Showing 6001 words to 9000 words out of 104433 words
Chapter 3 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
Ana gama Ruwan yasaketa, cikin tsoro tace "mutafi gida"
Bece mata komai ba yariqe hannun ta suka fara tafiya, mutane kowa yafuto yanata harkar
gabansa
Sunzo wucewa ta wata bishiya su kaga mutane suna gudu ana cewa Zuma! Zuma!! Zuma!!!
Kallansa tayi tace "la'ila, wallahi mugudu karya cijemu"
Nan take suka fara gudu duk yanda sukaso kaucewa saida zuman yacijeshi awuyansa, kafin ya
farga wani yashiga cikin hancinsa, lokaci d'aya ya rikice ya tsaya yadena gudun, hannunta
yasaki, yarasa yaya zaiyi yafitar, wani me machine ne yazo wucewa ya gansu, ita yagane yace
"subhanallah Nihla, me yakawo ku nan wajan?"
Kafin tace wani abu yacacimi Abba yasakashi akan machine din, ita kuma yasakata agaba, be
tsaya ko'inaba sai Dan qaramin asbitin garin (Nuhu Alfa Hospital)
Saida ya danqasu ahannun likita, yaga sun fara duba Abba sannan yace musu zaije gidansu
yasanar
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Acan gida kuwa duk sun fito kofar gida, gaba dayansu har mahaifin Nihla, sunyi neman duniya
sun rasa Abba da Nihla
Me machine yana zuwa kofar gidan yafaka, suka gaisa da mahaifin Nihla, nan take ya sanar
dasu komai, cikin tashin hankali suka nufi asbitin baki d'ayansu
Waye yusif? Menene yake tsakanin Aisha da yayanta Abubakar? Wacce irin wasiyya iyayen su
suka rubuta? Duk Ku biyoni
Sharhi please
Mrs Usman ce ✍️
[6/14, 10:40 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{ Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
5&6
Suna zuwa asbitin sukaga Abba Akwance Idanunsa yayi jajir, Nihla tana zaune agadon kusada
qafafunsa, sai likitan daya dubashi a tsaye
Momy tace "subhanallah, sannu Abba,"
Sannan ta kalli likitan tace "doctor Babu dai wata matsala ko?"
"Babu komai hajiya, ai anyi masa allura ma, zaku iya tafiya, saide a kiyaye gaba"
Diddi tace "insha Allah likita, yanzu ma nemansu mukai muka rasa, amma insha Allah za'a
kiyaye"
Takai Kallanta ga Abba tace "Sannu Abba, kanajin zafi yanzu?"
Girgiza mata kai yayi, Bece komai ba
Momy tasa hannu ta kamashi yasauko daga gadon, su Usman suka riqoshi suka futo daga
asibitin
Suna hanya yadaga kai yakalli momy yace "Momy"
Kallansa tayi, "na'am Abba"
Yace "Momy nasha wahala bazan sake dawowa garin nanba"
Murmushi Momy tayi "a a Abba karka ce haka mana, kaida nakeso duk wata kana zuwa kana
duba Nihla"
Nihla ta kalleshi tasaka daria, shima Kallanta yayi yadauke kansa, amma baiyi mata ko
murmushi ba
Suna zuwa kofar gidansu Nihla tasake saka daria, Abba yajuyo ya kalleta, su kuwa su Momy da
Diddi rabuwa sukai dasu suka shige gida
Yace "me kikewa daria?"
Saida tasake yimasa daria sannan ta kwaikwayi maganarsa tace "Momy nasha wahala bazan
sake dawowa garin nanba"
Haushi tabashi sosai,beyi wata wataba yasa hannu ya tureta tafadi aqasa
Da gudu ya qaraso wajan, tun daga nesa yake kallansu, shima yana qaraso wa yasa hannu
yabige Abba yace "me tayima zaka bigeta?"
Cikin bacin rai Abba yace "menene ya shafeka? Qanwarkace ko qanwata?"
"bansaniba, amma idan kasake tureta, saina rama mata" yana fadar haka ya tsugunnawa
yadaga Nihla tatashi tsaye
Cikin fishi Abba yasa hannu ya fizge hannunta yace "cika mata hannu!"
Shima dayan cikin tsawa yace "bazan cika ba!"
Lokaci daya ransa yaqara baci, ya kalli Nihla batare dayace mata komaiba ya shige gida
Itama dayan ta kalla tace "yusif..."
Kafin taqarasa maganar da zatayi yace "karkiyi kuka, idan yadakeki ki fadamin Zan rama miki
kinji?"
Daga masa kai tayi, sannan tashige gida
Tana shiga taga Diddi tana ha'bo, Abba yana zuba mata ruwa abuta, bata wani damuba saboda
tasaba ganinta ta nayi, rana d'ai'dai ne Diddi bazatai ha'bo ba, Dan haka hauka irinna yarinta
dakuma gani yauda kullum yasa bata damu sosai ba, wajan Momy ta nufa tafada jikinta tace
"Antyyy" Girgiza kai Momy tayi, har cikin ranta bataso antyn nan da Nihla take fada, sotake
tadinga kiranta Momy Kamar yanda sauran yaranta suke fada, har zatayi mata magana saita
fasa
Diddi nagama wanke fuskarta suka dawo tabarma suka zauna, Abba yace "Sannu Diddi, idan
na girma Zan kaiki asbiti"
Daria Momy tayi, "wannan girma wannan girma, zamu gani dai, ga umara ga hajji, yau kuma
anqara da asbiti "
Diddi na goge fuskarta da gefen zaninta tace "kuma insha Allahu duk saiya cikasu"
Momy tayi daria tace "muma haka mukeso aisha, wai dama har yanzu kina wannan ha'bon
naki? Aisha yakamata kije asibiti fa kiga Babban likita akan haka, kina zubar da jini dayawa"
Murmushi Diddi tayi "Anty Rahma kenan, to Tun muna yara mukeyi nida yaya, saide ni nafishi
yi, kuma Tun umman mu tanada rai muke zuwa asibiti, maganin dai dayane ake bamu, kuma
anan ma inashan irinsa, amma bandainaba, shiyasa nake yanka albasa ina shaqar qamshin
nata, shima yana maganin ha'bo sosai"
Farouq najin haka yace "to Diddi bari na yanka miki yanzu ma, yatashi yadauki wuqa yanufi
wajan da take ajiye albasa"
Nihla ta kwaikwayi Abba tace "Sannu Diddi"
Kallanta yayi yasakar mata harara, yadauke kansa, Momy tana kallansa, cikin ranta tace to da
alama sunyi fada
Saita kalli Diddi tace "to Allah yasawaqe aisha, amma Zan sake yiwa yayanki maganar
gaskiya,abin yayi yawa"
Babu musu Diddi tace to, Dan itama abin yana damunta, wani lokacin tana bacci zataji jini yana
futowa daga hancin ta
Har dare, Abba Yaqi kula Nihla, da niyya take tsokanar sa amma saiya shareta, idan ya tuna
abinda yafaru dazu a kofar gida shida wannan gayan sai yaji haushi ya kamashi
Shiyasa itama yarabu da ita, da daddare ma ko kallan Inda take baiyiba, ita kuwa bata fasa
tsokanar saba, har sukayi bacci
Washe gari da yamma sunata shirin tafiya, Nihla duk tayi shiru bataso sutafi, har direba yazo
yagama zuba musu komai nasu amota, kowa yayi wanka ya shirya, dukansu qananun kaya
suka saka
Momy ta kalli Diddi, "to Aisha zamu tafi"
"to Anty Rahma Allah yakaiku lafiya, idan kinje ki gaida kowa,"
Momy tace "to yayanki fa?"
Daria Diddi tayi, "harda shi Anty Rahma, ki qara yimasa godia, ki gaishe shi sosai"
Tace "to zaiji, yanzu Aisha Allah bazaki bani Nihla ba?"
"Anty Rahma rigima, sokike na zauna nikadai agidan de"
Momy da taga alamar Aisha bazata iya rabuwa da Nihla ba, sai tayi shiru kawai, suka futo, har
kofar gida suka rakosu itada Nihla, suka tsaya daga bakin kofa suna kallansu
Yaran kowa yashiga Mota, Nihla tanata kallan Abba, shima ita yake kallo, lokaci daya idonta
yayi rau-rau, tasaka kuka tace "Diddi zasu tafi"
Hannu Diddi tasa tashare mata hawaye, jikin Abba ne yayi sanyi, Dasauri yabude motar yafuto,
duk 'yan uwansa suna kallansa, har gaban Diddi yaje, ya tsugunna agaban Nihla yace" kiyi
shiru, kefa qawata ce, You're my friend "
Kallansa tayi ta daga masa kai alamun to
Saida ya kalli Diddi, sanan yamatso da fuskarsa daidai tata, yasakar mata kiss akumatu
Zaro ido Nihla tayi tana kallonshi, kafin tayi magana yajuya ya shige motarsu da gudu
Qamewa Diddi tayi a tsaye, Abba datake ganinsa shiru shiru shine yayiwa Nihla haka?
Momy kuwa murmushi tayi, tace "Allah ya kyauta"
Sannan tayiwa direba umarni yaja motar sutafi
Cikin gida Diddi tajuya tashige, tana tunanin wani abu aranta
Nihla kuwa qin shiga gidan tayi, tazauna akofar gidansu tana wasa, Kamar daga sama taji
maganarsa "Nihla, mekike yi anan kinyi shiru?"
Kallansa tayi, lokaci daya tasaki murmushi, "yayunane suka tafi, nikuma banaso sutafi "
"haba? Yaushe suka tafi? Kinsan garin da suka tafi?"
Girgiza kai tayi, "nima bansan garin su ba"
Hannunta yariqe yace "zomuje gidanmu muyi wasa"
Gidan dayake kallan nasu gidan ta kalla, hadaddan gida ne daya gama haduwa, harda beni,
tace "to Muje"
Janta yayi suka shige cikin gidan, har falonsu suka shiga Nihla sai kalle kalle take, mamansa
tana zaune tana kallo, falon ya tsaru iya tsaruwa
Kamannin Ibrahim Mai hakuri da tagani a fuskar yarinyar hakan ya tabbatar mata da cewa
yarinyar Diddi ce
Wajan ta suka qarasa yace"Ummah kinga qawata, sunanta Nihla, Acan gidan take naje na
kirata zamuyi wasa "
Murmushi tayi, tashafa kan Nihla tace" a a masha Allah yanmata, to kuje kuyi wasan, banda
fada kunji ko "
Dakinsa yakai ta, nan taga kayaiyakin wasa iri iri, nan take suka fara wasansu, yana koya mata
abinda bata iyaba
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Har bayan sallar isha'i Nihla bata dawo gidaba, Diddi tayi neman ta harta gaji, haka ta tsaya
akofar gida tana Tambayar duk Wanda taga yazo wucewa ko yaga Nihla, amma Babu Wanda
yace yaganta
Umman yusif tazo rufe window tana daga saman beni, hango Diddi a tsaye akofar gida
Saukowa tayi tafuto wajan ta sameta, Diddi tace "a a Hajiya, ina gajiya,"
Tace "lafiya kalau, da alama de Nihla kike nema"
Dasauri Diddi tace"wallahi ita nake nema hajiya, Tun yamma ban ganta ba, "
Murmushi tayi tace" ai tana gidana, sunata wasa da yusif Yarona, yanzu kam nayi musu
shimfida ma sunyi bacci "
" to bari naje nadauko ta hajiya, kar babanta yadawo begantaba "
" haba Diddin, ki barta mana, dasafe sai akawo ta "
Murmushi Diddi tayi, cikin ranta tace nagode Allah, kowa yana qaunar 'yata, afili tace" Hajiya ai
wataran zata kwana, ina Ruwan yara "
Badan tasoba, suka shiga gidan, Diddi tanata yaba haduwar gidan, Dan bashiga takeba, amma
gashi yau wannan yarinya takawo ta
Baccinsu suke hankali kwance, ga esi nan yana sanyaya musu jiki, haka Diddi tasa hannu
tadauketa, suka tafi gida, tanata yiwa Maman yusif din godia
(idan naga ana Comments Zan qara yawan page d'in)
WhatsApp readers, ina qara godia sosai yanda kuka bani hadin kai, kuka bani lokacin ku wajan
karatu da kuma sharhi, ana mugun tare
Amnah El Yaqoub ✍️
[6/15, 2:27 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
7&8
Zaune suke acikin Babban falonsa dayake tarbar baqi, Babban falo ne daya hada komai da
Komai najin dadin rayuwa, tsaki yasaki yakalli Agogon hannunsa fuskarsa Babu alamun wasa
yace "me Basiru yakeyi ne har yanzu baizoba, bayan Tun jiya nasanar dashi da kaina cewa
akwai meeting karfe tara nasafe"
Kafin sauran biyun su bashi amsa aka turo kofar falon aka shigo, kana ganinsa kaga cikakken
magidanci, fuskarsa adaure yadubeshi "mekake yi bakazo a lokacin dana sanar dakai ba?"
Yace "yaya Abubakar ai lokacin yayi, gani kuma nazo akan lokaci"
Kai tsaye yace dashi "duba agogo karfe nawa?"
Kallan Agogon dakin yayi "goma da rabi"
Fuskarsa adaure yace "kuma karfe nawa nace kazo?"
"karfe tara kace, aini to inajin agogo nane yasamu matsala, karfe tara ya nunamin wallahi, inajin
matsala yasamu, duba kagani" ya qarasa maganar yana nuna masa hannunsa
Harara ya watsa masa yace "lusari, Wanda mace tagama shanye shi"
Shiru falon yasakeyi, ba qaramin girma suke bawa Babban yayan nasuba, hakan yasa Wanda
aka kira da lusari baice komai ba, yanemi waje Yazauna
Gyaran murya yayi yace "munyi magana da hajiya dangane da wani abu Mai girma Wanda ni
kaina bansan menene ba,...." nan take ya sanar dasu yanda sukai, sannan yaqara cewa
"nasanar daku ne saboda nima korai zaiyi halin sa,"
Hajiya Farida datake zaune, wadda ita kadai ce mace acikinsu tace "Amma yaya Abubakar
meyasa ba'a fadawa Aisha ba? Itama fa tanada 'ya, kuma 'yarta tana daya daga cikin wannan
family, Kamar yanda Iyayenmu suka bada wasiyyar dabamusan kota mecece ba akan yaranmu,
ai yakamata ace tasani"
Kallanta yayi fuskarsa adaure "da Aisha da abin data haifa duk suna qarqashin iko nane,"
Jinjina kanta tayi, sannan tasake cewa "to amma yaya ai yakamata ace munjata ajikin mu,
Kamar yanda aka fadawa yaya Basiru itama..."
Kafin ta qarasa magana yadaga mata hannu tareda fadin "Farida!!!"
Lokaci d'aya ta nutsu Kamar ba itace take zuba surutu ba, kallansu yayi yace "daga yanzu
kuma daga rana irinta yau, doka zata fara," yana fada musu haka yatashi yafice, yabar kowa da
tarin tambayoyi, Alhaji Baqir yatashi yana gyara Babbar rigar jikinsa yace "koma menene bazai
wuce maganar rabon gado ba, ni wannan bata gabana," shima yafice daga falon
Hajiya Farida ta kalli Agogon hannun Basiru dayake zaune kusada ita batare daya saniba, taga
karfe tara da kwata, ta kalli Agogon dake manne afalon taga goma da arba'in da biyar, tasaki
daria tasan sarai aikin matar sa ne wannan, wadda ya Auro musu ita tazame musu baragurbi
acikin family, Kallanta yayi "me kikewa dariya?"
Tace "yaya Basiru Babu komai, nina wuce gida sai anjima"
Daganan shima yatashi yadoru a bayanta yana darurar sanar da matar sa abinda yaya
Abubakar yace
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Labarinsu
Mazawaje family Babban family ne dayake da tarin mutane dayawa, Abubakar shine jigo na
wannan family yanada mata biyu Hauwa'u dakuma Fatima
Hajiya fatima itace babba, tanada yara biyu, Babban danta shine Yaci sunan babansa Wato
Abubakar, sai qanwarsa Aisha, sun taso sunasan junansu sosai da sasai
Sai Hajiya Hauwa'u, wadda suke kira da hajiya sak, tana da yara uku, Baqir shine Babban
danta, sai Basiru da kuma qaramar su Farida
Abubakar yayi aure ya auri daya daga cikin family dinsa na uwa, maisuna Rahma, suna zaune
lafiya saide murdaddan halin sa datake hakuri dashi wani lokacin, sunada yara hudu, Usman
shine babba, sai Aliyu,Sai farouq, Sannan Abubakar Wanda yaci sunan kakansa suna kiransa
da Abba,
Alhaji Baqir kuwa yaransa biyu, Aslam da kuma Adam
Sai Alhaji Basiru, yanada yara uku, Fawaz shine dansa na farko, bayajin magana kokadan, ga
kula abokan banza, sai Aisha qanwarsa wadda aka saka mata sunan Diddi, tanada hankali da
nutsuwa, sannan ta fannin kamanni suna kamada Nihla sosai Kamar yan gida daya, sai
qaramar Ilham, ita kuma ilham rashin kunya, kowa yasan batada kunya yarinyar
Sai hajiya Farida Mai yara biyu Dida, dakuma Diyana
Qa'idar familyn nasu shine tunda suke Babu wani Wanda yake auren bare, saide ka nema a
family ka aura, kowa yabi wannan dokar, kwatsam sai Alhaji Basiru yagano wata wadda bata
cikin family yace ita yakeso zai aura, adede lokacin itama Aisha Wato Diddi tace tanada saurayi
wani bafulatanin yalleman dake jihar jigawa, tace shi takeso, al'amarin yakawo rigima sosai a
tsakanin wannan family, har hakan ya haifar musu da rabuwar kai, wasu suna ganin aiba laifi
bane hakan tunda ba haramun bane, wasu kuwa suna ganin cewa bedace ba, tunda dokace ta
family, cikin su kuwa harda Abubakar, saida aka kai ruwa rana sannan aka rabu dasu sukai
auren, da sharadin duk abinda yabiyo baya su sukaja amma kada su nemi kowa
Babu Wanda yakai Abubakar bacin rai akan hakan, ganin idon qanwarsa Yarufe akan soyaiya,
hakanne yasa ya tattara ta yawatsar, yadena shiga cikin al'amarin ta, amma cikin qasan ransa
yana qaunar qanwarsa, ita kuma matar Basiru hajiya Abida tunda tashigo family din taga basa
sonta saita shanye mijin nata da kissa iri iri, idan tasa doka bai isa ya qetare ba, haka kawai
kuma Allah yadora mata kaunar Diddi aranta, tana son Aisha sosai, shiyasa tana haifar yarta
qanwar fawaz tace Aisha za'a sakawa yarinyar, babu musu mijin nata yayarda
Aisha Wato Diddi tana zaune lafiya da mijinta Mai Suna Ibrahim, amma ana kiransa da Mai
hakuri kasancewar mutum ne shi Mai mugun hakuri, dukda halin rashin dayake dashi bata taba
nuna masa ba, haihuwar ta ta farko tahaifi mace Mai kama da babanta sak, suka sakawa
yarinyar suna fatima, Wato sunan kakarta, amma suna kiranta da Nihla (kyauta)
Wannan shine labarin Mazawaje family
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"Diddi tunda su yaya Abba suka tafi ko, kullum sai nayi mafarkin su"
Dasauri ta kalli yarta ta taga hankalinta yana kan wasa ma Kamar ba itace tayi magana ba,
"suwa kike mafarki Nihla?"
Kallanta tayi cikeda qosawa tace "Diddi nace miki su yaya Abba, nayi mafarki shima munata
wasa dashi"
Diddi tace "shi Abban ne ya koma yaya Abba?"
"eh Diddi, ai shine yace nadena cemasa Abba, saide yaya Abba"
Diddi ta Jinjina kanta tace "to suma sauran ai yayunki ne, dukansu haka zaki dinga fada musu"
Tace "to Diddi, yaushe zamuje wajansu?"
Daria Diddi tayi tace "kinason zuwa wajansu ne?"
"eh inaso naje, wai a wanne garin suke Diddi?"
"Suna kano, Nihla, kibari idan akai muku hutu saina kaiki, kiga qawayenki su Aisha, da ilham,
da Dida, su Diyana"
"Diddi duk agidan suke suma?"
Diddi tace "duk suna gidan Nihla, idan mukaje zaki gani, gidane babba sosai, kowa aciki yake,
amma kowa yana part dinsa, kuma akwai nisa atsakani, amma duk gidanmu daya dasu"
Cikin murna tace "to yaushe zamu tafi Diddi?"
Cikin sauri qosawa da maganar ta tace "nace miki idan anyi muku hutu"
Tace "to Diddi"
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Haka Rayuwar taci gaba da tafiya, yara naqara girma, kuma har zuwa wannan lokacin Diddi
bataje gidaba, kuma bata taba kai Nihla cikin yan'uwanta sun gantaba, kullum tayi mata
maganar Abba saita shashantar da zancen
Zuwa wannan lokacin Abba yayi candy, Har Alhaji Abubakar yafitar dasu qasar Germany karatu
shida Aslam, Dan gidan Alhaji Baqir, tunda yalura hankalin yaron ya karkata akan jirgi ,
shiyasa yadage yanaso yacika wa dansa burinsa na ganin yazama cikakken pilot