Showing 15001 words to 18000 words out of 104433 words

Chapter 6 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf



Aslam ya kalleshi yace "Guy yatake ne? Kaida nayi tunanin ma kafin mudawo har anwuce
wajan?"

Kafin Fawaz yabashi amsa Adam yace "kun Manta da wasiyyar kaka kenan, ba taron biki ba
taron suna"

Daria suka sake sakawa gaba dayansu, Aliyu yace "tome muke jira? Muje gida kawai"

Motocin dasuka zo dasu guda biyu suka bude suka shiga, har sukaje gida suna ta surutu da
raha a motar, bakin Abba nede gim baya tofa albarkacin bakinsa

Suna qarasawa gida kuwa sukaga komai ya canja, anqara gyara gidan Kamar ba gidansu ba,
gaba daya 'yangidan suna tsaye a compound kowa yana jira sufuto amma banda Nihla,
Aikuwa suna futowa waje yakaure da ihun murna, Abba yana ganin Momy yaje ya rungumeta,
cikin shagwaba yace "Momy i miss you"

Daria suka fara yimasa, Momy tace "gidanku Abba, bakasan ka girma bane yanzu?"

Dariya akeyi musu, Daddy yanata farinciki yayi gaba, sannan kowa yayi part dinsa cikin murna

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Hayaniyar dataji afalo ne yasa gabanta yafadi, kode har sun zo? Kafin tasamu amsar ta Tajuyo
muryar yaya Usman yana cewa "Pilot, Pilot Shagwaba de tana nan "

"to waye kuma pilot?" ta tambayi kanta, kafada ta daga taci gaba da kwalliya

Gaba dayansu dining suka wuce, Daddy, Momy, Usman, Aliyu, farouq, Abba, abinci zasu faraci,
Usman yace "Momy banga 'yarki ba, ko ita muke jira?"

Daddy yayi Murmushi yace "ai tunda tayi 'ya takafa mana doka agidan bazamu ci abinci ba
kome take sai anjirata"

Aliyu yayi Murmushi "gaskiya ne Abba zaiyi kishi an qwace masa fadar sa"

Duk maganganun dasuke yana jinsu, Wacece suke magana akanta? Shida yadawo daga wata
qasa ba'a jirashi ba sai ita, Wacece ita?

Tunanin sane ya tsaya jin Momy ta daga murya tace "Nihla! Nihla!!

Cikin zazzakar muryarta tace "na'am Anty, gani zuwa"

"Nihla" ya furta hakan cikin ransa, lokaci daya ya zubawa kofar dakin dayake tunanin daga ciki
zata futo ido

Usman yazuba masa ido yanaso yagano yanayin sa, yayinda Aliyu yake murmushi

Ahankali tafuto daga cikin dakin, tana sanye da doguwar riga ta atamfa, daya daga cikin dinkin
da ya Aliyu yayi mata, tayi kyau sosai acikin kayan, daurin dankwalin datayi ya baiyanar da
dogon gashin kanta, dukda ta daureshi , yan madedetan Breast dinta shape dinsu yafuto sosai
ta cikin breast cup din rigar
Dashi tafara tozali, numfashinta ne yakusa tsayawa cak, saboda wani irin mugun kyau daya
qara, ya girma yazama Babban mutum, ga fatarsa taqara wani gogewa

Shima a nasa bangaren hakan take, idanu yazuba mata yana qare mata kallo,

Cikin ransa ya furta "tad'an girma kad'an, but still yarinya ce qarama "

"oyoyo ya Abba"

Maganar ta ce tadawo dashi daga tunanin daya tafi,
Usman yagama kallansa tsaf yasaki murmushi

Kai tsaye wajansa tanufa, taja kujerar datake gefensa ta zauna ta kalleshi dakyau
" Ya Abba sannu da zuwa, mekake cine haka, kaga yanda ka sauya kayi fari ka qara kyau
kuwa?"

Murmushin kefen baki yasakar mata "kema haka"

Abinda yace kenan

Murmushi tayi "haba de ya Abba wace ni? Gashinan kana nema ka kamoni fari"

tafadi haka tana matso da hannunta me dauke da dogayen yatsu kusa da nashi hannun, Dan
yagani ya ban bance

Bin farar fatar hannun nata yayi da kallo, d'an siriri dashi, Wanda yake tunanin idan yayi mata
kyakykyawan riqo zai iya karya ta ‍♀️

Kafin yace mata wani abu, Daddy yayi gyaran murya ganin suna nema su Manta dasu awajan
"Am yata zuba mana Abincin ko?"

Tashi tayi tabude Abincin, babu kunya tafara Jan flet din gaban Abba tazuba masa, sannan
tadauki na Daddy�

farouq, Usman, da Aliyu gaba daya suka koma yan kallo awajan, Aliyu cikin ransa yace anya
idan Nihla da Abba suka fara soyaiya Momy zata iya bude idonta?

Saida tagama zuba musu sanan tazuba nata Dan kadan, sannan kowa yafaraci

abinci takeci amma hankalinta yana kansa, tana kallan yanda yake cin Abincin cikeda nutsuwa,
Miqewa tayi tsaye Ahankali, tadauki just din dake gaban ya Usman ta tsiyaya a glass cup
sannan ta tura wa ya Abba agabansa, takoma tazauna tanaci gaba da cin abinci, Aliyu da
farouq suka hada ido tareda Jinjina kai Gaba daya Babu wata damuwa aranta take nuna masa kulawa, sai tarairayarsa take Kamar
Dan qaramin Baby

Tsawon lokaci suka dauka kafin su Gama, falo suka dawo suna kallo, su Usman sai tsokanarta
suke suna janta da fira, ahankali yatashi ya kalli Momy "Momy zanje nayi wanka nahuta"

"to Abba nah,"

Wani irin kallo yayiwa Nihla Wanda ni kaina nakasa fassara shi, amma tabbas za'a sami
matsala idan aka yiwa mutumin daya dade yana cikin soyaiyar ka "ina Diddi? Why bakizo da
itaba?"


Gaba daya falon shiru sukayi, kowa yakasa bashi amsa
Shikuma ya tsareta da Idanunsa, dago kanta tayi ta kalle shi takasa magana, karkata kansa
yayi alamun yana jiran amsa yace "uhm inajin ki"

Idanunta ne suka cika da qwallah, Ahankali ta dago kanta ta dubeshi "Diddi tarasu ya Abba"


"what?"

Dasauri ya kalli Momy yace "Momy, me yarinyar nan take fada haka?"

Jijjiga kai Momy tayi, alamun da gaske ne, Lokaci daya mutuwar Diddi ta dawowa Nihla
sabuwa, da gudu tatafi daki tana kuka

Lokaci daya jikinsa yayi sanyi "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Diddi tarasu, Momy meyasa
baku fadamin ba? Haba Momy, meyasa? Innalillah..."
Yadafe kansa da hannunsa‍♂️ya koma kan kujera Yazauna jagwab

Dafashi Momy tayi "kayi hakuri Abba, Aisha ta rasu Sanadin zazzabi na kwana daya, Daddynku
ne yace kada afada muku, hankalin ka zai tashi, addu'ah take buqata idan kuka dawo sai kuyi
mata"

"Momy yanzu Diddi tarasu?ashe ganin qarshe nayi mata?"

Su Aliyu dake zaune jiki a sanyaye, sune suka fara bashi hakuri, sannan ita kuma Momy tabi
bayan Nihla daki



Zuwa dare ta ware, tadan kwantar da hankalin ta tadena kuka a dalilin nasihar Momy, tana
kwance agadon dakinta tana daddana wayarta, yauma takira ya yusif yafi sau biyar amma
wayar taqi shiga, ko a wanne hali yake?
ta duba Agogon dakin karfe tara da arba'in da bakwai, Dasauri ta furta "kaiiii goma saura"

Dasauri taduro daga gadon tafuto falo, kitchen tashige tafara hada coffee Mai Dan karan dadi
Momy ce taji motsinta, ta furta alhmdlh aranta, tunda tasaki ranta harta futo falo

Kitchen din ta shiga taganta tana aiki "Nihla me kike hada mana ne da wannan daren?"

"Anty bafa mu nake hadawa ba, Ya Abba nake hadawa coffee, nasan zaiji dadinsa"

ha'ba Momy ta riqe, "to Allah ya temaka, nima kallo zanyi shine naji motsinki na futo"
Tana fadar haka tajuya zuwa falo

Itama Nihla tana gama hadawa tadauka adan qaramin tire, tazo tawuce tagaban Momy tashige
dakin nasa, saura kadan tasaki farantin dake hannunta, saboda yanda taganshi dagashi sai
gajeren wando , babu riga ajikinsa,gashi kwance a qirjinsa, yana kwance yana waya qasa
qasa, batasan dawa yake wayar ba
Qamewa tayi a tsaye, takasa qaraso wa ciki, tayi dana sanin shigowa dakin nan nasa batare da
nocking ba

shi kansa baiyi tunanin shigowar taba, futowarsa kenan daga wanka yasaka Dan gajeren
wandon, ko shirya wa baiyi ba aka kira wayarsa shine yad'an kishingid'a yana wayar

cikin ransa ya furta "yasalam! Yarinyar nan kada ta raina shi fa" ahankali yatashi zaune tareda
zubo qafafunsa zuwa qasa

Ya tsareta da ido Bece mata komai ba, hannunta ne yafara rawa, duk ta rikice, wanne irin qirji
ne dashi haka me fadi? Duk Ta diririce tarasa me zatayi

Shima ya lura da yanayin data shiga, ko menene ya tsoratata take karkarwa haka?
Ya tambayi kansa.

Cikin in-ina tafara magana "Am dama... dama coffee..."

"zoki ajiye"
Abinda yace da ita kenan

Ahankali ta taka ta qarasa wajansa, sai kawar dakai take, takasa kallansa, ta tsugunna ta ajiye
masa agabansa tafuto da sauri

Binta yayi da kallo, to menene abin tsoro ajikinsa ? To kodan ta ganshi haka ne dukta tsorata?
Tabe bakinsa yayi, sannan ya kalli wayar tasa yaga anma kashe, shima bai sake kiraba yayi
wulli da wayar yadauki coffee din data kawo masa

Tana futowa daga dakin tazauna afalo kusa da Momy suna kallo, amma gaba daya hankalinta
bayakan kallan,


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tsawon satin su biyu da zuwansu , koda yaushe da irin kulawar da Nihla takewa Abba, zuwan
yanzu kam, kowa yasan cewa Nihla nason Abba, Shidinne de suka rasa gane Inda yadosa

Alhaji ne yashigo falon nasu dawowar sa kenan daga wata tafiya dayayi, Momy tanayi masa
sannu da zuwa, ya amsa mata, yana zama akan kujera, "ina ya rannan ne?"

"Nihla bata nan taje wajan Ilham, Abba kuma ni Tun safe ma banganshi ba "

Wayarsa yadauka ya kira Abban
" kazo kaida Aslam ku sameni agida yanzu, kokuma ka turomin shi "
Yana fada masa haka ya kashe wayar

Basuda dauki lokaci ba sai gasu sun shigo shida Aslam din, cikin ladabi suka tsugunna
agabansa bayan sun gaida shi,Alhaji ya dubesu " Aslam inaso ka shirya kaje India ka dauko
Aisha daga makaranta, munyi magana da abokina cewa harma tarafa university, to Zan turoma
adress din gidan, saika shirya kaje kutaho tare "
Momy ta kalleshi tace " Amma Alhaji lafiya kuwa? "

" lafiya kalau Alhamdulillah, kawai de lokacin karanta wasiyyar hajiya ne yayi, tunda Allah yayi
mana Tsawon rai, gara intara kan kowa na family a karanta wasiyyar agabansa "

Momy ta Jinjina kai, tace" hakane, Allah Mai iko, kwanci tashi kenan "

Beyi mata magana ba, yadubi Aslam din yace " shine kiran dama, ka shirya katafi, ka tabbatar
kun dawo akan lokaci "


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

" gaskiya Ilham akwai matsala "

" matsala kuma Nihla? Allah yarabamu da matsala,
Meyake faruwa? "

" Ilham ina tunanin son yaya Abba nake wallahi, shikuma naga Kamar hankalinsa baya kaina,
ina yawan tunanin sa, sannan ni Tun ina qarama nakasa mantashi a raina, Ilham ina tsoro kar
yaya Abba Yaqi saurara ta "

" soyaiya Nihla? Kuma ma da yaya Abba? Anya baki debo da zafi ba Nihla? "

" nima abinda nake tsoro kenan Ilham, bansan ya zanyi ba wallahi "

" kinga ki kwantar da hankalin ki, shima nasan Babu yanda za'ai yaganki amma baiji aransa
cewa yana sonki ba,Nihla Allah yamiki kyau, sannan kuma ke dashi duka DANGI 'DAYA ne,
bazai qikiba, dan'uwanki ne, tunda duk cikin mu Babu Wanda yake sakewa da'ita Kamar ke,
amma idan zaki iya to kiyi masa maganar mana "
Kai tsaye tace" bazan iyaba Ilham, yanamin mugun kwarjini wallahi, kullum naganshi agabana
ma gabana tsananta faduwa yake, sannan yana cikamin ido, koba wannan bama bazan iya
tunkarar namiji da wannan maganar ba "

Ilham tayi ajiyar zuciya," hakane kam,gaskiya gara shiya fara furta miki, amma mezai hana cikin
siyasa kifara nuna masa? "

" to ta wacce hanya kenan Ilham? "

" kulawa, kidinga bashi kulawa yanda yadace "

" Ilham duk Wanda Yazauna a part dinmu zaisan cewa ina bawa ya Abba kulawa ta gaske,
saboda haka kicire kulawa a lissafi"

Girgiza kanta tayi tace "gaskiya ne wannan, nima shedace, ke kinga mudena bata lokacinmu
akan wannan tunanin, duk miskilancinsa qarya yake ya juyawa mace Kamar ki baya Nihla"

tace" da gaske kike Ilham? "

Girgizakai Ilham tayi," da gaske nake "

Cikin farin ciki ta rungume Ilham







(to ko yaya zata kasance?ko yaya bayanin wasiyya? Fatana kuci gaba da kasancewa Dani)




Kada amanta da sharhi da Comments






Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 12:52 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub


Like my page On facebook

https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


13&14


Bayan kwana biyu Aslam ya shirya yatafi India domin tahowa da Aisha, yaso sutafi tareda Abba
amma sai Abban Yaqi
Yana sauka a Airport yakira number da Daddy ne yaturo masa amma wayar taqi shiga, haka
yadinga tsaki shi kadai
Daga qarshe saiya kira Daddy yafada masa, a lokacin Daddy yasa Alhaji Basiru yatura masa
number Aisha

Aslam na ganin number nan take yakirata, amma yakira yakai sau hudu bata daga wayar ba,
haka yasake kiran Daddy ya sanar masa, daga qarshe de sai Daddy ne yayi masa kwatancen
gidan da kansa, shikuma yahau taxi suka tafi, daqyar ma me taxi din yagane abinda Aslam din
yake nufi, saboda shi Babu turanci, shikuma Aslam Babu yaran hindi
Sunyi tafiya Mai nisa sannan yasauke Aslam ya nuna masa bus din dazai shiga, zata kaishi har
kofar gida

Dole saida dala yayi amfani wajan sallamar me taxi din, sannan yafara jiran zuwan bus
Yanayin garin yake kalla da dan hadari kadan, Kamar wasa kuwa aka fara yayyafi, mutane
dasukasan kan garinsu kowa sai yake baza lema, Aslam kuwa sai kare ruwa yake da hannu
amma abin ba riba

Ruwan yafara jiqa masa kayansa saiga bus din tazo ta tsaya awajan, gani yayi mutane suna
shiga, shima yace ai ko ba ita bace wallahi shiga zaiyi, sukaishi koma ina ne

Duk kujerun motar ma sun cika, sai wata yarinya datake zaune gefenta akwai kujera daya, kallo
daya yayi mata yagane cewa Babbar arniyace, shigar ta kadai zaka kalla kagane hakan

Riga da wando ne a jikinta kayan ya kamata sosai, sannan gashinta awaje sai Dan qaramin
mayafi data dora akai Wanda dashi da Babu duk daya
Itama kallansa tayi, taganshi a tsaye yariqe karfen Mota, kayan jikinsa sunyi masa kyau sosai,
da yaren India tace masa yazo yazauna, taga ko Kallanta ma baiyiba alamun baima san dashi
takeba
Dan haka tace "hi"

Sai lokacin ya juyo

Tace "please come and sit"

Kallanta yasakeyi ya yatsina fuska, "no, thank you" yafada mata haka yana yatsina fuska
Hankalinta ta maida kan window bata qarabi ta kansa ba

Wayarsa yaciro yaciro daga Aljihun jeans d'insa yakira Abba, Abba yana dauka Aslam yafara
zuba "Abokina kasan me? Wallahi gara da Allah yasa baka biyoni ba, gani nan muna tafe awata
bus tana tafiya yanda kasan hawainiya, ni a tsaye ma nake narasa wajan zama"

Abba yace "Kamar ya?"

"to gashinan de kowa yana zaune, babu kujera sai guda daya, ita kuma wata qatuwar arniyace
azaune nake fadama , inani ina zama kusa da manyan arna
Shegiya harda cewa wai in zauna, d'an iska neni, ina zama zata liqemin daga nan kuma ta
addabi rayuwata"

Murmushi Abba yayi, yasan halin Aslam sarai, "to kayi hakuri mana, insha Allah zakuje lafiya"

Wani uban birki aka taka, hakan yasa Aslam yayi gaba yasake dawowa baya, nan take yakashe
wayar yasake riqe karfen

Mutum uku ne suka fita, kujerar datake gaban yarinyar Babu kowa, nan yakoma Yazauna,
yarinyar tanata kallansa

Kafin su qarasa Inda zaije motar ta lalace, kowa yafuto, wasu suka fara tare Mota, wasu kuma
suka tsaya, kiran sallah yaji anayi awani masallaci, Dan haka yaje wani dan case agefen su
yasiyo ruwa, yadawo wajan motar ya tsugunna yafara daura alwala

Yarinyar tana tsaye a gefensa, duk tana kallansa, ajiyar zuciya tayi, tataka Ahankali ta qaraso
wajansa cikin yaren hausa tace masa "bawan Allah Dan Allah idan kayi sauran ruwan inaso
nima zanyi sallah, kudin hannuna baida yawa bazai isheniba"

Shiruuu Aslam yayi Kamar an kwada masa sanda‍♀️
Kasa Dagowa yayi, bare yahada ido da ita

Tasake cemasa "dan Allah, kaji"

Sai a lokacin yadago kansa, cikin kuskurin kunya yace "yanzu ke, dama kinsan kina jin hausa
kika barni inata zuba?"

Murmushi tayi batare datayi magana ba, Ruwan ya miqa mata yace "gashi inde ruwa ne, ai
ruwa baya had'a fad'a, shi musulmi ai dan'uwan musulmi ne"

Hannunta ta meqo zata karbi gorar Ruwan idonsa yasauka akan wani abun hannunta irin

Wanda yan gayu suke daurawa maza da mata, amma nata anrubuta mata MAZAWAJE da
manyan harufa �

Fasa bata Ruwan yayi, ya tsaya yakalli fuskarta dakyau, aishi sai yanzu nema yaga yarinyar
tanayi masa kama da Nihla sosai, saide tafi Nihla cika dakuma 'yar qiba, yayi ajiyar zuciya yace
"ke fadamin, Yaya sunanki?"

Murmushi tayi tace "Aysha Basiru Abubakar Mazawaje" ‍♀️
Cikin ransa yace tabd'i, dara tasake cin gida kenan, yatsunsa biyar ya nuna mata yace "uwaki"


Yaci gaba da cewa "to a qasar nan qafata qafarki dake Zan koma Nigeria, Aslam ne Dan gidan
Alhaji Baqir yayan babanki"

Cikin sauri tace "yaya Aslam, Innalillah..., ya akai nakasa ganeka?"

"aikokin ganeni, ko baki ganeniba, daga nan, babu Inda zan barki kije,wuce Muje muhau wata
motar kikaini gidan"

"toka bari muyi sallah mana, bani Ruwan nayi alwala ni"

"da wannan shigar zakiyi sallah? Haba, haba, wannan kam baki isaba, ina wayarki ina kira baki
dagaba?"

Jakar hannunta ta duba tace "kaganta acikin jaka, niban saniba"

Yace "yayi kyau, to wuce Muje gidan"

Daga nan tajuya sukayi bakin titi domin tare wata motar


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kallanta yayi idonsa akan manyan qirjinta yace "gaskiya naji dadin rawar nan, gashi gayu sunzo
dayawa, club din yacika sosai, Ina alfahri dake Diyana kin iya rawa ba qarya"

Murmushi tayi tace "najjashi kenan, ai mutum ya mori yarintarsa, yayi amfani da lokacin sa kafin
yaqure masa, nan gaba idan natara yara ai bazanyi ba"

Yace "wannan gaskiya, toga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login