Showing 63001 words to 66000 words out of 104433 words
Chapter 22 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
Ilham tace "eto da gaskiyarsa, may be bayaso abubuwan sa suzube ne"
"mekike nufi Ilham?"
"Nihla kinsan goyo yanasa nonon wasu matan yazube, inaga shiyasa, inba hakaba ai bazai ce
kina goyo ba"
Nihla tadafe kanta ♀️ tace "Innalillahi.... Wallahi gayen nan yagama dani gaba daya"
Ilham tace "kema ai kinga ma dashi, Dan wallahi nide abinda na fahimta ko, ya Abba sonki
yake, kigafa yanda yawani matsa gab dake Kamar zaisaku ajikinsa keda Babyn kawai saboda
zai karbe shi, Nihla kiyi tunani mana"
"Ilham kenan, babu wata soyaiya, rannan ma sallama ya mana nida Momy yace yatafi zance"
Ilham tace "to nide abinda idona yagani aishi Zan fada"
Haka sukaci gaba da firarsu har hudu da rabi tayi, hajiya Na'ila takira wayar Ilham din tace tazo
kafin tatafi gida, tashi tayi tafara shirya wa, Momy takawo mata wani turaren wuta Dan Sudan
Mai qamshi, ta karba tana godia
Momy ta kalleta tace "Nihla karbo mata yaronta awajan Abba, zasu tafi"
Tashi tayi ta nufi dakin nasa, Ilham tanayi mata dariya qasa-qasa, ahankali ta tura dakin tashiga,
taganshi yana kwance yadora yaron akansa yana masa wasa
Cikin ranta tace ashe yana yiwa yara wasa, sallama tayi ta qaraso, tunda tashigo idonsa akanta
Ahankali shima ya amsa sallamar tata
Gabansa ta qarasa, ganinsa dagashi sai ita yasa taji duk yayi mata kwarjini, tana jan yatsun
hannunta tace "Momy tace akawo shi zasu tafi"
Da idonsa ya nuna mata yaron yace "gashi nan daukeshi mana"
Wai yaro akan qirjinsa bazai bata shiba saide tasa hannu tadauka, zuciyarta daya kuwa tasaka
hannu tadauki yaron
Jin hannunta yadan taba Kirjinsa hakan yasa ya lumshe idonsa, gaskiya yanzu kam yaqara
tabbatar wa kansa cewa soyaiyar yarinyar tayi masa mugun kamu
Nihla bata lura da yanayin sa ba tafuto daga dakin, bayansu yabi da kallo itada Babyn, sai yaji
dama basu tafiba, dama tazauna yasaka su agaba yana kallansu itada babyn
Bayan sun futo daga part din Momy Nihla tawuce part din umman Ilham itada Yaron, ita kuma
Ilham tawuce part din hajiya Na'ila
Ta dade a part din hajiya Na'ila kome take bata oho sannan tataho part din ummanta wajan
Nihla, takira ya Aslam yazo yadauketa suka tafi, Nihla taji dadin ziyarar da Ilham takawo musu,
Ilham tana sonta sosai, tazo gida amma bata wuni awajan sirikarta da ummanta ba, sai
awajanta tawuni
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Wanka yashiga ita kuma tana gyara masa dakin nasa, wayarsa ce tafara qara, tanufi wayar
taduba taga number ce take kira
Zuciyarta daya tadaga wayar, sai taji muryar mace tace "Malam Adam yau zaka shigo
makaranta kuwa?"
Gaban Diyana yafadi, cikin masifa tace "Wacece ke? Menene hadin ki da mijina?"
Alokacin yafuto daga wanka yayi gaban mirrow zai shirya, yana ganin wayarsa ahannun Diyana
sai masifa take amma ko Kallanta beyiba, shide yasan yanada gaskiya, kuma Babu wata mace
daza dauke hankalinsa daga kan Diyana a yanzu,yanda yakeji da amarcin nan ai Babu me
rabashi da maryam
Diyana kuwa sai masifa take, amma wadda takira wayar bata qara cewa komai ba Tun maganar
ta ta farko, daga qarshe ma saita yanke wayar
Diyana Tajuyo ta kalleshi tace "ashe yanmatan university har kiranka suke kuna waya bansani
ba"
Kayansa yake sakawa cikin sauri saboda yayi latti dayawa, yace "to menene abin damuwa
maryam, tunda kece Mai ni"
"wata yar'iska takira ka awaya da wannan safiyar kacemin menene abin damuwa? Amma yanzu
idan nice wani yakirani da yanzu kafara fada ko"
Hularsa yasaka yajuyo yana Kallanta, kishi qarara yagani akan fuskarta, Bece da ita komai ba
yadauki key din motarsa yana kokarin fita
Itama cikin haushi tafice daga dakin, da wayar tasa a hannunta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Wayar Dida ce a hannunsa yana sending pictures dinta zuwa tashi wayar, gyaran falo take,
yana ganinta tagama ta goge sauran kayan kallo, sai aikin take da jikinta Kamar batasan ciwon
jikinta ba
Kitchen ta wuce yatashi yabi bayanta, yana mata wani irin mayen kallo, "wai har yanzu aikin bai
qare bane?"
Kallansa tayi "bai qareba, abinci ma zanyi mana"
"kibar Abincin nan Dan Allah, basai naje nasiyo mana ba, ke kullum bakya hutawa"
Wani irin kallan soyaiya tayi masa "menene abin gajiya acikin girkin mutum biyu"
Ajiyar zuciya yayi yatako yazo bayanta ya rungumeta, yayi qasa da muryar sa yace "please
kibarshi"
"ya Fawaz Dan Allah kabarni nayi aikina, sokake kahanani kai kuma ka bata kudin ka, menene
amfani na da zakaje siyo mana abinci"
Kissing din wuyanta yayi, yasake qasa da muryar sa yace "wai wajan nan har yanzu bai warke
bane?"
Zaro ido tayi, takwace jikinta Dasauri "wallahi be warke ba, bari naje daki akwai abinda zanyi"
cikin sauri tafice daga kitchen din tabarshi anan
Murmushi yayi ya shafa kansa sannan yadawo falo Yazauna, yana ganinta takoma kitchen din
tana aikinta, harta gama tazo tazuba musu cikin flet daya, cikin nutsuwa suka gama cin Abincin,
sannan ta maida komai kitchen, kafin tafuto daga kitchen ya kwanta atsakiyar kafet din falon
yafara murqususun qarya Kamar gaske, Dasauri Dida ta qaraso wajansa "ya Fawaz menene?
Lafiya kake kuwa?"
Idanunsa a runtse yace "Dida cikina ciwo yake min, bayan kinsan meyake damuna, kuma gashi
kince wajan bai warke ba"
Gabanta yafadi, cikin in-ina tace "emana, be warke bafa da gaske dane, sannu insha Allah zai
daina"
Yace "shikkenan Babu komai idan na mutu ma shikkenan"
Dasauri tace "mutuwa! A a ba yanzu ba insha Allah,"
Yace "yanda nakeji Kamar mutuwa zanyi Dida"
Cikin shagwaba tace "to shikkenan kazo kayi amma Dan kadan gaskiya, kuma idan nace ya'isa
to katsaya ahaka"
Dadi yakama Fawaz, sai yau yaqara tabbatar wa Dida yarinya ce, yace "eh nayarda"
Lokaci daya yatashi ya janyo ta jikinsa, dayake yarinya ce kwata kwata bata ganoshi ba, yanda
yamiqe lokaci daya Babu wani alamar ciwo, anan falo yafara nuna mata yanda yayi missing
dinta, daga baya sukai ciki
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Zaune take akan kujera har yanzu dube dube take cikin wayar tasa, amma bataci karo da
number mace ko dayaba, koda yake tayaya zaiyi saving numbers din yanmatansa a wayarsa,
haka nan ranta yake mata zafi Tun safe
Shigowa yayi da sallama ta amsa masa batare data kalleshi ba, yayi Murmushi yana zama
agefenta, yace "wash Allah, nagaji wallahi"
Tanaci tayi banza dashi
Hannu yamiqa mata yace "bani wayata, dazu na Manta ban dauka ba"
Asheqe tamiqo masa wayar, ya karba yace "Maryam ina abinci"
"Dining"
Abida tace masa kenan, yatashi tsaye yace "wai saboda wata takira wayata shine kike wannan
fishin? Ni nayi tunanin ma kin huce, ai shikkenan, yau bazan samu damar da za'a kaini inci
Abincin bama, to zanje na Auro wadda takirani awayar, saitazo tadinga bani, tunda naga alama
nema kike ki rainani"
Nanma banza tayi dashi, shima yaje yaci Abincin sa hankali kwance, yana gamawa yakara
wayarsa akunne Kamar yayi kira yafara cewa "hello hajiya ta, kiyi hakuri dazun wata qanwata
ce tadauki wayar wallahi, kinaji na.. Kinsan me za'ayi yanzu....?
Diyana bataji qarshan wayar ba saboda shigewa dakinsa dayayi yarufo kofa, Baqin ciki
yakamata, dama ai tasan matar cushe bata daraja, wani kukane yazomata Mai cin rai, tatashi
cikin kuka ta nufi dakinsa, duk kayan ta dasuke dakin tafara hadawa tana hawaye
Dariya takama Adam, yayi fuska, sannan yatashi yazo bayanta ya tsaya yace "mekike shirin yi
haka maryam? Ina zakije kike daukan kaya haka"
"gidanmu Zan tafi, bazan zauna bakin cikin wata yadameni ba"
"saboda nace Zan qara aure kike kuka? To aikuwa ki shirya, Dan uku suna nan zuwa, Allah
yabani damar dazan ajiye mata har hudu acikin gidannan, kuma ni banyi miki alqawarin cewa
Zan zauna dake kekadai ba, garama kisa aranki kishiya tana nan zuwa"
Hannunta ta dora akanta tafashe da kuka, ta tsugunna awajan tana kuka bilhaqqi
Adam baisan lokacin da dariya ta kwace masaba, Yazauna agefen gadon yanata dariya yace
"maryam, yanzu saboda kishiya kike wannnna kukan?ashe kina sona haka? To kinga ni wasa
nake miki"
Kallansa tayi cikin harara, tatashi zata fice daga dakin
Cikin sauri yatashi yariqota, tafara fizge-fizge "nika cikani natafi gidanmu tunda dama baka
kaunar ganina"
Yace "maryam nifa wasa nake miki"
"Babu wani wasa, bayan gashinan kashigo daki kana waya da'ita, kacika...... Bata qarasa
maganar tataba yahade bakinsu waje daya, diff kakeji Diyana tayi shiru
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Itada Momy ne a kitchen sunata aiki kayaiyakin yin kek ne agabansu Nihla tana hadawa
Adede lokacin yafuto daga dakinsa yana daura agogo a hannunsa, yana sanye cikin suit,sunyi
mutuqar yimasa kyau, amma baisaka jacket dinba, a hannunsa ya riqeta, ko wajan Momy bai
nufa ba yafita Dasauri, zai qarasa campany wajan Aslam
A kitchen din kuwa Momy ta kalleta "Nihla idan kinsan bazaki iya yin kek dinnan ba Tun wuri
nasa ayi muku oder"
Murmushi tayi "Momy kenan, kede zuba ido kisha kallo, da kaina zanyi kek din"
Momy tace "shikam Abba da alama ma ya Manta cewa yau yake birthday, ke kuwa gashi baki
Manta nakiba Tun safe kin hana kanki sukuni, nima kin hanani zama saboda wannan bikin
birthday ganaki Gana Abba"
Murmushi tayi tace "Momy ai abune na rana daya, idan tawuce shikken"
"hakane, to Allah yabada sa'ah, guda daya zakiyi muku ne ke dashi kokuma daban daban
zakiyi?"
Kai tsaye tace "Momy da nawa Zan farayi, idan yanaso shima sai ayi masa"
"wacce irin magana ce wannan Nihla? Nafada miki Abba ya Manta yau yake birthday, ya za'ai
kuna gida daya keda yayanki kuma ranar birthday dinku daya aje ana rabe raben wani kek, kiyi
muku babba guda daya keda shi, sannan idan masu kayan Decoration din sun kawo kishirya
muku komai tare "
Jikinta ne yayi sanyi tace" to Momy "
Momy tafita daga kitchen din, ita kuma tayi shiru tana tunani, Allah yasa ta dinga control din
kanta agaban Momy karta ga tana tsanar danta qiri-qiri
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Cikin motarsa qirar Rang rover yafuto daga gidan, adede lokacin wani matashi yafaka motarsa,
yafuto hannunsa dauke da Wata leda anyi rapping dinta, cikin sauri ya Dakatar dashi yace
"yallabai Dan Allah nanne family house na Mazawaje ko?"
Yace "lafiya?"
Matashin saurayin yace "a a babu komai dama maigida nane ya aikoni daga Abuja wajan hajiya
Nihla, gift din birthday dinta ne yace ayyuka sunyi masa yawa bazai samu damar zuwaba,
amma very soon yana hanya"
Cikin mamaki yafara magana aransa Birthday? dama yau take yin birthday?to ai shima yaune
nasa, Waye wannan daya aiko mata da gift daga Abuja? Haushi ne ya kamashi, yaji wani irin
kishi aransa
Kallan matashin yayi yace "i don't no, ka tambayi wasu"
Daga nan yaja motarsa yayi gaba, matashin yayi sa qare yana kallan motar Abba, ikon Allah,
shikuma wannan daga tambaya?
Cikin gidan yanufa yaga maigadi anan yafara tambayarsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"kaga Abba idan muka saka hannun jarinmu Awannan campany zamu samu riba sosai, saboda
shima Babban campany ne ansan shi sosai"
Yana jiran yaji Abba yabashi amsa sai yaji shiru, cikin mamaki ya kalleshi "Abokina mekake
tunani ne?"
Nanma yaji shiru, ta'bashi yayi yace "Abba!!"
Cikin sauri yadawo daga duniyar tunanin daya lula, ya kalleshi "Aslam ya akayi?"
Dan qaramin murmushi Aslam yayi "kana nufin kacemin duk wannan maganganun danayi baka
jina?"
Kallansa yayi yadaga masa kai alamar hakane
Wani murmushin Aslam yasake yi "meyake damunka haka Abba? Tunanin me kake? Yanzu
fadamin menene matsalar?"
Ajiyar zuciya yayi "yanzu Aslam misali idan mace tana Birthday me kake ganin za'a bata
amatsayin gift?"
Aslam yayi Murmushi, sai yanzu yagano Inda tunanin Abba yadosa
Yakalleshi yace "um nide aganina za'a iya bata kyautar sarqa idan ranar birthday din tazo saika
saka mata, kokuma zobe kakama hannunta kasaka mata, kokuma ka tambayeta abinda takeso,
shine ma yafi"
Cikin damuwa Abba yace "zobe, sarqa, kokuma kayan ciye-ciye ai duk sun zama gama gari
Aslam"
Aslam ya kalleshi cikin mamaki, lalle Abba yashiga dayawa
Yace "tome kake gani za'a bata?"
"why not asiya mata Mota? Kamar zatayi murna da'ita"
Aslam yayi dariya yace "gaskiya Abokina Nihla tayima Babban kamu, irin wannan soyaiya haka
aiko Nadiya ba'a nunawa itaba"
Memakon yabawa Aslam amsa sai yace "please ka bincika min yanzu, inaso akawota yanzun
nan"
Aslam yace "okey" sannan yadauki wayarsa yafara dube-dube, yadago yadubi Abba yace
"wacce irin qira kake buqata?"
Kai tsaye yace "Camry"
Aslam yace "angama"
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Suna tsaka da aiki iliya maigadi yashigo yace tanada baqo, cikin mamaki tafuto anan taga
Baqon fuska, suka gaisa dashi faram faram, gift din hannunsa yabata yace "gashi daga Abuja,
inji ogana, yace kiyi hakuri shima yakusa zuwa"
Murmushi tayi jin daga Inda saqon yake, tasan ya Yusif ne, tace "a a babu komai wallahi,
zamuyi waya dashi, qaraso mana ciki kasha ruwa"
Yace "a a Hajiya, inakan hanya ne wallahi, babu damuwa"
Nihla tace "to shikkenan nagode" daga nan takoma ciki
Tana zuwa tabawa Momy gift din nata tace "Momy, ya Yusif ne ya aikomin da birthday gift"
Jikin Momy yayi sanyi, amma dukda haka saida ta nuna murnar ta afili, tace "masha Allah, Allah
yasaka da alkhaairi, da alama ko menene aciki zaiyi kyau Kamar kyakykyawar 'yata"
Murmushi tayi tafara kokarin budewa tace "Momy bari mu bude mugani"
Cikin sauri Momy ta riqe hannunta "a a, kibari idan mungama aiki, kinyi wanka, me makeup tazo
tazo tayi miki kungama bikin birthday dinku lafiya saiki bude abinki atsinake"
Tace "to Momy,"
Sannan tayi hanyar dakinta da kyautar tata
Dawowa tayi sukaci gaba da aiki, Momy tana ganin tsantsar baiwar da Allah yabawa Nihla, kek
din ta cire daga cikin oven tafara yaiyenke gefensa,sannan tadauko wifed cream na ruwa, ta
ajiye, tafara neman sauran kayaiyakin buqata
Kallan Momy tayi tace "Momy, wai yaushe Daddy zai dawo ne?"
"kinyi missing dinsa kenan, gobe zai dawo insha Allah,"
Cikin murna tace "to Allah yakaimu"
Momy taga yanda Nihla take murna saitaji dadi, amma itama kanta tana murna da dawowar da
Daddy zaiyi saboda tanaso tayi masa maganar matsalar Abba, gara su zauna dashi suyi masa
magana akan Budurwar sa Nadiya, yaushe zasuje anema masa auren nata, bazai iyu suci gaba
da zama dashi hakaba
Iliyane yasake shigowa cikin part din, fuskarsa dauke da murna, yafara kiranta
Dasauri ta kashe oven din suka futo daga kitchen itada Momy, Momy ta zauna akujera tace
"dama ni duk kin gajiyar dani, bari nadan huta"
Nihla ta kalli iliya tace "iliya danme qarfi lafiya kuwa?"
Yace "hajiya kinada wani Baqon ne, gashinan yashigo har ciki, yana compound"
Cikin mamaki tafuto harabar gidan, da wata hadaddiyar mota tayi tozali Ash color, qirar CAMRY,
na cikin motar da yaga tafuto yabude shima yafuto, yagaidata tareda miqa mata wats takarda
da key din motar yace "gashi inji yallabai"
Jikin Nihla yayi sanyi, yallabai kuma? Waye hakan? Cikin mamaki ta kalleshi tace "please waye
ya aikoka?"
Yace "daga campany ne"
Daga nan ya juya yatafi, batare daya sake cemata komai ba
Motar ta qarewa kallo, tayi masifar yin kyau na qarshe, amma waye wannan dazai aiko mata da
Mota?
Cikin sanyin jiki tajuya cikin falon su, Momy tace"yanaganki haka jiki a sanyaye, menene? "
Zama tayi kusa da Momy ta miqa mata car key din tace
"Momy Mota aka aikomin dashi"
Momy tace "Mota kuma?"
Daga kai Nihla tayi, Momy cikin sauri tatashi ta leqa taga motar Sabuwa ce dal sai daukan ido
take, dole nema ta birge Wanda aka mallaka wa ita
Tadawo wajan Nihla tace "waye ya aiko miki?"
"nima bansaniba Momy, amma gashi harda takarda bari nagani"
Momy tace "duba kam"
Nihla tabude 'yar qaramar takardar da aka hado da'ita tafara karantawa :
{ _Ina tunanin Babu Wanda_ _ya taba sanar da ke cewa__ _murmushin ki abin so ne ga_
_kowa,duk lokacin da kike yin_ _murmushi yana mayar da fuskar ki tamkar wata_ _fitila mai
hasken gaske, You're Beautiful, shiyasa_ _akoda yaushe qwaqwalwata take_ _zana mini
kyakkyawar_ _fuskar ki a cikin zuciyata, wadda ta zamo_ _abar kallo a gare ni a_ _duk lokacin
da nake_ _zaune ni daya cikin kadaici_ , _murnar qarin shekara._
*ABBA* }
Gabanta ne yahau luguden faduwa bayan tagama karantawa, cikin ranta tace ya Abba!
Momy dake zaune ta kalleta cikin matsuwa tace "waye ya aiko miki"?
Gaskiya banda bakin godewa masu yimin sharhi akan wannan littafin, saide nace Allah
yabarmu tare yabar zumunci, inajin dadin yanda kuke sharhi akan DANGI DAYA nagode
Amnah El Yaqoub ✍️[7/7, 2:00 AM] El Yaqoub: ❣️ DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
41&42
Gabanta sai faduwa yake, yayinda jikinta yayi mugun sanyi tadubi Momy tace "Ya Abba ne"
Ita kanta Momy saida tayi mugun mamaki, Abba kuma? Wannan yaron kuwa yasan meyake
shirin janyo musu? Aqasan ranta tabbas tayi murna sosai yar'uwa da