Showing 27001 words to 30000 words out of 104433 words

Chapter 10 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf

Advertisement

arba da santala santalan
cinyoyinta, baccinta take hankali kwance, magana yafara cikin ransa, to yanzu wannan tayaya
zakai tunanin yimata maganar sallar da akeyi raka'a biyu ga sababbin aure? Kallanta yasakeyi sosai, Diyana tanada komai da d'anamiji yakeso awajan mace but ba yarinyar
kirki bace, kuma may be hakanne yasa take tallar jikinta awajan sauran maza

Bata son haske inde tana bacci, ko yaya taga haske tofa zata farka, yanzu ma cikin magagin
bacci tabude idonta taganshi a tsaye yana qare mata kallo
Cikin ranta tace jikinnan dai haka za'a ganshi abarmin kayana
Tashi tayi zaune, har towel din yana kwance wa kana iya hango nashanunta takalleshi tace
"Yawwa nace ba, idan kagama kallon ka kashe min wutar dakin please, banasan haske idan ina
bacci"

Tana fadar haka tayi juyi ta rufe idonta, Adam kuwa kunya ce ta kamashi, karfa yarinyar nan tayi
tunanin neman wani abu yazo wajan ta, tsaki yaja, yafice daga dakin ko kashe wutar baiyi ba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Ilham kuwa tunanin Nihla take tayi, tayi shiru ita kadai agidan, gashi kowa yatafi Babu kowa,
tashi tayi tarage kayan jikinta tafuto falo ta kunna kallo ko Allah zaisa ta daina tunanin, gashi
tabar wayarta agida bare ta kirata

Tana kwance akan kujera tana kallo har bacci yayi awon gaba da'ita
Angon nata kuwa yana can awajan Abba Yaqi yataho gidan, daqyar yataho gida ganin karfe
daya tana neman yi, harda ledar kaza a hannunsa
Yana shigowa falon yaji qaran tv, falon yakalla tsarin komai yayi masa yanda yadace
Can yahangota tana bacci akan kujera, 'yan qananun kitson da aka mata yayi mata kyau kuma
yafuto mata da goshinta, sai fuskarta tayi fayau

Ahankali yataka yaje kanta ya tsaya, kayan baccin dake jikinta ya kallah kana iya hango yanda
qirjinta yake azahiri, haushi ya kamashi, ya za'ai wannan yarinyar tasaka wannan kayan
tazauna haka tsabar rashin kunya amatsayin sa na saurayin yayarta ‍♀️

Saida yasami dede cinyarta sannan ya d'aka mata duka, cikin firgita tatashi tace "subhanallah,"

Tabude idonta sosai taganshi a tsaye akanta, cikin bacin rai tace "ya Aslam lafiya zakamin irin
wannan dukan Kamar agidan kurame? Kira daya idan kamin ai Zan tashi"

"Ok ke saboda tsabar rashin kunya nizaki koyawa yanda Zan tasheki daga bacci?"

Tayi shiru tana jinsa, sosai taji zafin dukan, ledar hannunsa ta kaza ya wullo mata jikinta yace
"gashinan kici, idan kuma ba zakici ba shikkenan kinyi wa kanki"

Hararar ledar daya wullo mata tayi, tawurgar da ita awajan tayi cikin dakinta tabarshi awajan a
tsaye

Shikuwa da kallo yabita yace "Dani kike zancen"

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"mami bade kinfara bacci ba"

"wallahi nafara bacci Yusif, ina ka tsaya ne baka dawoba?"

"mami naje wani waje ne, ga Ice-cream nataho muku dashi ko zakusha"
Dukda tana bacci hakan bai hanata murmushi ba, wai ga ice-cream yakawo musu, ita da
girman ta ina ita ina wani ice-cream, kawai de yace ga ice-cream na kawowa Nihla
Kokarin tashi take tace "nikam na qoshi Yusif saide Nihla, bari nakai mata"

Cikin sauri ya Dakatar da ita yace "a a a a, mami aikin fara bacci, kiyi baccinki bari nakai mata"

Tace masa "to saida safe"

Daga dakin yafuto kai tsaye yayi dakin da aka bawa Nihla, abin mamaki a zaune ya taddata
tana kallan saman dakin tana hawaye, tana tausayawa Rayuwar ta sosai
Kallanta yayi ya girgiza kansa, sannan yaqaraso cikin dakin
Cikin sauri ta goge hawayen fuskarta tace "Sannu da zuwa yaya Yusif"

Yaji dadin yanda takira sunansa Tsawon shekaru

Zama yayi agefenta kan bedside drower, yakalli abinci agefenta alamun bataci komai ba

Fuska Babu alamun wasa yace "sauko kici abinci"

Babu musu ta sauko, tazauna aqasa, shikuwa be motsa daga Inda yakeba yazuba mata ido
yana Kallanta
Abincin ta dauka tafaraci amma wani irin daci takeji acikin ranta, daqyar take tura abincin,
idonta yayi rau-rau Kamar zatayi kuka, kafin kace me tuni hawaye sun zubo mata, saikuma
tasaki kuka sosai, daga qarshe ma saita saka kanta akan gwiwar ta taci gaba da kuka

Ajiyar zuciya yasauke yadawo kusa da ita Yazauna har tana iya juyo hucin numfashinsa akusa
da ita

Haushi ya kamashi, yace "kuka kike akan mijin naki ne?"

Cikin sauri tadago kanta ta kalleshi, sai ganinsa tayi dab da ita Kamar zai sakata cikin jikinsa,
nan take yayi mata kwarjini, ta girgiza masa kai tace "a a Anty"

Ajiyar zuciya yasauke, yace "to kici Abincin Karki zauna da yunwa"

Abincin tafara ci amma hannunta sai karkarwa yake, gashi Yazauna dab da ita, duk atakure

take tarasa yaya zatayi
Shikuwa ganin haka yasa yakai hannunsa kan nata hannun yariqe, sannan yadauki spoon din
da daya hannun yafara bata abaki, babu musu take karba tanaci, cikin zuciyar ta fal tunani,
kulawar da dan'uwanta ya Abba yakamata yabata, bebataba amma gashi wani bare yanayi
mata
Saida ya tabbatar taqoshi sannan yabata ledar ice cream din daya shigo da ita yace "ga
wannan, idan bazaki iyasha yanzu ba, ga fridge nan kisaka gobe sai kisha"

Daga masa kai tayi, yatashi tsaye yace "saida safe"

Daga nan yafice Yarufe mata dakin


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tun tana jiran zuwan Ango harta daina tahaqura, girman gidan yasa takejin tsoro sosai, gashi
bakajin qaran komai, shiru garin, haka tatakure waje daya afalo cikin kujera har bacci yadauketa

Shikuwa fauwaz yanacan mashaya, da temakon Allah da temakon wani abokinsa da sukasha
tare yadawo gida, dirin motar da taji ne yasa tatashi afirgice, Agogon falon ta kalla karfe biyu da
rabi, tashi tayi tsaye cikeda tsoro
Yana tangadi irinna yan maye yashigo cikin falon, gabanta yafadi, tunda take bata taba ganin
mutum murararan cikin maye hakaba sai yau, gadan-gadan yataho wajanta tana ja da baya, har
yazo gab da ita, cikin muryar maye yace "keeeee..uban waye yakawo ki nan eh?"

Girgiza masa kai tafara tace "yaya Fawaz Dan Allah kayi hakuri"

Idanunsa yake son budewa sosai amma yakasa, yayi tangal-tangal zai fadi qasa tayi sauri
tariqeshi aikuwa saiya dawo kanta gaba dayansa, dagashi har ita sukai baya suka fada kan
kujera, shine akanta ita kuma tana qasa, tureshi tafara kokarin yi amma yamata nauyi sosai,
shikuwa jinshi Akwance yasa nan take yafara bacci, kansa ta kalla taga yadora shi akan qirjinta,
nan tafara ture masa kansa, amma saiyayi juyi ma yaci gaba da baccin sa
Haka ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, wai ita Dida itace qato Akwance akanta, wannan
Baqin ciki da yawa yake

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Da asubar fari yafarka daga baccin da yake, amma Idanunsa a lumshe bai budesuba, qamshin
turaren dayake shaqa Mai dadi ne yasa cikin sauri yabude idonsa, da fuskarta yafara tozali,
mamaki ya kamashi, laushin dayaji akansa ne yasa cikin zabura yadaga mata qirjinta
Tashi yayi tsaye yana qarewa yarinyar kallo, gaba daya kunya ta kamashi, yaushe ya aikata
hakan? Yarinyar nan shi tunda yake ko kallo bata isheshi ba ko a family house dinsu, amma

tayaya zaizo cikin maye ya kwanta a qirjin yar mutane d'ame d'ame?
Cikin borin kunya ya wanka mata mari

Azabure tatashi ta dafe kumatunta, qwallah tacika idonta, cikin tsananin mamaki tace "ya Fawaz
menama?"

Yace "ashe dama ke ana ganinki shiru shiru ke 'yar iska ce bansaniba? Ni zakizo ki kwantawa a
jiki?"

Hawaye ne suka zubo mata tace "ya Fawaz kaine fa kaz..."
Kafin ta qarasa magana yace "waye yayan naki? Amma kuwa bakiyi sa'ar yaya ba, ki kirani guy,
bawani fauwaz kingane ko?"

cikin dakinsa ya shige fuuuuu, yana zuwa ya zauna akan gado yadafe kansa,‍♂️ Allah ya soshi
ya qwaci kansa awajan yarinyar nan

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"Ibrahim tunda auren yarinyar nan bai iyuba ai bekamata tazauna hakaba ko, yakama ace
takoma makaranta"

Baba yadubi Alhaji Isma'iel "to Alhaji wacce makaranta zatayi, kawai tazauna haka har Allah
yakawo mata miji tayi aure,"

"A a Ibrahim ba za'ayi hakaba, yarinya zata fara karatu idan Allah yakawo mijin sai tayi aure,
akwai maqocina me wannan gidan na hannun damana, already nayi magana dashi, yana aiki a
university, yanzu kaje ka dauko min takardun yarinyar Zan bashi, saiya nema mata admission
takoma school kawai "
Baba yayi shiruuu, sai can yace" Alhaji da wanne baki Zan gode maka? Alhaji kayimin kayiwa
yata? "

" kada kadamu Ibrahim, ai anzama daya "

Alokacin baba yaje ya bincika kayansa yadauko takardun Nihla, yakawo masa, adede lokacin
akayi wa Alhaji Isma'iel din kiran gaggawa daga office dinsa,Dan haka yakira wayar mamy yace
taturo masa da Nihla, a lokacin suna kitchen suna aiki tare, har Nihla tafara sakin jiki da mamy
saboda yanda take janta da fira Tana fadawa Nihla, tadauki hijabinta dogo tafuto compound din gidan wajansu
Har qasa ta tsugunna tace "gani baba"

Alhaji Isma'iel ya kalleta yace "yawwa yata, kije nan gidan kikaiwa matar gidan takardun ki kice
inji ni, tabawa mijinta su"

Cikin ladabi ta karbi takardun tafita

Tana fita taga unguwar shiru Kamar Babu kowa, kowa yana gidansa yana sabgar gabansa
Ilham ce tafad'o mata arai, cikin ranta tace Allah sarki Ilham ko ya take yanzu?


"kaga Mazawaje, nagaji da wannan halin naka, saina dinga kiran wayarka amma kashareni?"

karo sukayi da juna, har wayar dake hannun wadda take wayar tafadi qasa
Matar tace "subhanallah, qanwata me kike tunani haka har kina bigeni? Bakya kallan gabanki
ne?"

Nihla de tayi shiru tana tunani, inde ba kunnuwanta ne suka jiye mata qarya ba, to tabbas taji
wannan matar tace Mazawaje, to dawa take waya acikin family dinsu? Dawa take waya acikin
samarin dake Mazawaje family? Koda yake may be da d'an wani family din take wayar

Ganin matar ta girmeta yasa tace "kiyi hakuri Anty, wallahi ban kula bane"

Ita kuma matar jin angirmama ta ance mata Anty yasa lokaci daya taji yarinyar ta shiga ranta

Tayi murmushi, tadafata tace "kada ki damu qanwata, kema anan layin kike ne?"

Nihla tace "eh, bamu dade da dawowa ba, kinga gidan mu can"

Matar tace "laaa ai nasan gidanma, to dafatan de zamu dinga zumunci, menene sunanki?"

Tace "sunana Nihla"

Itama tace "ayya suna Mai
dadi, nikuma sunana NADIYA"






tofa wata sabuwa, anya wannan zumunci zai dore kuwa?

Shin Nihla ta gane Wacece Nadiya kuwa?


Duk kuci gaba da bibiyata, nagode

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/22, 1:47 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

19&20

Murmushi Nihla tayi "Allah sarki Anty Nadiya, nagode, bari inje an akenine"

Gidan tawuce zata shiga Nadiya tace "to ai gidanmu ne, Dan haka tare zamu shiga"

Daria sukayi gaba dayansu, sannan suka shige gidan

Nadiya ta lura yarinyar akwai abinda yake damunta, tabbas akwai damuwa a atattare da ita,
amma zata jata a jikinta har taji damuwarta, Dan ita kam haka kawai taji yarinyar ta kwanta
mata, Kamar qanwarta kasancewar batada qanwa mace sai namiji

Nihla tabawa maman su Nadiya takardun, cikin murmushi takarba tace idan yadawo zata bashi,
daga nan Nihla tayi musu sallama tafuto, amma fafur Nadiya tahanata tafiya, qarshe ma dakinta
tajata suna fira kadan kadan, Nihla ta lura Nadiya Babu ruwanta, gata da son mutane, Tun tana
dari-dari da ita harta sake sukayi ta fira Kamar sun saba
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune suke su uku Sunayin break fast, mamy tadubi Alhaji Isma'iel tace "Alhaji Nihla fa batada
kayan sakawa sosai, sannan Babu waya ahannun ta irinta 'yanmata,kuma ace wannan
kyakykyawar yartawa Babu waya Alhaji, yanzu idan tafita ta samomin siriki wacce number zata
bashi?"
Yusif yana jinta, ahankali ya kalleta, yamaida hankalinsa kan Abincin dayake ci

Alhaji Isma'iel yayi Murmushi, yaga alama hajiya tanaso ta maida yarinyar tata Babbar yarinya
yace"to hajiya ai ga yayanta nan, suje su siyo duk abinda takeso, idan sun kawo kinga akwai
abinda babu saikiyimin magana asiyo mata "

Dadi yakama Nihla ta kalleshi tace"Nagode Dad"

"Babu godia a tsakanin mu Nihla, sannan ga albishir ki shirya zuwa next week zaki fara zuwa
makaranta, saide kuma zaki bar mamynki da kewa"
Daria sukayi gaba dayansu

Suna gama cin Abincin suka tafi shopping ita dashi, suna tafiya ahanya Babu Wanda yakewa
dan'uwansa magana, shi har yanzu maganar mamy ce take masa yawo a zuciya, wai saboda
tabawa samari number Hmm

Ita kuma Nihla ganin Yaqi bata fuska akan maganar yasa itama tayi shiru

Har sukaje super market din ataqaice yace mata "Futo"

Babu musu kuwa tafuto, sukayi ciki

Dogayen riguna suka diba, masu shegen kyau, saida suka duba Wanda sukayi mata dai dai
sannan suka dauka, inde yaga kalar riga zata karbi fatar jikinta saiya dauka yaqara musu, har
mamaki yake bata
Da sukaje wajan kayan kwalliya komai Set yake dauka
Kallansa tayi "yaya Yusif sunyi yawa fa"

Yace "zaki dade kina amfani dasu"

Daga haka bata qara magana ba, suka koma wajan perfume dakuma inner wears, Kallanta
yayi, yanzu kam bashida damar dazai zaba mata, yace "dauki mutafi"

Kunya ce ta kamata, haka ta matsa taba zaba, da yaga tana kunyar sa saiya kauce yabar wajan

Atamfofi kuwa sun kwashe su sosai, sannan suka tafi shagon saida wayoyi

Anan ma Kallanta yayi yace "wacce iri kikeso?"

Tace "irin tawa tada, iphone ce"

Haka nan yaji zuciyarsa tana zargin cewa mijinda zata aura ada ne yasiyamata wayar, cikin
kishi yace "dole sai irinta?"

Itama da taga fuska ad'aure Babu alamun wasa sai tace "A a, ko wacce ma asiya inaso"

Babu musu yasiya mata Babbar waya Qirar Huawei

Sannan suka dawo gida da kaya niqi-niqi

Mamy suka samu afalo tana ganin su tare taji dadi, harga Allah tanason Yusif da Nihla, anan
Nihla tabata kayan itama tana gani

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin satin mahaifin Nadiya yanema mata admission a wata private university, Base university,
yayan manya ne acikin makarantar kowa tanajin kanta ita watace, gayu kuwa ba'a magana, ko
wacce mace tanaji da tata wayewar
Direban gidan zai kaita yadawo da ita, saide kawai zuwa take, amma bata gane komai,
damuwar datake ciki ma ta isheta, gashi babu wanda zatai sharing damuwarta dashi bare ta
cire maganar datake ranta abata shawara ko zataji dadi baba yahanata kiran kowa na kano
Ahankali sabon su da Nadiya yake qaruwa harta kai kowa yana ziyartar kowa acikinsu

Yauma bayan tadawo daga makaranta tana daki tana duba hand out, Nadiya ta kirata awaya
suka gaisa sannan sukai sallama, dena karatun tayi tafuto falo, anan taga mamy tana zuba
danbun nama dayawa acikin wata roba, tace "mamy wannan ina za'a kai?"

"Na yayanki ne, zai tafi dashi yanzu"

"mamy ina yaya yusif din zaije?"

Murmushi tayi, ganin yanda Nihla tayi mata Tambayar cikin sauri haka, tace "china zai tafi,
akwai aikin dayake son yayi"

Jikinta ne yayi sanyi, ahankali ta karba tace "to mamy kawo nazuba masa"

Bar mata tayi, tazuba masa sannan tace "mamy bari nakai masa"
Bata jira amsar mamynba tayi hanyar dakinsa, akaro na farko Tun zuwan su gidan

Turawa tayi ta shiga dakin nasa da sallama, yana zaune yana hada kayansa acikin truly

Ya amsa mata batare daya kalli Inda takeba, zama tayi akusa dashi tace "ya Yusif gashi inji
mamy"

"ajiye anan" abinda yace mata kenan

Ta ajiye masa, zuciyarta tana karyewa Kamar zatayi kuka, duk sai shamata kunu yake tunda
yadawo, wai ita ya sukeso tayi ne?

Dauka yayi yasaka acikin jakar tasa sannan yatashi tsaye yace "idan kinsamu time kuje keda
Nadiya abude miki account idan kina buqatar kudi saiki kirani ki fadamin, zan tafi yanzu, may
be nadawo dawuri"

Yana fada mata haka bakowa ne yafado mata araiba sai ya Abba, duk alamomi sai yanzu suke
nuna mata cewa dama ya Abba baya santa, itace takasa gane hakan soyaiyar sa ta rufe mata
ido, duk su ya Usman Babu abinda basuyi mata lokacin data dawo kano, kowa yana nan nan da
ita, amma shi ya Abba itace take nan nan dashi, � Gashi shima ya Yusif yadawo amma bata bashi kulawar komai ba sai shine yake hidimta mata,
batasan lokacin da hawaye yazubo mataba, ahankali ta miqe tsaye tafada jikinsa tana sakin
wani irin kuka abaiyane

Qam Yusif yaqame a tsaye, shibe tureta ajikinsa ba, shikuma bai saka hannu ya rungumeta ba

Kuka take sosai har hawaye yana d'isa agaban rigarsa

Wata irin ajiyar zuciya yasaki, sannan yasaka hannu ya rungumeta gaba daya, yana bubbuga
bayanta, wani irin yanayi ya tsinci kansa aciki, Wanda bai tabajin irinsa ba, cikin kasalalliyar
murya yace"kiyi hakuri mana kiyi shiru, menene na kukan? Me aka miki?kokuma Wanda zaki
aura kika tuna? "
Girgiza kanta tayi, tace" dan Allah kayi hakuri, kadena fishi "

Yaga alama idan akaci gaba da tsaiwa ahaka to yarinyar nan zatasa yayi mata ba daidai ba,
Dan haka ya janye tadaga jikinsa, yace" ya'isa to, ni bana fishi dake, kuma kece yakamata
nabawa hakuri, tunda kina ganina kika share ni, saboda kin samu wani"

Wasa tafara da yatsun hannunta tace "kayi hakuri, kuma ba kullum saina kiraka ba, amma
wayar taqi shiga"
Tafadi haka cikin shagwaba

Murmushi yayi "to naji, komai yawuce, yanzu Muje ki raka yaya Yusif zai tafi kada yayi missing
flight, but banda bawa samari number, kinji ko?"

Daga masa kai tayi, tace "to"

Sannan ta janyo masa jakar suka futo daga dakin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login