Showing 54001 words to 57000 words out of 66141 words

Chapter 19 - Auren Soja Book Complete Hausa Novels by Feenerh..txt

Feenerh   

17 Jan 2025

18594

sacrifice_


*~Story written by~*
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


54&55


_"Ba tare da Bata lokaci ba likita ya shigo ya fara Bata taimakon gaggawa saida suka samu nasarar daidai ta numfashin ta cikin ikon Allah ta far fado saidai ta gala baita duk jikinta yayi weak"_




_"A dimauce Kamal ya karasa kusa da ita don saboda rudu ko motsi yakasa yi saida yaji Ance ta farfado sannan ku zari nshi ya dawo jikinshi "_




_" Riko hannun ta yayi yafara jero mata sannu tana kallon shi ji yake kamar ya maida ta cikin shi saboda so Husnah ta gama da komai nashi "_


_" A hankali ta rufe idanun ta Allurai da likita ya mata domin ta samu hutawa da kuma karfin jikinta "_


_" Shigowar su Inna cikin dakin yasashi saurin matsawa gefe Nurses suka miko musu kyawawan yaran kowannen su cikin kayan sanyi"_




_"Jikin shi na rawa ya karbi daya "tareda fara jero mai Addu'o'i bakinshi har kunne saboda tsananin farin ciki"_




_" Masha Allah kaga yara kamar yaran larabawa wannan uwarku kuka biyo Amma kwabani kishiya ina mijin yake shi nake so "_


_" Kar wannan fatar ta sa Alhaji ya ce ita yakeso Kamal ya mika mata yaron ya karbi Yarinyar daya tareda tanbayar waye babba "_?


_" Nurse din dake like a wurin tana famar sanabe taga handsome man din Husnah tayi saurin cewa Ai an sa musu number a hannu yayi saurin duba hannun yaga wani Abu kamar agogo a hannunta"_




_"Yaga itace farko Atake yayi musu khuduba yabasu suna Tafarkon ya Bata Aisha wato sunan margayiya uwar gidan Baba Alhaji ta biyun Maryam sunan Inna Amarya sai kuma namijin Ibrahim wato Sunan baba Alhaji "_




_" Ita kanta Inna Habi taji dadin karar da yayi ma Alhaji sosai nasa sunan matarshi da kuma nashi don mace ce mai halacci Allah ya jikanta Ameen "_


_" Inna sahura sai sa Albarka takeyi tana Allah ya bar zumunci "_




_" A cikin daren dole ya koma Jaji saboda basu San baya gariba yabar su Inna Habi a Asibitin "_




_" Yana isa ya kira Samir lokacin yana bacci yadaga waya ' Lafiya malam da daren nan kasan dai ni ba gauro bane? Eh nasani kuma nima kasan inada matar " dama zan fada maka nazama Dady sai kudaina min gori"_




_"Kara bude idanunshi yayi da kyau domin jin Karin bayani yafada mai y'anda komai ya kasan ce"_




_"Cikeda farin ciki yace Allahu Akbar mun samu yara har uku kai mun godewa Allah Amma "gaskiya kamal bakada sauki yanzu ka janyo Yarinya ta haihu lokaci bai yiba"_




_" kashe wayar shi kawai yayi ya matsu safiya Bata waye ba burin shi kawai yagan shi kusa da matarshi da kuma yaranshi 'A ranar kwana yayi yana jero Addu'o'i na godiya da ubangiji "_




_"Safiya na wayewa ya shirya a gurguje ya je office nasu yayi report batareda ya koma gidan shiba ya wuce cikin gari tareda sojojin shi ya jibgo ma iyalin shi kaya "_




_" Kamar bayason kudin haka ya cika bayan motar shi tab har kan seat "_


_" Yakashe kudi kamar bayaso don in natsaya bayanin Abubuwan da ya siya zan cinye lokacin"_




_"Driver yaja motar sai Zaria koda Samir ya kirashi yace shi yanzu haka suna kofar doka yace suma gasunan zuwa"_




_"Gidan su ya wuce sai dai yasamu Inna Amarya kawai suka gaisa ya tanbayi Gwaggo " tace suna can gidan shi saboda An sallame ta Alhaji ya ce su wuce can kawai gaba daya"_




_"Yayi matukar farin cikin hakan kuma harda Inna Habi taje gidanshi shikanshi yasan da ba don Husnah ba Inna bazata taba zuwa gidan shi ba"_




_"Ya nufi gefen baba Alhaji ya gaishe shi tareda yimai barka " yace nasa Safiyanu ni yakai raguna can a yanka saboda kauri dakuma masu zuwa barka"_




_"Haka yayita godiya "yace Allah yara ya manasu Akan sunnah yasa kuci Albarka cin su kamar y'anda muke cin naku"_




_"Ya Amsa da Ameen sannan ya mike domin tafiya gidan shi"_




_"Duk ya matsu yasa matar shi a idanun shi tare kuma da yaran shi " suna isa yaba yaran shi umar nin shiga da kayan da ya zo dasu sannan ya shige cike da zumudi "_




_"Gidan cike yake da yan uwa da kuma Abokan Arziki yana shiga tun daga falon Abokan wasa na mai tsiya Angon karni ya iso, " Amsa gai suwar kawai yake yi tare da dokin sanya matar shi a ido"_




_"kama hanyar kawai yayi kanninshi duk suna gidan suna famar hidima da jama'a yan barka Dakin ya sa kanshi duk su Gwaggo na ciki Inna Habi ta tasa mata Abinci irin na gargajiya a gabanta tanata turawa"_




_"Suka fara yimai barka yana Amsawa cikeda kunya suka mike zasu fita " yace Inna Kuyi zaman ku tafiya zanyi ai' Inna sahura tace aa kaga yaranka dama falo zamu koma"_




_"Suna fita ya bi bayan su ya kulle kofar sannan ya harde Hannayen shi ya zuba mata idanu cike da kauna da kuma tsananin burge shi da tayi cikin Côte devoir green Riga da zani tafito kamar sabuwar Amarya"_




_"Ga dakin na zuba kamshin turaruka ga kuma yaranta Jere akan gado suna kwasar baccin su saboda likita ya hana daukar Su saboda jikin su ba kwari"_




_"ya dade a tsaye yana kare mata kallo ta dukar da kanta Sannan ya karasa ya zauna a kusa da ita "_


_" Wata irin wawuyar Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo da ita yariketa yana aika mata da wani irin kallo mai dauke da ma'a noni da dama"_


_"Tank you Husnah """" ya furta can kasan makoshin shi'_


_"Ta dago idanunta ta kalle shi " tank you for what? "_


_" For everything Husnah """'' ke Alkhairi ce a rayuwata " Abu na farko kece burin raina Allah ya mallaka min ke " na biyu saboda ke Husnah har Inna ta tako gidana a yau "_




_"Husnah nasan saboda ke ne har Inna ta iya zuwa gidan na godewa Allah da ya mallaka min ke a matsayin mata"_




_" Sai babbar kyautar da kika bani Husnah shine wa innan kyawawan yaran Ya juya yana kallon su "Allah ya miki Albarka kin gama min komai Husnah "_




_" Ya juyo tareda rungume ta tsam a cikin jikin shi saida tace Ashh " yayi saurin dagowa " meke damunki ? Cikeda kulawa da kuma damuwa yake tanbayar ta"_




_"Tace "Ai dinki sukayi min shine ka fama min " ya zaro ido waje " ina dinkin yake mugani " tayi saurin cewa " a'a zai warke "rowa kike mun bakyason inga dinkin namu?_




_" Tayi dariya aa "ya dago fuskar ta " I love you Husnah"""' ya furta har saida tajishi cikin zuciyar ta ta furta " I love you too Ruhi"""'_




_"Yace wow I love this name "" A hankali ya matso da fuskar shi kusa da tata ganin Abinda yake da niya yasa ta saurin ja baya"_




_"Saida yaja numfashi saboda yaso ya d'an tsotsa ko kadan ne ya rage Abinda yakeji game da ita"_




_"Angel ki rage gayun nan in ba hakaba...... Ba ruwana gaskiya don bazan yarda ba'_




_"Kallon shi tayi ta Karka ce tana tunanin fadan dasu Gwaggo sukayi ta yimata akan karta yarda ta shigewa miji gata da yara har uku"_




_"Tunawa da tayi da maganar su yasa ta saurin cewa " Ruhi kafita haka karsu dauka wani Abu mukeyi"_




_"Ya kalle ta tareda dage gira daya" me zasuyi tunanin munayi? tayi shiru " ya kuma matsota tareda manneta a jikinshi"_




_"Tell me' mezasuyi tuna ni? Kafin tace wani Abu aka fara kwankwasa kofa "da Sauri ta tureshi " kagani ko ' dakyar ta mike tafara takawa a hankali yana bin bayanta da kallo "_






_" Saida tabude ta fita sannan ya sauke Ajiyar zuciya ya koma wurin yaran shi ya kuma zuba wa kyautar da Allah yabashi ido tareda Hamdala "_




_" Kareema ce " tace ke y'an barka na zuwa kun shige kun kulle kofa ko"_




_"Sum sum ta wuce zuwa falon ta zauna cikin yan uwa, saida ya dade yana kallon yaran shi kafin ya fito daga cikin dakin ya kira murja"_




_"Ku kula da yaran nan please kar a cika daukar Su' tace " toh yaya " sannan yafita Abokanshi sai kiranshi sukeyi suna mai congrt "_




_" Su Zainab ma sun iso sai rawar jiki takeyi Husnah kuwa ta karbi takwa rar ta yarin yar tayi wayo sosai saboda basu haduba a Kaduna nakuda ta taso"_




_"Zainab din ma sai tsiya take mata wai tabi miji ya ballo lebour "_






_" Haka suka kwana hada hada Anbudewa yara dakinsu an shirya gadaje ga kayan wasa ta ko ina kamar wa inda sukayi wayo"_




_"Kamal bai samu natsuwa ba koda yaushe yana zarya daga Zaria zuwa jaji saboda har yanzu basu sallame suba sun koma units dinsu"_




_"haka yaraba hankalin shi guri biyu ga iyalin shi kuma ga aiki duk yanda yaso da zama a kusa dasu dole ya hakura saboda yanayin aikin shi "_




_" kullum yafita sai ya siyo musu kaya dakinsu ya cika tab da tarkacen kayan su"_




_"Husnah ta kara cika da kyau daka ganta kaga matar so yar gata a wurin miji kowa yasan Husnah tayi sa ar Aure "_


_"kullum sai dare yake samu ya shigo gidan saboda mutane ga kuma Inna ta cire kunya tsab tana kulawa da yarta itada Gwaggo rabi "_




_" Ana gobe suna ya kawo musu akwatuna kamar zasu bude kasuwa kowa da nashi saitin Husnah harda wata sabuwar mota dalleliya tukuicin haihuwar yan uku "_




_" Ita kanta kayan sun Bata tsoro tun ranar da ta haihu kullum cikin kashe musu kudi yake gashi kuma tun ranarda suka kulle daki Bata kuma sanya shi a I idoba "_




_" Ko kiranta bayayi Amma bai fasa yimata hidima ba iyakar shi idan ya shigo ya aika akawo mai yaranshi"_




_"Amma ganin wa innan kayan da tayi gaba daya takara sakan kancewa da Al amarin mijinta "_




_" Sulalewa kawai tayi ta nufi dakin shi batareda tunanin komai ba tana shiga taji karar ruwa ta wuce sif din shi ta zabo mai wasu kayan don tasan fita zai kuma yi "_




_" Tana gama cirowa Yana fitowa " tsaya wa kawai yayi ya zuba mata idanu kamar bai taba Ganin ta ba"_




_"Tafara takawa tareda zuba mai idanunta cikeda son sojan ta kuma jarumi kirar jikin shi kawai take kallo ta jaruman maza"_




_"Tana karasawa kusa dashi Bata tsaya Bata lokaciba ta rungume shi ta sanya hannunta ta duko da kanshi ta Dora lips dinta akan nashi"_




_"Batareda dogon tunani ba tafara tsotsar lips dinshi har ta isa cikin bakin shi tuni ya kan kameta cikin jikin shi yana sauke numfashi "_




_" Saida suka tsotse bakin juna sosai kafin tayi kokarin janyewa daga gareshi"_




_"Girgiza mata kanshi kawai yake yi har idonshi ya canja kala saboda ta tsokano mai inda yake Kai kayi "_






_Da dubara ta zame bakinta saida ya fisgo numfashin shi sannan ya fada kan gadon tareda mika " Tayi saurin waro ido waje" ganin irin fitinar data to no yanzu ta wuce da tuna ninta"_






_"Dole ta matsa kusa dashi tafara shafa kirjin shi a hankali ta bude bakinta"_






_"Am sory Ruhi""na nasan nayima laifi kayi hakuri banaso in yi Abinda zai Bata ma Inna rai ko kuma insata jin kunya banaso ta takura kuma don ni tazo nan gidan kuma tana iya bakin kokarin ta a kan mu kaga bai kamata mu Bata mata ba"_






_"Dariya kawai yayi ya mirgino tareda rungume west dinta yana shakar kamshin jikinta"_






_"Madam bazan taba iya fushi dakeba kin gama faran tamin rai ba zan yi fushi dake ba ni Kaina saboda Inna nake daga kafa don nasan bazata iya sakewa ba idan har tana ganina"_




_"Yanzu ina yarana? suna wurin Gwaggo yanzu suka sha nono' da saurin shi ya kwantar da ita yabi kirjinta da suka cika fam fam kamar zasu Faso rigar ta da ido"_






_"Toh a taimaka a tsamma baban su shima ya sha ko ' yafada hade da daga mata gira tayi saurin matsawa gefe "_




_" Nifa godiya nazo yi Ruhi""" ya kuma matsowa tareda kara matseta " ki bar bakin ki ya huta banason godiya da baki ki gode min a aikace "_






_" Ruhi na Am sory biki fa nakeyi "" Sai yaushe zaki samu tsarki'? sai nayi wata biyu " yayi saurin tashi zaune "_




_" Don Allah kifada min gaskiya karki sani shiga wani yanayi " ina laifin sati biyu"_






_"Kinga ranar suna me gidan ki zai samu Karin girma daga lieutenant colonel zuwa colonel insha Allah "_




_" Ta rungume shi cikeda farin ciki " Allah ya kaimu ranar " Ameen ki shirya this time ke zakije kimun hanging na rank dina bayan mun dawo Akwai walimar da Abokaina suka shirya samir yabada contract din komai a shagalin ku hotel "_






_" Za akawo canopies a sa a harabar gidan nan sannan nagama shirya komai nawa bayan suna zankoma units dina a legos"_




_"Zanyi kokarin neman posting dina zuwa Arewa banason yarana su taso a kudu "tace Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a yace Ameen"_




_"ita ta taimaka mai ya shirya yanata faman shige mata jiki saida ya fito fes sannan ta tsuguna a ga banshi ta riko Hannayen shi biyu "_




_" Ya kamal na gode da kaunar ka a gareni Allah ya kareka da ga dukkan nin sharri na gode da hidimar ka a gareni Allah yakara budi "_




_" Wani irin farin ciki yaji yana ratsa shi saida ya dagota "Madam ba godiya a tsaka nin mu " it's my responsibility "_




_" Me zanyi da kudin da da na samu a Sudan meye Amfanin salary na meye banida shi ? Idan na a jiye kudin banyi muku hidima ba me zanyi dasu?"_






_"Ta rungume shi hawaye na zubowa a idanunta ya dagota tareda share mata hawayen "banason kuka muje inga yarana Akwai wata kyautar ma sai ranar suna zan baki ita "_




_" Ruhi ai ka gama bani kyauta tunda ka a jiyeni a matsayin Matar ka nasan nafi kowace mace sa'ar miji"_




_"Yayi murmushi ya ce muje madam ingan su jaji zankoma yanzu "_






_*" Hakuri my fan's uzuri yayi yawa ina yinku sosai Allah yabar kauna"*_
[4/17, 8:08 PM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨‍✈
_patients love & sacrifice_


*~Story written by~*
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*






56&57


_"Komai na suna ya kammala Samir yayi kokari sosai, fannin kayan rabo kuwa Zainab ta hada na suna calendar na baby's da kuma su stickers ga littafai da ta buga da hotunan baby's "_




_" Abokanshi sun hada mai nashi na Karin girma komai masha Allah sai dai muce Allah ya bar kauna ya karo dankon zumunci "_




_"Fatima ma ta zo wato babbar Amini yar su tace bazata bari sunan yan uku ya wuce ta ba ita ma Ansa ranar Auren ta da Sadiq Abokin su Kamal"_




_" Sai muce Allah ya kaimu lokaci Ameen "_


_" Sun shirya dawuri domin zuwa jaji daga ita sai kawayen ta Zainab da kuma Fatima Kamal dama yana jaji ya Ajiye musu Driver da zai kai su"_




_"Tafito cikin wani tsadadden Swiss less daka ganta kaga matar Oga ga yaranta kowane An shirya shi cikin lafiyayyan kaya An dunkule su A cikin bargunan su masu tsada"_


_"Ta sanya takalminta mai saukin tudu fari ga gyalenta ma fari tana rike da y'ar karamar Po's silver colour mai stones ga wani irin head da aka nada mata kamar Amarya "_


_" Masha Allah har na matsu kamal ya dora idanunshi akan kyakkyawar matar shi domin nasan sai ya rude "_




_" Zainab ma ba laifi itada Fatima sunyi suma ba karya kowannen su na rungume da baby daya a hannu Small husnah kuwa a wurin Inna suka barta domin tayi wayo tana cin Abincin ta"_




_"Suka shiga mota sai jaji suna tafe suna tattaunawa a tsakanin su" A gaskiya nafara jinkunya yanda zan tsaya a gaban mutane " zan ma iya hangin din rank din kuwa"_?




_"Zainab tace bakomai mun tafa zuwa da Abban husnah nagani ba wani wahala kawai ki kwantar da hankalin ki "_




_" *JAJI MILITARY CANTONMENT*_
_That is the House of infantry soldiers*_




_"Kallon gate din kawai takeyi tana tuna sati daya data shigo nakuda ta balle "_




_" Sai kusa da babban katon dakin taron ya Ajiye su ya zagayo ya bude wa matar Oga kofa ta fito sannan ya budewa su Zainab "_


_" Shi ya jagoran ce su zuwa cikin dakin taron "Sun samu jama'a da dama manyan sojoji da kuma matansu kawai uban gayya ake jiran isowar shi"_




_" Wato chief of Army staff, Kamal na ganin Shigowar su ya taso da hanzarin shi ya tarbi uwar gidanshi wani irin kallo yake jifanta da shi kamar ya rungume ta saboda ta gama ta fiya da dukkan tunanin shi "_




_" Kujera ta musamman ya nuna musu ya karbi Babyn shi daya bayan daya yayi kissing dinsu "_




_" Gaba daya Abokanshi sun taso domin ganin kyautar da Allah yabashi sunata yimata sannu madam "You are blessed"_


_" Yes I believed them husnah is blessed" ga yara uku ga Karin girma sannan gashi Ankwaso kudi a Sudan Allahu Akbar "_


_*ware are you military wifes ?"u no how it feels*_


_" Kowa sai son barka yakeyi kowa dake wurin yasan zun zama star abin kallo da kuma burgewa wasu har kyauta sukeba yaran na rafofin kudi "_




_" Yana like da su yana faman shigewa matarshi ita kanta kallonshi take yi cike da so da burgewa a cikin green kakinshi wannan shine karon farko data tafa ganin shi cikin irin wannan kakin sai ya mugun burgeta fiyeda Wanda tasaba ganin shi aciki"_




_"Ya duk'a Ahankali zuwa saitin kunnen ta batareda ya damu da jama'ar dake wurin ba " ko su Zainab_




_"Madam banyi kyau bane irin wannan kallon? kallon shi tayi tareda Sakin wani irin kayataccen murmushi " tace kayi kyau sosai har ma nafara jin kishi "_


_" Kaga wasu y'an mata nata kallar min kai' tafada tareda matse fuska " yayi murmushi yace "_




_" Husnah duk macen da kenan tasan ni mijin Hajiya Husnah ne tasan sai yanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login