Showing 36001 words to 39000 words out of 104433 words
Chapter 13 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
ya shafa yaji zafi sosai, lokaci daya yashiga
damuwa, yace "Sannu, sannu kinji, bari nahada miki ruwa kiyi wanka sai Muje asbiti"
Dagota yafara yi daga jikin sa amma taqi tashi, ya sassauta muryar sa cikin sigar lallashi yace
"kiyi hakuri, zaki denajin zazzabin insha Allah, kinji ko?"
Ahankali ya maida ta ya kwantar da ita, Sannan yashige toilet dinta yahada mata ruwa, yadawo
yakamata zai tasheta, ta miqe kenan taji zuciyarta tana tashi, lokaci daya taji amai, cikin sauri
zata shige toilet yatareta zai kamata suje, aikuwa sai amai ajikinsa, farar rigar yadin daya saka
ya kalla, gaba daya tabata su da amai, tayi tunanin zataji Saukar duka, amma abin mamaki sai
yace mata "Sannu, sannu kinji,"
Daga masa kai tayi, yadaga hannunsa ya cire rigar jikinsa, yadawo daga vest sai dogon
wandon jikinsa
Kamata yayi suka shige toilet din, sannan yafuto yabarta aciki, dakin ya gyara tsaf, yasake
gyara mata gadon, sannan yabude kayan ta yana dubawa kozaiga Mai Dan sauqin sakawa,
amma gaba daya da riga da wanduna yayi ar'ba
Wata atamfa yagani yajanyota, ya ajiye mata akan gadon, shikuma ya juya ya koma dakinsa
yasake shirya wa sannan yadawo dakin nata
Bude toilet din tayi tafuto, taganshi yasaka qananun kaya, cikin ranta tace ashe yana saka
qananun kaya,kayan kuwa sun karbi jikinsa, Kallanta yayi sau daya yakawar da kansa cikin
sauri, yace "ga kaya nan kisa, saimu tafi asbiti yanzu"
Yadauki wayarsa yayi kira "hello monitor ki fadawa kowa cewa bazan samu damar zuwaba,
matata batajin dadi"
Dasauri Diyana ta kalleshi, yanzu saboda ita yaya Adam zai fasa zuwa wajan aikinsa?
Fita zaiyi daga dakin tace "ya Adam"
Juyowa yayi Bece da ita komai ba tace "banda pad, kuma inaso zanyi amfani dashi"
"idan mun fita sai asiyo" yana fadar haka yafice daga dakin, yaga alamar Diyana batasan cewa
bayasan ya zauna da ita Awannan halin datake ba, kokuma kallan dutse take masa waya sani,
ita kuwa ko a jikinta
Kalau ta shirya suka tafi asbitin aka dubata aka bata magunguna Sannan sukaje suka siyo pad
din, suka dawo gida
A sauqaqe yadafa mata indomie da dafaffan qwai saboda bazai iya soyawa ba, yadoro
spoon akai tareda gorar ruwa, sai ganinsa tayi yashigo dakin da abinci, karon farko da taji
Tausayinsa ya kamata, meyasa take masa Wulaqanci? Tabbas sai kana jinya zaka zaka gane
masoyinka na gaskiya
Zama yayi akusa da'ita, yace "maryam tashi kici abinci kisha magani saiki kwanta"
Ahankali tatashi tasa hannu zata karbi flet din, yace "A a, ai naga jikin naki Babu qarfi, kibari
nabaki"
Ta Girgiza kanta tace "zan'iya ci ya Adam"
"maryam banason musu fa"
Shiru tayi, takasa yimasa gardama, ahankali ya matsa kusada ita har jikinshi na gugar nata,
yafara bata indomie din abaki, saida yaga ta qoshi sannan yabata maganin tasha, yace "ki
kwanta kihuta, Allah yasawaqe"
Tace "amin" idonta akansa, tashi yayi daga kan gadon Yazauna akan bedside drower yayi shiru,
itama haka Babu me magana acikinsu, saide cikin ranta tabbas ta Jinjina wa ya Adam, saika
zauna da mutum sannan zakasan halinsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe ya shirya yabi jirgi zuwa Abuja, yakamata yaude yaje yaga Nadiya yaji A'ina suka
tsaya akan maganar aurensu, yanaso kawai yaturo iyayen sa agama maganar komai
Baisha wahala ba daga Airport kai tsaye wani abokinsa dayake tuqin jirgi amma bangaren state,
yadauko shi a motarsa suka qaraso gidan nasu Nadiya,akofar gidan sukai Parking ,suka futo
daga cikin motar yakira wayarta nan take tashiga
Tana dauka cikin muryar sa Mai cikeda aji yace "Nadiya gani agidan ku"
Cikin mamaki tace "gidanmu kuma?"
"eh, nazo ne muyi magana dake Mai muhimmanci, koda yaushe kina tambayata yaushe zanzo
yaushe zanzo, banda lokacin ki, banida kirki, to yaude gani"
Tace "ayya, gashi kuma wallahi bana nan, naje lagos gidan Antynmu, munata shirin biki"
Be tambayeta bikin waba, sannan Beyi tunanin komai ba yace "okey, to shikkenan idan kindawo
saiki sanar Dani, lokacin dana samu dama sainazo, but yanzu Zan turo miki 50k sai kiyi anko
dashi"
Tace "to shikkenan Sadiq nagode"
Suna ajiye waya yatura mata kudin, sannan yadubi abokinsa yace "kaji batanan taje lagos, next
time kawai"
Maigadi yaji dirin Mota abakin get kuma yaji shiru baiji ance yabudeba, Dan haka ya leqo, yana
futowa yaga su Abba, nan take yagane shi
Cikin farin ciki yace "a a yallabai ashe kune kuke tafe, toku qaraso ciki mana"
Abba yace "A a sammani kada kadamu, ai munyi magana da ita ma yanzu tace taje lagos ko?"
Sammani maigadi yace "eh wannan gaskiya ne yallabai, ya hakuri kuma?"
Cikin mamaki Abba yace "wanne irin haquri kenan sammani?"
Yace "to yallabai Wanda yarasa mace Kamar Nadiya ai yayi Babban rashi dole a jajanta masa,
ai lagos din data tafima sunje hado kayan lefenta ne itada mijinda zata aura ,
bikinma yanzu haka saura sati uku" ♀️
Lokaci daya kansa yasara, cikin tsananin mamaki yace "sammani me kace?"
Sammani maigadi yace" wallahi gaskiyar kenan yallabai "
Lokaci daya yafara karanta kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju'un abaiyane, da abokinsa da
sammani maigadi basu zataba kawai sai ganin Abba sukai aqasa♀️
Cikin sauri sukayi kansa suna kira, abokinsa yana cewa "Abba! Abba!!"
Shikuwa sammani yana kira "yallabai! Innalillahi..."
Daqyar suka cacimeshi suka saka amota, sannan abokin yaja cikin sauri, sukabar kofar gidan
Asbiti yakaishi, anan doctor yake tabbatar wa da abokin cewa kawai yaji abinda ya razanashi ne
shiyasa ya suma, allura akayi masa, ba'a dauki lokaci Mai tsawo ba yafarka, amma yakasa
cewa komai, abokin nasa yabashi hakuri, amma Abba bai iya cewa komai ba, daga qarshe ma
tashi yayi ya cewa abokin yagode amma yanaso yabar garin yanzun nan, duk yanda abokin
yaso hanashi tafiya abin ya gagara, dole sai Airport yakaishi yabi jirgin dazai tashi zuwa kano
Ikon Allah ne kawai yakai Abba gida, Momy tana zaune afalo sai ganin shigowar Abba tayi yana
tafiya yana layi Kamar d'an maye, baima kalli Inda takeba yashige dakinsa da alama baima lura
da'itaba
Fadawa yayi akan gadonsa, Baqin ciki yazame masa goma da ashirin, kenan kudin ankon
aurenta yatura mata?
Lokaci daya yaji hawaye yana zubo masa, ga wani zazzabi dayakeji me mugun zafi, blanket
dinsa yaja yashige ciki yana kuka, tabbas Nadiya taci amanar soyaiya
Momy taturo kofar dakin tashigo, ganinsa cikin bargo yasa ta qarasa da sauri tazauna a
gefensa tace "subhanallah... Abba na lafiyarka kuwa?"
Dasauri yatashi yadora kansa a cinyar Momy cikin kuka yace "Momy Dan Allah kiyi hakuri,
kuyafemin keda Daddy, bazan sake ba Momy"
Gaban Momy yafadi, bafa qaramin abu ne yakesa Abba kuka ba, anya kuwa kalau yake? Cikin
tashin hankali tace "Abba meyake faruwa ne? Me kayi kake bada hakuri? Kayimin bayani"
Kuka yake harda Jan zuciya, yakasa fadawa Momy abinda yake faruwa, tayaya zai fada mata
cewa yarinyar dayaso bijire musu, yaso Yaqi yi musu biyaiya akanta ta yaudareshi zata auri
wani? Tayaya?dole ne yanemi yafiyar iyayen sa akan qin biyaiya dayaso ya musu
Momy tace "to shikkenan bari nafadawa Daddynka tunda ni bazaka fadamin ba"
Nan take takira Daddy, yana dauka tace "Alhaji takwaranka fa Babu lafiya, gashinan yazo
yanata kuka wai nayi hakuri"
Daddy yace gashinan zuwa, Momy ta kalli Abba taga ko alamar dena kuka bayayi tace "to inaga
addu'ah zanyi ma Abba, meyiwa gamo kayi"
Alokacin Daddy yashigo dakin, Abba yana jin shigowar Daddy yace "Daddy Dan Allah kayi
hakuri, natuba Daddy wallahi bazan sakeba"
{Allah sarki Abba,Dani kabawa kudin ankon ma wallahi }
El Yaqoub ✍️
[6/24, 11:52 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to DANGI DAYA GROUP
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
25&26
Daddy yadubi Abba yace "yanzu Abubakar da girman ka kasamu agaba kana kuka kamar
mace!, sannan mun tambayeka abinda yake damunka kayi shiru, sai hakuri kake bamu, to
hakuri akan me?"
Shiru Abba yayi Bece dasu komai ba, shi ya'isa yafada musu gaskiya? Ai kaf family dinnan sai
sunyi masa dariya wasu ma suce Allah yaqara
Dan haka yayi shiru yaqyalesu
Momy tace" Alhaji Abba fa ba magana zaiyi ba, nikam kaga tafiya ta "tasa hannu tadauke kan
Abba dayake cinyarta tafuto daga dakin
Shima Daddy yace" to ai shikkenan tunda haka kazaba "
Yafuto daga dakin, yaje wajan Momy yace"ko menene yake damunsa? Amma miskikanci ya
hanashi magana?"
Momy tayi Murmushi tace "to awajan wa yadauko halin"
Shima murmushi kawai yayi, yashige dakinsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tun bayan dukan dayayi mata ta tattara shi ta watsar, gaba daya tadena shiga sabgarsa, idan
taji yashigo gidan ma tana falo cikin sauri take shigewa dakinta Tun kafin yashigo falon, abinci
kuwa zatayi tabarshi anan, idan yaci shikkenan idan baici ba kansa yayiwa itade tasan cewa
batada haqqin kowa akanta, koda rasuwa tayi tasan tafita haqqin sa saide nata haqqin dayake
kansa
Tunanin abin datasa aranta yasa duk tafara ramewa, idanunta duk sun futo
Yauma shi kadai ne azaune afalon, Tun safe baije ko'inaba amma baiga futowarta ba, Kamar
wasa saigata tafuto daga daki zataje kitchen, ta kalleshi ta watsar ko gaisuwa Babu, taje ta
dauko ruwa tasake komawa dakin
Shikuwa Fawaz Yana binta da ido kawai
Yayi ajiyar zuciya yatashi yabita cikin dakin, yaune karon farko daya taba shigowa dakinnata,
yanemi waje Yazauna yana Kallanta tanashan ruwa, saida tagama sannan yace "meyake
damunki kika lalace haka?"
Shiru tayi masa, Dan renin hankali kawai, yagama dukanta yadawo yana Tambayar me yake
damunta, idanunta sukai rau-rau zatayi kuka
Sassauta murya yayi yace "bazaki fadamin ba?"
Duk yanda Dida taso boye hawayen ta saida suka zubo, tasa hannu tashare tace "banasan
abinda kake aikatawa ya Fawaz, kana dukana, kanashan kayan maye, nikuma banaso"
Tana qarasawa tasake fashewa da kuka
Fawaz yayi shiru yana tunani, Wato yau sabodashi ake kuka, yau saboda andamu da abinda
yake aikatawa ake kuka yadena,nan take yarinyar tabashi tausayi
Kallanta yayi yace "to kiyi hakuri, dena kuka, insha Allah daga yau nadena"
Cikin mamaki ta kalleshi ido duk hawaye tace "da gaske?"
"yes da gaske nake"
"harda dukanma?"
Yasake cemata "nace miki nadena, kema saiki daina kukan ko? "
Aikuwa nan take tashare hawayen idonta
Yatashi tsaye yace "Zan fita, but banaso kina zaman dakinnan, kifuto falo ki zauna, kici Gaba da
abinda kikeso kinji ko?"
Cikin murna Dida tace "to"
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda Diyana tafara rashin lafiya Adam yake kula da'ita, kokadan baya barin ta tayi aikin komai
Yauma shida kansa yakawo mata abinci har daki, ya tarar tana gyara dakin, yace "maryam ga
abinci"
Tace "ya Adam aina warke ma, nagode sosai da temakon dakamin, yau nice yakamata nadafa
ma Abincin"
Adam yayi Murmushi yace "nagode, amma ba yanzu ba,kici Abincin kishirya zamuje gida"
Cikin farin ciki Diyana ta rungumeshi tace "yawwa nagode ya Adam"
Cak jijiyoyin jikin Adam suka tsaya, yarinyar nanfa kada tasa yakasa aiwatar da abinda yayi
niyya, cikin wata irin slow voice yace "Diyanaaah" yaja sunan nata
Ahankali tadago daga jikinsa ta kalleshi yaune karon farko data tabaji yakirata da wannan
sunan, koda yaushe maryam yake cewa, gashi yanda yakira sunan nata ma kadai ya'isa
yasaka mutum cikin wani hali, ya'iya kiran sunan, tana gama wannan tunanin tayi fari da idonta
tace "na'am"
Yace "kije kishirya mana, university nakesan wucewa daga gidan"
Murmushi tayi tace "to"
Sannan tasakeshi tashige toilet
Sai a lokacin yasaki wata irin ajiyar zuciya sannan yafuto daga dakin yadawo falo, abinda yake
shirin yi shine daidai, dole zai nunawa Diyana kuskurenta, idan akaci gaba da zama ahaka to
akwai matsala
Bata dauki Tsawon lokaci ba tafuto, ko hijabi bata sakaba kawai wani yalulun mayafi tayafa
suka futo, shima Bece da ita komai ba, suna tafiya ahanya yana driving qira'ah tana tashi acikin
motar
Har sukazo bakin get din gidan nasu Babu Wanda yace da dan'uwansa komai, amma Diyana
tunanin Adam ne fal acikin zuciyarta, ashe haka yake da kirki? Babu ruwansa duk abinda take
masa ko ajikinsa
Tsayawa ya kalleta yace "kishiga ciki, nizan wuce makaranta"
Cikin mamaki ta kalleshi tace "Kamar ya nashiga ciki, kai bazaka shigo ku gaisa ba?"
Fuskarsa Babu alamun wasa yace "kema ba gaisuwa nakawoki ba, gaba daya nadawo dake
gida, kije saina nemeki"
Gaban Diyana yafadi, cikin rawar murya tace "ya.. ya.. Adam"
Cikin tsawa yace "yes abinda kikaji hakane, Maryam kitashi kifice min daga Mota kitafi gida
saina nemeki"
Wani irin kuka ne yazo mata, Dasauri tabude motar tafuto da gudu tana kuka tayi cikin gidan
Kansa yadora akan sitiyarin motar idonsa yayi jajir, cikin kwana kin nan datayi batada lafiya
tabbas yasan cewa yakamu dason yarinyar, saide bazai taba nuna mata hakanba, saita gane
kuskuren data aikata abaya, shi aure ko wanne iri ne ba abin wasa bane
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Damuwa tayi masa yawa, gashi abin acikin ransa yarasa wazai fadawa yaji dadi aransa
Wayarsa ya janyo yakira Aslam "hello Aslam idan kasamu lokaci kazo gida inason ganinka,
banda lafiya wallahi"
Aslam yace "subhanallah, to gani nan zuwa Abba"
Dama yana kan hanyar zuwa gida ne, Dan haka ya juya kan motarsa zuwa family house dinsu
Kai tsaye part dinsu Abba yaje, suka gaisa da Momy yashige dakin nasa
Akwance ya ganshi yana danna waya Yazauna yace "Abba da alama ka warke, tunda gashi
wayace a hannunka"
Ajiye wayar yayi bayan yagama goge pictures din Nadiya da numbers dinta
Yace "banasan tunani yamin yawa ne''
Aslam yace" menene yake damunka? "
Abba shiru yana tunani, kode yafadawa Aslam ne? Kaiii wallahi Aslam ma sai yafi kowa yimasa
dariya, Dan haka yace" kawai banajin dadin jikina ne "
" to Abba kaima kayi aure kaqi, ka zauna agaban Momy tuzuru dakai "
" Aslam bana tunanin yin aure yanzu "♀️
"meyasa?" inji Aslam
Abba yace "haka nan, banda ra'ayin auren yanzu"
Ajiyar zuciya Aslam yayi "to shikkenan Allah yakaimu lokacin, daga campany nakefa kakirani,
mungama tattara list din ma'aikatan da za'a dauka, yanzu kawai ina jiran kiran wayarsu ne,
sunce zasu saka mana date din dasuke ganin shine yadace da bude campanyn, wallahi Abba
banasan komawa gida, Ilham tacika rigima, yarinyar nan jiya gishiri tazuba min acikin abinci na,
batajin magana "
Ran Abba yabaci " meyasa zaka tsaya yarinya ta raina ka haka Aslam? "
Aslam yace" to Abba ba dole raini yashiga tsakanin muba, tunda taga tashigo dakina taganni
haka "
Murmushi Abba yayi yace " Aslam ni aganina zancen boye boye yaqare atsakaninku, why not
ka koya mata hankali sau daya, daga ranar zata dinga yima biyaiya, shikkenan anwuce wajan "
Dariya Aslam yayi yace" kai Abba, akwai shawara, toshknn Zan wuce gida, inaso nahuta kafin
Baqin sukira wayata "
" to Aslam "
Aslam yafuto yatafi gida yana mamakin yanda suka shaqu da Abba, kowa yana fadawa kowa
damuwar sa, gashi de bayasan magana amma inde da Aslam ne tofa zakaji maganar sa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Da gudu ta qaraso part din nasu, cikin kuka tafada jikin mahaifiyarta tace "Mom ya Adam ya
tsaneni"
Hajiya Farida ta dagota tace "ke kiyi shiru kimin bayani, meyake faruwa?"
Hawaye ta share tace "Mom cewa yayi natafi gida saiya nemeni, Allah Mom bazan zauna ba"
Hajiya Farida tafara salati "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un... Diyana ki fadamin gaskiya me kika
yi masa?"
"Allah Mom banyi masa komai ba, kuma saida yaga na haqura Zan zauna dashi zaice natafi
gidanmu, Dan Allah Mom kibashi hakuri"
Hajiya Farida tace "yi shiru bari nakira babanku awaya,"
Alhaji habib takira, ta sanar dashi komai, nan take yazo gidan, yadubi Diyana datake zaune
aqasa yace "ke maryam, fadamin gaskiya, me kika yimasa?"
Tace "Allah banyi masa komai ba, saide in wayar dayaji inayi da wasu maza ne yan ajinmu,
kuma ni wallahi yan ajinmu ne, da rannan dana tafi biki ban fada masaba"
Alhaji habib yace "to ai kinji, haba maryam, da hankalin ki da girman ki tayaya zaki dinga waya
da maza bayan da auren ki, ko qanwarki Dida bazata yi hakaba, ai shikkenan tunda kin kaso
auren naki, saiki zo muzauna agida"
Cikin sauri tace "dan Allah, kubashi hakuri Mom Allah nadena, wallahi Zan dinga yimasa komai
har girkin ma"
Zaro ido hajiya Farida tayi "yanzu Diyana kina nufin har girki ma bakya yiwa wannan bawan
Allah? Diyana me kikeso ki zama?"
Alhaji habib yace "to nide yaron nan yana ganina da mutunci, idan yaganni har qasa yake
tsugunnawa ya gaishe ni, Dan haka ba zanje nabashi hakuri daga baya ki qara yin wani laifin
yadena ganin girma naba"
Yatashi yafice daga falon nasu
Hajiya Farida tace "toke kinji, saiki haqura ki zauna, idan ya huce yazo yace kifuto kutafi saiki
koma, tunda yace saiya nemeki"
Diyana tatashi tayafa mayafin ta tace "Allah Mom bazan zauna ba" daga nan tafice daga part
din nasu tatafi part dinsu Adam wajan hajiya Na'ila
Hajiya na zaune tanacin abinci taga Diyana tashigo tana kuka, Abincin hannunta ta ajiye tace
"subhanallah, ke Diyana lafiya kike kuka? Me aka miki? Ko wani abu ne yasamu Adam din?"
Zama tayi akan kujera tace "Hajiya wai cewa yayi natafi gidanmu saiya nemeni"
Hajiya na'ila tahau salati "shi Adam dinne me yanke wannan hukuncin?"
Diyana ta daga kanta
"to kiyi hakuri, kidena kuka, zama na mutum biyu dole kowa yanada laifi, Zan kirashi gaba
dayanku nayi muku fada,