Showing 78001 words to 81000 words out of 104433 words

Chapter 27 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf

fara karbar wani irin saqo, wani irin zirrr yakeji
tundaga tafin qafarsa har zuwa kansa, kansa yasake turawa cikin wuyanta yana shaqar wani
sihirtaccen qamshi dake tashi a jikinta, bayaso yadena jin abinda yakeji ajikinsa, baiqi ace su
dauwama ahaka ba, ahankali yadago bakinsa, yadora Dan qaramin lips dinsa akan kunnanta
yana gatsawa Ahankali

Wani irin numfashi Nihla tasaki, gabobin jikinta suka saki lokaci daya

Motsi tafara tanaso taraba jikinta danasa, cikin shagwaba tace "ya Abba please kasake ni
mana, Momy fa zata iya zuwa"

Wata irin murya yayi magana da'ita, wadda tunda take dashi bata taba Jin muryar sa hakaba,
cikin shagwaba yace "to kice kin yafemin mana please "

Ahankali ta zare jikinta daga nasa ta kalleshi tace "ya Abba kenan, kada kadamu, nayafe maka,
komai yawuce kaji ya Abba na, duba kaga yanda ka rame, Pls kasaki ranka kaji?"

Yace "da gaske kike kin yafemin?"

Tace "ya Abba, nace nayafe ma, komai yawuce fa, Muje ka rakani unguwa...."

Cikin sauri yafarka daga mafarkin dayake
Sakamakon qaran wayarsa data tashe shi, a dalilin wani abokin aikinsa dayake kira


Kansa yadafe da hannunsa duka biyu ya furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un..." ‍♂️

Jikinsa yataba yaji zafi sosai, ga kansa dake sara masa, zuciyarsa ce yaji tana tashi, cikin sauri
yasauko daga gadon yanufi toilet yafara kwara amai, babu komai acikinsa sai riqe cikin sa yake
ga ciwon kai, ga zazzabi, haka yadawo ya kwanta agadon, yanzu duk abinda yafaru dama
mafarki yake? Ya Allah!
Saida yaji dama dama sannan ya koma toilet din yayi wanka, yadauro alwala yafuto, jallabiyar
sa yasaka fara qal da ita, sannan yatada kabbarar sallah, yadade yana sallah sannan yadaga
kansa ya kalli agogo yaga sha biyu da kwata

Ahankali yamiqe, yafuto daga dakin nasa, kai tsaye dakin Nihla yanufa, wannan shine karon
farko daya fara shiga dakinta

Ahankali yatura kansa cikin dakin, tana kwance agado wayarta da ya yusif ya aiko mata take
gani, tana sanye da riga da wando na bacci, wandon ko gwiwar ta baizoba, rigar ma batada
tsawo hakan yasa fararen cinyoyinta suka fara futowa

Ganin mutum kawai tayi akanta, cikin sauri tatashi zaune tace "subhanallah... Ya Abba lafiya?"


Ahankali yake ta kowa har yazo gabanta, ganin yana nufota yasa taja blanket din kan gadon
tadora a jikinta

Bai tsaya a ko'inaba saida yazo saitin qafafunta, yazuba gwiwar sa aqasa har kafarta tana
gogar gwiwar tasa

Shiru yayi yazuba mata ido yana Kallanta, Bece da ita komai ba

Nihla sai kallan mamaki take masa tace "lafiya ne?"


Ahankali, cikin sigar rada yace "kiyi hakuri"

banda dare ne kuma su kadai ne a dakin Babu abinda zai hana takasa jin Mai yace

Tace "for what"

"for Everything, please kiyafemin, nakasa bacci, hankali na yakasa kwanciya, meyasa bazaki
yafe minba Nihlaaaa" ya qarasa maganar yanajan sunanta

Shiru tayi masa batace komai ba, Yakalleta yaci gaba da cewa "nasa ranki yabaci saboda
nafasa miki wayarki, kiyi hakuri, insha Allah bazan sakeba, but kidena waya agabana, raina
yana zafi, idan kikaci gaba dayi zan'iya fasa gaba dayan wayoyin hannunki, Allah ne yasakamin
kishin ki acikin zuciyata, bazan dena ba kuma saboda ina qaunar ki, Nihlaaa! kidubi girman

Allah kiyafemin, kisoni"

Kallansa tayi, mamaki ya kamata, lalle ya Abba

Ahankali tace "idan kagama inaso Zan kwanta, a tunani na mun dade da gama wannan
maganar, babu abinda yayi saura bayan wannan"

Tana fadar haka takwanta, tajuya masa baya sannan taja blanket dinta tarufe jikinta dashi gaba
daya

Bayanta ya kalla, yau shi Nihla take juyawa baya, shine yasa kafarsa aqasa yana neman
yafiyarta amma taqi, yau shida Nihla takeso shine takasa bashi soyaiyar ta akaro na biyu

Dumin dayaji akan kumatunsa ne yasa yagane hawaye ne suka zubo masa, ahankali yasa
hannu ya share, yamiqe yafuto daga dakin tareda ja mata kofar dakin

Yadade awajan ya tsaye idonsa arufe, tsayuwa ma neman gagararsa take, cikin damuwa ya
juya yana tafiya ahankali Kamar zai fadi, yayi hanyar dakinsa

Momy ta duba gefenta taga Alhaji yayi bacci, ahankali ta sauko daga kan gadon tafuto daga
dakin nasa, Allah nagani bazata iya runtsawa batare dataga halinda yaranta suke ciki ba, dakin
Nihla tafara zuwa taganta tana bacci amma wutar dakin akunne, tasa hannu ta kashe mata
wutar sannan tajuya, Nihla tana jinta, saboda ba bacci takeba
Dakin Abba tanufa, tana budewa taganshi azaune atsakiyar gadonsa yana kuka wiwi

Gaban Momy yafadi, cikin sauri ta qarasa wajansa tana fadin "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un...
Abba!!"

Tana qaraso wa wajansa yafada jikinta, kansa tashafa tace "me yafaru?"

Ahankali yazame yadora kansa akan cinyarta, cikin kuka yace "Momy bata sona, naje wajanta
yanzu taqi kulani, Momy zuciyata zafi take min, rannan ma nabata hakuri taqi kulani Momy,
yanzu ma haka,Momy ya zanyi? Wallahi ina sonta, kowa Yaqi bani goyon baya, shikkenan ni
Kowama ya tsaneni..." hannu tasa tarufe masa baki
Ahankali tace" kayi hakuri Abba, kadinga maimaita kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,
insha Allah zakaji sanyi aranka "

Beyi musu ba haka yafara fada cikin ransa, Momy tana shafa kansa, tunani fal ranta, ahaka
sukai bacci, Momy de baccinta ragagge ne, amma shi ya danyi kadan

Kiran sallar farko ne yatashe su, taji jikinsa da zafi, tabashi magani yasha sannan yatafi

masallacin gidan, ita kuma ta nufi dakin Daddy



Bayan an idar da sallar asuba Momy bata koma bacci ba, addu'ah taci gaba dayi har gari
yawaye tashiga kitchen da kanta tafara hada musu break fast

Karfe tara da minti uku tagama komai, takai musu kan dining, har lokacin Nihla bata futoba da
alama bata tashi ba, Abba ma haka

Hanyar dakinta tanufa zataje ta watsa ruwa wayarta tayi qara, duba me kiran tayi mamaki ya
kamata, afili tace "Mai hakuri!"

Sannan tadaga wayar, bayan sun gama gaisawa baba yace "hajiya dama maganar yar taki ne"

Tace "to Allah yasa de bamuyi laifi ba,"

"A a bakuyi laifin komai ba, jiya de munzauna da mahaifin Yusif dakuma yan'uwana dasuke
yalleman, anyanke ranar bikin yartaki nanda wata biyu masu zuwa insha Allah, saiki fada mata,
sannan kuma idan ansamu lokaci Zan turo muku da naku goron saka ranar saiki rabawa
mutanan gidan "
Jikin Momy yayi sanyi sosai, cikin sanyin jiki tace" to shikkenan Ibrahim, mungode sosai, Allah
yasa ayi damu, insha Allah zan sanar mata itama idan tatashi, yanzu tana bacci "

Yace" to shikkenan hajiya, ki gaida mutanan gidan "

Daga nan sukai sallama, Momy ta zubawa wayar ido tana kallo, wannan al'amari yafara bata
tsoro fa, qamshin turaren daya saka ne yasa tadago kanta da sauri ta kalleshi, sanye yake cikin
qananun kaya dasuka karbi jikinsa, ta kalli fuskarsa tayi fayau, kana ganinsa zaka hango
tsananin damuwa a tattare dashi, tace "Abba na katashi?"
"yes natashi Momy, good morning"

Bata kula da gaisuwar dayake mata ba tajashi har dining tace "zoka zauna nabaka abinci, duk
idonka yafada, kacire damuwa aranka fa"

"A a, Momy, bazan iyacin komai ba, kibarshi kawai, inaso zanje saudia, may be nadawo after 3
day's, Momy nasan Daddy yana fishi dani, Kibashi hakuri, kifada masa naje saudia"

Tausayinsa ya kamata, duba yanda yashiga damuwa ahaka ma baida labarin saka mata rana,
ahankali tace "saika dawo, zan sanar dashi, amma kayimin alqawarin zaka kula da kanka"

Badan yaso ba ya qaqaro Murmushi yace "insha Allah Momy"

Ahankali yatashi yafita daga falon Momy tabishi da kallo jiki a sanyaye





Sharhi please











Amnah El Yaqoub ✍️
[7/11, 11:52 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}


Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


49&50


Tasan cewa ba komai ne zai kaishi saudia ba saidon saboda damuwar dayake ciki
Kuma hakan ma tunani ne Mai kyau, domin kuwa addu'ah ita kadai ce mafita Awannan halin da
yake ciki, ta Inda yake birgeta kenan, kokadan baya Manta Allah acikin dukkanin al'amuransa

Dakin Daddy tawuce domin sanar dashi yanda sukai damai hakuri

Tana shiga taganshi yafuto daga wanka yana shirya wa

Waje tasamu tazauna agefen gadon tace "Alhaji barka da tashi"

"yawwa Rahma"

Tasake dubansa tace "Alhaji kana nunawa al'amarin yaron nan Kamar bai dameka ba, kuma
yana cikin matsala sosai fa, jiya kasa bacci yayi, ita Nihla taqi amince wa dashi, kai yazo da
maganar ka koreshi, yanzu haka jikinsa Babu dadi yatafi saudia nasan kuma saboda hakan
yatafi, dazu Mai hakuri yakirani yace ansawa Nihla rana nanda wata biyu bikin "
" daidai kenan "

Cikin sauri ta kalleshi tace" Alhaji,yakamata aduba wannan al'amarin, bazai iyu nasamu yarinyar
nan da batun taso danaba, Kamar na tursasata ne, tunda batayi niyya ba"

"kinsan da hakan kikazo kikemin magana, ni mezan iyayi akai?"

"Alhaji kaine kuwa zaka iyayin komai, tunda idan kafada tazauna"

"ba kuma zan fada dinba bare tazauna, angama break fast ne?"

Momy ta kalleshi cikin mamaki, Annabi yayi gaskiya dayace abu uwa har sau uku, sannan yace
uba

Tace "angama"

Sannan tashige toilet domin yin wanka


Zaune suke a dining Sunayin break su uku, Momy ta kalli Nihla cikeda kulawa tace "Dazu munyi
waya da Mai hakuri yace zai aiko mana namu goron"

Dago kanta tayi "Momy goron me?"

Cikin farin-ciki Momy tace "nasaka ranar yata nanda wata biyu"

Cikin kunya tasa hannu ta rufe idonta

Daddy yayi Murmushi ya kalleta yace "saiki Rubutamin list din abinda kike buqata kije daki ki
dauki atm dina kuje keda yayanki kusiyo, abinda Babu kuma saiki shirya kuje Dubai keda
momynki kusiyo Acan"

Kanta aqasa cikeda kunya tace "nagode Daddy"

Momy ma tayi Murmushi cikin ranta tana Jinjina irin yanda Allah yasaka musu qaunar yarinyar

aransu baki daya



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda yaje saudia baije ko'inaba, yana zaune cikin harami yana addu'ah, ya kashe wayoyin
hannunsa, bai nemi kowaba, kuma bayason a nemeshi adede wannan ranakun
Addu'ah yake Allah yakawo masa mafita akan wannan al'amari, idan har Nihla matarsace to
Allah yahuci zuciyarta ta soshi, idan kuma ba matar sa bace Allah yabashi hakuri da juriya akan
rashin ta, Allah kuma yasa hakane yafi alkhaairi a gareshi

Sosai yaduqufa wajan neman zabin Allah, yana kaiwa Allah kukansa saboda shine Mai kowa
Mai komai,kowa ya juya masa baya, banda 'yan'uwansa da Aslam Babu Wanda yake sonsa da
Nihla, sai kuma Momy datake tausaya masa, abinci ma ba sosai yake cinsa ba, gaba daya ya
rame cikin kwana kin, ya lalace, ga qirjinsa dayake masa zafi sosai idan yatuno da cewa Nihla
tayiwa baban ta maganar Yusif, jiyake Kamar ana zuba masa barkono acikin qirjinsa

Allah shine gatansa a yanzu, bashida wani gata daya wuce yakai kukansa wajan mahaliccinmu

Daren juma'ah kuwa yayi addu'ah sosai, yayi kuka yayi kuka harya gaji, sannan cikin dare
yabiyo jirgi yadawo gida, su kansu su Momy basusan yadawo ba, saboda Saukar cikin dare
yayi



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune yake afalon shi kadai, yana sanye da three quater, da wata riga marar hannu, computer
ce agabansa yana ta typing cikin sauri, gaba daya hankalinsa ya tattara shi akan abinda yakeyi

Momy ce tafuto falon sai ganinsa tayi, ta tsaya tayi turus, tace "Abba na yaushe kadawo Babu
sanarwa?"

Dagowa yayi daga typing din dayake yadubeta "Momy cikin dare nasauka, bansan na tasheku
ne shiyasa banje dakin ki ba"

"to sannu da zuwa, duk wayoyinka akashe, ina kabarsu ne?"

"Momy kashe su nayi wallahi, ina Daddy?"

Zama tayi a gefensa tace "yana dakinsa, yanzu zai futo shima"

Yace "Ok" sannan yaci gaba da abinda yake

Futowa tayi daga dakinta tayi kyau sosai cikin wani Material,qamshin ta dayaji ne yasa Ahankali
yadago kansa ya kalleta, karaf idonsu yahadu, itace tafara janye nata idon, shikuwa Kallanta
yayi yana mamakin canjawar datayi cikin kwanaki hudu, jikinta yayi lumai, sai wani qara cika
takeyi, hankalin ta kwance , sauke kansa yayi yaci gaba da abinda yake

Momy ta kalleta tace "wannan gyaran jikin nasu gaskiya sun iya sosai, idan aka miki na 3week
ma ya'isa, saiki zauna agida kidena fita ko'ina, saiki sanar awajan service din naku ma"

Tace "to Momy"

Ta kalli Abba dake zaune yana typing amma tunani ne da tambaya fal ransa, gyaran jikin me
ake mata? Ko bikin qawarta za'ayi?

Bai samu amsar Tambayar tasaba yaji tace "Ya Abba ina kwana"

Wani irin sanyi yaji aransa, koba komai yana jin dadin yanda take kiran sunansa, gaba daya
jiyake Kamar tafi kowa iya fada
Idanunsa har wani lumshe wa suke yadago yazuba mata wani irin kallo Mai karya garkuwar jikin
yanmata
Cikin kulawa yace "lafiya"

Daga haka bata sake cemasa komai ba, Momy ma taji dadin yanda Nihla koda wasa bata raina
yayun nataba, gashi de Abba bawani shiri sukeba, ba qaunar sa takeba, amma tana bashi
girman sa yanda yadace

Momy tace "Nihla jeki kitchen kidaukomin wannan garon, saiki kaiwa maqota"

Ahankali tatashi, yana jin tashin ta yadaga kansa yabita da kallo, ba komai ne yafi daukar
hankalinsa ba irin hips dinta, Momy ta kalli Abba taga inda hankalinsa yake ta girgiza kai

Saida yaga tashige sannan yasaki wata ajiyar zuciya Mai nauyi, yamaida hankalinsa ga abinda
yake

Murmushi Momy tayi cikin ranta tace oh Abba, babu ta ido, inaga mantawa yake da kowa idan
Nihla tana waje, agefe daya kuma tausayin dannata yana damunta

Goron takawo da alawa Momy tafara yimata bayani "kikai duka gidajen Dan Allah, idan an
tambayeki na menene kifada musu, idan kuma bazaki iyaba kice su kirani awaya"

Tace "to Momy"

Kasancewar unguwar Babu mutane sosai yasa tasaka hannu ta kunce Babban dankwalin
kanta, gashin kanta yazubo gafen fuskarta, tasa hannu ta maida shi baya sannan tayafa
dankwalin a jikinta kasancewar da girman sa, tadauki goron tanufi hanyar fita

Cikin sauri yatashi yasha gabanta yaje bakin kofar falon ya tsaya, daga Momy har Nihla
mamakin yanda yayi tsalle yaje bakin kofar dakin ya tsaya suke

Shikuwa ko ajikinsa yace "haba Momy Dan Allah, ya za'ayi kibarta tafita ahaka, haka kawai taje
tadauko mana magana"

Momy ta girgiza kanta "Abba kabata hanya tawuce mana, menene haka"

Cikin shagwaba yace "gaskiya Momy a a"

Momy ta dubi Nihla tace "dawo ki zauna Nihla, bani goron"

Babu musu tadawo tazauna tareda bata goron

Momy ta kalleshi tace "to tunda ka hanata kaiwa, gashi saikazo kakai"

Yace "wai goron menene ma Momy, saikace masu shirin taro"‍♀️

Momy kanta tsaye tace "goron saka ranar qanwar ka ne, na saka ranar auren Nihla ne"

Wani dummm! Yafara ji akansa, gabansa yafara faduwa, numfashinsa yafara yin sama, daqyar
ya'iya cewa "Momy saka rana kuma?"

Momy data fara tsorata da yanayin sa yace "emana, menene?"

Hannu yasa yadafe kansa dake masa mugun ciwo, qirjinsa ya riqe numfashi yana neman
gagararsa, ahankali yadora dayan hannunsa akan qirjinsa, Idanunsa suka fara rufewa, yafara
ganin duhu-duhu har suka rufe gaba daya yadena gani dajin komai, nan take ya sulale awajan
yafadi
Cikin sauri Momy tayi kansa tana fadin "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un.... Abba!"

Girgiza shi tafara yi amma Babu alamar numfashi awajan Abba, gaba daya Momy ta rikice sai
jijjigashi take, hasbunallah wani'imal wakil... Abinda take guje musu kenan dama, nan take
hawaye ya balle mata

Ta kalli Nihla cikin kuka tace" yi sauri ki kira Daddynku mutafi asbiti"

Da gudu tajuya zuwa dakin Daddy yana zaune yana duba jarida, ganin yanda tashigo dakin
hankali tashe yasa yatashi tsaye da sauri yace "lafiya?"

"Daddy kazo inji Momy"

Cikin sauri yafuto itama Nihla ta biyo bayansa, yana qarasa wa wajanda Abba ke kwance ya
tsugunna yana taba fuskarsa yace "meyasa meshi ne Rahma?"

Cikin kuka tace "Alhaji kaga abinda nake fadama ko? Kaga irinta ko? Babu abinda aka masa,
kawai dagajin ansa ranar Nihla shine yayanke jiki yafadi"

Daddy yace "subhanallah... Kamamin shi Muje asbiti"

Daqyar suka dagashi, suka tafi asbiti baki dayansu, sai adala kawai aka bari agidan

Zuwan su asbiti keda wuya likitoci suka karbe shi cikin gaggawa, suka shiga bashi temakon
gaggawa, Daddy da Momy kam kasa zama sukai, sai Nihla ce take bawa Momy hakuri akan
tadena kukan datake amma ina! Hawaye Yaqi tsayawa a idanun Momy

Sun kusa awa daya da zuwa asibitin sannan likitocin suka futo, cikin sauri suka nufesu suna
tambaya

Babban cikin su yace "kuyi hakuri Alhaji, ku kwantar da hankalin ku, amma Dan Allah ku kiyaye
fadar abinda zai dinga tsorata mutum lokaci daya, yanzu haka danku yaji abinda ya tsorata shi
ne sosai, shiyasa yasuma, kuma dama bugun numfashin sa ba normal yake fitaba sakamakon
ciwon da zuciyar sa take son kamuwa dashi "

Daga Momy har Daddy hada baki sukai wajan fadin
" ciwon zuciya Doc.?

Kai tsaye yace "qwarai kuwa, amma tunda kunzo asbiti insha Allah zamuyi kokarin ganin
yasamu lafiya, yanzu za'a futo dashi a sauya masa daki"

daga haka ya juya yabasu waje

Momy kasa magana tayi daga nan, kawai de tana goge hawayen idonta, kuma har zuwa yanzu
kokadan batajin haushin Nihla, fatanta daya, Allah yabawa danta lafiya


Daddy yakira Alhaji Basiru da Alhaji Baqir ya sanar dasu abinda yake faruwa, nan take suma
suka Garzayo asbitin
Cikin lokaci qanqani jinyar Abba tacika family din Mazawaje

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Aslam yafi kowa shiga cikin tashin hankali, musanman daya tambayi Momy menene yake
faruwa tafada masa komai bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login