Showing 21001 words to 24000 words out of 66141 words

Chapter 8 - Auren Soja Book Complete Hausa Novels by Feenerh..txt

Feenerh   

17 Jan 2025

18566

shima yana zaune rike da remote ahannun shi jin kam shin turaren ta mai laushi yasa ya dago kanshi yakafeta da idanunshi'_




_duk da bawata kwalliya ta yi ba but tayimai kyau sosai cikin simple dressed din ta kokallonshi batayiba dankwalinta ahannu acewarta bazata kuma kunshe kantaba yanzu harmasu gadi ma suganta oho'_






_"madam yafada cikin wata irin murya tajuyo dakyau aranta tace sabon salo " yunwa nakeji a taimaka minda Abinci ta kama kugu cikin girgiza har taso Tabashi dariya'_






_"ina Babyn taka kakirata tazo tabaka Abin cin cikin zolaya yace " da nace ta huta madam tazo yanzu' Amma yanzu kintuna min bari inkirata. ta wani hade rai " kace tazo kawai saboda ni girki zanyi shi Amma don cikina kawai tafara dube dube yana kallon ta har tasamu hanyar kicin din_






_gaba daya zancen shi ya tsaya mata arai koda tashiga kicin din ai saita manta komai saboda yatsaru fiyeda y'anda take mafarkin kicin dinta ya kasance'_




_na urorine birjik na Amfani gefe daya ga store w'anda cike yake da nau'o'in abinci ta bude kwalin indomie taciro guda biyu tafito saboda yunwa takeji sosai bazata iya dafa mai wuya ba ta ajiye tabude deep freezer dake cikin kicin din ta ga komai Akwai kifi naman shanu kaji harma da na kana nan dabbobi,hanta ta zaro ta yanka ta kanana ta wanke ta ajiye agefe tayanka su carrots da Green beans su piece duka ta wanke kafin ta kunna gas tafara markda yan kayan miyanta sama sama'_






_cikin minti goma kamshin gidan ya canja zuwa na girki yana falon yakasa daurewa yabiyo bayanta bataji Shigowar shiba kawai ji tayi an rungumeta ta baya yana shakan kam shin jikinta'_






_"rikon dayayi mata yakashe mata karfin jikinta " Ashe ina tareda chef ya furta ahankali cikin saitin kunnenta ya kara rike west dinta dakyau " mekike dafa mana? Alokacin taji dan karfin fara tureshi tana cewa " ni bazan yimaka girki ba tun wuri kanemo mai yima Abinci'_






_"hmm Asmah hakan zai yuwu kuwa ahaka ne zamuji dad'in zama da juna iyayen mu sun hadamu Aure ba don mu watsa musu kasa a idoba don haka kiyi hakuri mu rungumi junan mu Husnah'_






_yakarasa maganar cikin sanyin jiki " takara matsa wa "Auren dolen da aka hadamu na y'an watanni shine zaisa nayi maka komai da kakeso? no way kabarni kawai idan ka gaji ka mayarda ni wurin Inna ta'_




_" Husnah ni Auren gata Baba na yayimin ba Auren Dole ba kuma ita Inna dakike magana kina tunanin zataji dadin ganin kinkoma gida a gaban ta ki zauna'_




_"Husnah remember she is my mother no matter what she love me, kina tunanin batajin zafi idan kika nuna bakya son gudan jininta to be sincere tafi sona da duk sauran kanni na karace kawai da kunya irin ta d'an fari, idan zaki kwantar da hankalin ki mu zauna lafiya ki kwantar idan kinki keda kanki zakiyi nadama don haka zabi yarage naki'_










_"juyawa kawai yayi yafita kicin din "yazanyi da wannan Yarinyar ne ? Yana kallon ta tsabar neman dalili ta zubo Abincin a plate yana kamshi daga gani zatayi mugun dad'i a baki' gashi ta yanka dafafaffen kwai akanta atsakiyar falon tamike kafa ga exotic a gefen ta tasa fake zata faraci taji anrike mata hannu carab'_






_" horon zaimin yawa don haka ko kibarni muci tare kokuma kije ki girka wani Amma wannan na wane. tana kallon shi ya dauke fake din harda gyara zama agaban ta yafara kai loma "hmmmm yummy yafada Yana me runtse idanunshi saboda girkin ba karya ganin idan tayi wasa zai cinye yasa ta dakko wani fake tafara ci don gaskiya yunwa takeji sosai'_




_" kallon ta kawai yakeyi y'an da takecin Abincin cikin burgewa dakuma natsuwa tunyanacin Abincin baisan lokacin da ya tsaya ba tsabar shagala dayayi da kallon ta'_




_saida takoshi tamike saboda kiran Sallar magrib dataji anayi sai Alokacin yadawo hankalin shi lokacin harta isa kofar dakinta'_




_"tunda tashige Bata kuma fitowa ba dama ba Salla zatayi ba kawai tahaye lafiyayyan gadon tafara game a wayarta tana cikin yi kiran Zainab yashigo suka sha hirarsu sosai harzuwa wani lokacin da taji kamar motsin mutum akusa da ita tayi saurin kashe wayar tajuyo ganinshi ya mugun tayar da hankalin ta'_






_tafara data sanin rashin kulle kofarda batayiba yana sanyeda tree quarter na kaki tareda singlet shima na kakin tunda take dashi Bata taba ganin shi ahaka ba ta zaro ido "malam lafiya?...............oops ✍_






*Afuwan fan's Ku cigaba da biyo Matar SOJA zakusamu y'an da kukeso love you All*❤
🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨‍✈
_patients love & sacrifice_


*~Story written by~*
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


*mom Inteesar wannan naki ne ki yi yadda kika ga dama dashi nagode Allah yasaka da Alheri da gudun muwar kati*




21&22
_me kike tunani? Um, nazone inga lafiya baki fitoba? ta wani turo baki "ni bacci nakeji' yayi wani irin murmushi mai sauti " zaki iya kwanciya ke kadai? "Eh mana tafada cikin Sauri'_






_"dama da mutum nake kwana tafada cikin ranta yace " OK good night, yajuya abinshi cikin takunshi na kasaita falon yakoma ya zauna akan kujera ya runtse idanunshi ya na me sauke numfashi Ahankali_






_tunda yafita tayi saurin dirowa tareda garkame kofar dakinta tana me sauke ajiyar zuciya irin Allah ya kwato ta sai muce Asuba tagari'_






_karfe shida na Asuba bayan yadawo masallaci ya fara kwankwasa mata kofa cikin magagin bacci ta mike tana Jan tsaki "baccin ma mutum baza abarshi yayiba haka dai ta bude cewa kawai yayi " kitashi haka kiyi Salla yajuya'_




_kuma kulle kofarta tayi takoma baccin ta ba ita ta tashiba sai karfe takwas na safe tafada bayi tayi wanka tareda brush tafito ta shirya cikin wata irin doguwar rigar shadda ruwan hanta Wanda tayi bala in yimata kyau cikin kayan da Inna tayi musu ne na fitar biki ita da Zainab abinka da farar fata ta shafa turaruka masu taushin kamshi'_




_"cikinta da yafara kugi yasa dole tafito batareda ta ko dauki dankwalin kayan ba don tana sa ran yafita ahalin yanzu tana tafe tana tunanin mezata dafa mai sauki saboda Sam Bata sha'awar shan tea'_




_turus tayi ganin mace tanata aikin gida tako ina kuma budurwa tana sanyeda wando na kaki da kuma t shirt na kakin da alama dai soja ce ita kanta jin motsin mutum yasa tayi saurin juyowa'_






_cikin halshen turanci tace "hy sister' imani yacika mata ciki to wacece wannan ta wuce war ta kicin domin karasa girkin datake yi batareda ta kuma sauraran taba_






_wannan dai ba mai aiki bace daga gani kuma soja ce to wacece ita tama sandare awurin takasa motsi gaba daya yunwar komawa tayi tana kallon ta tafito tareda cewa " till I come back sis bye '_




_kallonta kawai takeyi harta fita gidan tasamu wuri daya ta zauna tareda hade tagumi " meke faruwa ? Karuwar shice kome'?_






_"daga baya takuma mikewa ta wuce kicin din tasamu tagama shirya abinci gasunan kala kala a Warmer's sai kamshi ke tashi Amma jitayi Sam bazata iya cin wannan Abincin ba cikin minti da baifi talatin ba ta soya wainar fulawarta da kwai tasamu Garin kunun tsamiya na Leda ta dama ta dawo falon saida tayi nak'_






_takwashe kayan takoma kicin saida ta wanke abubuwan da ta Bata ta kara goge kicin din sannan tadawo falon sai Alokacin taga wata farar takarda akan dan glass center table dinda ke tsakiyar falon ta bude'_






*Nafita office idan kina bukatar wani Abu ki kirani sannan Akwai masu kula da gidan basai kin wahala ba bye*




_mtswww tayi dogon tsaki tareda nadeta tamayar inda ta dauka takunna kallo a TV dake falon aka danna bell din dake gidan sanin hanyar da suka shigo yasa tanufi kofar ta bude'_




_"ganin wata matashiyar mata tayi wayayya daga ganinta ba yarinya bace hutune kawai ya rat'sa ta cikin fara'a "sannu Amarya itama cikin respect tayi mata maraba tareda Bata umarnin shigowa'_






_" saida ta kawo mata drink hade da glass cup akan tire ta kara gaisheta "tace " ni Matar ogan megidan ki ce kuma ina nan kusa da ku naso inzo tun jiya Amma naje gidan mu ne a apapa saboda ni yar nan legos ce"_




_"sannu Aunty tafada cikin fara'a tace "ina fatan ba damuwa ko? " a'a ba komai Aunty' to sai kinyi hakuri da rayuwar bariki da kuma mazajen mu kinsan su ba mazauna bane so dole sai munyi hakuri'_






_"kanta aduke tace toh Aunty' "baki sha lemon ba? Tayi dariya ta tsiya ya kadan a cup cikin raha tace nazo cin Abincin Amarya ne inji ko ta iya girki'_






_" tayi murmushi itama tace "to Aunty bari in dora miki yanzu cikin dan lokaci kadan ta hada mata lafiyayyar jalof rice dataji namomi da kuma kayan lambu sai tashin kamshi takeyi'_






_Atsakiyar Capet din tajera mata komai saboda tace bazata hau dining ba tafara kwasar gara taci sosai tareda santin girkin tace 'masha Allah gaskiya iyayenki sunyi kokari sosai wajen kula da iya abincinki'_






_" kuskuren da ake samu kenan awannan zamanin za a Auradda yarinya komai Bata iyaba gaskiya naji dadi sosai kuma inaso idan har kinada matsala " (don't hesitate) ki sameni kawai_




_"karki damu ki dauke ni kamar yayarki inada yara guda hudu biyu maza biyu mata babban su yana Sudan yana karatu mai binshi kuma yana nan a *UNILAG* matan twins ne suna secondary'_




_tayi mamaki sosai kamar wane Matar tanada many an yara tace nagode sosai Amma zan rika kiranki da maman Sudais daga yau sunan babban yaronta da ta fada mata kenan'_






_tayi dariya "ai dama haka ake kirana nima na gode kuma gidana shine na gaban ku dinnan da kinfita so zamu yi zumunci sosai insha Allah'_




_" sunkai lokaci mai tsawo da maman sudais harta saki jikinta kafin zuwa lokacin da ta mike "Amarya ni zan tafi gida Oga yakusa dawowa don haka sai nakuma lekowa ko kuma inkin shigo'_






_taji dadin kasan cewa da Matar sosai ta kwanta mata har jikin zuciyar ta haka ta gyara ko ina ta shige dakinta ta tube ta fada bathroom ta watso ruwa saboda dan zafin da akeyi agarin na legos'_






_karfe biyu kamal yadawo gidan agajiye odilin shi ya shigo mai da wayoyinshi tareda briefcase ya ajiye su yasara mai kafin ya fuce abinshi'_




_kofar dakinta yake kallo ita yakeson yaga ni ahalin yanzu harya daga kafarshi zuwa kofar ta fito rike da wayarta tana faman danna wa kanta akasa gashi ta canja shadda zuwa Riga da sket na atanfa sai kamshi take zabgawa'_






_ji kawai tayi tayi karo da mutum tayi kokarin tsayawa da kafarta Amma ta kasa har zata Kai kasa yariko ta cikin Sauri sai kan faffadan kirjin shi'_




_wayarta kuwa tuni ta tarwatse a tile's din dake falon ta yi matukar tsorata don Bata San da dawowar shi ba kara mannata yayi da kirjinshi ga kamshin shi mai tsada yana ratsata har cikin zuciya'_






_kallo mai tsada yake aika mata ita kanta kallonshi takeyi don tsawon rayuwarta yaune ganinta dashi na farko da uniform sun yi marukar karbarshi'_




_zata iya cewa yaune karo na farko da ta fara ganin sojan da ya burgeta a kaki ta shagala a sosai awurin kallon shi shikanshi kamshin jikinta yake shaka tareda kallon kyakkyawar fuskarta'_






_yakai fuskarshi akan tata ta dawo hankalinta tayi saurin janyewa "saida yaja wani irin numfashi kafin ya furta wata Kalmar aka turo kofar batareda ko sallama ba'_






_har zata juya ta koma dakin taja dole ta tsaya saboda ganin wadda ta shigo budurwar da tagani dazu ce da safe yanzu ta canja kakin zuwa wasu irin arnan Riga da wandon Jean's ga wasu takalmi masu uban tsini'_




_cikin yanga da karairaya take takowa gaba daya ya hade fuskar shi tana isowa tareda nufin rungumeshi tana cewa" oh dear I really miss you, & I came in the morning u already left that is why I come back "_






_yayi Saurin tareta alamar ta tsaya karta taba shi' still Bata fasaba taci gaba " da cewar tama samu sister dinshi dazu gaskiya suna kama sosai"_




_baki kawai ta saki tana kallon karuwanci kiri kiri harda fadamai ita ta sallami cooker dinshi zata rika yimai kullum kafin taje aiki'_




_"kuth shine abinda yafito bakin Husnah yajita don har wani murmushi yayi Wanda ya kara tsuma wannan budurwar don ta dauka yaji dadin duk abinda ta fada ne_




_"yadan bada hankalin shi kadan akanta cikin basarwa da kuma Jan aji yace "tank's. gaba daya jitayi wani irin Abu ya tsaya mata arai wato karuwa r shi ce sun saba lalacewar su'_






_" kafin tayi wani tunanin yaja hannunta zuwa waje Husnah saida takusa daskarewa tsabar kaduwa to ina zasuje? suna fita waje ya hade fuskarshi "lateefa" cikin harshen turanci "_


_" karki kuma zuwa gidana inada mata yanzu' ta wani irin firgita "what? Aure ina Alkawarin Auren mu dakai? Kamal ya zaka yimin haka bayan kasan ina sonka'_




_" All that long ina jiranka shine zaka je ka Auro karamar yarinya? " nataba rokonki da kijirani? Ko ni kamal nataba gaya miki dole kece zan Aura ko lokacin da na yarda da zancen Aurenki inada dalili"_






_"iyayena sun zaba min mata kuma dole inyi musu biyayya saboda saida suka gama dawainiya dani kafin Kice kina sona don haka stop coming to my house'_






_"hawaye na gangarowa cikin idanunta tace "that means u love this small girl" yace " not ur concern just stay away from my house and my wife ya juya ciki ya barta cikin bakin ciki da kuma kunar zuciya'_








_aciki kuwa ta cika matuka ace agidan Aurenta karuwa lallai wato halinda take mai zato gaskiya ne, tanajin motsin dawowar shi tayi saurin juya wa zata shige taji An fisgo ta idonta arufe tajuyo tafara tureshi kafin kace me hawaye sunfara fitowa'_




_Karka ce kanshi yayi kamar kalar tausayi "Asmah' lafiya? kallon karenamin hankali tayimai, taci gaba da kokarin fisgewa yace " relaxed what is All this? Ya lakuto hawayenta'_




_"sai sukaci gaba da zurarowa "meyasaki kuka waya tabaki " kinsan kina tareda yayanki baikamata kina zubarda hawaye ba still fisgewa takeyi'_






_"abinkada karfin soja kawai daukarta yayi cak yanufi cikin dakinshi ganin yana nufar wani dakin daban yasa tayi saurin hadiye hawayenta mukuth tace" nayi shiru yaya" cikin tsananin tsoro'_






_"baisaurareta ba saida yatura dakinshi yashiga tana hannun shi kamar wata Leda ya dauka ba mutum ba, wani irin kamshi ta ziyarci hancinta mai tsaya wa azuciyar mutum'_




_tuni tafara ware idanunta tana kallon ko ina Ashe wani falo ne daban Wanda kujerun cikin shi sunfi na falon haduwa ga komai na jindadin rayuwa Akwai abinda yafi komai daukar hankalin ta shine'_






_hotunanta da nashi dake jikin kowane bango da kuma kusurwar dakin mamaki yagama cikata kawai direta yayi Ahankali ya furta mata" ki gama kallon bari inyi wanka ko'_






_batako jishiba ganin wani hotonta tunbata wuce shekara goma ba sannan ga kuma wani Wanda bazata taba manta wa ba lokacin wata Salla sunje tudun wada ita da Zainab suka dauke shi su biyu abin mamakin ta shine wannan ita kadai ce "_






_ina yasamu wannan hoton ? Sannan ga hotunan su da sukayi na ranar crossing of sword sunyi bala in kyau batama San lokacin da suka dauki hoton ba gakuma nata ita kadai sai kuma nashi gaba daya kanta ya daure'_






_" mai zaisa ya jera hotunanta acikin falon shi har haka wata zuciyar tace to aike kanwar shi ce' to da baisa na Zainab ba ko su Safwan why me?_




_wani hoton shi yakuma daukar hankalin ta gaskiya uniform na balain daukar shi ta sha'afa sosai wajen kallon hoton har takai hannunta tana shafo saitin lips dinshi pink masu tsari kamar ba namijiba'_






_agefen hoton kuma wani irin frame ne mai dauketa wasu irin kananan rubutu masu daukar hankali taji tanason ganin meye aciki'_




🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
~she is my Angel I love her and I will Always loved her, love you so much my Angel~❤❤




_tafara ja da baya cikin sanyin jiki wato yana son Yarinyar sosai har haka tanufi hanyar fita dakin yafito lokacin "ina kuma zakije? batada niyyar dawowa yakira ta can kasan makoshi"_




_" Husnah' dole taja ta tsaya yakaraso cikin takunshi na mazantaka zuwa gareta " kingama kallon ne? bata kodaga kai ta kalleshi ba yasa hannu yadago habar ta ganin hawayenta yasa ya mannata akirjinshi "_






_meyake faruwa Asmah? meke saki kuka ? nayi miki laifi ne tadan zame tareda share hawayenta yace "OK am hungry please ki taimaka min da Abinci'_






_" aita yima girki kaje kaci' "nop naki nakeson ci banata ba ki taimaka tunsafe coffee kawai nasha a office taki motsawa yakuma cewa please' tajuya tafita yabita da kallon da shi kadai yasan ma'anarshi'_




_cikin minti kadan ta juyomai sauran Abincin da ta dafama Maman sudais ta dawo cikin falon nashi yana zaune kofar yake kallo harta karaso ta duka ta ajiye mai plate din tajuya wajenda taga firij dinshi tabude ba komai aciki sai tsadaddun wyne Jere aciki'_






_" ta tuna ta taba ganinshi da irinsu ko a Zaria wato giyace shiyasa ko lokacinda su ka yimai bincike har suka fasa yace zai zanesu aikuwa tasa hannu ta dakko katuwa ta kawo mai duk yana kan binta da tsadaddun idanunshi'_




_tana ajiyewa tajuya zata fita yariko hannunta ta tsaya cak "kidawo ki zauna anan har ingama ba musu tanemi nesa dashi ta zauna akasa tareda lankwashe kafafunta shima kasan yadawo yana me fuskantar ta yafara cin Abincin'_






_godiya kawai yakeyi acikin zuciyar shi saida ya cinye tas kanta na duke yace " kidebe kwanoninki nakoshi kuma ki kawomin cup'_




_tarasa meye dalilin ta nakasa yimai musu tana kawowa yabude tana kallon ikon Allah saida yacika cup ya nufi bakin ta dashi tayi saurin ja baya tare da cewa Allah ya kiyaye insha giya'_






_"yace nima haka saida yasha cup biyu yamika mata kwalbar yace inafatan kinje makaranta don haka indai ba asarar school fees akamun ba kikaranta'_






_ta dubi kwalbar taga anrubuta non Alcohol tadan basar tamike ni zantafi dakina' "ai nan ne dakin ki don haka zoma kiga ko ina Yarikemata hannu harzuwa wani daki gabanta na faduwa ganin kayan motsa jikina birjik yasa tayi ajiyar zuciya'_






_jallabiyarda kejikinshi ya zame ya rayate akan wani karfe datsaya daga shi sai tree quarter tayi saurin rufe fuskarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login