Showing 87001 words to 90000 words out of 104433 words
Chapter 30 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
Cikin kunnanta yadora bakinsa yace "kin hakura?"
Wani irin abu taji yana yawo a jikinta, kode ya Abba ya Manta da ya Aslam ne, ahankali ta
janye jikinta daga nasa
Shima sai murmushi dayayi, yamatso kusa da Aslam yace "Abokina ina Abba nah"
Aslam yayi Murmushin waskewa yace "kaiko, Hmm"
Dahaka suka qarasa cikin gida, suna zuwa tabude motar tafuto jikinta asanyaye, tayi part dinsu
Momy da Daddy na zaune afalo, Adala tana gefen Momy tanayi mata lissafin abubuwan dazata
siyo mata, haka Nihla tazo ta samesu, cikin ladabi ta gaishe su tareda zama aqasa
Momy tace "a a, yana ganki yanzu, yanxun nanfa nake cewa Alhaji yatashi mutafi"
"Momy ai an sallamemu, yace yawarke"
Daddy yayi Murmushi, a lokacin suka shigo falon shida Aslam, suma gaida su sukai suka zauna
aqasa
Daddy yace "Abba ashe jiki yayi sauqi"
Lallausar sumar kansa ya shafa yace "eh Daddy"
Yace "to Alhamdulillah, Dafarko de kayiwa Allah godia, sannan ka godewa Aslam,idan da hali
ma kayi masa Babbar kyauta sannan kaida Aslam din Idan jikinka yagama warware wa
kushirya kuje can Abuja kuyiwa yaron nan Yusuf godia, yayi mutuqar kokari kuma yayi maka
halacci, sannan dazu mahaifiyarka tayi waya da Ibrahim ta sanar dasu ka farka, sunce asaka
musu lokacin da za'ayi biki yan'uwan mahaifin ta zasuzo daga jigawa ahadu anan, na Abuja ma
zasu so gaba dayansu duk ayi komai anan, nikuma nafada musu nasaka sati daya, saboda
haka sai kayi kokari zuwa next week din kagama shirya komai, saiku tare a gidanku "
Cikin farin-ciki yadan sosai qeyarsa yace" to Daddy insha Allah"
Sannan yakalli Nihla yace "kinji abinda yafaru ko?"
Tace "naji Daddy"
"to kiyi hakuri, ki qara akan Wanda kikai abaya, Allah yabaku zaman lafiya"
Tace "amin Daddy"
Momy ta miqe tace "Nihla taso Muje kitchen"
Bayan Momy tabi abaya, suna zuwa kitchen Momy tabata wani magani tace "kisha wannan
yanzu, sai kici abinci kishirya kitafi gidan gyaran jikin"
Cikin ladabi tace "to Momy" tadauka tafara sha tana tunani aranta, Ilham tabata, Momy tana
qara mata wani itakam yaya zatayi?
Momy ta kalleta tanajin tausayin yarinyar, gani take Kamar ba'a kyauta mata ba, Allah yasa de
taso Abban nata, koda yake tasan Abban ma da naci, zai rarrasheta
Bayan tagama sha tawuce dakinta tazauna agefen gadon tana tunani, yanzu haka aure ne
akanta fa, ashe yaya Abba yasani shiyasa yake min wasu irin abubuwa a asbiti, tatuno lokacin
da ya Aslam yake cemata yaya marar lafiyarta, Hmm ashe duk sun sani, wayarta tadauka takira
Anty Nadiya tabata labarin komai, nan take Nadiya tace zatazo bikin itama domin ta nemi
yafiyar sadeek, tayi musu ala sanya alkhaairi, bayan sun kashe tatashi tashiga wanka, tafuto ta
shirya tsaf taci abinci, sannan tayiwa Momy sallama tatafi driver yakai ta gidan
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Sai bayan sallar ishsha'i tadawo gida, zaune suke afalo su biyu shida Momy, Momy tana bashi
coffee abaki, sallama tayi tashigo cikin falon idonsa yasauka akanta, doguwar riga ce a jikinta
Mai godon hannu amma rigar abaje take sosai, ya dinta yanada santsi Kamar na abaya, da
mayafin rigar tayi amfani tayafa akanta sauran kuma ta zuba shi baya, dukda fadin rigar hakan
bai hana ka hango bajajjan hips dinta, yayinda cikakken qirjinta yadago ,hakan yasa cikinta
shafewa, da yar qaramar jakar ta a hannunta
Cikin ransa yafara magana
ya'ilahi! Yanzu haka duk anganta ahaka, amma yaya zaiyi? Bazai iyamata magana ba tunda
shine yake neman sulhu
Zama tayi akujera kusa da Momy, tace "wash Allah Momy nadawo"
Zaman datayi awajan kawai wani irin qamshi na daban yake tashi, ahankali ya lumshe idonsa
sannan yabudesu
Momy tace "Sannu Nihla, ai gara da Allah yakawo ki, zanje in dubawa Alhaji wasu takardu,
karbi wannan coffee din kibashi"
Baki taturo gaba alamar bataso, ita Momy batasan halin ya Abba ba, kawai shagwaba ce take
damunsa, amma aiya warke
Haka tasa hannu ta karba Momy tashige dakin Daddy tabarsu anan
Gyara zaman sa yayi akan kujerar ya dauki fillo din kan kujera yadora a cinyarsa yazuba mata
ido yana murmushi
Gaskiya yaji dadin abinda Momy tayi, wani irin nishadi yakeji aduk lokacin dasuka kasance su
biyu shida ita
Kallanta yayi yace "zeyi sanyi fa"
Dago idonta tayi ta kalleshi, ta janye idonta, sannan tamatso kusa dashi ta diba a Spoon din
takai bakinsa, Dan qaramin bakinsa yabude tasaka masa Spoon din, yanasha ya lumshe
idonsa, haka taci gaba da bashi yanasha harya qare tas, bedena bude mata bakin ba, ta
kalleshi tace "yaqare"
Murmushi yayi yace "bazan samu qari ba?"
Tashi tayi tsaye kanta tsaye tace "eh"
Cikin sauri yasauko daga kan kujerar yace "kawo nariqe miki jakar to Muje dakin"
Babu musu tabashi handbag din nata , shikuma yabita abaya har cikin dakinta
Abakin gado tazauna shikuma Yazauna aqasanta tareda dora mata jakar akan cinyar ta, bayan
yadora mata jakar a cinya memakon yadauke hannayensa sai yabarshi akan cinyar tata,
bayaso kokadan yadena jin wannan qamshin nata dake rinjayarsa
Nihla tarasa yaya zatayi dashi, ahankali tace "inaso ne nashiga wanka"
Yace "akwai maganar danake so muyi"
Fuskarta Babu yabo Babu fallasa tace "to"
Kallanta yayi yafara tunani, yarasa meyasa har yanzu taqi sakin jikinta dashi, idan yadubi
qwayar idonta yana hango rashin sabo atattare da'ita, kokuma har yanzu bata yafe masa bane
bai saniba
Ajiyar zuciya yayi, cikin maganar sa Ahankali cikin sigar rada, Wanda dagashi sai itane zasuji
yace "ina qara baki hakuri akan abubuwan dasuka faru abaya .... Nihlaaa! "
Yaja sunan nata
Sannan yaci gaba da cewa "Wallahi yawancin kowanne dare bana iya kwanciya harna samu
nayi bacci saboda tunaninki, koda yaushe jinake inason ganin ki a kowanne lokaci, duk lokacin
dana kasance tare dake inajin wani irin dadi acikin zuciyata, abaya nayi kuskure dana kasa
bawa wadda nashaqu da'ita kulawa harta hakura dani,domin kuwa nagama ganewa shaquwa
ce kawai tasa na furta mata kalmar soyaiya, amma soyaiya daya Tun ta yarinta ta kena bawa
Nihla..... a yanzu nayi miki alqawarin Zan kula dake fiyeda yanda Zan kula da kaina, kiyi hakuri
kiyafemin kisaki jikinki dani please "
Shiru Nihla tayi bayan tagama jin duk bayanin sa, Kamar ba shiba wani lokacin idan Yazauna
yana yimata wasu abubuwan
Ganin tayi shiru ba tace komaiba yasa shi motsa hannunsa dake kan cinyar ta, ahankali yafara
shafa cinyar ta, kasancewar rigar jikinta me santsi ce saitaba shi damar shafa cinyar tata
dakyau
Ta kalli fuskarta yace "kinji"
Gaba daya yafara kashe mata jiki da salonsa,
Cikin shagwaba tace "ya Abba nide kabari"
Yace "to kin yafemin?"
Ahankali tadaga masa kanta, sannan tace "Allah yayafe mana baki daya"
Yayi Murmushi yace "Amin, kinga wani abu"
Yabude wayarsa ya nuna mata wasu pictures
Kanta ta matso tafara ganin pictures din, shima yaturo nasa kan domin su gani tare,tana gani
tace "laaaa pictures dina"
Murmushi yayi ya kalleta, yanda kansu yahadu ne yasa yaji Kamar yayi kissing Dan qaramin
bakinta, musanman yanda ta bude shi dinnan tace laaaa, amma bazai yiba, gara yabi komai
Ahankali
Yace "yes, Tun lokacin da mukaje garinku nayi miki pictures din, kin tuna? Abakin ruwa, har
ruwa yadakemu"
Cikin murmushi tace "wallahi na tuna, bani na gansu gaba daya, waye yatura ma?"
Dadi yafara kama Abba, yanda yaga tafara sakewa dashi, yace "ya Usman ne yatura min"
Tace "wayyo,lokacin banda qiba wallahi"
Kallan qasa qasa yayiwa cikakkun nashanunta yace "yanzu ai kinyi"
Nihla bata gane komaiba tace "wallahi sune, zaka tura min kuwa"
Kallanta yake yanda take jin dadi sai yaji dadi shima, gashi shiba wani surutu ba, kuma bayaso
firar taqare,bayaso yadena jin daddadan qamshin dake tashi a jikinta, bayaso yayi nesa da'ita,
yarasa mezaice mata domin tasake jin dadi shikuma yaga farin ciki akan fuskarta, ya kalleta
yace "nagoyaki?"
Cikin sauri ta kalleshi, cikeda mamaki, wanne irin goyo kuma ana zaune lafiya? Saikace Wanda
zai iya goyon, tasan kawai fada yayi, amma domin taga gudun ruwansa sai tace "eh"
Cikin sauri yace "to zo ki hau"
Yadauke hannunsa akan cinyar ta ya tsugunna a gabanta
Mamaki yagama kashe Nihla, anya ya Abba ne kuwa wannan? Yau ya Abba ne zaice tahau
bayansa ya goyata? Ta ajiye wayar tasa agefe sannan tafara tattare rigar jikinta, tad'ane
bayansa, lokaci daya yamiqe tsaye, beji nauyin taba kokadan, hanyar kofar dakin yanufa da ita
yace "muje nakaiki falo saina dawo dake?"
Zaro ido tayi tafara girgiza kanta tace "laaaa a a babu ruwana"
Ganin yanda ta tsorata yasa yayi Murmushi yace "Allah Muje"
Riqeshi tayi sosai tace "dan Allah kar Muje"
Lumshe idonsa yayi, numfashin sa yafara sauyawa, qarfin jikinsa yafara raguwa, kasala ta
lullube shi sakamakon jin nashanunta agadon bayansa yanda tasa hannu ta rirriqeshi
Nihla taji shiru, tayi tunanin bai haqura ba, tasake jijjigashi tace "dan Allah"
Nan take yaqara daukan caji, yashiga cikin yanayi, yaji qafafunsa suna neman gaza daukarsu,
sai gyara kafafunsa yake, ita kuma takasa gane komai
Yana motsawa kuwa suka tafi kan gadon nata gaba dayansu suka fada kai
Nihla tayi tunanin da niyya yayi hakan, batasan yanayi ne yasa ba
Nan take tafara dariya, yajuyo da kansa yana Kallanta, yajima rabon daya ga tana dariya Kamar
haka, ahankali yadago hannunsa ya dora shi akan dimple dinta
Sharhi, share please
Amnah El Yaqoub ✍
[7/15, 11:04 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
57&58
Juyowa tayi tana kallansa, cikin murmushi tace "Aidama nasan bazaka iya daukana ba, shiyasa
nahau banyi ma musu ba, yanda nake d'innan"
Ta qarasa maganar tana jijjiga jikinta
Shima murmushin yayi mata "nayi tunanin zan'iya ne, bansan haka ake jiba"
Nihla kwata kwata bata gane maganar dayayi ba, Dan haka tayi shiru, hannunsa dake kan
dimple dinta yadauke yadawo dashi dede karan hancin ta, yace "kinada kyau"
Cikin sauri ta kalleshi, tayi Murmushi sannan ta yunqura tatashi zaune, ta kalli Agogon dakin
tace "kaiiii shadaya saura, ya'akai lokacin yayi gudu haka, bari de in shiga wanka"
"to kitashi kishiga mana"
"to ai baka fita ba"
"idan kika shiga Zan fita, kona kaiki?"
Cikin sauri tace "a a, tsaf zaka sake kayar dani" tashige toilet din da kayan ta a jikinta tareda
rufo kofar
Yana ganin shigarta ya lumshe idonsa tareda yin ajiyar zuciya, yatashi jiki a mace yafuto daga
dakin nata, har lokacin Momy bata falon, ya kashe kayan kallo sannan yawuce dakinsa, cikeda
begen matarsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Acikin satin su Abba sukaje Abuja suka yiwa Yusuf godia, Abba har kunyar sa yakeji akan
abubuwan dasuka faru abaya Sosai suka fahimci juna
Tundaga lokacin Nihla tadena zuwa wajan gyaran jiki, dede da falo Momy hanata futowa tayi
saide dole, kullum tana cikin hijabi, hatta qafarta akwai safa, data zauna aqasa kuwa Momy
zata sata tatashi takoma kan gado ko kujera duk saboda kada sanyi ya shige ta
Magunguna kuwa Momy bata take iri-iri masu inganci, Nihla qwarai ta yaba irin sonda Momy
take wa ya Abba, haka kuma duk cikin surukanta Nihla ta daban ce, dama Tun tana qarama
soyaiyar Nihla take cikin Zuciyarta, kokadan Momy bata qyashin yiwa Nihla abubuwa, domin
kuwa tayi alqawarin zata riqeta Kamar itace ta haifeta, shiyasa take mata duk wani abu da uwa
zata yiwa 'yarta
Abba da Aslam Babu zama, danma wani lokacin su Adam da Fawaz suna yin wani abun ta
wani bangaren, gida kam komai yaji, sun qawata shi yanda yakamata da kayan kamfanin A&A
Furnitures, yayinda Anty Salama matar ya Usman da hajiya Farida maman su Dida suka shirya
sukaje Dubai suka hadowa amarya kayan lefenta
Anty Firdaus kuwa matar ya Aliyu itace tashiga tafita wajan kawo anko, dayake abune na kudi
nan take kowa yayi, duk Wanda kaduba yana cikin farin ciki, kuma doki yake wannan rana tazo,
andade ba'ayi wani taro a wannan family ba, ko bikinsu Aslam da akayi Babu wani biki da akayi,
kasancewar kowa yasan Babu Wanda yake son auren, kowa dole aka masa
Ana sauran kwana biyu biki 'yan'uwa na nesa dana kusa duk sunzo, yan'uwan mahaifin ta duk
sunzo, kuma family anhadu anyi musu kara duk Inda suka so anan suke kwana, yan Abuja ma
duk sunzo, mamy kam wajan Momy ta sauka suka hadu suke gudanar da Komai
Yusuf yana wajan angwaye, saide duk abinda yake yana kokarin danne zuciyarsa ne kawai,
saboda kada yazobe ladansa, bayan badan komai yayi ba saidon Allah
Ranar kamu kuwa kowa ya shirya, amarya tanata sauya shiga kala kala, Acan gidan sheik
Adam kuwa Diyana kuka tasaka masa da qaton cikin ta na wata shida, gaba daya dinku nan
sunyi mata kadan, haka tasa Adam agaba tana masa kuka, yarasa yaya zaiyi da'ita haka
yadauko mata wasu kayan suka Taho gidan bikin, Dida kuwa normal take harkar ta, domin
kuwa har yanzu batada komai
Washe gari da rana amare suna zaune a part dinsu Ilham, cikin tsohon dakin Ilham datake ciki
kafin tayi aure, bayan angama yiwa amarya kwalliya, zuwa dare za'a tafi wajan dinner
Diyana tana gefe, da ciki agaba tana karanta wani littafi, Nihla ta kalleta tace "meciki"
Diyana tace "saura ke ai"
"A a, aini ya Abba yana sona, saiya qara reno na, sannan"
Gaba dayansu suka saki dariya, Dida tace "tab, ina Ruwan yaudaran kai"
Dariyar dasuka sa ne yasa lil Abba kuka, Nihla tace "kai Innalillahi... Dan Allah Ilham ki dauke
wannan yaron naki, gaba daya ya ishemu da kuka"
Ilham tace "angonki nede, yanda kuka sashi kuka yasin kema lokaci yana zuwa saiya saki kuka"
"ni Ilham Dan Allah kidena min irin wannan maganar, Allah banaso"
Wayarta ce tadauki qara, Dida tabata tace "ga Ango yana kira"
Karbar wayar tayi, ashe yanada number ta, betaba kirantaba, rage murya tayi tace "Hello"
Saida yaja wasu second sannan yace "Amarya bakya lefi kokin kashe Dan masu gida"
"to waye Dan masu gidan?"
Murmushi yasaki Mai aji yace "farouq mana"
"Hmm kaiko, shiyasa kullum kuke fada ai"
"muna gidan Aslam, kuma suna jin yunwa"
"toooo, to saide Ilham din tadawo tadafa muku abinci"
"A a, kece zaki kawo mana"
"yanzu ya Abba fisabilillah tayaya Zan Taho ni kadai, idan Momy ta ganni ma zata hanani"
Shagwaba yafara yi yace "uhm.. uhm.. Allah nide yunwa nakeji"
♀️Kanta da dafe da hannunta tace "to naji"
qit takashe wayar sai mita take, mutum ana tabashi sai shagwaba, saikace shine autan duk
duniya, nida nake wajan iyayena ni kadai banyiba saishi, haba ni wallahi nagaji
Mesu Diyana zasuyi inba dariya ba, Dida tace "wai Dan Allah ya Abba ne yake miki shagwaba?"
Tace "tab, ai saide in bamu zauna ba"
Diyana tace "ya birgeni, yanzu ba kowanne namiji ne yake wa matarsa shagwaba ba, saide ke
mace kullum ki daddage kiyi, duk saboda ki faranta musu, maganin mata ne, mata ne suke
nema, maganin tsumi ne mata ne, shagwaba ce mata ne, ke mace kullum kede kina kokari kiga
kinyi Dan ran mijinki yayi fari, amma Ba kowanne namiji ne zaisha magani ba, saboda matarsa
taji dadi, komai de saimu, saboda haka idan yafara miki shagwaba kema ki masa, zai dinga
tattalinki, Dan kowanne namiji dakike gani Babu Wanda zaice bayason yasamu mace wacce
ta'iya shagwaba "
Ilham tace" wallahi gaskiya ne kam "
" salamu alaikum "
Gaba dayansu suka juya suka kalli kofar dakin, baquwar fuska suka gani,yarinya ce qarama da
alama zatakaisu shekaru, wata shegiyar gown ce a jikinta datahau jikin nata sosai, kallo daya
zakayi mata kasan cewa lalle mace ce har mace, haka kana ganin hancin ta zaka tabbatar ita
din bafulatana ce, duk yanda doguwar rigar ta baiyanar da hips dinta hakan baisa tasaka
Babban mayafi ba, Dan qarami ne sai tayi rolling dashi
ganin yanda suka zubo mata ido suna Kallanta yasa ta qarasa shigowa cikin dakin ta ajiye
jakar kayanta, sannan tazauna agadon ta cire mayafin datayi rolling tana firfita dashi
Tace "ku qaramana esin mana"
Ilham tana kallan ikon Allah tace "aqure yake ai"
Tace "to inaga Dan daga rana nake ne shiyasa,"
Ta kalli Nihla tace "amarya, wai baki ganeni bane? Naga duk sai kallona kuke, naje wannan part
ance bakwa nan, naje wannan ance bakwa nan, saida nazo nan nayi sa'ah akace kuna ciki, ina
qawayen naki naga saiku hudu kawai?"
Nihla tace "banfa gane kiba"
Dida ma tace "amarya batada qawaye, qawayenta yan'uwanta, mune kuma"
Itama tace "to gani naqaru, Rafi'ah cefa, yar gidan yayan baban ki Abdullahi na lagos"
Nihla tace "kut, au Rafi'ah wai kece? To ina Zan gane ki, kinga yanda kika koma kuwa"
Ta kalli su Ilham tace "cousin sister nace, yar gidan yayan babanmu ce, alagos suke dazama,
babansu yana canji"
Gaba dayansu sukai murna,Dida tace "to yanzu ai kinga kinsamu qawa yan'mata"
Nihla tace "to Rafi'ah ko zaki kaiwa angwaye abinci, suna gidan Ilham"
Rafi'ah tace "angwaye? Sunada yawa?"
Ilham tace "gaskiya bazasu rasa yawa ba"
Tace "a a toba lalle nashiga ba gaskiya, dade mu biyu ne,bari na gyara fuskata,nikam Nihla ina
yusuf Dan unguwar ku? Kwanaki naji baba yana waya da baban ki naji yace kuna Abuja agidan
su"
Murmushi Nihla tayi "ya Yusuf, shima yana wajansu ai, idan kinje saiku gaisa dashi"
Tashi Rafi'ah