Showing 57001 words to 60000 words out of 104433 words
Chapter 20 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
musu de"
Haka sukai ta firarsu cikin jin dadi, kasancewar haduwa tana musu wahala
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Ahankali kwanaki sukaci gaba da shudewa, Abangaren Dida, tunda tasamu ya Fawaz ciwon
cikin sa yalafa tadena damuwa, sabgarta kawai takeyi, domin kuwa itade tana kunya bazata iya
masa komai akan haka ba, cikin Ilham kuwa yaqara girma tana nan haihuwa yau ko gobe, babu
wanda yakai Aslam murna saboda yasan cewa kwana kusa zai zama uba
Yau bataje makaranta ba Inda take service, ta dade tana bacci dasafe sai wajan goma da rabi
tatashi, doguwar riga ce a jikinta ta bacci amma me kauri, rigar batada hannu, sai hula datasa
akanta, tana hamma tafuto falon anan taga Momy itada wani da alama likitane sun futo daga
dakin ya Abba, yanayin Momy ta kalla kawai tasan Babu lafiya saboda yanda jikinta yayi
sanyi,kuma hakan baya rasa nasaba da abinda likitan yafada mata, sallama sukai da Doc din
sannan tajuya zata koma dakin nasa, Nihla tace "Momy lafiya?"
"wallahi Abba ne baida lafiya Nihla"
Tace "subhanallah, Allah yabashi lafiya Momy" tafadi haka tana kokarin juyawa dakinta
Momy ta kalleta da mamaki tace "yayanki baida lafiya, amma kina kokarin juyawa daki? Ba
zakizo ki ganshi ba?"
Turo baki tayi gaba alamar shagwaba, Sannan tabiyo bayan Momy suka shiga dakin nasa, yau
ne karo na farko data shigo dakin Tun bayan barin ta gidan, gaba daya dakin saiya koma mata
sabo saboda ansauya komai nasa
Yana kwance yana bacci, dagashi sai wando three quater, da vest fara qal ajikinsa, kallonsa
Nihla tayi, faffadan qirjinsa gashine kwance, sai Dan qaramin bakinsa daya fara bushewa, ko
menene yake damunsa oho?
Kallan Momy tayi tace "Momy ai bacci ma yake, bari naje nayi wanka kafin yatashi" tafadi
hakanne kawai danta gudu, saboda bata fatan ace yafarka yaganta a dakinsa
Abinda bata saniba kuwa shine idonsa biyu, kawai yana kunyar hada ido da Momy ne, tayaya
zai iya Kallanta bayan fama dayayi da ciwon ciki Tun cikin dare kuma yau doc yazo yace
yakamata ayi masa aure saboda sha'awa datake damunsa, tayaya zai iya hada ido da Momy?
Momy tace "a a, ai hakuri zakiyi da wannan wankan, nasa Adala tahada masa Tea, zanje na
karbo, ki zauna karya farka shi kadai kozai nemi wani abu"
Wannan karan kam, ran Nihla baci yayi, harta kasa boye hakan akan fuskarta, Momy ma taga
yanda yanayin ta ya sauya amma haka tayi shiru tafice daga dakin, taga alama Nihla har yanzu
yarinya ce, yanda takejin ta aranta Kamar su Usman Babu yanda za'ai tadinga Hadata Da Abba
Dan wata manufa, itace ta haifi Abba amma dole zata nuna masa kuskurensa akan abinda
yayiwa Nihla abaya, amma hakan ba zaisa tazuba musu ido tana kallansu suna zaman doya da
manja ba, koba komai dukansu yaranta ne, babu wanda zata nunawa banbanci acikinsu, tana
wannan tunanin ta qarasa cikin kitchen din
Shiru Nihla tayi tana tana zaune akan bedside drower, ko Inda yakema bata kallo, shima yana
jinta a gefensa amma bai bude idoba, asali ma jiyayi bugun zuciyarsa yana qara sauya wa,
kuma yarasa dalilin hakan, yasan cewa a dole take zaune dashi, saboda yanda yake ganin
tsanarsa qarara acikin idonta, yasan kozai mutu bazata kulashi ba
Ahankali wata dabara tafado masa, bari ya gwada, yasan idan yayi hakan dole zata ambaci
sunansa, sannan tabashi kulawa
Ahankali yafara motsi tareda yatsina fuskarsa, cikin alamun ciwo yace "wayyo Allah nah....
Momy... Momy Zan mutu..."
Cikin sauri Nihla ta kalleshi, amma abin mamaki ko sunansa bata kamaba tace "subhanallahi,
sannu"
Haushi yakama Abba, waime yarinyar nan take nufi ne? Murqususu yaci gaba dayi Kamar
gaske, duk ya rikice Kamar bashi ba, handle din dakin da aka kama za'a bude yasa Nihla tayi
tunanin Momy ce zata shigo, kuma tasan fada zata mata tace tana ganinsa ta qyaleshi, hakan
yasa cikin sauri tatashi tadawo gefensa tazauna tana cewa "Sannu, sannu"
Jinta akusa dashi yasa yatashi Ahankali Yazauna, sannan yazuro qafafunsa qasan tiles din
dakin yamiqe tsaye zai shige toilet, yana Miqewa kuwa mararsa ta murda agaske, cikin azaba
yadawo Yazauna, baisan lokacin da yadora kansa akan kafadarta ba, hannunsa kuwa yana kan
cinyarta, gaban Nihla yahau luguden faduwa, itafa tarasa gane Inda ya Abba yadosa, meyake
nufi hakane?
Ahankali yaji maransa tadena ciwo yabude idonsa, amma me? Saiya kasa dauke kansa daga
kan kafadarta, yanda ya kwantar da kan nasa hakan yabawa idonsa damar hango cikakkun
nashanunta farare tas, cikin ransa yace wallahi natane Babu qari, but ya'akayi yarinyar nan
takoma hakane cikin shekara hudu?
Turo dakin Momy tayi tashigo hannunta dauke da cup din Tea, ganinsu ahaka yasa ita kanta
gabanta yafadi, anya Abba kuwa bason yarinyar nan yakeba? Me Abba yake shirin janyo
musu? ♀️
Haka de takawar da tunanin aranta, takawo masa Tea din tace "gashi Abba, tashi kasha Tea"
Ahankali yadago kansa daga kafadarta, cikin dabara ta matsa can gefe dashi tana hamdala
aranta, Tea din ya karba yafara shan ahankali, cikeda shawaga yace"Momy zafi "
Tace" nifa Abba dama ba rashin lafiyarka ba kadinga langabewa mutum kenan, kaiba qaramin
yaro ba amma kadinga shagwaba, kuma wannan gashin na qirjinka ka zauna ka askeshi Dan
Allah"
Dukda yana jin jiki, saida ya danyi murmushi kadan, yasaci kallan Nihla, sai yaga kanta a
sunkunye batama kallansu
Saida Momy tabashi magani yasha sai runtse ido yake alamun bayaso, sannan suka futo daga
dakin itada Nihla
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe tatashi da matsananciyar naquda, daqyar ta'iya kiran Aslam dayake wajan aiki,
yana jin yanayin muryarta yasan ba kalau ba, haka yadawo gida suka tafi asbiti
Tayi doguwar naquda sai cikin dare ta haihu lafiya, tahaifi danta namiji Mai kamada ita sak
Tun asuba labari ya'isa family house cewa Ilham ta haihu, dasassafe kuwa asbitin yacika sosai
da yan'uwa, Nihla kam tafi kowa murna, gata da ihlam haka suke zaune a dakin, sai wajan
la'asar sannan suka dawo gida, amma Nihla sai dare tadawo agajiye, hajiya Na'ila bataga ta
zamaba, tunda akai haihuwar tayi kane-kane akan komai, ko kara bata yiwa hajiya Abida ba,
Wato Maman Ilham
Ita kuwa hajiya Abida abin ma bai wani dameta ba tunda ana kula da yarinyar ai shikkenan, ita
dadi ma taji, tasan cewa hakan alama ce ta Ilham din tana zaune da sirikarta lafiya
Bayan kwana bakwai aka radawa yaro suna Abubakar Wato Abba, suna kiransa da lil Abba
Da yamma ta shirya tsaf cikin riga da siket na leshi, Mai launin dark blue da sirkin fari, qananun
kalba ne akanta, da kanta ta tsara kwalliya taci daurin dankwali Mai kyau, ta tattare kalbar tata
tadaureta abaya, wayarta ce take qara taqi dauka, su Dida ne suke kiranta Tun dazu, tasan
kuma bazai wuce suce basu ganta ba
Saida ta shirya tsaf sannan tayafa mayafin ta Dan ma dedeci tafuto falo, hayaniyar su ya
Usman take juyowa a dakin ya Abba, tace to wannan yaushe sukazo, gefenta ta kalla taga wata
waya qirar iphone tayi Murmushi tadauka tace may be ta ya farouq ce, tana daukar wayar kai
tsaye tatafi camera tadinga yin Selfie masu shegen kyau, sai Style take qarawa tana yin
pictures din, saida tagama sannan ta ajiye wayar ta qwalawa Momy kira
Sai gata tafuto daga dakin ya Abba ita dasu ya Usman ashe ma tare suke, suna futowa farouq
yace "kai kai kai, ina zakije haka Kamar Wanda zakije wajan gasar sarauniyar kyau?"
Murmushi tayi, tace "ya farouq gidan suna Zan tafi"
Ya Usman yace "gaskiya wannan wankan nawa ne"
Murmushi tayi batace komai ba, Aliyu kuwa baiyi mata magana ce kawai de yana murmushi
cikin ransa yana yaba kyawun surar yarinyar
Shikuwa Gogan abakin kofar dakin nasa ya tsaya hannunsa zube cikin aljihun wandonsa, yana
qare mata kallo Bece dasu komaiba, yatsani yaga tanayiwa mutane murmushi saboda yanda
take yin mugun kyau, musanman ma yanda dimple dinta suke futowa
Fuskarsa adaure Babu alamun wasa yake kallanta, amma yakasa cewa uffan
Momy ta kalleta tace "masha Allah, yanmatan Momy kinyi kyau sosai, bari na gyara miki daurin
dankwalin naki"
Nihla ta tsaya Momy kuwa ta qara gyara mata daurin, sannan tayi mata sallama tatafi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Gidan suna yayi albarka sosai, Mazawaje family duk sunje, iyayenne mata kawai basujeba,
saikuma 'yan'uwan mahaifiyar ta suma duk sunje sosai, maijego tana shiga cikin kayaiyaki na
alfarma itada Baby
Har dare yayi anata hidima sannan mutane suka Dan rarragu, duk wannan abun da ake jikin
Dida asanyaye yake, sai bayan mutane sun watse ne da daddare Nihla take cewa "Dida
meyake damunki ne Tun yamma kinyi shiru"
Tace "tunanin ya Fawaz nake, ina tsoron karyaqi shan ma ganinsa"
Diyana tace "Dida kina shagwaba ya Fawaz wallahi, koda yake soyaiya ce, rannan ma munyi
waya da mum take cemin tabawa driver yakawo miki jakar ki tunda kintafi Babu sallama"
Murmushi tayi kawai
Ilham tace "kice anaji da yayan nawa, toki sakarwa dan'uwana jiki de yamore ehe"
Diyana tace "um, nikam danba qara, Tunna farko bansake yarda ba"
Nihla tace "waiku Dan Allah miye hakan, kawai saiku dinga yin wannan firar agabana, salon ku
lalatani"
Dida tace "kwana nawane kema Nihla, ai Kamar yaune"
Diyana tace "ke gwauruwa waye zaizo yadauke ki ne? Kingani ya Adam zaizo, kuma Dida ma
nasan ya Fawaz zaizo"
Tace "nikam driver, dama shiya kawoni"
Itama Diyanan tace "wai kina nufin ya Abba ba zaizo yadauke ki ba?"
"ya Abba fa kikace, ashe kuwa saide na kwana anan, keni fa ko magana bamayi, kowa
harkarsa yake agidan nan infada miki"
Ilham tace "haba Nihla, ya Abban kine fa, kudena Dan Allah"
Itade Nihla shiru tayi tanajin su suna zancen su ta qyalesu, taga alama Ilham ta Manta cin
mutuncin dayayi mata
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Fira suke sunata kwasar daria amma shi yana zaune akujera shi kadai ya zubawa wayarsa ido,
farouq Tun dazu ya lura kwata-kwata hankalin Abba yanakan wayarsa, ko kallansu Babu kawai
ya qurawa waya ido
Ahankali yatashi yayi kitchen Kamar gaske
Soyake yaga menene yadauke hankalinsa haka, daya dauko Ruwan da niyya yazo wucewa ta
bayan Abba,karaf idonsa yasauka akan screen din wayar Abba, pictures din Nihla ne, kuma da
kayan data fita dashi dazu da yamma ne, toya akai Abba yasamu pictures din? Yaushe yayi
mata? Dama sun fara shiri shida itane harya fara yimata photo awaya? Ganin Babu me bashi amsa yasa ya tsaya yana kallan Abba dayake kallan pictures din daya
baya daya, idan yashiga cikin guda daya saiya dade yana kalla sannan zai sake zubawa
nagaba ido
Momy data lura shurun nasa yayi yawa tace "Abba na lafiya de ko?"
Kafin Abba yayi magana farouq dayake bayansa a tsaye yace "lafiya Momy, yana ganin abinda
yake rayuwa tare dashi ne acikin gidan"
Cikin sauri ya juya ya kalli farouq, Dasauri yasaka wayar aduhu, sannan yasakata cikin aljihun
wandon jeans dinsa, Innalillah... Baiso farouq ya kamashi yana kallan pictures din yarinyar
nanba, kada yayi tunanin wani abu, ahankali yamiqe tsaye yace "Babu komai Momy"
Farouq ya kwashe da daria ganin yanda qanin nasa yayi fuska Kamar bashi ba, yace "idan tayi
tsami maji"
Momy kam bata gane komai ba, danhaka tashare su, haka sukaci gaba da firarsu sannan sukai
mata sallama kowa yatafi gidansa
Shima Abba compound din gidan yafuto, Momy kuwa daki tashige tana waya da Daddy akan
matsalar Abba da likita yafada mata, yace ta bari idan yadawo gida saisu yi masa magana
Yadade a compound din yana kallan get din gidan, Agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya
kalla kasancewar akwai yalwar hasken fitilu agidan yaga goma saura, zagaye yafarayi awajan
hannunsa daya yana cikin aljihunsa, har zuwa wani lokaci kuma Yaqi komawa cikin part din
nasu, Agogon yasake kalla afili yace
"why bata dawoba har yanzu?"
Gashinan anyi dayawa, dafatan zanga Comments, facebook readers ina godia sosai da sosai
Amnah El Yaqoub ✍️
[7/5, 12:37 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
37&38
Babu me bashi amsa, haka yadinga zagaye wajan har saida ya hango maigadi yana bude get
alamun itace suka dawo, sannan ya juya cikin sauri ya koma ciki
Ita kuwa Nihla bata lura dashi bama, ana sauke ta tashigo part din nasu, kai tsaye dakin Momy
taje ta sanar da'ita dawowar ta sannan tatafi dakinta tayi wanka, tafara shirin bacci
Har shigowar ta falon yanajinta, sai a lokacin ya kashe wutar dakinsa shima ya kwanta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"Doctor magunguna na sun qare inaso kahada min wasu" cewar Fawaz
Doc yadubeshi yace "to Alhamdulillah gaskiya naga ana samun cigaba"
"hakane kam, but wani lokacin inajin raina yana baci haka kawai, kuma cikin raina inajin inason
nasha qwayar ko kadanne"
Murmushi Doc yayi "hakane, dama dole zakaji haka, amma kaci gaba da hakuri, kana kai
zuciyarka insha Allah zuwa nan gaba kadan zakaji tafita daga ranka ma gaba daya"
"ina fatan haka Doc, domin duk abinda mata ta bataso nima banaso, banason bacin ranta ko
yayake"
"masha Allah, kanason matar nan taka Fawaz, dukanku kunason junanku,amma bansan wacce
irin soyaiya ceba wannan, duk yanda kake sonta bazata iyama abinda kakeso ba, domin ta
cetoka daga halaka"
"mekake nufi Doc?"
"matarka takirani rannan da alamun ma Kamar tana kuka, tace bakada lafiya inzo, nafada mata
cewa maganin ai yana wajan ta, tabaka haqqin ka kawai, kai tsaye tacemin bazata iyaba"
Murmushi Fawaz yayi "ai tanada kunya Doc nima nasan bazata iyaba, kuma ni hakan datayi ya
birgeni, inason mace Mai kunya, nikuma gaskiya kunyar tunkaranta nake da wannan abun,
bansan ta Inda zan fara ba, please ko zaka bani wasu magungunan Wanda Zan dinga sha duk
lokacin dana jini cikin wannan yanayin "
Dariya likitan yayi" lalle, ina Ruwan laila majnun, Wato ahakan batayi laifi awajan ka ba, kuma
kai bazaka iya kai kanka wajantaba, lalle Fawaz irinku kadanne Awannan zamanin, to maganar
gaskiya bazan baka kowanne irin magani ba, inzaku nemi haqqin junanku ku nema, idan
bazaku nemaba shikkenan, amma kanada aure kanada mata bazan baka wani magani ba,
wannan ai sai yarinyar ta rainaka ma tace baka iya mata komai "
Murmushi Fawaz yayi " tace komai ma Doc, amma ni bazan iyaba "
Likitan yayi shiru yana kallan Fawaz, ikon Allah kenan, Awannan zamanin?
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tun bayan dasukai magana da Doc. Ya tattara maganarsa ya watsar yaci gaba da sabgarsa,
har Tsawon sati daya, zaman su da Dida kuwa komai lafiya, yau Tun safe yakejin cikin sa yana
murdawa, haka yatashi yafita, Dida na daki sai dirin motarsa taji, wajan wani abokinsa yaje,
abokin na ganin Fawaz cikin damuwa ya tambayeshi meyake damunsa, nan take yafadawa
abokin nasa, murmushi abokin yayi yace "dadina da gobe saurin zuwa"
Yatashi yaje daki yadauko masa wata kwalbar wine yace "abokina baka taba shan wannan ba,
kasha ta, zakaji dadi, damuwar ka zata kau nan take"
Fawaz ya karbi kwalbar giyar nan yariqe, idan ya tuna cewa Dida bataso sai yaji jikinsa yayi
sanyi, uwa uba shi duk shaye shayensa baitaba shan giya ba, to amma kuma idan ya tuna
cewa damuwar sa zata kau saiyaji gara hakan "
Memakon yasha anan sai yatafi da ita gida, yana zuwa falo kuwa Dida tafuto daga daki zataje
kitchen, kallan farko tayi masa ta hango rashin gaskiya awajan sa, taga sai boye hannu yake,
bata zurfafa bincike ba tayi masa sannu da zuwa tawuce kitchen, shima cikin sauri yashige
dakinsa, yadauko cup ya tsiyaya giyar aciki, Yazauna zai fara sha kenan taturo kofar dakin
tashigo, abinda tagani agabansa ne yasa gabanta yayi mugun faduwa, giya? Dasauri taje
tadauke gaba daya, ita dama tunda taga shigowarsa tasan cewa akwai abinda yake boye mata,
cikin bacin rai tace "ya Fawaz miye hakan? Menene wannan?" idanunta suka cika da qwallah
Shiru yayi yakasa bata amsa, ita kuwa ta tsareshi da ido tana jiran amsa
Kallanta yayi sannan Dasauri yayi kasa da idonsa, cikin rashin gaskiya yafara yimata magana "
Dida... kiyi hakuri, wallahi ba laifi na bane, wani abokina ne..."
Kafin ya qarasa ta tareshi tace "to laifin waye?ya Fawaz Dan Allah yaya kakeso nayi da raina
ne eh? Kai yaro kullum zamu dinga magana akan abu daya shekara da shekaru?"
Hawaye yazubo mata, tasa hannu ta goge, sannan tadauke kwalbar giyar da wadda yazuba
akofin, ta miqe zata futo daga dakin cikin fishi
Dasauri yatashi ya fusgota jikinsa, ya rungumeta tabaya, tsayawa tayi cak, hawaye yana zuba
a'idonta, Tun tana na hawaye harta dawo yi abaiyane, shi kansa yasan cewa bai kyauta
mataba, amma yaya zaiyi? Kansa yadora akan wuyanta yayi shiru kuma yariqe ta gam ajikinsa,
Ruwan dataji yana Saukowa daga wuyanta yana shirin shiga cikin rigarta ne ya tabbatar mata
da cewa kuka yake
Saikuma jikinta yayi sanyi, tadena nata kukan tanajan zuciya, cikin hawaye yace "kiyi hakuri,
bazan qaraba, Allah abokinane yabani, bansan yaya zanyi ba Dida, ina cikin damuwa, cikina
kullum ciwo yake min"
Nan take Dida tafara tunani, karfa garin kunya tasa mijinta ya koma ruwa, bayan tasamu daqyar
yadena shan komai, yanzu inda yasha giyar nan tasan cewa alhaki yana kanta, kuma dalilin ta
ne yasa mijinta bayan shan qwaya ya koma shan giya, dolen dole zatai kokarin raba ya Fawaz
da wannan abokin nasa duk da batasan