada jiki" oh my Kamal I have came to visit you bcos I missed you so much "_




_" tafara kokarin rungume shi yayi saurin tureta gefe" " stop it OK and get the hell out of my house "_




_" Impact who let you in? I thought I have warned you to stay away from my life_


_"Know am married with three children and I love my wife so much " so am warning you to stay away from me and my family "_




_" Cikeda kissa da kisisina tafara cewa" Kamal what A about me? " saboda kai nakasa yin Aure naki kula kowane namiji nafada maka zan iya zama dakai a haka"_




_"Ni ko baka Aureni ba inaso mu kasance tare tafara matsawa kusa dashi tana mai zubawa faffadan kirjinshi idanu tareda muscles dinshi"_




_"Kafin yayi wani yunkuri harta fada kirjinshi saida yakusa zubewa saboda wani irin shocked da yaji " Yama kasa tureta saboda a hannu yake dama "_




_" tafara shafarshi tareda kokarin hada bakinta da nashi " sai A lokacin ku zari nshi yadawo ya hankadeta gefe tareda zabga mata lafiyayyan mari"_




_"Have you lust your mind? Kin taba ganin na hada jikina da kazamin jikinki da kowane namiji ke runguma? Am warning you for the last time lateefa stayed away from me idan ba hakaba zakiyi regretting sanina a rayuwar ki"_




_"Ya bude kofar ya hankadata waje Sannan yakira sojan dake kula da gidan yamai warning'_




_"Samuel what is your work hare' ? I don't want to see are in my house "_do you understand? Ya yi saurin sarawa " yes sir"_




_"Yana shigewa tayi saurin karbar wayarta a hannun Samuel " ta bude pictures din tayi wata irin shewa " tank you Samuel you are good to go"_




_"Tajuya zata tafi yayi saurin shan gabanta "ware is my promise? " oh don't worry am free for you today ta kashe mai ido daya Sannan ta juya tana kada duwai wuka"_




_"Shi kuwa sai kallo yake yana lashe baki ' ta tafi da burin saita nunamai illar kiranta da yayi da Ashawo"_






_"Kamal kuwa yana shigowa ya dafe kanshi Gabadaya ji yake yau idan baije ga Husnah ba Akwai matsala "_




_" Duba lokaci yayi yaga karfe hudu da kusan rabi a gurguje yake shirya kayan shi tareda kiran odilin shi yamai bucking plight zuwa Kaduna "_






_" Yau Husnah ta samu kanta da gyara jikinta har zuwa tayi saloon tayi gyaran gashi tareda tsantsara lalle tafito kamar wata sabuwar Amarya "_




_"su Inna dake gidan sai tsiya suke mata " tace " gida takeson zuwa ta kwana tanason ganin su Inna r ta rabonta dasu ta kwana biyu "_




_" Ta shirya yaranta tashinfide biyu a bayan motar ta Sannan ta sanya daya a gaba ta dauki kayan su da suke bukata ta saka a boot saida ta sanya musu belts Sannan tafada mota ta tayar "_




_" Tafiya takeyi cikeda natsuwa saboda yaranta har Allah yakaita lafiya lokacin karfe biyar na yamma tasamu su bilal a kofar gidan yana hango motar ta yataso"_






_"Aunty sannu da zuwa " kece da yamman nan? tace " eh bilal kashiga da ummulkhair kadawo ka daukar min kaya na zuwa cikin gidan"_




_"Ita tasaba guda biyun ta nufi cikin gidan sukayi karoda shi zai fito" ka kulle min motar key na jikinta idan ka Ciro kayan"_




_"Cikeda zumudi ta nufi dakin Inna Habi tana kwala mata kira " gani nan y'ar gidan Inna r ta " Sannu kinji da fama da wa innan buhun fulawar "_




_" Tasa hannu takarbi daya " muje wurin Gwaggo ta ga yayanta Inna Amarya na zaune tace " ai inajin ihun ta nace yaufa tazo An girma harda yara Amma hankalin da sauki"_






_"Ta fada jikin Gwaggo " tace shi kenan zata karasa ni" kai ni ku miko min ya'ya n kwarai ingani"_




_"Kowa sai yace masha Allah yara saikace ba bakwaini ba' sunyi kiba abinsu gasu kamar yaran tura wa "_




_" Inna Amarya tace " yanzu kina ganesu wa innan masu fuska iri dayan" tayi dariya tace eh " wannan ce takwa rar ki ga ummulkhairi nan"_






_"Da yake shi namiji dole Akwai banbancin kaya sukuwa komai nasu kala dayane har takalmin su"_






_Yaran sai hidima sukeyi dasu suncire kunyar su tsab suna kulada kyawawan jikokin su"_






_"Husnah kuwa tamike kafa tana kwasar faten tsakin da Inna Amarya tayi domin marmari Abinka da zage Zagi "_






_" Ta gama kenan tafito domin wanke hannunta tajuyo sallamar shi cikin muryar shi mai dadin sauraron"_




_"Sakin baki kawai tayi tana kallon shi domin ya mugun mamayarta "_




_" Cikeda takun shi na isa yake nufota fuskar shi cikeda Annuri '.........✍












_*"Hakuri da irin typin din danake yi my fans Akwai hidimomi da yawa ne kurika yimin uzuri don Allah"*_
🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨‍✈
_patients love & sacrifice_


*~Story written by~*
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


64&65


_"tayi saurin ja dabaya kar yace zai rungume ta wani ya gansu" tace " ya kamal Kaine yanzu'? " yace " eh bakya murna da gani na ne?_




_"Tace no " kawai kayi surprising dina ne ya hanya" domin bataso yayi Abinda zasuji kunya " Ka shigo su Inna na ciki dukan su"_




_"Gwaggo tace wane Kamal dinne nakeji yanzu? Dama kinsan da zuwan mijinki kika fito yawo? "Aa Wallahi bai fadamin yana zuwa ba"_




_"ya tsuguna ya gaishe su Sannan yace " tafiyar kawai tazo min ne ban shirya ba shiyasa batasan da zuwana ba"_




_"Kuma bansan tana nan ba nadai biyone mugaisa kafin in wuce can"_




_"Matsawa yayi kusa da yaran da aka shinfide yafara daukar daya yana mamakin girman su "_




_" Gwaggo tace kaga kajin tura wanka ko? Yayi dariya kawai batareda yace komai ba Inna Amarya tace " dan gidana gashi fate mukayi yau kuma ba Abincin ka bane"_




_"Yace ba damuwa Inna banajin yunwa ma' bari inje inyi Salla naji ana kira" ya Ajiye yaran Sannan yafita"_




_Bai shigo gidan ba sai bayan isha saida suka sha hira da baban shi Sannan ya shiga dakinshi dake gidan ya kirata a waya"_




_"Haba madam sabo dake fa nazo Amma baki damu daniba ko? Tace " gani nan zuwa Ruhi na"_




_"Dama tayi wanka ta shirya cikin wata yar guntuwar rigar bacci mai gidan bra da kuma hannun singlet ta dora ta samanta doguwa har kasa budaddiya"_




_"Hijabin ta ta dora akai Sannan tafito zuwa wurin Oga kamal" Tana shigowa ya sunkuce ta sai kan gado"_




_"Tafara dariya " Oga meye haka muda zamu tafi gidan mu" noo bazan iyaba gaskiya dole sai nasamu natsuwa kar inje in yarda mu a hanya"_




_"Sabo dake fa na bar aikina nazo kuma gobe da yamma zankoma dole don haka ki taimaka ki ciremin kishin ki dake wahalar da rayuwata"_




_"Cikeda tsokana tace Oga Bansamu tsarki ba har yanzu" ya wani irin zabura " Wallahi ko teku ne baki isaba haba barima kigani"_


_"Yafara wurgi da kayan jikinsu gaba daya ya rikice mata ganin irin rawar da jikin shi keyi ya mugun Bata tausayi don tasan halin kayanta"_






_"Tafara bashi taimakon gaggawa tuni ya manta da inda yake suka afka fagen daga ranar saida suka karar da Arnan Zaria kaf"_


_"Sai kusan karfe daya suka sararawa juna ya janyota zuwa jikin shi " my sugar meye sirrin ne wai? Najiki ne kamar kwaryar Zuma "_




_" Tayi dariya " Abun sirri ne "Don Allah acigaba da sirran tamin I really enjoyed idan ma ana bukatar gudun mawa zan bayar"_




_" Gaba daya sun manta da zancen yaran su sai more war su suketa yi " ranar ya more yanda yakeso batareda ta nunamai gaza warta ba"_




_"Ita kanta tayi mamakin jarumtar ta don bataji ta gajiba ko kadan yana farawa zata bada hadin kai tasan da taimakon irin hade haden da tasha ne bayan haihuwa "_




_" Gaba daya ranar kwana sukayi suna Abu daya , Yaran kuwa da sun farka Inna zata basu madara haka tayi ta fama dasu batareda tayi baccin kirki ba"_




_*Hmm Inna jika wahal da kaka*_


_"Saida gari ya waye yafara neman yaranshi " yana idar da Salla ya tasheta" madam ina kika y'ar min da yara?_




_"Kallon zakayi bayani take mai " tace ni ina nasan inda suke bakai ka kirani ba kafin inyi wani Abu ka fara......"_




_"Me nafara? Tayi shiru" OK kitashi ki kawomin su " tab saidai kaje da kanka bayan na gudu na barsu yanzu inje in ce Abani su don rashin kunya "_




_"Ni dai kije ko ni inje da kaina' Wallahi kaje da kanka zaifi"_




_mikewa kawai yayi batareda ya kuma cewa komai ba ya nufi cikin gidan " kawai ganin shi tayi dauke da guda biyu a hannun shi" ta waro ido "yanzu dakko su kayi?_




_" Ya Ajiye su ya koma ya karbo dayan dama Inna ta gaji da renon tana ganin shi tace kai " ka kaisu wurin uwar su sunma yi kokari tunjiya basu shaba "_




_"shiyasa abin yazo mai da sauki " saida tayi wanka Sannan ta daukesu tafara basu nono daya bayan daya"_




_"Yayi zaune ya zuba musu ido gwanin sha' awa da kuma burgewa ya fitoda wayar shi yafara daukar su hoto "_






_"ji yaje Kamar ya Mayar da su ciki saboda so da kuma sha'awar su"_






_" Da kanta ta shirya yaranta Yana taya ta goge musu jiki tareda shafa musu mai " sai binshi takeyi da idanu Yana Bata mamaki"_






_"Ya ta karkare sai hidima yakeyi da yaranshi ta sanya musu kaya masu kyau Sannan itama ta shirya "_




_" Karfe tara suka sallami kowa suka kama hanyar gidan su cikeda so da kuma nishadi "_




_" Suna isa bayan sun gama gaisawa dasu Inna ta mika musu yaran suka kuma shigewa daga ciki kamar zasu cinye juna"_






_"Sun samu natsuwa sai yan wasan nin su suke irin na ma aurata wayar shi tayi kara "ta mika hannunta ta dauka " Ruhina msge ne"_




_"Ki bude mana " tana daga kwance saida ta yi wani irin zabura ganin sako daga mace"_




_*"ware are you sweetheart? Missing you very badly*_




_"Tayi saurin jefa mai wayar zata mike ya rikota saboda yaga irin canjin da fuskar ta tayi"_




_"Lafiya Angel? Sai hawaye tafara zubowa tana fisge hannunta "_




_" Meye Amfanin zuwan ka gareni ? Bayan ka ajiye karuwar ka Agida, "Ya kamal ba zan iya dauka ba " ko can da farko ban dau kaba bare yanzu,_






_"Yana rikeda ita ya duba wayar tareda yin murmushi ya kuma janyo ta da kyau zuwa jikin shi"_




_"Husnah "" yakirata cikin kwanciyar hankali'

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login