Showing 30001 words to 33000 words out of 104433 words

Chapter 11 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf

mamy bata falon, kai tsaye dakinta suka nufa
domin yayi mata sallama

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Dawowar sa kenan daga makaranta duk yagaji, ga yunwa dayakeji yaji Kamar ana buga get din
gidan
Tsaki yaja sannan yatashi yafita, yana budewa yaga samari su uku dukansu yarane bazasu
wuce 27 ba, gaba dayansu sun tsuke cikin qananun kaya, kallansu yayi dakyau yace "samari
lafiya kuwa? Ko wani gida kuke nema?"

Daya daga cikin su yace "dama munzo wajan qawarmu ne, munyi waya da ita, so tace mana
tadawo nan gidan dazama"

Cikin mamaki yace "qawarku kuma? Inaga kunyi batan hanya ne, ba nan bane"

Na biyun yace "bawan Allah ya zakace mana ba nan bane, bayan nan gidan tayi mana
kwatance?"

Yace "Wacece qawar taku?"

Na ukun yace "Diyana"

Tsayuwarsa ya gyara yace "Ok ai sai yanzu nagane ku, ashe wajan aminiyarku kukazo, to
bismillah, kushigo mana"

Wanda yace wajan Diyana sukazo yakalli Adam dakyau, anya kuwa zai shiga? Da alama fa
wannan yayan tane, karfa su shiga yamusu shegen duka

Saiya girgizakai yace "no, Barshi kawai,"

Ya kalli sauran yace "Baba kuzo mu ware kawai"

Sukuma biyun suka dage sai sun shigo, Adam yana tsaye cikin zuciyarsa yana addu'ah su
shigo gidan, ysce"ku qaraso mana, tana ciki fa maryam din "

Sunfara shigowa gidan kenan sai daya yalura da yanda Adam yake tattare hannun rigarsa
aboye , sai yaja dan'uwansa ya tsaya

Adam yajuyo ya gansu sun tsaya yace" me kuka tsaya yine? Rakaku zanyi "

Adede lokacin tafuto daga cikin dakinta zuwa compound din gidan, tunda aka kawota gidan

yaune kawai Adam yaganta da atamfa a jikinta dinkin riga da Zani, kuma sai kayan yayi mata
kyau sosai

Tana ganin mazan tasaki murmushi tace" guy's, ya garin? Yakuka tsaya daga nan? "

Murmushi sukayi, atare sukace" zamu dawo, Karki damu zamu dawo next time "daga nan suka
fice da sauri

Itama tajuya cikin gidan ko kallan Adam batayi ba, shikuwa binta yayi da kallo yace" Allah ya
shirye ki "

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Da yamma suna zaune afalo shida ita, kanta ko dankwali Babu dana daddana wayarta,
shikuma yana can kujerar qarshe yana cike wasu takardu daya karbo awajan Abba
Tun safe rabonsa da abinci, Dan haka yana gama cike takardun yadago kansa ya kalleta
Besan meyasa yarinyar nan take san zama kai Babu dankwali ba, amatsayinsa na saurayin
yayarta ai yadace ace tana shiga ta kamala, amma kullum kai Babu dankwali, wani lokacin ma
shigar da zatayi idan yaganta daqyar zai dauke idonsa akanta
Badan yana ganinta amatsayin qanwar budurwar sa ba ai zata iya saka shi awani hali

Ajiyar zuciya yayi yadaga murya yanda zata jiyoshi, saboda basa zama waje daya yace "ke
tashi kikawomin abinci"

Hankalinta yana kan waya tace "banajin yunwa banyi abinci ba"

Yace "Wato Ilham na lura kanki yana rawa acikin gidannan, rashin kunyar ki tafara kaini bango,
Karki qureni kuma"

"to yanzu yaya Aslam girki akace nazo nayi kome? Ni wallahi bazan iyaba, saikace wata jaka"

Yace "okey Wato nida nake nemowa na kawo gidan na ajiye nine jaki,
To bari kiji Dan Allah ki yarda nasake yimiki maganar abinci acikin gidannan"

Yana fada mata haka yatashi yafice ransa abace, wannan qaddararran auren yafara isarsa,
haba!


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"A'a, yanmatan Yusif, kece atafe kenan"

Ajiyar zuciya tayi "wallahi nice Anty Nadiya, mamy tafita unguwa, saini kadai agidan shiru, shine

nace bari nataho wajan ki kawai" cewar Nihla

Nadiya tace "hakane kam, kin kyauta masha fira, gashi saurayin naki ma yagudu china"

Murmushi Nihla tayi "wai yaya Yusif, aiba saurayina bane Anty Nadiya, Yaya Yusif yaya nane,
yayi min abinda dan'uwana yakasa min, inajin sa a raina tamkar yayana da muka futo ciki daya"

Gyara zama Nadiya tayi tace "waye dan'uwan naki?"

Kai tsaye tace "yaya Abba"

"yaya Abba kuma? Kifuto fili kimin bayani Nihla, NI DAKE, munzama Kamar yaya da qanwa,
yakamata kibani labarin ki, menene yake yawan sakaki tunani, har kike bige mutum ahanya
batare dakin saniba?"

Nihla tace "Anty Nadiya, labarins yana cike da abin tausayi, nida iyayena natashi, mahaifina ne
qaramin qarfi ne, bayan na girma mamana ta rasu, nakoma gidan yayanta da zama har Allah
yadawo dashi daga qasar waje"

Nadiya tace "wakenan? Kici Gaba mana"

Hawaye ne yataru a'idonta, tace "yaya Abba, Tun muna yara nasaba dashi, har na girma da
tunanin sa acikin qwaqwalwata,ganin irin sabon damukai dashi muna yara yasa ya daya dawo
daga qasar waje nake kula dashi, yanda nake masa zaki dauka ansaka mana ranar aure ne,
ashe shi ba haka bane acikin ransa, yanada budurwa, ranar da akace anhadamu aure acikin
mutane yace bayasona, akwai wadda yakeso, ahaka iyayen sa zasuyi mana auren bayan an
lallabashi ya amince, sai ranar auren babana yaje yadauko ni, muka Taho nan garin ta dalilin
baban yaya Yusif, wannan dalilin ne yasa naje ganinsa Kamar yayana uwa daya uba daya,
Yaya Yusif yamin abinda yaya Abba yakasa min shi "tana gama bata labari tashare hawayen
idonta taci gaba da cewa" bansani ba ko bankai yasonin bane kokuma banida abin dazai gani a
wajena yasoni "

Kai tsaye Nadiya tace" qwarai kuwa bakidashi Nihla "
Da sauri Nihla ta kalli Nadiya cikeda mamaki

Nadiya tace"Nihla Dafarko ki kalli Hijabin dayake jikinki, ki kalli irin atamfar datake jikinki, wallahi
idan ni kika bawa wannan atamfar taki saina tambayeki dalili, saina zaunar dake nace Dan Allah
meyasa kika bani wannan kayan? A a kin renamin hankali ne kokuma tsabar kin maidani yar
qauye ne yasa kika banisu? Nihla samarin wannan zamanin fa saida dabara, na farko namiji yanason mace Mai aji, Nihla
kinje kina zubda ajinki agabansa abanza, wasu mazan zakiga duk wata mace Mai yi musu
biyyaiya to zakiga hankalinsu baya kanta, idonsu yanacan wani waje, Nihla tunda nake dake
bantaba ganinki Babu hijabi ba, kullum kina cikin hijabi, tayaya zaiga kwalliyarki har wani abu

yaja hankalinsa yaji yana sonki?
ni macece 'yar'uwar ki amma tabbas na yabawa kyanki, kinada kyau Dan kyau, amma awajan
wani na mijin hankalinsa bayakan kyau kokadan, hankalinsa yafi karkata kan abubuwan more
rayuwa, kuma ke bakidasu"

Nihla tayi shiru tanajin maganganun Nadiya, acikin maganar ta Babu ta qarya

Nadiya ta dafata tace " babanki yamiki gata daya dauko ki,saboda dakin aure shi ma wahala
kawai zakisha, sannan kuma ki godewa Allah dakika hadu Dani, domin kuwa komai yazo
qarshe, zan temaka miki, kishigo gari Kamar ko wacce budurwa da takeji da kanta, ta yanda
Abba kikace kowa? Bashi kadai ba kowanne namiji ma idan yaganki, saiya sake kallan ki,
amma bazai iyuba saikin kwantar da hankalin ki, kin cire shi aranki "

Nihla ta kalli Nadiya tace " gaskiya Anty Nadiya inason ya Abba "

Murmushi Nadiya tayi tace" matsalar ku kenan yara, saiku dauki soyaiya kusa aranku Tun
bakuje ko'inaba, kinganni nan Nihla, babu na mijin dazan zauna ya renamin hankali,
Idan naga take takenka agu Zan tattaraka na ajiye agefe, akwai wani saurayina SADIQ
MAZAWAJE, naje germany karatu anan muka hadu, shida kansa ya nuna yana sona kuma na
amince, sai daga baya nagane cewa nayi kuskure danake saurarensa, na farko bayamin
kalaman soyaiya, sannan bayasan kirana nice nake ta kiransa, ke qarshe ma kwanaki dana
kirashi muna waya kawai naji yana magana da wata mace agefe, naji yana cewa zoki ajiye
anan, wallahi Nihla tunda nakashe wayata ban sake nemansa ba sai rannan, amma ni Inda
yake birgeni akwai riqe alqawari, munyi alqawari dashi zamuyi aure, amma gaskiya Nihla nagaji,
ko wacce mace tanason kulawa, amma ni bana samu awajansa, aikinsa kawai yasa
agaba,tunda nagane haka saina saka shi awani bangaren daban na ajiye, naci gaba da kula
samarina masu bani kulawa, ()
To kinga ko rabuwa mukai dashi bazanji wani haushi ba, bari kiga pic dinsa "
Wayarta tadauka tadubo pic dinsa, tadorawa Nihla data zama mutum mutumi wayar akan cinya,
tace "bari in shiga toilet na futo"

Batare data lura da yanayin Nihla ba tashige toilet

dak! dak! Gaban Nihla yake faduwa, cikin ranta ta furta yaya Abba!!!
Gaskya ne, Sadiq yana nufin Abubakar kenan, yanzu dama yaya Abba shine saurayin Anty
Nadiya? Saboda Anty Nadiya yaqita?
Kallan pic din tayi, karon farko data taba ganinsa cikin kakinsu na pilot Mai launin fari da baqi,
yayi bala'in yin kyau a pic din, yana zaune akan kujera wajan da'ake tuqa jirgi

Wato ita da yakeso harta samu pic dinsa, amma ita batakai wannan matsayin ba

Jikinta har rawa yafara saboda tsananin firgita, abin yabata mamaki sosai, dole dole tasan
abinyi

Nadiya ce tafuto daga toilet tace "kin ganshi?"

Cikin in'ina tace "eh na.. naganshi Anty Nadiya, amma yayi kyau"

Nadiya tace "ke rabu da wannan kyan yarinya, kyau Babu kulawa ina wani kyau, idan na aure
shi kyan zanci ko kulawar zanfi buqata, shareshi kawai"

Hausawa sukace naka nakane, hakanan taji bataji dadin furucin Nadiya ba, meyasa zata
fadawa dan'uwanta haka?

Nadiya tace, kishirya gobe zamuje kasuwa akwai abubuwan dazamu siyo, sannan kincemin
akwai atamfofin da Yusif yasiyo miki basuda dinki, zamuje wajan telana ya gwada ki yayi miki
dinki nagani nafada, Sanna wannan kan naki zamuje wajan saloon awanke shi, wani satin kuma
sai Muje wajan gyaran jiki ayi miki, sonake qanwata ta sauya ta yanda Babu wani na mijin dazai
qara rena miki hankali "

Murmushin yaqe Nihla tayi" tace " to Anty Nadiya, Allah yakaimu, dama akwai kudin dayamin
saura irin Wanda ya Yusif yake bani, saimu hada dashi"

Nadiya tace "Karki damu nima akwai kudi a wajena,"

Washe gari Tun safe suka yiwa many sallama suka tafi wajan tela, Nadiya ce ta karbi tif din da
kanta ta aunata, kuma itace tabasu irin Style din datake so ayi mata, daga nan kasuwa suka
wuce suka sai :

Alkama
Shinkafa
Gyada
Ridi
Dawa
Hulba
Gero
Aya
Zogale
Kanumfari
Waken soya


Sannan suka dawo gida,Nadiya tace" Sai gobe kuma zamuje wajan saloon,da wankin qafa, "

Nihla tayi shiru ta kalli kayan dasuka siyo tace" yanzu Anty Nadiya me za'ayi da wannan hadin?
"

Murmushi tayi tace" kece zaki dinga sha kullum safe, da dare, idan zaki iyama har rana, zakisa
ka ruwa kadan ya tafasa saiki debi garin wannan maganin kidamashi a cup dadan kauri, saiki
zuba acikin Ruwan zafin nan nakan wuta kina juyawa har yayi kauri saiki juye kidinga sha da
madara ko nono kindirmo, Nihla nabaki wata uku cikakke qirjinki zai qara cikowa sosai, Sannan
hips dinki ma zasu sake budewa "

(yanmata masu buqata da matan aure zaku iya gwadawa yanayi sosai, shine de ake zuba
mukushi aroba azo asiyar muku shi dubu uku uku, dukansu zaki hadesu waje daya ki soya su
sama-sama, saiki kai aniqa miki, ki tankade kidinga damawa kinasha )


Jikin Nihla yayi sanyi, jiki a sanyaye tayi mata godia ta tafi gida dashi,da daddare tana zaune
agadon ta har sha biyu na dare takasa bacci, tunanin Nadiya kawai take, dame zata sakawa
Anty Nadiya? Yazama dole ta cire ya Abba daga cikin zuciyarta kodan Anty Nadiya,dole zata
dage da addu'ah akan Allah ya yaye mata, afili ta furta " insha daga yau nahakura dakai ya
Abba, koda sanka zaimin illa insha Allah daga ranar yau, nahakura da kai, saide yamin illlar"















(kunga laifin Nihla? )



Ina godia sosai da sosai masoyana, yan group din DANGI DAYA kuna sani nishadi, wallahi
sharhinku yana bani dariya � oh Abba ma yaga takansa

Amnah El Yaqoub ✍️[6/22, 11:41 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



21&22




Tunani taci gaba dayi, mahaifin ta bashi dashi Mai qaramin qarfi ne, meyasa ma Tun farko
hankalinta Yaqi karkata kan karatu? Wata zuciyar tace saboda soyaiyar Abba
Juyi tasakeyi, gashi wadda yaqita saboda itanma bawani sonsa takeba, ita kuma yafuto bainar
jama'ah yace baya sonta, gara ta hakura itama dashi, idan taci gaba da sonsa har Anty Nadiya
tagano gaskiya haqiqa zatace ta munafurceta, to gara Tun wuri ta tsaida Rayuwar ta waje daya,
itama ta haqura dashi dukda tasan abune Mai wahala amma dole zata kamanta , tsaki tasaki
afili, tayi juyi tareda addu'ah tarufe idonta

Washe gari suka tafi wajan saloon bayan tadawo daga makaranta,ba Nadiya kadai ba, hatta
masu shagon tsayawa sukai ganin yanda gashinta yaqara tsawo, gashi Kamar ba 'yar hausawa
ba, ita kanta wata irin iska takeji tana shigar ta

Duk lokacin data ga Anty Nadiya saita tuno da ya Abba, amma tana kokarin kawar da tunanin
sa acikin zuciyarta

Sati na zagayowa sukaje wajan gyaran jiki, Nihla saita koma Kamar wata amarya, mamy de
tanata Kallanta tana wannan bidiri, saide tayi Murmushi kawai, taga take taken Nihla qarfi dayaji
sotake ta sauya

Sosai ta maida hankalinta akan karatu, babu ruwanta da kowa a makarantar, kawai karatun ta
tasa agaba,dinkunanta da sukaje suka karbo shi tafara sakawa, babu meyi mata kallan raini,
bata shiga harkar kowa bama bare ta fuskanci wani bacin rai

Kamar yauma tana zaune awaje daya cikin makarantar, littafi ne a hannunta tana dubawa, taji
anyi mata sallama, dago kanta tayi ta dubeshi, batare data ce komai ba, shima yayi Murmushi
Yazauna dab da ita yace "baki ganeni ba ko?"

Tace "eh, bangane kaba"

Yayi Murmushi yace "qanin Anty Nadiya nefa Abdallah, anan makarantar nake nima, tacemin
kullum kina shigowa shine taturo min number ki tace nanemeki, to nakira taqi shiga sai ita
nakira tafadamin Inda zan sameki"

Lokaci daya tayi Murmushi tace "ashe kaine, ai inajin labarin ka awajanta,amma ban taba
ganinka ba, ya gari?"

"wallahi ina wajan friend dinane, kawo natayaki karatun"

Yaja littafin ta yana gani, itama da taga yanada kokari saita fara Tambayar sa abinda bata
saniba


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe take shiri zataje wajan biki, wanka ta dauka taci kwalliya Kamar me, sannan ta
shirya tsaf tafice batare data kalli ko Inda dakinsa yakeba, shima daya shirya yafuto zai tafi
makaranta bai gantaba, kuma beyi tunanin neman Inda tatafiba, Yarufe gidan yayi tafiyar sa

Tun azahar yagama abinda yake amma saiya zauna baidawoba sai yamma, daya dawo
gidanma abin mamaki bata nan, yayi shiru yana tunani, yarinyar nan tunda akai aurensu
gaisuwa ma bata Hadashi da ita, ga mu'amula datake da samari awaje duk yana sane da ita,
me zaiyi mata ne yaja hankalin ta ta daina abinda take? Dariyar dayaji ne yasa yadago kansa da sauri ya kalleta, wani shegen mayafi tayafa ga kayan
datasa dinkin irin dede da itan nanne, ta kalleshi taci gaba da wayarta tana cewa "ashe pictures
sunyi kyau, kaima kagani ashe,"
Ta saki dariya tashige dakinta

Adam yabita da kallo, yanzu idan Diyana zata fita bekai tafada masa Inda zataje ba? Anya
yarinyar nan kuwa tasan me ake nufi da aure?

Binta yayi cikin dakin tana zaune tana cire Dan kunnanta, yace" daga ina kike? "

Hankali kwance tace "daga gidan bikin wata qawata"

"ke ba'a isa da keba kenan, kindauki qyale qyalen duniya kinsa aranki, maza suna kawo miki
ziyara, kinada aure akanki kina waya da wasu qartin banza, to Karki Manta de da aure na
akanki, kuma duk abinda kika aikata zunubi kike kwasa akanki"

Kallansa tayi tace "zunubi?"

Takaici yakama Adam, tabbas idan yaci gaba da kula yarinyar nan, zai iya yimata dukan tsiya,
kuma yasan hakan a addinance Babu kyau, cikin bacin rai yafice yayi dakinsa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Kalau yadawo gidan yau yana cikin nutsuwarsa,yana sanye da qananun kaya sunyi masa kyau
sosai, kayan kallo take gogewa tadago taganshi taci gaba da abinda take, beyi mata sallama ba
yaqaraso falon Yazauna yana ganin yanda take komai cikin nutsuwa, itama ko kallan Inda yake
batayiba, harta gama tashige kitchen
Bayanta yabi da kallo kenan shi yarinyar nan saboda bata daukeshi a mijiba ko gaida shi ba
zatayi ba bare sannu da zuwa
Ajiyar zuciya yasaki yatashi ya shige d'akinsa, Dan qaramin fridge din dakin nasa yabude
yadauko magungunan maye ya ajiyesu a gefensa, Yazauna agefen gadon yabude kowanne
yasha, sannan ya koma gadon ya kwanta yana lumshe idonsa

Acan kitchen kuwa Dida lemon Kankana tahada Mai dadi tahada da Abincin datayi tazuba masa
sannan tafuto zata kawo masa, tana zuwa falon taga baya nan, Dan haka kai tsaye tashige
dakin da Abincin

Tana zuwa gabanta yafadi ganin uban kwalaben dake gabansa shikuma gashinan Akwance
yana bacci ko takalma bai cire ba

Girgiza kai tayi ta ajiye Abincin agefe ta tsugunna tadauke kwalaben, karantawa tayi, afili ta
furta "Benalyn, Codein,Emzolynn, ‍♀️tabdi harda su Emzolynn acikin kayan mayen?"

Karaf maganar ta shiga kunnansa, a lokacin bacci yafara fizgarsa

Dida kuwa kwashe shu tayi, ta ajiye masa agefe,kafarsa takama tafara kokarin cire masa
takalmin, tana cirewa ta zubawa kafarsa ido tana gani, kafar me kyau kuwa, saide Mai kafar
bashida kyan hali, ahankali tatashi zatabar wajan yasa kafarsa yabigeta, lokaci daya ta'iyo
kansa tafada Kirjinsa, sai jin mutum yayi akan Kirjinsa, Dasauri yabude idonsa yazuba mata ido
yana Kallanta

Dida kuwa idonta yana kan bakinsa, meyasa yana shan kayan maye amma lips dinsa beyi baqi
ba?

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kasancewar yasan Babu me shigo masa daki yasa daya futo daga wanka yana daure da towel
iya qugunsa yanufi cikin kayansa yadauko manyan kaya, saboda baqi dazasu gani shida Abba
akan shirye shiryen bude campany nsu.
Kayan yadauko ya ajiye sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login