Showing 18001 words to 21000 words out of 104433 words
Chapter 7 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
kazar taki, nasan kinason kaza shiyasa nasiyo miki ita, zakiji dadin
ta"
Yafadi haka yana miqa mata ledar kaza
Hannu tasa ta karba tace "to najjashi nagode, kaga dare yayi, sha d'aya saura, Zan shiga gida"
Idanunsa ya lumshe sannan yabude su, ahankali yadora hannunsa akan qirjinta, kafin ta farga
yafara murzawa,♀️
Cikin kasalalliyar murya yace"to yanzu ya za'ai kenan? "
Da qarfi kuma cikin fishi ta bige hannunsa, bacin rai ya baiyana akan fuskarta qarara, ta kalleshi
dakyau tace" najjashi bude min Mota nafita kafin na tsinka maka mari anan, anfada maka ni
'yar' iska ce? Saboda ina yawo club club bashi yake nuna jikina nake kaiwa ana amfani da niba,
"
Runtse idonta tayi cikin tsananin bacin rai taci gaba da fadin " najjashi nace kabudemin kofa
kafin inbude idona "
Dariyar yaqe yayi, yayi tunanin zai samu abinda yakeso awajan ta, yayi tunanin itadin yar hannu
ce,koda yaushe yanaso ya gwada sa'arsa akan Diyana ko zai dace, amma abin ya faskara,
cikin borin kunya yace " dama fa gwadaki zanyi,
Kuma kinci Interview"
Cikin fishi tace "uwar Interview, nace kabudemin kofa," ta qarasa maganar cikin tsawa, babu
musu yabude mata kofa, tawullo masa ledar kazar tafice daga cikin motar
Adede lokacin Adam yadawo daga wajan meeting din dasukai a Makaranta, qare mata kallo
yayi tana sanye da riga da wando, duk shape dinta yafuto, babu wani namiji Mai cikakkiyar
lafiya dazai ganta ya qyaleta
Yakalli Agogon motar yaga shadaya saura, yana Kallanta tashige cikin gidan, sannan najjashi
yaja motar sa yabar kofar gidan, shima Adam din yayi horn megadi yabude masa, cikin ransa
yana fadin Allah ya shirya, yarinya kam tagama lalace wa saide addu'ah , Dan nasiha bazata
karbuba adede wannan lokacin
Tana zuwa part dinsu taga Babu kowa afalon danhaka tashige cikin dakin su itada Dida, tana
shiga ta gansu azaune dukansu, Ilham, Nihla, da Dida
Zama tayi akan gadon tana sakin tsaki, dukansu suka kalleta, Nihla tace "meyake faruwa ne
Diyana?"
Cikin bacin rai tace "wallahi daga club nake, wani gaye ya ajiye ni abakin gate d'an iska jiyake
nima irinsa ce shine yasa hannu yana tabamin nono"
Gaba dayansu suka hada baki suna fadin "Nono"
Kallansu tayi, "to miye abin hada baki anan? Ku daga anbaku labari zaku nemi ku ta rawa
mutum jama'ah"
Nihla tace "tab, ai abinne da nauyi, kema Diyana kidena wannan yawon, wannan shigar dakike
duk bai kamata ba"
Ilham ma tace "ato shikuwa gaye ina ruwansa yaga abubuwa asarari ai dole ya gwada ko zai
dace"
Dida tace "gara de ku fada mata ko zataji," sannan ta maida Kallanta ga yayar tata tace "gara
ma wallahi, gaba kya sake fita"
Diyana de tayi shiru tana jinsu, amma tabbas yaukam najjashi ya nuna mata cewa ita
yar'qaramar 'yar club ce
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Aslam yasamu tarba sosai daga wajan abokin daddy, cikin kwana biyun dayayi a qasar ya
fahimci halin Aysha, tanada nutsuwa sosai da sosai, bako Mai ne yake qara birgeshi da yarinyar
ba sai Kallanta, duk lokacin data daga ido ta kalleshi sai yaji wani abu ya soki zuciyarsa
Haka nan ya tsinci kansa dajin dadin kasancewar su tare da yarinyar, kwata-kwata ya Manta da
maganar Daddy dayace kada su dauki lokaci Mai tsawo basu dawoba
Yau kuwa Tun safe Daddy ya kirashi yace sukamo hanya su Taho gida, Dan haka washe gari
sukai shiri suka Taho shida ita
Acikin jirgi ma tana gefensa, sau uku tana kamashi yana Kallanta
Tace "yaya Aslam lafiya kuwa?"
"akwai abinda yake damuna qanwata"
Kokarin saka belt take saboda sanarwar da ake cewa jirgi zai tashi
"meyake faruwa?, meyake damunka?"
Yace "kece, kece damuwata Aysha, narasa yanda zanyi da soyaiyar ki"
Sakin belt din Hannunta tayi ta rufe fuskarta cikeda kunya
Dab da ita ya matso yadauki belt din zai saka mata, tanajin sa akusa da ita, Kamar zai maida ta
jikinsa
Harya saka mata belt din bata bude fuskarta ba
"kibude fuskar ki mana"
Cikin kunya tabude fuskar tata
Hannunsa yadora akan nata yariqe yace "Aysha kimin alqawari duk rintsi bazaki rabu da niba"
Wani iri takeji yanda yakama mata hannu, danta taqaita maganar tace masa "insha Allah yaya
Aslam, nayima alqawari"
Ajiyar zuciya yasauke, sannan yasaki hannunta yana jin farin ciki naqara ratsashi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tsaye suke a Airport, Fawaz, Adam da Abba
Suna jiran jirginsu Aslam ya sauka, Fawaz yace "guy's kunsan menene, ni arayuwata kwata
kwata mata basa gabana wallahi, amma tunda nayi karo da'ita take nema ta addabi nan d'ina"
Yaqarasa maganar yana dora hannunsa asetin zuciyarsa
Da mamaki Abba da Adam suka kalleshi, Adam yace "Wacece?"
Ahankali yace "Nihla"
Dasauri Abba ya kalleshi, haka nan yaji haushin maganar Fawaz din, yayi shiru baice komai ba,
Adam yace "Babu laifi tanada hankali, yarinyar akwai Face, duk family dinnan idan kana neman
kyau kazo wajanta kagama Alhaji"
Fawaz yace"no ni bawai kyanta ne yajani ba, ina tunanin idan na aure ta bazata damu da
halaiyataba, zata barni insha abinda raina yakeso "
Wannan karon Abba kasa hakuri yayi yadubi Fawaz din yace masa "Nihla?"
Hankali kwance Fawaz yace "yes"
Adam yace "nikam gaskiya idan Zabi za'a bani ko to Zan Zabi Dida, najima ina son yarinyar but
narasa yanda Zan fuskanceta in fada mata, bazan iya zuwa wajanta da girmana ina qaramar
murya akan tasoni ba, amma gaskiya sosai nake sonta, dama inka dauke Nihla da Dida da
Aysha, tofa sauran biyun sai Ahankali, Ilham rashin kunya, Diyana kuwa Hmm karma kasata
acikin lissafi, Dan rannan ma wani gaye nagani yasauketa amota "
" dan Allah kundameni da maganar wannan yaran, ku yanzu ko kunya bakwaji kuzauna kuna
cewa qannan bayan ku kukeso? Ahaifi yaran agabanku amma kudinga wannan maganar? "
Cewar Abba
Fawaz yadafa kafadarsa
" zamu ga yarinyar da zaka Aura Abba "
Suna wannan maganar su Aslam suka futo, shine yake riqe da jakar ayshan, Tana ganin Fawaz
ta qarasa ta rungumeshi tace
" yaya Fawaz "
Cikin farin ciki yace " Sannu da zuwa qanwata, "
Su Adam ta gaisar, gaba daya sun sauya mata, in akan hanya ta gansu ba lalle taganesu ba,
shima Fawaz din dan kullum suna gaisawa dasu ne ta cht
Hannun ta yaja yabude mata Mota ta shiga, Adam ma yashiga, shikuma Aslam zasu tafi shida
Abba
Ta glass din motar ya leqo kansa yace "my dear shikkenan sai munyi waya ko?"
Kunya ta kama Aysha, shi yaya Aslam ko kunyar qaninsa Adam dayake wajan bayayi zai yi
mata wannan maganar?
Ahankali ta daga kanta, Fawaz ya kalli Adam suka hada ido
Basu cemusu komai ba, sukaja motar suka tafi
Shima Aslam ya shige ta Abba suka tafi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan dawowar Aysha da kwana biyu Aslam yazo part din su Abba, suna zaune agefen gado
da takardu agabansu suna tsara yanda zasu gina wani sabon kamfanin dasuke son budewa
tare
Suna gama tattaunawa Aslam ya ajiye file din a gefensa yakalli Abba "Abokina gaskiya inason
yarinyar nan, Aysha tagama tafiya da nutsuwa ta, zan jira agama wannan meeting din da Daddy
yace za'ayi bayan angama Zan sanar dasu kawai ayi mana aure, inyaso saita dawo nan taci
gaba da karatun ta tunda yanzu tafara"
Kallansa Abba yayi "Aslam kuna bani mamaki yanda kuka dage akan wannan qananun yaran"
"Abba karka renamin hankali, haka kakeso muyi ta zama ne? Ko kana tunanin muna germany
bana sane da irin juyin dakake cikin dare kakasa bacci?"
"Malam ni bana wani juyi cikin dare"cewar Abba
"qarya kake Abba, to lemon tsamin danake gani cikin dozbin fa?ni bazan kashe kaina ba, aure
nakeso kawai"
"to karka min kuka" inji Abba
Adede lokacin taturo kofar dakin tashigo, bakinta dauke da sallama, tana riqeda flet me dauke
da meat pie
Kallansa tayi "ya Abba ga meat pie nayima,"
Agajarce yace mata "Ok"
Ta kalli Aslam tace "Barka da wannan lokaci ya Aslam"
Cikin sakin fuska yace"yawwa Nihla, mungode sosai "
Murmushi tayi tajuya tafice daga dakin
Aslam na ganin fitarta ya kalli Abba "Abokina yarinyar nanfa nagama lura tana sonka, irin yanda
take kula dakai zaisa kowa yagane hakan"
Kallan Aslam yayi "wacce irin magana kake haka Aslam? Yaushe Nihla ta girma dahar zatasan
wani soyaiya? She's 17 year's fa"
"to menene aciki?"
Hannu yadaga masa "no, no, dakata Aslam, kafi kowa sanin nafisan na Auri mace babba,
wadda ta waye, me ilmi, ta mallaki duk abinda nakeso ajikin mace, sannan me hankali, amma
Nihla renonta kawai zanyi, Aslam nasan kaina inada tsananin sha'awa, kuma ni kadai nasan
yanda nakeji, wannan yarinyar zan'iya kakkaryata Tun a daren farko idan ma ta nuna kenan,
bare ma yanzu dabata nunaba "
" dan Allah ka dakata Abba, wannan yarinyar fa qanwar ka ce, menene aciki idan ka aure ta?
Meka dauki mace Abba? Kana maganar nuna ai kaine zaka maida ta hakan "
" dan Allah kadena min wannan maganar Aslam, nafadama bazan iyaba, nafisan mace me tarin
ilmi, wadda tahada komai, amma Nihla amatsayin qanwata nake ganinta "
Aslam yace" nasan dalilin dayasa kake wannan maganar, kuma kasan hakan ba qaramin
kuskure bane idan ka aikata shi, ba kuma ranka ne kadai zai baci ba harda namu baki daya,
inaso ka tuna halin da Diddi ta shiga itada baba Basiru akan hakan "
Yana fadar haka yayi wulli da file din dasukai magana akansa yafice daga dakin cikin fishi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"wayyo Allah ummah cikina ciwo, zan mutu ummah, ummah Dan Allah kiyafemin, kicewa
Abbanmu shima yayafemin"
Hajiya abida tashare hawayen idonta "Aysha kidena maganar mutuwa, ba zaki mutu ba, 'yata
bazaki tafi kibarni ba"
Ilham idanunta sunyi jajir tace "Anty Aysha kiyi shiru Dan Allah, bazaki mutuba, zaki tashi mu
rayu tare"
Hannun Ilham ta riqe tace"ilham kicewa yaya Aslam ina sonsa, bazan tashi ba Ilham ni nasan
yanda nakeji, nadade ina wannan ciwon cikin, amma nayau dabanne ilham "
Alhaji Basiru ne yasa hannu da kansa yadauketa suka futo daga cikin motar suka shiga cikin
asibitin dasuka qaraso
Likitoci ne suka karbi aysha, nan take suka shiga bata temakon gaggawa, Alhaji Basiru
Yazauna awajan yayi tagumi
Daga baya yan gidan gaba dayansu suka qaraso asbitin, Aslam yafi kowa shiga tashin hankali,
Daddy ya kalli Alhaji Basiru yace "wai dama batada lafiya ne?"
"wallahi yaya Abubakar kwana mukai bamuyi bacci ba, cikin ta yana ciwo, bayan wani dan
lokaci saiya lafa, shine muka Taho Asbiti yanzu"
Alhaji Baqir yace "subhanallah, Allah yabata lafiya"
Gaba dayansu sukace amin, haka suka zauna jugum jugum, babu wanda yankewa dan'uwansa
magana, har likitocin suka futo
Gaba dayansu sukai kansu da tambaya, Likitan ya goge gumin fuskarsa yace "Alhaji saide kuyi
hakuri, Allah yayi mata cikawa, munyi iya kokarin mu ganin mun ceto Rayuwar ta, amma hakan
ya gagara sakamakon ciwon Hanta datake dauke dashi, hantarta tariga ta lalace, kuyi hakuri"
Ilham najin haka ta yanke jiki tafadi, yaran kuwa kowa kuka yake, Aslam ya sulale Yazauna
aqasa yana maimaita kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju'un acikin ransa
Gaba daya waje ya kaure da koke koke, babu me lallashin wani, haka suka dauki gawar Aysha
suka tafi gida, akai mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya, Aslam kuka Kamar mace, duk
yafita a hayyacinsa, saide muce Allah yaji qanta, idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda akai wannan mutuwa gidan yadawo shiru, Diyana kuwa kullum tana cikin hijabi
tunda taga aysha qiri-qiri tamutu da quruciyarta, sosai mutuwar tataba matasan gidan, saboda
basu taba kawowa kowa mutuwa acikinsu ba
Ranar ukunta yayi daidai da ranar da Daddy ya sanar za'ai meeting, amma ganin anyi musu
rashi yasa aka sanarwa kowa sai bayan sati biyu akwai gagarumin family meeting.
Hakan ce kuwa ta kasance,ranarda sati biyu tacika kowa yatafi Babban dakin taro nacikin gidan
mata da maza manya da yara, Usman shida matar sa da yaransa biyu, sai Aliyu shima yazo da
matar sa da dansa daya namiji, farouq kuwa matar sa ko haihuwa batayi ba
kowa yazo yanaso yaji abinda wannan wasiyya ta qunsa
Samarin ne awaje kawai basu shiga ciki ba suna jira saisu Daddy sun qaraso
Sunata fira kadan kadan amma Aslam baya magana, Adam kuwa gabansa ne yake ta faduwa
harya kasa boyewa yace "nifa gaskiya meeting dinnan danya zama dole ne amma gaskiya da
bazan zoba, yau inada lacture, sannan gabana faduwa yake narasa dalili"
Fawaz kallansa yayi bai tankaba, Abba ma shiru yayi, Aslam kuwa daja tunda aysha tarasu
suka kasa gane kansa
Kallansu yayi yace"wai badaku nake bane duk kunmin shiru?"
Ajiyar zuciya Fawaz yasauke yace" kai sai yanzu kakeji,? ni Tun jiya gabana yake faduwa,
Kamar akwai abinda yake san faruwa Dani, amma koma menene Allah yasa ya sameni ni kadai
banda Nihla "
Kallansa Aslam yayi cikin mamaki, to kode Fawaz nason Nihla ne?
Kafin wani yace wani abu su Daddy suka qaraso wajan, shida Alhaji Baqir da Alhaji Basiru
Dakin taron suka shiga, sannan suma samarin suka bisu abaya
Wajan meeting din yayi kyau an qawata shi da lemuka da ruwa domin baqi
Nihla tana kusada Momy, yayinda Ilham ma take gaban ummanta hajiya abida, suma su Dida
itada Diyana suna gaban maman su hajiya Farida
Su daddy suna zama hall din yayi shiru, Kamar ruwa ya cinyesu, megadin gidanne yaqaraso
dauke da akwatin da aka rufe takardar wasiyya aciki ya ajiye yajuya yafita
Daddy dakansa yatashi yabude, kowa yazuba masa na mujiya, yadauko takardar Yazauna
sannan ya'ajiyeta agabansa
Yakai dubansa wajan samarin sun zauna waje daya gaba dayansu, Adam ya kalla yace "Adam
taso kabude mana taro da Addu'ah"
Babu musu yatashi yadinga kwararo musu addu'ah, sannan aka shafa
Daddy yayi gyaran murya, yafara magana "Alhamdulillah, muna qara yiwa Allah godia akan
Tsawon rai dayayi mana har muka kawo wannan lokaci cikin kwanciyar hankali, wadanda suka
rasu acikin wannan family Aisha, da takwararta Aysha, muna yi musu addu'ah Allah yaji qan su"
Gaba daya aka amsa masa da "Amin"
Sannan yaci gaba da fadin
"insha Allah yanzu zamuji dalilin daya taramu anan wajan "
hall yaqara yin tsit, Daddy yabude takardar yayi tozali da rubutun Ajami, yadaga kansa yasake
duban Adam yace"da Ajami sukayi rubutun, Adam kaine malami zoka karanta mana"
Hajiya na'ila tafara karkad'a kafarta tana hura hanci , jin ansake kiran dannata akaro na biyu
Jikin Adam a sanyaye yaje gaban iyayen nasa ya karbi takardar yafara karanta wa :Assalamu
alaikum jama'ar wannan dangi Mai albarka, ni Abubakar Mazawaje mun zauna tareda matana
guda biyu mun rubuta wannan wasiyya badan komai ba saidon hadin kan wannan zuri'a,mun
yanke shawarar hada jikokinmu aure domin zumunci yaqara qullu wa,...
Adam yana zuwa nan yaji gabansa yafadi, jikinsa yafara rawa, hannunsa sai karkarwa yake yaji
maganar akansu ne Wato jikoki
Cikin daure fuska Alhaji Baqir ya kalleshi "kai menene haka? Cigaba mana"
Muryar Adam na rawa Kamar ba namiji ba yaci gaba da karatun
"Duk mazan da suke cikin wannan family an mallaka wa kowa filin dazai gina,duk Wanda yayi
aure acikin wadannan yara dazamu ambata, to lalle lalle ya tabbatar yasake wani auren yacika
namu Burin
munyanke shawara tareda umarnin cewa Ilham 'yar gidan Basiru zata auri Aslam Dan Alhaji
Baqir
Dida yar gidan Farida zata auri Fawaz yaron Alhaji Basiru
sannan Adam yaron Alhaji Baqir zai auri Diyana, yarinyar hajiya Farida
saikuma na qarshe takwarana Abubakar Wato Abba, zai auri Aisha yar gidan Alhaji Basiru
tareda Nihla yarinyar Aisha "
Wannan dalilin ne yasa mukayi muku hani akan duk wani taro acikin family, na suna kona aure,
saboda gagarumin taron dazaku hada na auren jikokinmu, muna yiwa kowa fatan alkhaairi "
Takardar ya ajiye, saboda jiri-jiri dayake gani
Cikin fishi hajiya Na'ila ta miqe tsaye tace "wallahi bazata sa'buba, kowa yasan kaf family dinan
yarana sunada hankali, babu wanda yakai Adam sanin Allah yace, annabi yace,
amma arasa yarinyar da za'a liqa masa sai Diyana, yarinyar dakowa yasan tagama
tambad'ewa atiti, shikuma Aslam wai Ilham, da rashin kunyar ta zaiji koda aikin gabansa "
Hajiya Farida cikin sauri itama tatashi tsaye ta maida wa hajiya Na'ila martani,
" ke saurara hajiya Na'ila, dakike cewa 'yata tagama tambadewa ambawa danki jinake yata
Dida aka hada da qungurumin Mashayi ♀️, ni nace wani abu ne? Saike me bakin magana?"
Hajiya abia tayi shiru, tabbas taji haushin furucinsu akan yayanta, sai yau take dana sani akan
halin Fawaz na shaye shaye, ta kalli hajiya Farida tace
" Farida Karki sake danganta min dana da sunan shaye shaye, "
Hajiya Farida tace " besha bane? Jinake Tun yana yaro kika gama lalata masa tarbiya, antashi
an Auro mana baragurbi cikin family"
Gaba daya hall din ya kaure da surutu, da hayania, Aslam yayi shiru yana tunani, tayaya zai iya
Rayuwar aure da qanwar Aysha? Yanzu kenan da ace tana raye ma Abba zata aura?
Innalillah...wannan wacce mahaukaciyar wasiyya ce?
Momy kuwa hamdala take cikin ranta, shikkenan Abbanta zai auri nihila
Adam kuwa me karanta wasiyya yana ganin Ance Diyana zai aura yatuna lokacin data futo