Showing 3001 words to 6000 words out of 104433 words

Chapter 2 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf

shirya mana zuria "

Tace" Amin Anty Rahma "

Hankalinta ta maida kan Nihla tace"ke tashi kije kicire kayanki kiyi sallah saikizo kici abinci "

Tace "to Diddi" sannan tatashi tayi cikin d'akin datake kwana aciki, anan taci karo da kayan
abinci da katan katan d'in lemuka, lokaci d'aya wani farin ciki yakamata, saida taje ta tattaba su
sannan tafara cire kayan nata

Usman Wanda shine babba acikinsu yakalli Diddi yace "Amma Diddi idan zamu tafi tareda Nihla
zamu tafi ko, saiki bawa Momy ita"

Shima Aliyu Wanda yake binsa yace "eh wallahi, kinga bamuda qanwa mace, mu kadai ne,
Diddi kibamu ita Dan Allah"

Abba yakalli Usman harya gama magana, Aliyu ma yana farawa yasake maida kallansa kan
Aliyu, saikuma farouq Wanda yake bin Aliyu yace "Diddi, idan kika bamu ita kinga tazama
qanwar mu, komai mune zamu dinga yimata, munasan Baby amma Babu agidan mu, saisu
dinga tafiya makaranta itada Abba"
Momy ta kalli Abba dayakebin yayun nasa da kallo tace "Abba nah bakace komai ba, kanaji duk
brothers d'inka sunyi magana, kaima kanaso abamu Nihla saiku dinga wasa tare ko?"

Ataqaice yace mata "Eh"

Girgiza kanta tayi sannan ta kalli Diddi tace "Aisha, kinsan lokacin bikina da yayanki, duk yaran
nan da hankalin ki aka haifesu, Tun kafin Allah yabani haihuwa nakeso Allah yasa nahaifi mace,
amma Allah da ikonsa bai baniba, saide maza, Aisha Dan Allah kibani Nihla wallahi inason
yarinyar sosai, bazan iya kwatanta miki yanda nake santaba, "
Daria Diddi tayi"yanzu Anty Rahma banda rigimarku idan na baku ita nikuma fa?"

Cikin sauri momy tace " Sai Allah yabaki wata, may be ke Allah yayi mata zaki dinga haifa
shikuma yayanki maza"

"A a Anty Rahma, kuyi hakuri amma bazan iya baku ba, 'yar tawa ita kad'ai jal Zan dauka
naqara miki, sun zama su biyar fa kenan, nikuma Babu ko daya"

"idan kika bani ita saikiga Allah yabaki wata"

"Anty Rahma, Allah hakuri zakuyi, amma kyauta kacokam, inaaa"

Cikin sanyin jiki Momy tace "to shikkenan Aisha, Tun farkoma dana sani Mai hakuri na yiwa
maganar ba keba, nasan shi bazai min musu ba,"

Diddi tace "zata dinga zuwa muku hutu dai, shima ai yayi"

Momy tace "Aisha irin wannan soyaiya idan zakiyi auren ta yaya zaki yi?"

"ni kaina bansaniba Anty Rahma, amma banason rabuwa da 'yata"

Murmushi kawai momy tayi, tana Jinjina irin wannan qauna da Diddi takeyiwa Nihla, saide anata
bangaren kawai jinta take,banda de itace ta haifi Nihla dazata iya cewa duk duniya banda ita
Babu Wanda yakai ta son yarinyar, jitake Kamar ta d'auketa gaba daya

Diddi ta dubeta tace "Anty Rahma ban tambayekiba, yaya labarin matar yaya Basiru kuwa?
Tasauya ko halin ta yana nan?"

Ajiyar zuciya tayi "Aisha ai wannan baiwar Allah halin ta bazai sauya ba sai wani ikon Allah,
gaba d'ayafa nema take ta lalata tarbiyar yaranta, shi Fawaz nema yakema yafi qarfin iyayen,
abokan banza yake kulawa, idan su Abba zasu tafi school bayason binsu sai anyi da
gaske,gaba d'aya sunansa yabace, idan zaki wuni kina cewa fawaz bazai amsaba, saide gaye
, ita kuma Aysha takwararki tace bazata sake zuwa makaranta ba saide afitar da'ita qasar
waje, Acan zatayi, ita kuma qanwarta Ilham tana nan tana zuba rashin kunya, bata barwa
kowaba, yara qanana sai rashin kunya "

"Amma yaya Basiru yana gani yazuba musu ido yana kallan su?"

"to yaya zai musu Aisha?Kinsan hali dai, dama yayanki ne Mai tsawatarwa, to shima yayi
shiru yazuba musu ido, yace lokacin dazaiyi auren ai baiyi shawara dashiba"

"to ina Diyana da Dida, su Aslam da Adam?"

Momy tace "wallahi kowa yana lafiya,"

Haka sukaci gaba da firarsu, Diddi tana Tambayar Momy labarin gida, ita kuma tana fada mata,
har yamma tayi liss
Diddi ta dubi Nihla data baje kayan wasan 'yar tsana tanayi tace "Nihla tashi kidauki nera
hamsin agefen katifar nan kije shagon bashari kisiyo omo naduka"

Tace "to Diddi"
Sannan ta kalli Abba daya zubawa kayan wasan nata ido tace masa "zakaje?"

Girgiza mata kai yayi, alamun bazashi ba, saida ta harareshi sannan tace "karkaje d'in"
Ta d'auki kud'in tayi ficewarta

Momy tayi daria tace"walllahi kuwa,yasha zamansa kema kin huta abinki, "

Ta kalli Abba tace" kaide akan wannan halin naka na miskilanci bakada ranar samun matar
aure, Dan babu wacce zata soka ahaka "

Diddi tace" Haba Anty Rahma, meyasa kike fad'ar haka, tayaya zai rasa matar aure? Abba
nefa, ABUBAKAR SADIQ, me sunan mahaifina sannan kuma me sunan yayana, nida kaina Zan
samo masa matar dazai aura muna nan dake "

Daria yayi, sosai kuma dariyar tayi masa kyau yace"Diddi Zan kaiki umarah"

Cikin farinciki tace "Umarah Abba!"

Yace "harda Hajji"

"Alhamdulillah yau haihuwa tayi rana, Yaya bekaini ba gashi Abba zaikaini"

Momy tace "inde Abba ne zamu ganku arana"

Dariya sukayi gaba dayansu

"Diddi ga omon" cewar Nihla data shigo yanzu

Karbar omon tayi, tace "jeki zuba ruwa inzo na wanke miki kanki, saina miki wanka ma gaba
d'aya"

Ruwan tazuba tadawo ta zauna agaban Diddi kusa da Abba, sannan ta d'ora kanta akan cinyar
Diddin, hannu tasa ta warware mata gashin kanta, daga Momy har yaran nata duk kallan yawan
gashin yarinyar suke,
Saida tagama warware mata sannan tace "Muje na wanke miki to"

"Diddi Zan wanke mata"

Cikeda mamaki kowa yake kallansa, musanman Momy, cikin ranta tace tabd'i
Amma a fili sai tace, "lalle Nihla kin ciri tuta"

Diddi tayi daria tace"lalle yau haihuwa tanamin rana sosai"

takai Kallanta ga Nihla tace " ke tashi kije yayanki ya wanke miki kanki "

Babu musu tatashi ta cire kayan jikinta, daga ita sai pant tabishi suka futo tsakar gidan ta
tsugunna, shima tsugunnawa yayi sannan yafara zuba mata ruwa akan, ba komai yasa yace
zai wanke mata kanba, saidan yanaso yataba gashin yaji, omon yad'auka yazuba mata akan
sannan yafara wankewa yana dirzawa da duka hannunsa biyu Momy dasuke zaune a rumfa kallansu take tanajin d'ad'i aranta, ashe Abban nata ya'iya wankin
kai, shikuwa Usman hannu yasa a aljihun jeans d'insa yad'auko wayarsa yana musu photo

Kannata yafita sosaai amma haka yaita wasa da gashin sannan yadena zuba mata Ruwan, ya
kalleta Ahankali yace "kicire wandon nayi miki wanka"

Hannu tasa ta goge Ruwan daya zubo mata a fuskarta ta d'aga murya tace "Diddi wai yamin
wanka?"

Cikin rashin damuwa tace "Eh yayi miki mana"

Ahankali tatashi ta cire wandon sannan ta tsugunna, babu bata lokaci yafara yimata wankan,
saida ya wanke mata jikinta tass sannan yacemata "tashi kije"

Bata damu da yanda yayi mata maganar Kamar bayaso ba, tatashi tatafi d'aki da gudu

Da yamma Usman da Aliyu da Farouq suka fice yawo ganin gari
Nihla kuwa tunda Abba yayi mata wanka ta shiga d'aki tasaka wata 'yar qaramar riga marar
hannu tashan iska, ta kwanta tana wasa tana surutun ta ita kad'ai anan bacci ya dauke ta

Diddi ta kalli Abba da Idanunsa suke lumshe wa tace"me sunan yaya nah, kai ba zakaje yawon
kaga gari ba? "

Hamma yayi yace" Diddi bacci nakeji "

" to tashi ka shiga d'aki mana, jeka kwanta kahuta, dama ai akwai gajiya kunsha hanya "

Yana shiga d'aki yaga Nihla na bacci, katifar tanada girma sosai, shima ya kwanta agefenta,
nan da nan kuwa yayi bacci

Saida Momy ta leqo d'akin taga sunyi bacci dukansu sannan ta kalli Diddi tace" Aisha kin
tambayeni kowa amma baki tambayi yayanki ba, "

Lokaci d'aya yanayin Diddi ya sauya," Anty Rahma yaya bayasona yanzu, wannan shine dalilin
dayasa bazan iya baki Nihla ba, qiyaiyar dayakemin bakan kowa zata komaba sai kan
'yata,nikuma ina son yata, banasan wani abu yasameta, yanzu haka tsoron irin amsar dazaki
bani ne yasa ban tambayeki shiba, saboda nasan ba zanji amsa Mai d'ad'i ba "
hawaye ne suka zubo mata, wasa wasa Tun ta nayi marar sauti harta dawo tana kuka sosai
Kamar qaramar yarinya

Ajiyar zuciya Momy tayi, ta dafata "Aisha yayanki baya fishi dake yanzu, idan ma yanayi to
kad'anne,kisaki ranki kidena damuwa, wai Aisha ke kadai kikai wannan laifin ne? Baga Basiru
nanba, ganin yarane yasa banyi miki fada ba, ki kalli jikin ki aisha kin kasa kwantar da hankalin
ki duk kin rame, meyasa hakan Aisha "
Cikin kuka tace" dole zanyi kuka Anty Rahma, ki kalli irin Rayuwar danake nida 'yata, Yaya yana
dashi bazai tallafamin ba, uwarmu d'aya ubanmu d'aya, wacce irin qiyaiya ce wannan? "

"Aisha idan kika sake zancen qiyaiyar nan tsakanin keda yayanki ranki zai baci yanzun nan,
yanzu haka yayanki ne ya shirya mana wannan tafiyar, kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki,
watarana komai zaizo qarshe"

Jakarta ta bude tadauko kudi masu yawa ta miqa mata, Diddi tasa hannu takarba,sannan

tasake dauko mata wata sarqa ta gold tabata, sannan tace "ki ajiye wannan sarqar awajan ki,
dakaina nasiyo miki ita, tanada tsada, duk lokacin dakika buqaci kudi idan babu ahannun ki kije
kasuwa kisiyar kiyi amfani da kudin, shikuma wannan kudin dubu hamsin ne,yayanki yace
akawo miki"
Hawaye masu d'umi suka zubo wa Diddi, taji dadin kyautar amma wani bangare na zuciyarta ya
kasa yarda cewa yayanta ne ya aiko mata da kudin, ta kalli Momy tace "nagode sosai Anty
Rahma, Allah yasaka da alkhaairi"

Momy ba tace komaiba tajata jikinta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, saida taga ta daina
kukan tasaki ranta, sannan suka tashi suka fara shirye-shiryen had'a Abincin dare


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Cikin bacci taji anajan gashin girarta, zafi taji, lokaci d'aya tabude idonta, dashi tafara yin tozali
yana kwance agefenta yazuba mata ido, tace "kai meyasa kakejamin girata, Allah Zan fadawa
Diddi"

"to sai bacci kike kitashi mana, tashi natayaki wasa"

Kafada ta maqale masa "bazanyi wasa dakai ba,saboda d'azu kaine kaqi rakani shago nasiyo
omo"

Kansa ya nuna da hannunsa yace "nid'in? bana wanke miki kanki ba?"

Daria tasaka, gefen kumatunta duka biyun suka lotsa, ahankali ya d'ora hannunsa awajan,
itama hannunta tasaka ta janye nasa hannun daga fuskarta tace "eh natuna, kamin wanka, to
mun shirya, meyasa kai baka magana? Anty tace baka magana"

"inayi mana, gashi ina magana dake"

Gyara kwanciyar ta tayi Tajuyo tana fuskantarsa, kusancin yayi kusanci Kamar zata shige
jikinsa, tace"meyasa to kakeyi Dani?"

" because You're my friend "

Girgiza kanta tayi tace " niban gane me kace ba"

"Zan fad'amiki"

"yaran Momy kun tashi daga baccin kenan" Dagowa sukai dukansu suka kalleta, Dasauri Nihla

tace "yawwa Anty, me You're my friend take nufi?"

"Nihla Anty, Anty, nahanaki cewa Antyn nan kinqi ji, to zamu bata dake, kutashi ku futo kuyi
shirin sallah, magrib takusa,"

tana fadar haka tafice daga d'akin, itama Nihla tashi tayi tafice tabar Abba shi kad'ai


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️



Da daddare dukansu suka baje a tsakar gidan akan tabarma, Nihla ta liqewa Usman tana ganin
game a wayarsa, gama cin Abincin su kenan, sai lemuka dasuke ajiye agefe Wanda suka sha
sukabar sauran

Baba ya kalli Momy yace "Amma hajiya ai zakuyi mana sati d'aya ko"

Momy tace "sati Ibrahim! Haba Mai hakuri, sati ai yayi yawa, jibi jibin nan zamu tafi insha Allah,
kwana biyu zamuyi muku, saboda yara suna zuwa school, yanzu ma saida muka sanar a
makaranta sannan muka Taho dasu"

Yace "to hajiya, ai hakanma kunyi kokari sosai, su Alhajin de duk suna lafiya ko?"

"lafiya kalau alhmdlh"

"to yaya wajan su hajiya Farida da yaran nata su Dida da Diyana?"

Wannan karan saida Momy tayi Murmushi, saboda tasan duk cikin mazawaje family baya shiri
da kowa Kamar hajiya Farida, tace masa "suma suna nan kalau"

Yace "to madallah, Allah yasaka da alkhaairi Hajiya, Aisha duk ta nunamin abin arziqi"

Murmushi Momy tayi ba tace komaiba, suna nan zaune suna taba hira har dare yayi, suka nemi
makwanci, Usman da Aliyu da farouq sukabi baba d'akinsa, Momy da Diddi da Abba da Nihla
suka tafi dayan d'akin suma, Momy ce ta gyara musu shimfida daga nan taja Nihla jikinta suka
kwanta, yanda tasata a gabanta Kamar wani zai qwace mata ita, har Diddi nayi musu daria

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari bayan sallar asuba yaran duk bacci suka koma, sai Diddi da Momy ne kawai suke
fira sama-sama, gari nayin haske suka fara had'a abin karya wa, zuwa tayi d'aki tataso Nihla

tashiryata tsaf sannan tabata nera ashirin tace ta tatafi makaranta
Yauma tana fita kofar gida taga gate din gidansu abude,direban gidan yana goge Mota, shikuma
yana tsaye da lunch box ahannun sa, lokaci d'aya farin ciki ya kamata, yau itace da kanta tafara
d'aga masa hannu, cikin sauri ya ajiye Abincin nasa aqasa yafuto da gudu, direban yana
kiransa amma ko waiwayowa baiyi ba, qyaleshi yayi amma de yabishi da kallo yanaso yaga
Inda zaije
Kusa da ita yaje ya kalleta "meyasa jiya ban ganki ahanya ba da aka tashi daga school?"

Zaro ido tayi "laaaa ashe kaima kana nemana, nima inata kallan hanya banganka ba"

Zuba mata ido yayi yace "yaya sunanki?"

Tace "Nihla Ibrahim Mai hakuri, kaifa?"

Cikin farin ciki yace "Yusif Isma'eeil,"

Hannun ta yaja yafara tafiya "zomuje direba yakaimu school tare"

Qwace hannunta tayi tace "um um Babu ruwana Diddi zata dakeni, tace karna tsaya ako'ina"
Tana fadar haka taqwace hannunta tatafi da gudu, shima Kallanta yake yana daria, sannan ya
juya ya koma cikin gidansu

Da azahar ana tashinsu daga makaranta bata tsaya wasaba tataho gida, tana hanya bataga
motarsu ba, saida ta kusa qarasawa gida sannan ta hangi motarsu suna shiga gida

Bayan sallar la'asar dukansu suna zaune suna fira, Nihla tana kwance akan tabarma Momy
tajata ta d'ora mata kanta akan cinyarta
Sukuma mazan suna buga ball Ahankali kasancewar gidan akwai d'an fad'i kad'an yau harda
Abba akeyi, yana sanye da qananun kaya riga me Jan duhu da wandon jeans amma ya tattare
wandon daga qasa ya maidashi Kamar three quater
Saida sukayi suka gaji sannan kowa Yazauna, wayar Usman Abba ya karba yafara game, Nihla
tanajin qaran game tatashi takoma wajansa tana gani, qasa-qasa tayi muryarta tace masa
"zomuje yawo"

Shiru yayi ya qyaleta, tasake cewa "kaji"

Kallanta yayi becemata komaiba ya kashe game din yasaka wayar a aljihunsa yatashi yace
mata "Muje"

Daria tayi itama tatashi, takama hannunsa suka fara tafiya ya kalle Momy yace "Momy munfita"

Cikin farin-ciki tace "to Abba na, amma Karku d'ad'e naga garin akwai hadari"

Basuce mata komaiba suka fice daga gidan ita kuwa Nihla takama hannunsa ta riqe sosai
Suna fita suka dinga zaga garin, sai surutu take masa amma amsar datake samu kad'ance
daga wajansa

Kallanta yayi "ina zamuje?"

Tace "zakaje rafi innuna ma ruwa dayawa muyi wasa saimu dawo?"

"akwai ruwa sosai?"

Tace "eh akwai sosai baka ganiba harda kwale-kwale"

Yace "to Muje mu"

Tafiya sukayi me nisa sosai, Yakalleta yana haki yace "kewai bamuzo bane?"

"to idan munzo ai zakaga Ruwan ko? Kaide kataho kawai"

Bece da'ita komaiba suka cigaba da tafiya har sukazo wajan, hannunsa tasaki tatafi wajan
Ruwan da gudu tana daria, abaki bakin Ruwan ta tsaya, sannan tasaka hannunta tad'ebo
Ruwan ta watsa masa

Firgigit yayi, yadawo hankalinsa daga kallan yawan Ruwan wajan, yace "kika jiqani?"

Kafin tabashi amsa ya qaraso wajan shima yad'iba ya watsa mata, bata damuba, dariya ma tayi
tasake diban wani tajiqashi, shima yasake ramawa, haka duk suka jiqa jikinsu shima ya
biyemata sai daria suke cikin farin-ciki

Hijabin jikinta ta cire tana wullashi sama, tana cafewa, sai tsalle take tanata farin ciki, wayar
Usman yadauko acikin aljihun wandon sa ya tsaya yanayi mata photo, gani tayi yana binta da
waya ta tsaya tace "photo kakemin?"

"eh" shine kawai amsar daya bata

Tace "to tsaya na gyara"

Tsayuwa ta gyara, yanata yimata photon iri iri, ya shagala yanayi mata pictures din, ta tsugunna
ta d'ebi yashin dayake wajan ta zuba masa ajikinsa

Wandonsa ya kalla yanda tazuba masa yashi,memakon ransa yabaci saiyayi murmushi
yabiyota da gudu, tana gudu tana waiwayensa har tazo wajanda aka tara wani yashin da yawa,
tana zuwa wajan tafad'i

Shima yana qarasowa wajan yariqe gashin kanta yace "wana kama?"

Daria tayi tace "nadena, Allah nadena"
Rabuwa yayi da ita ya kwanta anan gefenta akan yashin, sai haki suke maidawa kowa yana
kallan Dan'uwansa, wayar hannunsa yadaga yayi musu pic suna daga kwancen

'Dis taji an d'iso mata ruwa, Dasauri tatashi duk yashi yabata mata gashin kanta tace,"ABBA
ruwa"

Hannunta ya fizgo tadawo ta kwanta yanda take da, yace "me kikace?"

"Abba" tabashi amsa kai tsaye

Girgiza kansa yayi yace "Yaya Abba zakice"

Daga masa kai tayi, kafin tace wani abu sukaji Saukar ruwa akansu, cikin sauri suka tashi,
tadauki hijabinta, yariqe hannunta suka tafi qasan wata bishiya da gudu, suka tsaya anan, Tun
ana yayyafi aka dawo ana shara ruwa da karfi, duk tsoro yakamata, ta rikice, shikuwa Babu
wani tsoro atare dashi, iskar da akeyi ne yasa bishiyar dasuke qasanta kad'awa, nan take ruwa
yajiqe musu jikinsu jagab,kallan gashin kanta yayi, gaba d'aya yajiqe ya kwanta sosai yana
sheqi Kamar Wanda ake saka masa Mai, hijabin jikinta ya karba Yarufe mata Kannata dashi,
sannan yajata yasakata ajikinsa yace "kidena tsoro"

Bata iya cemasa komaiba, ahaka suka tsaya har aka qare Ruwan tas, Inda Allah yarufa Asiri
ba'a dauki lokaci ana Ruwan ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login