Showing 69001 words to 72000 words out of 104433 words
Chapter 24 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
yakamata ace ya Yusif yazo ko yaya ne taganshi,
zamanta agidan nan tana hango yar qaramar qura, kowa cewa yake ya Abba yana sonta, Shin
idan Momy da Daddy sukaji wannan batun yaya zasu dauki maganar? Su Ilham ma dasuke
DANGI DAYA dashi suna bashi goyon baya to inaga iyauensa? Tasan cewa suma sai sunfi
kowa murna, kuma da kunya tana zaune acikin gidansu taqi dansu na cikin su,abinda kunya,
saide kuma yanda takeji aranta ko duniya da abinda yake cikinta ya Abba zai bata bazata iya
auren saba kwata kwata, baba kansa yasan cewa ya Abba baya sonta, amma ya Yusif yayi
mata komai, yaso ta a lokacin da Abba yagujeta
Saboda haka Tun ana yad'a jita jita a family gara tayi maganin abun Tun kafin ya furta mata
kalmar soyaiya
Hannunta tadaga sama tayiwa Allah godia daya saka soyaiyar ta acikin zuciyar Abba, ko banza
zaiji abinda taji abaya
Gift din ya Yusif tafara budewa
Bude ledar keda wuya kwalin Sabuwar waya qirar iphone ya baiyana
Murmushi tayi tace "Allah sarki ya Yusif"
Lokacin dazai siya mata waya tatuna, ya tambyeta wacce takeso tace iphone amma a lokacin
kishi ya hanashi siya mata, shine sai yanzu kenan yasiyo mata
Kwalin wayar ta dauke anan taga wani kati Dan qarami Mai kyau sai sheqi yake, saikuma rafar
kudi yan dari biyar guda daya, Wanda ta tattabar da cewa rafar dubu hamsin ne
Katin tabude taga rubutu aciki Mai kyau, nan take tafara karantawa :
_Alkawari ne na dauka, ba zan taba barin damuwa ta wanzu_ _a cikin zuciyar ki ba matukar
muna a tare da_ _juna, ina fatan nan da dan wani lokaci kadan zaki_ _tabbatar da hakan bayan
kin zamo mallakina kuma mata_ _a gare ni, ke kadai zuciyata ta amincewa Nihla,naso_ _nazo
naciyar da mata ta kek da kaina amma aiki yamin_ _yawa, dafatan zakimin uzuri, Happy
birthday_
Tana gama karantawa tayi kissing katin, tace "i luv u ya Yusif"
Wayarta tadauka ta kirashi, ringing din farko yadaga, cikin farin-ciki tace "ya Yusif, irin wannan
gift haka, gaskiya naji dadi nagode sosai, i luv u so much dear"
Murmushi yayi tareda lumshe idonsa "saqona ya'iso gareki kenan"
"yes, yazo, kuma wayar tamin kyau sosai, naji dadi"
"da gaske kinji dadi?"
"emana ya Yusif, naji dadi sosai"
Yace "to tayaya Zan gane hakan?"
"mekakeso nayima Wanda zaka gane?"
Yace "um think about it"
Fari tayi da idonta Kamar yana ganinta tace "to idan kasamu time kasamu baba kayi masa
magana akan soyaiyar mu, kaga shikkenan dana gama service sai bikinmu "
Sosai Yusif yayi mamakin kalaman ta, Murmushi yayi yace "Really?"
Tace "yeah"
Murmushi yasaki har tana jiyoshi sannan yace "gaskiya naji dadi, nagode sweethrt,kuma zan
sameshi a gobe muyi maganar, zan fadawa Abbana ma, but yanzu yaya taron?"
"Alhamdulillah ya Yusif, komai yayi daidai, rashin daidai dinsa shine baka nan"
"to kiyi hakuri, tuba nake, idan nasamu time zaki ganni verry soon"
"to shikkenan ya Yusif thnks"
Yace "yr wlcm"
Daga nan sukai sallama.
Momy ce taturo dakin tashigo, cikin murna Nihla tanuna mata abinda Yusif din ya aiko mata
dashi
Murmushi Momy tayi, tazauna abakin gadon, saide wannan ne karon farko da taji tausayin
Abba aranta, saboda yanda taga Nihla tana farin-ciki akan kyautar da saurayinta yayi mata,
saide Babu yanda zatayi, dole sai Abba yagane laifin dayayi abaya, bazata biyewa son zuciya
dason datake wa danta ba
cikin nutsuwa tace "nagani Nihla, Yusif yayi kokari sosai, amma dafatan de dashi za'ayi ko 'yar
Momy?"
Ahankali tadagawa Momy kai cikin kunya
Momy tayi Murmushi "to shikkenan, idan kunyi waya dashi kifada masa momynki tana gaishe
shi, sannan kifuto muci abinci, goma saura yanzu"
Ahankali tace "to Momy"
Falon suka futo itada Momy, yana zaune shi kadai a dining yana daddanna waya, tunani yake
aransa meyasa har yanzu Nihla bata sakewa dashi tayi masa magana Kamar da? Bayan kuma
tasan cewa shi bawata magana yakeba dama can
Yayi tunanin dazu da farouq yace pictures dinta suna wayarsa zatace yatura mata, amma sai
yaji tayi shiru, yarasa me zaiyi mata tadinga sakewa dashi suna magana Kamar da
Zuwansu wajan ne yakatse masa tunanin dayake, Nihla ta kalleshi yana sanye da jallabiya fara
qal wadda ta karbi jikinsa, sumar kansa ta kwanta luf tana sheqi gwanin sha'awa, hankalin sa
yanakan waya
Zama sukai, Momy tace "Nihla zuba mana Abincin"
Tashi tayi tafara zuba musu, ahankali ya ajiye wayarsa yazuba mata ido yana Kallanta, rigar
jikinnata tayi mata kyau,wadda ta kasance marar hannu,kyakykyawar fatarta ya kalla tayi luwai
luwai da'alama zatayi laushi
Momy ta kalleshi taga ya zubawa Nihla ido, duk abinda take akan idonsa, tunani tafara to kode
Abba ya Manta tana wajan ne yakebin 'yarta da wannan mayen kallon?
ahankali ta dauke kanta
Nihla tazuba wa kowa sannan tazauna kowa yafara cin Abincin
Suna tsaka dacin Abincin yadubeta yace "please inason Tea"
Dago daradaran idanunta tayi ta kalleshi batare da tace komai ba tatashi ta janyo flaks din dake
gabansa tadauki cup tazuba suger kadan sannan tasaka madara
Momy ta kalleta, gaskiya ne Nihla ta karanci Abba tas, Inda wanine zai hada masa Tea dinnan
da tuni yayi magana yace kar asaka suger dayawa, amma ita ko magana baiyi mata ba saboda
yasan tasani
Ruwan zafin tafara tsiyayowa by mistek hannunta yazame Ruwan zafin yazubo ahannunta
Flask din ta ajiye dasauri tace "auch..." tafara yarfe hannunta tana runtse idonta
Spoon din hannunsa yasaki yatashi dasauri ya nufeta, yanda take girgiza hannun ne yasa
qirjinta suke rawa Wanda batasaka musu ko 'yar breziya ba, numfashin sane yafara kokarin
daukewa, badan tana cikin jin azabar zafi ba da Babu abinda zai hanata ganoshi, jiyake Kamar
ya fuzgota jikinsa Ahankali yadora hannunsa akan nata yariqe hannun data qone din, gaba daya damuwa ta
baiyana a fuskarsa, hannun yakai bakinsa yafara hura mata iska awajan,runtse idonta tayi yace
"wayyo Momy hannu na"
Kallanta yayi yaga idonta yacika da qwallah, yace "Sannu, kidena kuka"
Hannun yakalla dogayen yatsunta masu kyau sunyi jajir, yasake hura mata iska awajan
Cikin shagwaba tace "wash!"
Dago kansa yayi yazuba mata manyan idonsa, rakinta yana birgeshi, haka yatsira mata ido
yana Kallanta ga hannunta yariqe cikin nasa
Momy tadena cin Abincin ta tsaya tana kallan ikon Allah , kode sun Manta tana wajan ne?
Lalle wannan Inda ace Nihla tana sonsa Kamar yanda yake sonta a yanzu, Toda Babu abinda
zai hana su hanata zaman gidan mijinta, irin wannan rashin kunya a gabanta har ina!♀️Ita Nihla
yanda take shagwabar saika rantse da Allah da niyya takeyi, shikuma gaba daya ya susuce
akanta yasakata agaba Kamar zai maida ta cikin jikinsa
Gyaran murya tayi, Abba yajuyo ya kalleta batare daya cika hannun Nihlan ba, itama sai a
lokacin tabude idonta ta kalli Momy
Momy tace "jeki saka qanqara akan hannun, zakiji yadena zafi, Allah yasawaqe"
Cikin sauri yace "bari a dauko"
Yasake kallan Nihla yace "Sannu" sannan yasaki hannun nata yawuce kitchen batare daya jira
ta amsa masaba
Tausayinsa yad'an kama Momy yanda taga gaba daya ya rikice, to idan yaji akwai wanda Nihla
take tare dashi yaya zaiyi kenan?
Tana tsaye sai turo baki take gaba yadauko qanqarar yadora mata ahannun sannan ta danji
dama dama
Suka zauna kowa yayi shiru, Momy tadubeshi, taga ko kallan Tea din beyiba, magana tafara
aranta, yasa yarinya tahada masa abu, a dalilin haka ta qone amma baima kula Tea dinba, tace
"Abba kasha Tea din mana"
Bece da'ita komai ba, kawai de ya girgiza kansa
Ajiyar zuciya tayi tace "nikam na qoshi, saida safen ku,"
Ta kalli Nihla tace "idan hannun be daina zafi ba koda cikin dare ne kizo ki fadamin saina
tasoshi yakaiki asibiti"
Abba yayi Dan qaramin murmushi saboda yasan sarai dashi take
Wajan yarage saisu biyu kawai,kowa yayi shiru Babu me magana, ta dago ta kalleshi ta kawar
da kanta, shikam, zuba mata idanu yayi, wani irin dadi yakeji cikin ransa, besan cewa ya takura
taba, dazai matsa da tafi cin Abincin yanda ya kamata, tunda shi baci zaiyi ba
Bata tsammata ba taji yace "kek yayi dadi"
Ahankali batare data kalleshi ba tace "thank you"
Daga nan tayi shiru, tana tunanin maganar Momy da tace idan yadawo tayi masa godia akan
motar daya bata, tarasa tayaya zata gode masa, kwata kwata ma batasan tuno da maganar
motar, saboda wannan takardar daya hado mata da'ita tarasa gane Inda yadosa, shi ya Yusif
dasuke soyaiya tayi masa godia yanda ya kamata amma shifa ya Abba?
Ahankali tadago kanta ta kalleshi, karaf idonsu yahadu, tayi saurin janye nata idon tace "nima...
Nagode sosai"
Murmushin yayi, zaiso ace taci gaba da magana saboda yana jin dadin yanda Dan qaramin lips
dinta suke motsawa dan haka yace "for what?"
Kai tsaye tace "motar daka turomin"
Memakon yayi mata maganar motar saiya jefo mata tambaya "Can you drive?"
Tace " i can't, but yaya farouq saiya koyamin"
Shiru yayi na Tsawon mintuna, farouq, farouq, karfa tasa yafara kishi da yan'uwansa, ya kalleta
yace"dole sai shi?"
Amnah El Yaqoub ✍️
[7/7, 11:07 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
43&44
Kanta tsaye tace "ehmana"
Fuskarsa ta nuna alamun damuwa yace "no, kibarshi, zan koya miki"
Kallansa tayi, lalle ya Abba yasakko, ahankali tace "nagode, amma kabarshi"
Tsam ta miqe daga wajan, Dan taga alamun zancen yakeso, kawai yazo yasa ta agaba, hanyar
dakinta tanufa batare data qara masa magana ba, shima binta yayi da kallo, saida yaga tashige
dakinta sannan yasaki ajiyar zuciya
Shima dakinsa yatafi ya kwanta, tunani yafara akan tayaya zai shawo kanta? Har tausayin
kansa yakeji wani lokacin, tana bashi irin wannan amsar tayaya zaiji qwarin gwiwar fada mata
abinda yake ransa?
Har qarfe biyu da rabi yakasa bacci yana tunanin ta, yaji haushin kansa yafi a qirga, Inda ya
amince da'ita Tun farko daduk haka bata faruba, ganin tunanin Babu Inda zai kaishi yasa
yatashi yanufi toilet yadauro alwala yazo yafara fadawa Allah kukansa
Bayan ya idar ya kashe wutar dakin ya kwanta, bai taba barin wayarsa akunne ba idan zaiyi
bacci, koda yaushe kashe ta yake idan zai kwanta, amma yau akunne yabarta, rigar jikinsa
yazare dagashi sai boxer yaja fillo ya rungume a qirjinsa sannan yadau wayarsa yana kallan
pictures dinta, ahaka bacci ya daukeshi.
Dadewar dayayi beyi bacci bane yasa daya koma bacci bayan sallar asuba, yajima yanayi, bai
tashi ba sai wajan shadaya
Wanka yayi yafuto domin ya gaida Momy,ganin su yayi gaba dayansu zaune afalo,ga Daddy ga
Momy ga kuma Nihla agefen Daddy tana sanye da Jan leshi Wanda akayi mata dinkin riga da
siket amma wuyan rigar irin budaddan nan ne da'ake yi yanzu
Cikin murna ya qaraso Yazauna ya gaida Daddy da Momy
Itama Nihla fuskarta Babu yabo Babu fallasa ta gaida shi ya amsa cikeda kulawa
Daddy yace "Tun karfe takwas nadawo momyn ku tace baka tashiba"
"eh Daddy, ban kwanta da wuri bane shiyasa"
"to Alhmdlh, kuma bana nan sai qanwar ka tazo service harma kasiya mata Mota"
Shiru yayi Bece komai ba
Daddy yace "to Allah yasaka da alkhaairi, Allah yabar zumunci"
Ahankali yace "Amin"
Tashi Daddy yayi yakalli Momy yace "idan yagama break fast ki turomin shi"
Momy tace "to Alhaji"
Bayan yagama cin Abincin kuwa Momy ta turashi dakin Daddy, sannan itama tabi bayansa,
Nihla kuwa kwanciya tayi tana daukan remote
Zaune yake agabansu kansa aqasa, yarasa dalilin wannan kira, Daddy yadubeshi yace
"Abubakar Momynka ta sanar Dani rashin lafiyar dakayi kwanaki harma da abinda likita yace"
Abba najin haka cikin ransa yace Innalillah.., yayi shiru Kamar ruwa ya cinye shi
Daddy yaci gaba da fadin "nadade inama kallan marar lafiya ashe ba haka bane kalau kake
tunda gashi har kana rashin lafiya akan haka, ina ita yarinyar dakace kanaso din take, inane
gidansu sai Muje ayi magana guda daya, ka dade da sanar damu cewa kana sonta, amma
maganar aure kayi shiru"
Shiru Abba yayi, idonsa yayi jajir, ga kunyar iyayen nasa dayakeji Ahankali yace "Daddy tayi
aure"
Cikin sauri iyayen suka kalleshi, Daddy "to shikkenan Allah yakiyaye gaba, sai kayi kokari
kasamo wata ka aura, bazai iyu kaci gaba da zama da rashin lafiya ba"
Jinjina kansa yayi yace "insha Allah Daddy"
"zaka iya tafiya"
Ahankali yatashi yafuto daga dakin, ta gabanta yazo yawuce yashige dakinsa, itade Nihla taga
shigar sa daki Kamar yana cikin damuwa, tabe baki tayi taci gaba da kallonta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan sati daya tana kwance tana bacci da weekend kasancewar bazata ko'inaba
Wayarta ce tahau ruri cikin magagin bacci takai hannu tadauki wayar cikin sexy voice tace
"Hello"
"Baby na kina bacci kenan"
Tace "Um"
Murmushi yayi "to albishirinki"
"goro ya Yusif"
"yau ina kan hanyar zuwa naganki, aide adress din dakika taba turomin kina nan ko?"
Bude idonta tayi "ya Yusif da gaske kake zakazo?"
"Yes, yau zanzo insha Allah, yanzu hakama wanka zanyi nabiyo jirgin dazai tashi 12"
"wayyo ya yusif, mekakeso na shirya ma?"
"Karki wahalar min da kanki, kiyi zaman ki kawai"
Murmushi tayi, amma Babu yanda za'ai zaizo takasa shirya masa wani abu
Daga nasa bangaren yace "me kikeso nataho miki dashi?"
"mamy ya Yusif, ita nakeso, nayi missing dinta"
Murmushi yayi yace "tunda zaki ganni ai Kamar zaki ganta ne"
"to shikkenan ya Yusif sai kazo"
Tashi tayi taje ta sanar da Momy, nan da nan kuwa Momy ta aiki Adala kasuwa tasiyo musu
abubuwan buqata, Adala tana dawowa suka hau aiki itada Nihla,ko sau daya bataga Abba
yafuto ba, may be baya gidan ne, aikin sukaci gaba dayi lokaci daya gida yadauki qamshin
hadadden girki
Saida Nihla taga komai yayi normal sannan taje tashiga wanka
Karfe biyu saura yakirata yace yana bakin get
Kwalliyar datayi ta doguwar riga ta atamfa ya karbi jikinta, tayi mutuqar kyau sosai
Da kanta tafuto taje ta taryoshi daga bakin get,ta karbi key din motarsa tabawa Direban gidan
tace yashigo masa da ita
Yusif sai Kallanta yake, kwalliyar tata tayi bala'in tafiya da imaninsa, ahankali suke ta kowa
gwanin sha'awa har suka qaraso part din Momy, Nihla sai Fara'ah take, a falon suka zauna
Momy tafuto suka gaisa, tayaba da Yusif din Babu laifi, cikin sakin fuska tace "yaka baro
mutanan Abuja" yace "Alhamdulillah, suna lafiya wallahi"
"aaa masha Allah, ai kullum muna jin labarinka awajan Nihla"
Yusif yayi Murmushi cikin ransa yana yabon matar
Tashi tayi tace "bari akawo maka Dan ruwa, Alhaji yafita aida kun gaisa dashi "
tatafi tasa Adala takawo masa kayan motsa baki dakuma Abincin da aka shirya masa
Kallanta yayi yace "wannan ce Momy ko?"
"itace ya Yusif"
"tanada kirki gaskiya, idan naje gida saina fadawa baba cewa kina nan kalau wani kyau ma kike
qarawa"
Murmushi tayi masa, tatashi tazuba masa Abincin, yafaraci, Dan kadan yaci yace ya'isa
Yakalleta yace "Nihla gaskiya bazan boye miki ba ina qaunar ki, kuma naji dadin yanda naganki
hankalin ki kwance, fatana mu kasance inuwa daya amatsayin Ma'aurata nanda Dan wani
lokaci qanqani"
Kallansa tayi "ina fatan hakan ya Yusif"
Fira sukaci gaba dayi har yamma tayi, yatashi yayi sallah suka dawo falon suka zauna, wayarta
ce tayi ringing, cikin zolaya tace "bakada kirki yaron nan"
Daga daya bangaren akace "ninema yaron, gaskiya kin cuceni, koke aka kawomin yanzu tsaf
Zan riqeki"
Dariya tayi "lalle ma Abdallah, aikuwa baza'a kawo makaba, yakake yagida, ya service"
"gida lafiya Nihla, dama nashigo kano ne shine zanzo mugaisa saina wuce"
"Ok to shikkenan abdallah saikazo, zan turoma adress din gidan yanzu"
Wayar ta katse ta kalli Yusif "ya Yusif abdallah ne yakirani, wai zaizo mugaisa"
Yace "Ok Abdallah qanin Nadiya qawarki"
"eh shi"
Yace "to saiyazo, ina pictures din birthday din naki baki turomin ba, nunamin nagani" ♀️
Hankalinta kwance tabashi wayarta tace "gashinan suna cika duba kagani"
Bude wayar yayi yashiga gallery anan yaga pictures din, lokaci daya yanayin fuskarsa ya sauya
yace "ashe bake kadai kikai ba"
Jikinta ne yayi sanyi "eh nida ya Abba ne"
Tabe baki yayi yabata wayarta, sannan yatashi yace "toni Zan tafi"
Shagwaba tafara masa "haba ya Yusif, ya za'ai katafi Tun yanzu, karfe hudu nefa"
Jiyayi ta birgeshi, yace "karfe hudu nakeso nabi jirgi nakoma, bakina tareda wani masoyin
nakiba, menene zaki damu?"
"saboda ina sonka, kuma kai zuciyata ta'aminda dashi shiyasa nabaka dama ka gabatar da
soyaiyar mu awajan mahaifina"
Yaji dadin maganar ta, kuma ya gamsu sosai, danhaka shima ya lallabata yace bayason yayi
missing flight ne, daqyar ta yarda, takira masa Momy sukai sallama sannan suka futo harabar
gidan tare domin tayi masa rakiya
Awajan motarsa suka tsaya suka jingina da motar, sai kallan soyaiya suke sakarwa junansu,
yabude bayan motar yabata wata leda cikeda coculate, ta karba tayi masa godia, yace "to Zan
tafi, mezaki fadamin Wanda Zan