Showing 84001 words to 87000 words out of 104433 words
Chapter 29 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
wayarta tafuto, fuskarta Babu yabo Babu fallasa, ya Aslam
sai Fara'ah yake yace "Amarya kinsha qamshi"
Nihla bata kawo komai ba, tunda kowa yasan ansa mata rana Dan haka tace "na'am ya Aslam"
Yace "yaya marar lafiyar naki kuma"
"ya Aslam namu de"
Yayi Murmushi yace "A a, mun barmiki, keda dan'uwanki, kinga ai yanzu yazama naki"
"duk da haka de ya Aslam, kaima ai dan'uwanka ne"
Ilham ce tajata gefe tace "ke rabu dashi, zomu zauna"
Tabashi Abincin tace "ga Abincin nasu, ka shiga musu dashi ciki tunda zakaga jikin nasa"
Abincin ya karba yawuce cikin dakin
Yau Tun safe ransa fari tas, Baqin cikin sa daya yanda Abba yake kwance bai farkaba, yaso ace
shine mutum na farko dazai fara bawa Abba labarin aurensa da Nihla , amma yaya zaiyi?
Wayarsa yafara dubawa yaga batanan, da alamun agida akabar masa wayoyin, yar drower din
gefen gadon yafara dubawa cikin sa'ah yaga biro da wani littafi, cikin sauri yayagi qaramar
paper yayi rubutu aciki, sannan ya linke takardar yaqaraso gaban gadon na Abba yana dube
duben Inda zai saka takardar ko Allah zaisa Abba yagani batare da Nihla ta lura ba, hannunsa
ya kalla, yadaga hannun yasaka masa takardar aqasa hannunsa, yasan ma Nihla zata gani,
amma duk da hakade yana fatan karta gani din
Awaje kuwa Ilham ta dubi Nihla tace "amarya, amarya, ah ah, kaga amarya kinsha qamshi"
Tsaki taja tace "keni ba wannan ne yake damuna ba, Ilham yanzu Dan Allah tayaya Momy zata
tafi gida ta barni tareda ya Abba, bayan tasan surutun wannan family din yanzu sai kiji
ankasamu a faranti ana qananun maganganu akan mu"
Ilham tace "Babu wani maganar da za'ayi, to waye ma ya'isa yace muku wani abu?"
"Ilham bazaki ganeba, bafa muharrami na bane sannan wai Momy harda cewa wai...." shiru tayi
takasa qarasa wa
Ilham tayi Murmushi tace "kinga, ki kwantar da hankalin ki Nihla, babu abinda zai faru, tome zai
miki shida bashida lafiya? Kisaki jikinki kiware ki kula da dan'uwanki, karkiji komai tunda su
Momy sunsan kina tare dashi, kifa saki jikinki dashi"
Cikin sanyin jiki tace "to Ilham, amma de.."
Ilham tace "kinga, karbi wannan hadin kisha, kinga yanzu bawani zaman gida zakiyi ba bare
Momy tadinga baki kina sha, kuma mazan yanzu saida gyara, ke masu gyaran ma yaya aka
qare dasu, Dan haka gara kije gidan mijinki tsaf"
Babu musu takarba tace "to Ilham nagode"
Dariya sai cin Ilham take, Nihla kuwa bata kulaba
Fira sukaci gaba dayi har ya Aslam yafuto sannan sukai mata sallama suka tafi, ita kuma tajuya
cikin dakin
Wajan shadaya na dare likita yazo ya dubashi yace "idan akwai matsala zaki iya kiranmu"
Tace "to"
Likitan nafita tadauki wayarta tafara kiran ya Yusuf amma baya dauka, Tun tana yin na marmari
harta gaji da tadena, sai message ta tura masa
Tashi tayi tadauro alwala tazo ta shimfida sallaya tatada sallah, data idarma addu'ah kawai tayi
tayi sannan tatashi ta linke sallayar takoma kan kujera tazauna, zuba masa ido tayi, gaskiya ya
Abba qarshe ne, yahadu iya haduwa, halin sa ne bai haduba, ajiyar zuciya tasaki ta kalli girarsa
datake kama da tata girar, Allah de yabashi lafiya tadena wannan zaman shirun
Tun tana kallansa tana tunani harta gaji tadan dora kanta agefen gadon nan take bacci ya
kwasheta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"Rahma sai murna kike Tun safe"
Momy ta kalli Daddy tace "Alhaji ai dole nayi farin ciki, yau Abba na yasamu abinda yakeso,
koda na mutu nasan yarana dukansu sun samu mata nagari"
Jinjina kansa yayi yace "hakane, Allah yabasu zaman lafiya"
"Amin Alhaji, ni dama nasan Dan bakasa baki bane, amma inde an fahimci juna ai komai Mai
sauqi ne"
"hakane, yabata min raine yaron, haba yaro sai taurin kai"
"Hmm Alhaji kenan, kowa yasan de halin Abba gaba daya naka yadauko, kuma kaga laifin
yaro?, amma Alhaji yanzu ai sai afara gyara musu gidansu, idan komai ya kammala saisu koma
can"
Daddy yace "Haba Rahma, korar yaran nawa kuma kike? me zaisa sukoma wani waje Rahma?
Da badamu suke zaune ba? Yanzu ma ai sai suyi zaman su"
Cikin sauri Momy tace "um um Alhaji, kayi hakuri da wannan maganar, ba zaman gidan kake
bane shiyasa, amma nida nake zaune dasu nasan abinda yake faruwa, Abba bashida kunya
gara su tafi kawai"
Murmushi Daddy yayi yace "to bansan de mekika ganiba, amma tunda kince haka, idan
angama gyare gyaren komai saisu koma ai"
Tace "yawwa yanzu naji batu"
Asuba tagari Daddyn Momy
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Karfe hudu da rabi na dare yaji kansa yasara, Ahankali Ahankali yafara bude idonsa
Hasken dayagani adakinne yasa yasake runtse idonsa sannan yasake budesu Ahankali, Nihla
kuwa bacci yayi bacci kanta yanakan dantsan hannunsa tayi fillo dashi
Kallan kansa yayi anan ya tabbatar da asbiti aka kawoshi, ahankali yafara tariyo abinda yafaru
dashi harya tuna komai, yana gama tunowa yaji wani irin Baqin ciki aransa
ga kansa dayake masa ciwo,qirjinsa nauyi idan yanajan numfashi, jin alamun mutum akan
hannunsa dakuma gashinta daya bazu akan hannun nasa shiyasa yakai dubansa ga hannun
damansa anan yayi tozali da dogon gashin kanta, babu dankwalin yazame yafadi qasa
Gabansa yafadi,meyakawota nan?
Ahankali yafara motsawa zai tashi yaji hannunsa na hagu akan takarda, komawa yayi ya
kwanta sannan yadauki takardar Ahankali baiyi tunanin komai ba yabude, mamaki ya kamashi,
wannan ai rubutun Aslam ne
Ahankali yafara karantawa :
_Ango mijin amarya, congratulation_ _Abokina, Allah yasa kada wani_ _yarigani sanar dakai
cewa_ _Nihla tazama mallakinka_ , _but ka kiyaye batasan komai ba "_
Cikin sauri yatashi zaune Kamar ba marar lafiya ba, sai yaji yana nema yanemi ciwon kan nasa
yarasa, ita kuwa Nihla jin kanta ya koma kan katifa yasa ta danyi motsi, sannan tasake gyara
kwanciyar ta tajuya taci gaba da bacci
Dube dube yafara yana neman wayarsa amma bai gantaba, wasiqar yasake karantawa, ya
karanta ta yakai sau biyar
Yajuya yasake Kallanta tana bacci hankalinta kwance, Hawaye ne suka zubo masa, yasaka
hannunsa duka biyun ya share, sannan yadaga hannunsa sama yana yiwa Allah godia, domin
kuwa yasan cewa banda addu'ah Babu abinda zaisa yasamu Nihla cikin sauqi
Alerm din wayarta ne yafara qara, Ahankali ya koma ya kwanta Yarufe idonsa Kamar me bacci,
nan take masallatai suka dauki kiran sallah
Saida Alerm din yaqare yasake bugawa sannan tabude idonta, bacci takeji sosai
Kallan kanta tayi Babu dankwali tace "subhanallah," tadauko shi aqasa ta daura dankwalin ta
sannan ta kalleshi, tasaka hannu ta gyara masa fillo din da kansa yake kai sannan tashige
toilet, yana jin alamun shigar ta toilet yabude idonsa yatashi zaune yana daga hannu yana ta
murna
Haka yaita murna saida yaji zata futo sannan ya koma ya kwanta, harta idar da sallah duk yana
jinta, wayarta tafara qara, tadauka yaji tace "Hello Momy"
"Nihla kuna lafiya deko?"
"lafiya kalau Momy, yanzu na idar da sallah ma"
"toya jikin nasa"
"gashinan nan de Momy, har yanzu shiru"
"to Allah yasawaqe, Karki Manta da goge masa jikinsa de anjima, akwai Ruwan zafi a flask,
anjima za'a kawo muku abinci"
"to Momy sai anjima"
Tayi shiru tana azkar, har gari yafara haske, ganin idonsa biyu kuma ga lokacin sallah yana
wucewa shiyasa yafara bude idonsa Ahankali, ya kalleta da gefen ido yaga tayi tagumi tanajan
carbi
Ahankali yafara cewa "Momy!, Momy!! Momy kaina"
Cikin sauri ta zabura tayi kansa "ya Abba! Katashi? Sannu, bari akira Doc."
Tajuya tafice daga dakin cikin sauri
Wani irin murmushi yasaki, yana jin wani masifar dadi aransa yabi bayanta da kallo, wai yau
shine Nihla take nuna masa wannan kulawar, aikuwa in hakane Babu shi Babu warkewa
Tare suka dawo da likitan, ya dubashi, yasake kallansa yace "abin mamaki, ya akai ciwon naka
yaragu haka sosai?"
Maida kansa yayi majinyacin sosai, ya langabe yace "qirjina yana min ciwo kadan, kuma ko'ina
ma ciwo yake min na jikina"
Doc. Yayi Murmushi yace "insha Allah Ahankali zaka dena ji"
ya kalli Nihla yace "please ki goge masa jikinsa idan zai iya saiyayi sallah ma, idan ma zai iya
wanka saiyayi ko zaiji qarfin jikinsa"
Jikinta a sanyaye tadaga masa kai, yafice daga dakin yarage saisu biyu
Kallansa tayi, cikin sauri takawar da kanta tafara linke sallayar datake kai
Shikuwa sai binta yake da wani irin kallon soyaiya , badan kada ya to nawa kansa Asiri ba da
Babu abinda zai hana tajita ajikinsa
Toilet tashiga tahada masa ruwa, sannan tafuto tazo wajansa tana kallansa qasa qasa tace
"Anhada Ruwan wankan ko zaka shiga kayi?"
"Ai bazan iyaba, saide nagoge jikina"
Cikin sauri tace "to" sannan tahada Ruwan zafin agabansa, tadauko qaramin towel takai masa
gabansa ta ajiye tace "gashinan ankawo"
Kallanta yayi har yana lumshe idonsa alamun jin jiki yace "bazan... Iyaba fa"
Shiru tayi, tarasa meyake mata dadi, shikuma yana Kallanta yanaso yaga yaya zatayi
Ajiyar zuciya tasaki ta qarasa wajansa ta matsar da Ruwan gefe, ta kalli rigar jikinsa tace "to
dan gyara"
Sarai yagane nufin ta sai yace "jikina ne Babu qarfi, bazan iyaba"
Wannan karon kam kawarda kanta tayi gefe, itade wannan zama baiyi mata ba kokadan, sai
hura hanci take, takasa yin komai
Kamar wadda aka tsikara Tajuyo takama rigar jikinsa Ahankali tafara yin sama da ita, babu
musu yadaga mata hannunsa ta cire masa rigar duka, gabanta yafadi ganin yanda hannunsa
yake a murde, ga gashi daya kwanta akan qirjin nasa,lokaci d'aya yacika idonta yayi mata
masifar kwarjini, fat... fat... fat... takejin bugun zuciyarta nayi, ta ajiye rigar sannan tadauko towel
din dake cikin Ruwan ta matse, tadora shi akan qirjinsa
Zirrr yaji wani irin abu acikin jikinsa, cikin sauri ya lumshe idonsa yanajan wani irin numfashi
Satar kallansa tayi taga idonsa arufe, dan haka tafara goge masa cikin sauri, shikuma wani irin
dadi yakeji Kamar karta daina abinda takeyi, bayaso yadena jin abinda yakeji din
Ita kuwa sai kawarda kanta takeyi, har wajan wuyansa saida ta goge masa, sannan ta ajiye tace
"nagama"
Ahankali yabude idonsa yasauke su akanta, meyasa Nihla ta kasance damuwar sa dakuma
maganin damuwar tasa? Meyasa yakejinsa Kamar ba marar lafiya ba? Tabbas dole ne yayi
azumi domin nuna godiyar sa ga Allah
Gari kam har yayi haske sosai, ahankali yafara kokarin tashi yadubeta tareda miqa mata hannu
cikin shagwaba yace "kikamani natashi"
Kallansa tayi, tadauke kanta, inaga yamanta itace atare dashi ba Momy ba shiyasa yake mata
wannan shagwabar
Ahankali ta dora hannunta cikin nasa, yanajin haka yariqe ta sosai, saboda yanda yaji hannun
nata da taushi, yatashi tsaye yadora kansa akan kafadarta, yasaka dayan hannun yariqe waist
dinta
Yanayin yadda ya tura saqon nasa kuwa ya karbu, nan take tayi taga zatayi baya, amma saiya
sake riqe waist dinnata sosai, cikin shagwaba yace "Uhm... Uhmm.... Nifa bazan iyayin wankan
ba"
Zaro idonta tayi, sannan tazare jikinta Ahankali, ta kalleshi tace "tome kake nufi? Ban fahimta
ba?"
Saura kadan tasaka shi dariya, amma saiyayi Dan murmushi yakawar da fuskar sa, yadafa
bangon dakin harya shige cikin toilet din Ahankali
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya tasauke sannan takoma kan gadon ta zauna tareda dafe
kanta♀️
Inda yariqe mata dinnan wani iri takeji
"Zoki gani"
Ta tsinci muryar ya Abba yana kiranta
Dak.. Dak.. Gabanta yafara faduwa, Innalillahi.... mekuma zataje tagani?
Abba dake toilet yaji shiru, yasaki yar qaramar dariya yasake cewa "Kizo kigani"
Nihla kuwa mayafin ta tayafa, tana jiran likita yashigo tagudu gida, sarai tana jinsa tayi shiru, da
yasan zai iyayin wankan amma shine zaisata wahalar goge jiki
Masu cewa naqara yawan typing suma su qara yawan Comments, dama nafada more
Comments more typing
Amnah El Yaqoub ✍
[7/15, 12:34 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
55&56
Jin bata amsa masa ba yasa yayi Murmushi yafara wankan sa, yasan cewa sarai tana jinsa
Bai dauki lokaci Mai tsawo ba yafuto, yana sanye da kayan jikinsa, Nihla tana jinsa yafuto
amma bata daga kai ta kalleshi ba, idonta aqasa, ya kalleta yayi Murmushi yasaka hannu
yadauki sallaya sannan Yazauna abakin gadon yayi qasa da muryar sa Kamar Wanda yake
rada yace "please yaushe mukazo asbiti?"
Yatsun hannun ta take wasa dasu batare data dago ta kalleshi ba tace "Shekaran jiya"
"kwana biyu kenan?" yasake yimata Tambayar
Kanta tadaga masa alamun hakane
Kansa ya Jinjina alamun gamsuwa sannan yatashi yatada kabbarar sallah
Yasha addu'ah sosai acikin sallar tasa, yana qara yiwa Allah godia, bayan ya idar ya ajiye abin
sallar sannan yafara kokarin hawa gadon
Cikin sauri tatashi takoma kujera tazauna, Sam taqi yarda suhada ido dashi
Shikuma kwanciyar ta isheshi, haka Yazauna yasata agaba yana Kallanta, tanaji a jikinta ana
Kallanta Dan haka koda wasa taqi yarda suhada ido dashi
Wayarta tadauka takira Momy, Momy na dagawa cikin shagwaba tace "Momy yaushe zakizo"
Momy tace "Nihla me zaisa nazo asbiti bayan gaki nan? Menene yake faruwa?"
"Momy Babu komai"
"A a ki sanar Dani idan akwai abinda yake faruwa"
"Babu komai Momy, dama ya farka ne"
Momy tace "to Alhamdulillah, Allah mungode ma, yana ina Abban?"
Satar kallan Abba tayi daya zubawa lips dinta ido yana kallo tace "gashinan"
"to bashi wayar"
Ahankali ta miqa masa wayar, memakon ya karbi wayar kadai sai da yahada da hannunta
yariqe sannan yazare wayar yayi qasa da murya yace "Momy...."
"Abba na ashe jiki yayi sauqi, to Alhamdulillah bari mu shirya muzo"
"A a Momy, kiyi zaman ki, banajin ciwon sosai, sonake ma yasallame mu"
"to shikkenan idan kana buqatar wani abu de karka yi shiru ga Nihla nan"
Murmushi yayi yace "to Momy"
Wayar ya ajiye gefensa, a lokacin likitan dayake aiki da safe yadawo yadubashi,shima yayi
mamakin yanda Abban ya warke
Abba yace "Doc. Ai ina ganin ma dazaka temaka daka sallamemu, saboda banajin komai
yanzu, inajin karfi ajikina banajin ciwon komai"
Likitan yace "ka tabbatar?"
"da gaske nake Doc."
Yace "to shikkenan, zaku iya hada kayan ku, zanje nadawo yanzu"
Yana ganin Fitar likitan ya kalleta yace "madam kira min Abokina mana"
Kallansa tayi, taga wayar tana gefensa, tace "gata nan awajan ka"
"eh nasani, kinsan wayar yanmata, saisu"
Ahankali tamiqo hannunta zata dauki wayar yabi hannunta da kallo gwanin sha'awa dogaye
dasu
Tadauki wayar tadannawa ya Aslam kira
Ringing din farko kuwa yadauka, batayi magana ba tabashi wayar
Cikin aji yace "Abokina"
Cikin murna Aslam yace "kaga Ango, Ango kasha qamshi, kace kanajin qamshin amaryar taka
kamiqe"
Murmushi yayi kawai yace "naga saqon ka ai"
"Hmm ai addu'ah nayi tayi kada Nihla tagani, amma yanzu de jikin da sauqi ko"
"babu komai, na warke"
Aslam yasaka dariya yace "toganinan zuwa"
Daga nan sukai sallama, doc. Yazo yabasu takardar sallama, sannan Nihla tafara hada musu
kayansu, ko minti goma ba'aiba Aslam yazo, suka tafi, sun shiga cikin Mota su agaba ita kadai
abaya, wayarta tafara qara, tana dubawa taga baban tane, cikin ladabi tadauka "Baba ina
kwana"
"lafiya Nihlan Diddi, Yaya su hajiya"
"suna nan kalau baba, inasu mamy"
"mamy tana nan lafiya, bakya wani abune yanzu ko"
"eh baba"
Gyaran murya yayi yace "to abinda nakeso dake shine ki saurari abinda Zan fada miki,jiya su
Alhaji Abubakar sunzo andaura miki aure da Dansa Abubakar"
Gabanta yafadi, cikin sauri tadafa qirjinta tace "Aure kuma baba"
Abba da Aslam dake gaban Mota suna jinta, Aslam aransa yace to fada mata ake kenan
Abba kuwa shiru yayi yana jinta
Daga daya bangaren baba yace "eh aure, Yusuf da kansa shiya fara yiwa mahaifin sa magana
akan ya hakura, saide bai yarda ba, saida sukazo jiya muka sake tabbatar wa, ga sadakinki
ahannu na dubu dari cif,kiyiwa mijinki biyaiya sannan kiyiwa Yusufa addu'ah Allah yabashi mace
tagari, mahaifin sane ya tsaya akai komai aka gama, sannan Alhaji Abubakar yanemi yafiyata
da kansa, Dan haka banason wani tone tone, kiyi hakuri Allah yabaku zaman lafiya "
Hawaye suka silalo daga idonta, muryarta ta sauya tace" to baba "
" yawwa Allah yayi miki albarka "
"amin baba"
Daga nan sukai sallama, tayi shiru tana goge hawayen idonta, yanzu ashe dama shiyasa Momy
ta barta awajan ya Abba, wani hawayen yasake zubo mata, Allah sarki ya Yusuf, haqiqa tayi
rashin masoyi, yasha wahala akanta, tasa hannu tashare hawayen
Ahankali Abba yadubi Aslam yace "dan tsaya Aslam"
Babu musu kuwa ya tsaya, yabude gaban motar yafuto yadawo baya wajan ta Yazauna, Aslam
yayi Murmushi yadauke kansa yaci gaba da driving
Sake matsawa yayi jikinta, tanajin yanda jikinta yake gogar nasa, yasaka hannunsa ta bayanta
ya rungumota jikinsa, batada zabin daya wuce ta dora kanta akan faffadan qirjinsa
Bayanta yafara bubbugawa Ahankali, yasunkuyo da kansa dede kunnanta cikin rada yace "kiyi
hakuri kidena kuka kinji, kukan ki yana tabamin zuciyata, kiyi shiru, kinji?"
Ahankali tadaga masa kanta, wani irin dadi Abba yaji, yanda yaga lokaci daya taji maganarsa