Showing 24001 words to 27000 words out of 104433 words
Chapter 9 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
safara'u sister na, tamin
maganar gyaran jiki "
Haushi yakama Ilham, wai gyaran jiki, tarasa wa zata gyara wa jiki sai saurayin yayarta♀️
Suma su Dida haka hajiya Farida tasasu agaba tahada musu kaza kowa dai-dai,
Diyana kuwa tafi bata maganin matsi, saboda ita kanta batasan adadin mazanda yarta takula
ba♀️
Haka akaci gaba da hidimar biki kowanne bangaren Babu maiso, har Allah yakawo satin biki
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Rana bata qarya, ayaune aketa hada-hadar daura aure, iyaye maza kowa ka kalli fuskarsa zaka
ganshi yana farin ciki, amma iyaye mata kowa da abinda ya isheta
Tun karfe goma mutane suke ta tururuwar zuwa wajan daurin auren, saboda iyayen maza sun
sanar, su kuwa yaran a tsakanin su ko walima Babu Wanda yahada
Angwaye kowa yayi kyau da fararen shaddodin da Alhaji Basiru ya dinka musu, Kamar ka
sacesu ka gudu
Kowa ya hallara acikin Babban masallacin unguwar domin daurin auren, liman ya gyara zama
da nad'in rawanin kansa, yace "to Alhamdulillah , wanne za'a fara daurawa?"
Alhaji Baqir yabashi sunayen yaran a rubuce kowa da matar sa agaban sunansa
Adam -maryam(Diyana)
Fawaz-Khadija (Dida)
Aslam - Ilham
Abubakar - Fatima (Nihla)
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tun safe yafuto daga gida yanaso yaqaraso gidan amma matsalar go slow tasa ya makara,
mutanan daya gani a masallacin unguwar ya tabbatar masa da cewa anan ake daurin auren,
kai tsaye yatafi masallacin shima,
Kutsawa yake cikin dandazon jama'ar wajan har ya qarasa cikin masallacin
Adede lokacin liman yake cewa "yawwa Alhamdulillah saura na mutum daya kenan,"
Ladan yace "eh saura na Abubakar da Nihla"
Qarewa mutanan wajan kallo yayi, Alhaji Baqir, Daddy, Alhaji Basiru, da Alhaji habib mijin hajiya
Farida, dakuma mazan family din baki dayansu su Usman dasu Aslam Wato Angwaye
Dasauri yadaga hannu yace "A dakata!!"
Gaba daya idanu suka dawo kansa, Daddy cikin ransa yace "Mai hakuri"
Amma afili baice dashi komai ba, yazuba masa ido yana kallansa
Baba ya kalli liman yace "ala gafarta Malam, nine mahaifin Nihla, amatsayina na ubanta ban
yarda adaura wannan aure ba, yarinya ta kawai nazo dauka, ita nake buqata"
Ko kallan Inda su Daddy suke baiyi ba, bare gaisuwa ta hada su, yajuyo yafice daga cikon
masallacin, yanaji ta cikin Speaker anata salati
Daga nan baba ya koma gidan,ya tsaya abakin get, yasa maigadi yashiga gidan yakira masa
Nihla, ace inji babanta tazo
Maigadi kai tsaye yatafi part din Momy, jama'a sun taru anata hidimar biki, gaba dayansu
yanmatan suna zaune a dakin Nihla, Mai kwalliya tana tsantsara mata
Diyana ce tafuto falo tana amsa wayar wani saurayinta
Maigadi yana ganinta yace "yawwa Diyana, kicewa Nihla babanta yana kiranta, yana can
abakin get"
Ta amsa masa sannan ta amsa wayarta tajuya dakin tace "Nihla babanki yana bakin get, yace
kije"
Yanda ta dade tana kiran wayarsa Yaqi ya amsa, tana tura masa saqo Yaqi yayi reply, hakanne
yasa ta naji ance babanta tatashi tace "Baba nah!!!"
Sannan ta kalli maiyin kwalliyar tace "ina zuwa, bari naje nashigo da babana ciki"
Futowa tayi, Momy bata lura da ita ba tanata baqi
Kai tsaye Nihla tafuto bakin get din ko mayafi Babu
Tana zuwa taganshi fuska Babu Rahma tace "Baba!!!"
"wuce mutafi gida" abinda yace da ita kenan
Mamaki yakamata, bata taba ganin baba cikin fishi irin wannan ba, tace "Amma baba Anty...."
"Kiwuce mutafi gida nace!!!"
Yadaka mata tsawa
Tace "To baba Babu ban dauko hijabi..."
Kafin ta qarasa yaja hannunta, suka fara tafiya, sai dankwalin da aka nad'a mata akanta ta ware
tayafa a jikinta
Suna zuwa bakin titi yatare musu adedeta suka shiga, gaba daya tarasa gane kan baban nata,
tashar Mota sukaje, daga nan suka wuce jigawa
Awa biyu ce ta kaisu gida, kuma har lokacin Bece da'ita uffan ba, suna zuwa kofar gida sukaci
karo da motar Alhaji Isma'eeil qirar Range rover
Alhaji Isma'eeil yace "Mai hakuri ina ka shiga Tun dazu angama zuba kaya amota kai muke
jira?"
Baba yace "Alhaji wallahi kano naje Tun safe, yarinya ta za'ayi wa aure batare da iznina ba,
shine naje nadauko ta"
Adede lokacin yafuto daga gidansu shida mami, karaf maganar tasauka acikin kunnansa,
Dasauri yakai kallansa kan yarinyar da ake magana akai
"Nihla my friend" yafadi sunan cikin ransa, fuskarta ya qarewa kallo har yanzu kyanta yana nan
saima qaruwa dayayi
Cikin mamaki yakalli baba yace "Baba wai wannan yarinyar za'ayi wa aure?"
Ko a mafarki taji wannan muryar bazata taba mantawa da ita ba, kallansa tayi tafara magana
cikin ranta "yaya Yusif! Innalillah.. Yaushe yadawo?
Alhaji isma'iel yayi Murmushi yace" Mai hakuri, hakuri yaqare kenan "
Mami da baba sukai daria, Nihla tayi shiru, ga tashin hankalin rabuwarta da yan kano ga kuma
mamakin ganin yaya Yusif
Handbag din mami ce a hannunsa, ahankali ya matsa ya wullawa Nihla jakar yace "ke riqe
wannan "
Dasauri ta cafe jakar, saboda karta fadi qasa
Alhaji isma'eeil yakalli Yusif yace "nasa Mai gadi yadauko kayan Mai hakuri ansaka amota, bani
key naja motar da kaina, ban yarda da driving dinka ba na ganganci, idan kuka samu titi kuna
gudu Kamar bakwa son ranku"
Sumar kansa ya sosa,sannan yabashi car key din
Sai a lokacin Nihla tagaidasu, mami da Alhaji Isma'eeil suka amsa mata cikeda kulawa
Alhaji ne yabude motar yashiga, shima baba yashiga gaba, mamy da Nihla suka shiga baya,
sannan shima Yusif yashiga bayan daga daya bangaren, Yazauna agefen mamy
Mamy ta kalli Nihla cikin kulawa tace "Nihla kinsha hanya sosai ko 'yata, nasan kin gaji, zoki
kwanta kihuta"
Taja Nihla jikinta sannan ta dora kanta akan cinyarta tana bubbuga bayanta Kamar wata
qaramar yarinya
Shikuwa Kallanta yake, Wato bazatayi masa magana bako? It means batayi missing dinsa
ba,koda yake yaushe zatayi masa magana tunda ta Manta dashi harta samu wani zata Aura
(tofa)
Ahankali Alhaji isma'eeil yatada motar, suka dauki hanyar Abuja.
To Alhamdulillah anan na kawo qarshen labarin DANGI DAYA, zan Dakatar da typing dinsa
badan komai ba saidon Comments din readers da ban gamsu dashi ba, sharhi yayi qaranci,
idan akwai wadda na batawa rai Sanadin wannan labari to tayi Hakuri
WhatsApp readers banida bakin dazan gode muku, kunyi min komai akan wannan littafi
masu yimin sharhi daga cikinku nayi saving number dinsu insha Allah zansakaku asabon group
dina, mudinga gaisawa
Yaya labarin Mazawaje family?
Wanne hali Momy zata shiga dangane da tafiyar Nihla?
Yaya Rayuwar Nihla zata kasance a Abuja?
Ina labarin amare masu shirin shiga daka ciki?
Amnah El Yaqoub ✍️
[6/21, 1:40 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Tabbas hakane, laifin wani baya shafar wani, amma kuma Babu dadi kayi rubutu a karanta ma
bayan ansan kanason Comments a share ka, danku nake wannan rubutun, be kamata agani ayi
shiru ba, masu kirana, masu min private text, masuyi min magana ta group, da Wanda suka min
ta page d'ina, duk naji maganganunku, nagode da soyaiyar dakuke nunamin, insha Allah zanci
gaba da typing, daga qarshe wannan page din na sadaukar dashi ga dukkanin masoyan Amnah
El Yaqoub
'yan labe ina kuke? To Allah yasa ku d'ore dayin Comments ehe
17&18
Liman ya kalli Alhaji Abubakar kozaice wani abu tunda shi ne babba, amma tashin hankalin da
Alhaji Baqir ya hango a fuskar Daddy ne yasa shi yayi magana dasu yace "ala gafarta Malam
mungode, mungode sosai,"
Yadauko kudi a aljihunsa masu yawa ya ajiye musu, Sannan yakama hannun Daddy suka futo
daga masallacin, Alhaji Kabeer kuma shine yake sanarwa da mutane ansoke daya daurin
auren, daga nan yaci gaba da godia ga jama'ar dasuka gayyata
Uban gayya kuwa fuskarsa Babu yabo Babu fallasa Wato Abba
Angwaye dukda dama can suna cikin bacin rai, sai abin yasake qaruwa
Usman yadafe kansa, meyasa baba Ibrahim zai musu haka? Amma aida yayi hakuri anbi komai
Ahankali ko, amma abu acikin taron mutanen da sukazo daurin aure
Dan haka yayiwa su Aliyu alama da ido, nan danan suka futo gaba dayansu sukabi bayan
Daddy
Su Daddy kuwa saida sukaje bakin get sannan Alhaji Baqir yasaki hannunsa yace "Alhaji kayi
hakuri, nasan yanda kake ji acikin ranka, kayi hakuri" ya qarasa maganar yana bubbuga
kafadarsa
Su Usman ne suka qaraso, Aliyu yajashi hannun Daddy yace "Daddy Muje ciki"
Alhaji Baqir yawuce part dinsa jiki a sanyaye
Suma sukaja hannun Daddy suka tafi, mutane baqi anata hidima, dasuka shigo kowa sai gaida
su yake amma su Usman ne masu amsawa, suna shiga dakin Daddy gaba dayansu suka
zauna Babu me magana acikinsu, farouq yafuto daga dakin yayi wajan Momy
Yana zuwa yakama hannun yace "Momy zokiji"
Kallansa tayi tace "jarababbe, farouq Dan Allah kabarni nahuta yau ana bikinma bazaka rabu
Dani kaima kaje wajan mutanan ku ba"
Yace "Momy kitaho please"
Fuskarsa ta kalla taga Babu wani wasa ko Fara'ah, mamaki ya kamata, Dan haka kai tsaye
tabishi zuwa dakin Daddy
Kujera ta nema tazauna, tace "yanaganku haka jiki a sanyaye? Meyake faruwa ne?"
Daddy yayi shiru har lokacin Bece komai ba, Aliyu ne yafara magana "Momy Wallahi fa ansamu
matsala, anfasa auren Nihla da Abba"
Cikin mamaki tace "me kace Aliyu?"
Usman yace "hakane Momy, baba Ibrahim yazo yadauketa, suntafi"
Adede lokacin Abba yashigo dakin, yanemi waje Yazauna, duk Babu Wanda ya kulashi
Momy ta kalli Daddy tace "to Alhaji meyasa zakayi shiru? Yanzu de ka kirashi kafada masa Dan
Allah ni yadawo min da yarinya"
Ajiyar zuciya Daddy yayi, sai a lokacin yayi magana "Ibrahim ya nunamin yafini iko akan Nihla
ne, yanda na nuna masa iko da farko, shine yazo har gida ya nunamin yafini iko akanta"
Tace "mekake nufi Alhaji, bangane maganganun ka ba"
Yace "Rahma bayan rasuwar Aisha nashiga tashin hankalin da ban taba fuskantaba, Nihla
kadai Zan gani naji dadi, ita kadai Zan gani yarinyar inji Kamar Aisha tace akusa Dani, hakan
yasa lokacin dazamu dawo gida kai tsaye nace ku fito mutafi, saboda ina tsoron inyiwa Mai
hakuri magana yace bazai ban itaba, nasan shima yaji mutuwar Aysha, Awannan lokacin bazai
taba yarda yarabu da 'yarsa ba, nikuma Rahma bazan iya tahowa nabar jinin Aisha Awannan
wajan ba, shiyasa nadauko ta muka Taho batare da iznin mahaifin ta ba "
Momy tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,"
Dukda taji gaskiyar magana a bakinsu, wani bangaren na zuciyarta bai yardaba, wayarta
tadauka takira layin Nihla, Adayan bangaren wayar tana hannun Dida tana ganin sunan Anty
tasan cewa Momy ce, saboda ita kadai Nihla take cewa Anty
Ta daga wayar tace "Momy Nihla tafita bakin get, wai babanta yazo"
Kashe wayar Momy tayi tace "Innalillah... Yanzu Alhaji shikkenan Nihla tatafi? Inaji ina gani
anrabani da 'yata..." Sai kuka
Su farouq suka dawo gefenta suna bata hakuri, takalli Abba tace "duk abinda yafaru, laifin ka
ne, Inda ace baka nunawa yarsa qiyayya ba, babu abinda zaisa Ibrahim yazo yatafi da ita, idan
ma akan antaho da ita batare da sanin sabane to danaka laifin, na tabbatar labari yaj...j...ji"
numfashi tane yafara sama
Anan maganar ta tsaya, numfashinta yana qara yin sama, cikin tashin hankali Abba yataso
yacire Babbar rigar jikinsa yayi wulli da ita
Ya cacimeta yana kiran "Momy! Momy!!,"
Amma inaaaa, numfashinta ne kawai yake sama, qirjinta sai Dagowa yake, lokaci daya kuma,
jikinta yasaki
Cak Abba yadauketa yadawo da ita kan gadon Daddy, farouq yadauko ruwa a fridge ya shafa
mata, Usman kuma yafara kiran number family doctor nasu yace gashinan zuwa
Saida tadauki lokaci kafin ta farfado, tana bude idonta tafara kuka, Daddy yanaga yashiga
tashin hankali ashe duk abinda yakeji Rahma tafi shi
Mamaki yagama kashe Abba, yanzu duk saboda Nihla suke wannan abun? Lalle ba qaramin so
suke mataba
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Sai yamma liss suka sauka, saboda Alhaji Isma'iel bayasan gudu, futowa sukai daga ciki motar,
Yusif yasaki miqa yana fadin "wash Allah" idonsa akan Nihla
Mami tace "Yusif banasan wannan san jikin fa, to yanmata de basason rago, oya bude boot ka
dauki kaya mushiga"
Yace "yanzu ni dinne rago?"
Murmushi tayi, ta kalli Nihla data shagala wajan kallan hadadden gidan, yanzu itace zatayi
rayuwa acikin wannan gidan? Duniya kenan
Mami tace "Muje ciki Nihla"
Fuskarta Babu yabo ba fallasa tace "bari nadauki wata jakar mami"
Kusadashi taje ta tsaya, shi beyi mata magana ba itama haka, haushi yaqara kama Yusif, duk
murnar dayake zaizo yaganta yaga yanda takoma amma shine tashareshi,
Cikin fishi yadauki jaka guda daya yamiqe zaiyi ciki
Dasauri ta tareshi tareda miqa hannu zata karbi jakar tace masa "kawo jakar"
Lokaci daya hannunsu yahadu dana juna, kallan hannunta yayi zanen qunshin da akayi mata
yayi kyau sosai, Dasauri ya fizge jakar yace "no Barshi kawai"
Daga haka yayi ciki, sai wata tadauka acikin boot din tabiyosu ciki
Dakinda zata zauna mami ta nuna mata, sannan tashige ciki, anan taga babanta yana ciki, yana
futo mata da kayaiyakinta na sakawa daga cikin jakarsa, cikin ranta tace dama de baba yagama
shirya komai
Jakar yadauka yatafi Inda akayi masa masauqi daga can baya
Yana fita taga wayarsa ya mantata, Dasauri tadauka tasaka number Momy tafara kira
Acan kano kuwa gida duk ya hargitse yanmata duk sun shiga damuwa saboda labarin tafiyar
Nihla, Ilham tafi kowa Baqin ciki saboda Babu abokiyar shawara antafi, Dan dole ake saka su
abu su yi, yanzu ma wanka akasa ko wacce tayi domin anjima kadan za'akai kowa dakin mijinta
Apart din Momy kuwa kowa sai neman ta yake yarasa, tunda tashiga dakin Daddy bayan doctor
yazo yagama dubata bata sake futowa ba, wayartace data Nihla a gefenta, adede lokacin
wayarta tafara qara, Dasauri ta dauka tace "Ibrahim Dan Allah kayi hakuri, munsan munyi maka
laifi amma kayi hakuri kadawo min da yarinyar nan" hawaye yazubo mata tasa hannu tashare
Kuka Nihla tafara tace "Anty kidena kuka nice"
Dasauri tace "Nihla kece? Kina ina, gida kuka koma?"
"Anty gida baba yadawo Dani, amma yanzu muna Abuja, mun tafi Abuja gaba daya da zama
Anty"
Momy tace "Innalillah...Nihla banji dadi ba, banji dadin tafiyarki ba yata, kiyafemana kinji?"
Tace "Anty kidena neman yafiyata ba kiyimin komaiba, kedin Kamar mahaifiyata ce"
Momy tace "to ai kinji Nihla, kema kikace kama, ba kama nakeso nayi da mahaifiyar ki ba Nihla,
sonake ki daukeni amatsayin mahaifiyar ki, ki kirani da Momy Kamar yanda 'ya'yan cikina suke
fadamin, ke dasu bakuda banbanci a wajena"
Jikin Nihla yayi sanyi sosai, bata taba sanin cewa Momy batasan Antyn datake fada mataba sai
yau, ashe haka Momy take kaunarta? Wannan wacce irin soyaiya ce? Kasa magana tayi sai
kuka datake sosai abaiyane
Alokacin baba yashigo yadawo daga masallaci kenan, tana ganinsa takwashe wayar, idonta
jajir, tana share hawaye
Zama yayi agefenta ransa abace yafara magana "ke saboda rashin hankali, da hauka dayake
damunki zaki zauna kinawa mutumin dabai damu dake ba kuka,? idan akayi muku auren waye
zai wahala bayan ke?
Anayi wa mace auren dole kuma tayi hakuri tazauna din, amma namiji karkiyi tunanin lokaci
daya zai hakura Yazauna dake amatsayin matar sa, yaron yafuto yace bayasonki to kema ki
cireshi aranki, sannan daga yau ko awaya ne ban yarda ki nemesuba, "
Yana fadin haka yafice yabar mata dakin
Innalillahi... Baba bai taba fishi irin wannan ba, dama ance ka kiyayi fishin mutum Mai hakuri
Wai ita ta d'orawa kanta soyaiyar yaya Abba ne? Yaya zatayi da Rayuwar ta? Yanzu yaya Yusif
yadawo amma ta gagara yimasa magana, ba kuma komai ne yasa hakanba sai tunanin datayi
akan Abba, yadawo daga wata qasa tabi ta shishshige masa, daga qarshe ya Wulaqantata,
tana tsoron shima tayi masa magana daga qarshe yayi mata Wulaqanci, itada shigewa maza
har abada, ya Abba ya koya mata Hankali
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Shadaya da rabi kowa ya watse daga gidan amare anbarsu su kadai, mayafin da'aka lullube
mata kai dashi ta cire tayi wulli dashi tafara fada "ina dalili Zan takura kaina akan wannan
malamin, kun wani rufeni da mayafi ai zafi sai yamin illa"
Saukowa tayi daga gadon, tafara cire kayan ta, daga ita sai under wear a jikinta, tadauki towel
tashige wanka, da ruwa Mai Dan dumi tayi wankan saboda gajiyar biki
Tana futowa daga wanka tadawo gaban mirrow tafara shafe jikinta da turare, ko kayan bacci
bata nemaba ta kashe wutar dakin ta kwanta bacci
Shikuwa Ango Adam sai wajan sha biyu yashigo gidan, hakanan gabansa yake faduwa saboda
baisan mezai tarar ba
Falon yashigo da sallama, yaga Babu kowa, wucewa yayi zai shige dakinsa amma wata zuciyar
tace yakamata kaje kaduba yarinyar nan, haqqinta yana kanka
Dan qaramin tsaki yaja Kamar anyi masa dole, yakoma baya sannan yabude dakin nata yaga
duhu, zuciyarsa daya yakunna wutar dakin, lokaci daya yayi