Showing 12001 words to 15000 words out of 104433 words

Chapter 5 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf

Advertisement

kira da Diyana ta kalli Nihla "haba haba Nihla,
wannan hijabin fa, Kamar bakyajin zafin duniyar nan? Kinci wani uban hijabi Kamar matar liman
haba be wise mana"

Murmushi nihila tayi tana kallanta, yanda taci wannan riga da wando aidole tayi fada akan hijabi

Wadda batayi maganar ba tace "Nihla sannu da zuwa kinji, kirabu da Diyana, idan kina neman
mace Mai shegen son maza to Diyana ce" ‍♀️

Kallanta Diyana tayi "to Dida idan banso maza ba mata zanso?

Dida tace "kide rage wallahi, ai a yimaka shedar arziki ma abu ne Mai kyau"

Tashi tayi tsaye, batama kalli yar'uwar tata datayi mata magana ba, tace "Nihla, natafi, saina
sake dawowa kokuma inkin shigo, ai zaki zo ko?"

Nihla tace "Zan shigo Diyana, nagode "

Ilham ta kalleta, "sai ina kenan?"

Kai tsaye batare da tantamaba tace "wallahi unguwa zamuje nida wani cika ‍♀️, yanaso zaiyi
birthday zamuje mufara shirin komai, danya takura ne ma wallahi banso zuwaba"

Nihla ta kalleta cikeda mamaki anya kuwa Diyana kalau take?

Dida tace "ke dince zakice antakuraki? Keda yawo? To idan baki bishi ba ina zakije?"

Babu alamun damuwa tacewa qanwar tata "Dida nadade kema kinsan dadade banje nigh Club
ba , wallahi nan nakeso naje"

Wannan karan kam Nihla daria tasaka
Al'amarin Diyana akwai kallo, kuma duk maganar datake yi hankalin ta kwance, zuciyarta daya
take magana

"Ilham tace" to saikin dawo, idan Nihla zatazo Zan rakota masha fira "

Tace musu " ok" sannan tafice

Dida ta kalli Nihla tace "haka take wallahi, Karki yi mamaki , mune yaran Anty Farida, itace
babba ninake binta, kuma wallahi Mom dinmu tasani amma tazuba mata ido, tana zama idan ta
tsarata shikkenan sai kiji shiru"

Murmushi Nihla tayi, tace "Diyana kenan" sannan sukaci gaba sa firarsu gwanin sha'awa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari Ilham ce tasake dawowa taja Nihla zasuje ta nuna mata kowanne part na gidan,
part dinsu suka fara zuwa
Hajiya Abida tana ganinta ta karbeta hannu bibiyu, tana tausayin yarinyar sosai, taso Aisha
Wato Diddi, hakanne yasa ta sakawa yarta suna Aisha, kuma ganin Nihla tana kama da
Aishanta saitaji dadi, sai nan nan take da ita, sun dade sannan suka futo
Ji tayi taci karo da mutum, Dasauri tadago kanta taganshi a tsaye abakin kofar part din shima
zai shigo, dogo ne fari, saide bakinsa dayayi baqi, alamun yana shan wani abun,yaraba
gashin kansa biyu yasakawa Rabin colour Mai launin yallow, dayan gefen kuma yabarshi yanda
yake, hatta Dan gemun daya tara irinna samari yan gayu shima yasaka masa kala,ga wani
uban bluetooth daya toshe kunnuwansa dashi, da alama waqa yakeji, kana ganinsa kaga tantiri
na gaske, ahankali tace masa "ina wuni?"

Yace "normal ne, Nihla ko?"

Tanajin irin Tambayar dayayi mata jikinta yayi sanyi, ahankali ta daga masa kai kawai

Yace "okey kihuta"
Yana fadar haka ya shige ciki

Ilham taja hannun ta suka futo ta kalleta sannan tace "wannan shine yaya fawaz, shine Babban
yayanmu, dagashi sai Aisha saini, Tun suna yara yake kula abokan banza har suka koya masa
shaye-shaye, babu irin qwayar da baya sha, Tun su ummah suna fada har sun gaji sunyi shiru

Nikuma kinga banaso naga abinda akeyi nayi shiru, kokuma ban shiga sabgarka ba ka shiga
tawa, to Zan rama ne, shiyasa Tun muna qanana ake cewa nafi kowa rashin kunya.

Nihla tace "kai wannan gida kuna abinda kukeso wallahi"

Part dinsu Alhaji Baqir sukaje "hajiya na'ila ta amsa musu cikin sakin fuska, amma aboye
hararar Ilham take, saboda yarinyar batayi mata ba kwata kwata �

Daga cikin dakin hajiyan yafuto da car key ahannun sa, yana sanye da manyan kaya riga da
wando na wani yadi, ya kalli hajiyan yace" mama zanje school inada lacture da yamma "

Tace" to adam saika dawo "

Ilham tace" yaya adam ina wuni"

Sai lokacin yakula dasu, cikin farin ciki yace "a a Kamar Nihlan Diddi"

Daria sukayi, Nihla tace "nice wallahi"

"A a masha Allah, sannu da zuwa"

Tace "yawwa"

Fita yayi daga falon, basu jimaba suma suka fice, Ilham tace "wannan shine yaya Adam,duk
Mazawaje family shine ustazi, idan kina neman alaramma kikazo wajansa to kingama samu,
lacturer ne, yana koyarwa a yusuf maitama, Wato northwerst, yayansa yana germany shida
yaya Abba Wato Aslam, su biyu ne a part dinsu
Nihla tace "Allah sarki, aikuwa Babu ruwansa bawan Allah"

Part din qarshe sukaje kafin su shiga Ilham tace "wannan shine part dinsu Diyana da Dida,
maman su tana auren dan'uwanmu ne na family shiyasa taci gaba da zama agidan nan, basu
bar family house ba, tana son yaranta sosai, batasan abinda zai tabasu
Kuma ayanda ummah take fada mana hajiya Farida Maman su Dida tana shiri da baban ki
sosai"

Nihla tace "hakane kam, nima nasani Ilham"

Part din suka shiga, nanma Babu laifi sunsha fira da Dida, Dan Diyana bata nan , sannan
suka futo kowa ya koma part dinsu


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Watan ta d'aya agidan tafara sakewa, kuma tagama gane halin kowa, nacinda Ilham take mata
ne yasa suka saba da ita sosai, Dida da Diyana ma suna zuwa, saide Dida tafita zuwa saboda

Diyana kullum tana wajan yawo, yawon ma bada yan'uwanta mata ba, maza!

Su yaya Usman da Aliyu fa farouq sosai suke nuna mata gata, Aliyu yakai ta anyi mata dinku na
masu kyau amma kullum tana cikin hijabi, da wahala ka ganta tazauna haka Babu hijabi, haka
yaya farouq yakai ta shopping tasiyo kayan kwalliya ta jeresu agaban mirrow din dakin nata,
Yaya Usman kuwa Sabuwar waya yasiya mata qirar iphone Mai tsadar gaske. Rayuwar ta take hankali kwance, saide tunda Diddi tarasu wata nutsuwa tasake shigar ta, abu
dayane yake damunta, tunda tabar jigawa kullum takira wayar Baba baya dauka, tarasa dalili,
lafiya lafiya zata kira yan'uwansa su gaisa da ita amma shi idan takira baya dauka, idan tayi
masa text baya reply, amma tasan koma menene zai iya neman ta daga baya, tasan Baba da
wahala yayi fishi da ita Babu dalili.

Hisnul Muslim din hannunta datake karantawa ta ajiye tafuto falo, babu kowa da alama Momy
ma tana daki, zama tayi acikin kujerun falon tana kallan tashar aljazeera

Wayar Momy dake gefenta ce tafara qara, Ahankali takai hannu tadauki wayar, sunan dake
yawo a screen din wayar ta kallah taga ansa Abba nah, haka kawai ta tsinci kanta da faduwar
gaba, cikin ranta ta furta "Yaya Abba"

Wayar tana gab da katsewa tayi picking call din tace "Hello"

Shiru yayi anasa bangaren, Idanunsa a lumshe, yana kwance akan katifar robar nan ta cikin
ruwa, acikin swimming pool din gidansu, babu riga ajikinsa dagashi sai gajeren wando, gashi
Mai yawa kwance akan qirjinsa, cikin ransa ya furta "Sweet Voice"

Shirun dataji anyi ne yasa tasake cewa "Hello" still aka sake yin shiru, hakan yasa takashe
wayar ta ajiye ta

Sake qara wayar tayi akaro na biyu, adede lokacin kuma Momy tazo falon tazauna tareda amsa
wayar "Abba nah"

"Momy shikkenan ni duk kinmanta Dani ko nemana bakyayi, babu wanda yake missing dina"
ya qarasa maganar cikin shagwaba

Murmushi tayi "Abba kacika rigima wallahi, idan nakiraka kuna aiki kace baka kusa, idan naqi
kira kace bana nemanka"

Shiru yayi Bece mata komai ba, baisan mezai cemata ba,itama tasan hali Dan haka tace "yaya
aiki, ina Aslam?"

"Momy Aslam baya nan yaje Indonesia,"

"haka kuka iya dai, yau wannan qasa gobe wannan, amma banda Nigeria"

Yasan sarai abinda take nufi Wato sunqi dawowa gida, Dan haka yayi Murmushi cikin aji yace
"Momy toki shirya next week zamu dawo"

Cikin farin ciki tace "Alhamdulillah, Allah abin godia, da gaske Abba nah?"

"yes serious Momy, i will call you back" dif ya kashe wayar batare daya tambyeta wadda ta
d'aga wayar tasa da farko ba











pls Karku Manta da Comments da sharhi






Amnah El Yaqoub ✍️[6/18, 12:36 AM] El Yaqoub: ❣️ DANGI 'DAYA❣️

{Romance &Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub


Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


11&12


"Anty dawowa zaiyi?"
Nihla tayiwa Momy wannan Tambayar

Zama Momy tayi cikin farin ciki "Nihla Abba zai dawo next week"

Lokaci daya farin ciki yakamata, finally yaya Abba zai dawo, cikin murna tace "Tome za'a shirya
na tarbar su Anty? Medame yaya Abba yafiso?"

Hannayenta Momy takama Kamar qawarta tace "Yanzu de kije daki ki dauko memo saimu
zauna narubuta miki abubuwan da zamu iya buqata, sai kuje keda driver kusiyo, abinci za'a
hada Mai yawa yanda zai ishi kowa nacikin gidan nan"

Cikin murna tatafi dakin tadawo dauke da memo da biro tazauna kusa Momy, nan take Momy
tafara rubuta mata abubuwan dasuke buqata, duk irin kalar Abincin da Abba yafiso saida Momy
ta zayyanewa Nihla tas

"to Anty naje nayi wanka saimu tafi?"

"A a kibari sai gobe, sai kuje gobe da safe kidawo da wuri"

"to Anty"

Murmushi Momy tayi Wanda yayi kama da yaqe tatashi tace"zanje sauran part din na sanar
dasu "

Hankalinta ya koma kan tv, Dan haka ta cewa Momy" to Anty "

Fita Momy tayi cikin sanyin jiki, sai yaushe ne yarinyar nan zata dinga kiranta da Momy Kamar
kowa? Anya kuwa Nihla tasan yanda take jinta aranta kuwa? Yanzu idan tayi baqi tana murna ta
nuna musu ita cewa ga 'yarta kai tsaye sukaji takirata da Anty zataji dadi? Me zatayi wa Nihla
danta dauke ta amatsayin uwa?
Da wannan tunanin tafara zuwa part din hajiya Na'ila, da sallama ta shiga, hajiya na zaune itada
Adam da Alqur'ani a hannunsa yana dubawa
Gaisawa sukayi, shima ya gaida ta ciki girmama wa

Ta kalli hajiya Na'ila, "Hajiya munyi waya da Abba yanzu, yacemin suna nan zuwa Next week
insha Allah"

Hajiya Na'ila tayi farin ciki, amma meyasa ita nata Dan bai kirata yafada mataba sai abakin
facala zataji? Dama a family ana rad'e rad'in cewa angama shanye mata yaro, andauke mata
shi ankai shi wata uwa duniya da sunan karatu gashinan Yaqi dawowa, nan take ta nuna bacin
rai a fuskarta, Murya ciki ciki ta dubi Momy, "Allah yakawo su lafiya, nagode"
Jikin Momy yayi sanyi, tatashi tace "to sai anjima"

Tana fita Adam ya dubeta, "haba Dan Allah mama, meyasa kike hakane?" mutanan nafa sunyi
mana komai, mijinta yayi muku kara yatura dansa da danki karatu, gashi nima nagama karatu
na ina aiki na mallaki komai, to menene yayi saura awajan ki bayan godiyar Allah mama? "

" aikai dama ba dan agida na haifeka ba Adam to tabbas zan'iya cewa ansauya min kaine, da
anfara magana zaka fara kawo aya da hadisi, Allah yace, annabi yace, tashi kabani waje, d'an
kare me macacciyar zuciya Kamar ta ubansa "

Tashi Adam yayi yace" nina tafi masallaci "

Tsaki tasaki tace" haka de"

Washe gari Nihla ta shirya sukaje kasuwa itada driver da Dida, lafiya sukaje suka siyo komai
suka dawo, saboda Dida Babu laifi akwai nutsuwa sosai duk family kowa yayi mata wannan
shedar

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Bayan kwana bakwai wannan family ya haukace da hidima, kowa kaganshi yana cikin farin ciki
sosai, part din Momy yacika da qamshi anata girke girke, Nihla da kanta ta shiga kitchen tace
Momy tayi zamanta itace zata yiwa yaya Abba girki, Momy taji dadi sosai, Dan haka tatafi wajan
ma'aikatan gidan domin ta sanar dasu suje su gyara wa Abba dakinsa, a bangaren hajiya Na'ila
itama tanacan tana ta hidima

Diyana da Ilham da Dida ne suka shigo part din, dukansu kitchen din suka shige suka kama
mata aikin
Sosai Nihla taji dadin zuwan su

Ilham tace "Nihla duk kinyi kaca-kaca a kitchen gaskiya kinaji da yaya Abba"

Nihla tace "ke kuwa qawana guda zai dawo ba dole ba"

Diyana taja kujera ta zauna "nikam nagaji wallahi, kugama nazuba naci"
Ta kalli Nihla tace "Kekuma Nihla yaya Abba ne qawanki?, lalle baki samu qawaba wallahi,aini
dakika ganni nan gabana faduwa yake da dawowar su, saboda takura tadawo, harna fara
blocking numbers din gayu, saboda idan sukazo gida Babu shakka wataran koshi ko yaya
Aslam wani zai iya dukana"
Ilham tayi Murmushi tace "baki Manta marinda yaya Abba yayi mikiba ashe"

Nihla tace "au shi yaya Abban haka ya koma? Meyasa toni be taba nunamin ba?"

Diyana tace"inaaa ai zama ne beyi zamaba Nihla,� shiyasa, amma kowa yasan halin yaya
Abba a family dinnan, babu wasa, kwata kwata bayasan raini dagashi har yaya Aslam, shiyasa
ma jinin su yafi haduwa"

Jinjina kai Nihla tayi, wadannan karfa su saka mata tsoronsa

Dida ta wanke hannun ta yace"nikam duk family dinnan ko wallahi yaya Adam ne yake birgeni,
babu ruwansa shiru shiru dashi, gashi kyakykyawa inason manyan idonsa wallahi irinna hajiya
Na'ila "

Daria sukasa gaba dayansu Diyana tadubi qanwar tata" toke dama ai bakisan luv ba, yanda
kike shiru shiru ai dole kiso alaramma, to bari kiji kokin aure shi wallahi nasiha kawai zaki samu,
ko kiss bazai mikiba, kirasa wazakiso sai ustaz tirr"‍♀️ta qarasa maganar tana dafe kanta

Ajiyar zuciya Ilham tayi "gaskiya de Dida kinyi kokari, ni banga laifin yaya Adam ba amma
gaskiya banason maman su, hajiya Na'ila masifarta tayi yawa, danni da ace ita suruka tace ko,
wallahi saide ayita taqare bazan raga mataba" ‍♀️

Nihla tace "inama ace yaya adam din yazo yace yanason ki Ilham, muga yanda zaku kwashe
keda hajiya Na'ila ,"

Dasauri Ilham tace "wa? Allah yasawaqe, Dida ce take sonsa,danni kona aure shi idan
mamansa tamin ramawa zanyi saide yasake ni aranar, shiyasa duk family dinnan Babu Wanda
nakeso, gara kowa yayi harkar sa karma mufara soyaiya kayimin fada in rama azo ana cewa
nacika rashin kunya"
Dariya Diyana tayi "aini yaya fawaz yana birgeni, akwai hutu da gayu, danni duk Inda gayu yake
ina nan"

Ilham ta kalleta da mamaki tace "kirasa wazakiso sai Mashayi?"

Nihla tace "Ilham yayan naki kike cewa Mashayi?"

"to Nihla kowa yasan yaya fawaz mashayi ne, Dan qwaya, Dan yana yayana sainaqi fadar
gaskya?shiyasa ai ake ganin laifi na ace inada rashin kunya, bayan gaskiya nafada"


Diyana tace "keni can ta matse muku, anata zancen aure aure inma Allah yakawo mazajan
auren yazo haka za'ayi shi sulu, wannan tsohuwar dukta hana komai" ‍♀️

Dariya suka saka dukansu, suna wannan firar suna aiki ahaka suka gama suka adana komai
Inda yadace sannan suka dawo falo suna kallo, Momy ce tazo tabawa Nihla key "Nihla riqe
wannan key din na dakin Abba ne,nasa masu aiki sun gyara, amma kije kiduba kigani idan

akwai abinda baiyiba saiki gyara" karbar key din Nihla tayi, ita kuma Momy tayi ciki

Dida tace "Allah sarki Momy, dukta hana kanta sukuni saboda Dan autanta zai dawo"

Ilham tace "ai yanzu saide yayi hakuri dan Nihla ta qwace kujerar"
Tana fadar haka tamiqe tace "natafi nayi wanka na shirya, berage awa dayaba jirginsu yasauka"

Suma su Dida da Diyana tafiya sukai domin shirya wa, ita kuma Nihla tawuce dakin da'aka nuna
mata tun farkon zuwan ta gidan cewar na Abba ne, key tasaka tabude dakin, ahankali ta tura ta
shiga

Qamshin Air freshner ne yadaki hancinta, ta lumshe idonta sanan tabude, shigewa tayi ciki,
dakin yayi kyau komai yaji, daga kan labulen dakin har komai da Komai naciki duk launin blue
ne, gadon da aka lailaye ta kalla tasaki murmushi tareda fadawa kai, juyawa tayi tana kare wa
dakin kallo, anan taga pictures dinsa manya manya guda biyu, cikin sauri tatashi ta qarasa
wajan photon, zuba masa ido tayi, haka yaya Abba yakoma? Photon yayi kyau sosaai, daya ya
dauka da qananun kaya, sun karbi jikinsa sosai, shagala tayi da kallan pictures din tanajin wani
irin dadi da batasan dalilin sa ba, gyara zamanta tayi awajan kawai tana qare masa kallo, kira
Momy ta qwala mata hakan yasa tatashi Dasauri ta gyara gadon sannan tafuto

"kin gama ganin komai yayi? ''

" eh Anty komai yayi "

" to shikkenan kije kiyi wanka kishirya, su Alhaji sun tafi su dauko su"

Cikin murna tace "to Anty" sannan tayi cikin daki

Wanka tashige, tana qalqale jikinta Kamar ba gobe, ta dade tana wankan sannan tafuto

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Acan filin jirgin Aminu kano kuwa, zaratan samarin gidanne sukaje dauko 'yan'uwansu

Usman, farouq, Aliyu, Fawaz, da kuma Adam

Basu dauki lokaci wajan jiran su ba, jiriginsu yasauka
Farouq ne yafara hango su yace "yawwa gasu nan" nan yafara daga musu hannu

Gaba dayansu hankalinsu suka maida wajansu, Sunqara kyau, fatarsu ta goge, kana ganin
jikinsu kasan hutu Yazauna

Suna qarasowa wajansu suka saki ihun murna duk suka rungumesu, hankalin mutane yadawo

kansu gaba daya, mutanan wajan suka fara kallansu

Usman ya kallesu yace "Aliyu, yarafa sun girma, babu abinda zamu jira saide kowa yakawo
matar dayake so, musha biki"

Cikin aji Abba yadubi Usman "Aure kuma yaya?"

Dasauri farouq yace "aikai banda kai, nadade da yima mata, yanzu saura Aslam da, Fawaz,
dakuma Adam"

Daria Fawaz yayi, shida arayuwarsa mace ma bata gabansa, harkar qwayarsa kawai yasa
agaba, yaushe zaiyi wani aure, ahankali yace "Aure, Aure tab"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login