Showing 27001 words to 30000 words out of 78655 words
Chapter 10 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
ta ce
"Da wancan S.Man d'in mana yanzu dan yana bin Baba kud'i sai ya zo ya na yi masa irin
wannan kira, ai ko wan da bai sansa ba bazai yi masa irin haka ba bare kuma Baba."
kai Baba ya girgiza ya wuce d'akin sa.
Umma ta ce "Ai kuwa bai kyauta ba, dama rayuwa cikin turawa mene ne."
SEEDRAH ko kunkuni ta cigaba da yi kasa-kasa.
"To ai sai kuma kiyi shiru haka dan ke rashin kunya baya baki wuya yayanki ne dai ba kece
gaba da shi ba ko sai kin zage sa kihuta."
Suhailat ta fad'a tana aika mata harara.
baki SEEDARH ta murgud'a sannan ta ce
"Shikuma yanzu da yazo yabo yayi ai ba rashin kunya wa nagaba da shi ba."
ta juya tawuce d'aki.
Suhailat tabita da harara...
Tana shiga ta tadda wayarta na ring jin sauti na musamman dake tashi cikin wayar yasa ta
sakin murmushi dan sanin mai kiran nata, ta isa in da wayar yake ta d'auka tare da niman guri
ta zauna bakin gado, kana tayi picking na call d'in ta kai kunnenta tare dayin sallama.
daga cikin wayar Kamal ya ce........!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance
da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Page 9
"Albishirin ki." murmushi mai sauti tayi sannan ta ce
"Goro." a b'angaren Kamal shima murmushin yake zubawa da kaji shi zakasan yana cikin
farinciki sosai.
ya ce "An bani ke yau alhajin mu yake fad'a min yazo gurin Baba neman izini tun d'azu nake
kiran ki nabaki daddad'an albishir d'in nan bakya d'aga wayar."
cikin shaukin kauna da soyayya ta ce
"Wayar tana d'aki ne ni kuma ina waje ina yiwa Mama wanki, lallai ka kawo albishir mai girma
zan kuwa baka tukuicin ka yanzu."
ta karashe maganar tana y'ar dariya
ya ce "To ina jira ina jin ki bani tukuici na."
zaman ta ta gyara a sannu ta mai da bayanta ta kwanta jikin pillo,
cikin murya mai zaki da narka zuciyar masoya ta ce
"Rufa idanunka."
a b'angaren Kamal d'in shima zaune yake kan katifar sa a cikin d'akin sa, yana rungume da pillo
a kirjin sa.
a sannu ya maida idanunsa ya lumshe yayin da sautin muryarta mai zaki ke rasa cikin
kwakwalwarsa, sonta da kaunarta suna tsarga jini da jijiyarsa.
"Uhm ina jiran tukuici na."
yayi maganar yana dad'a lumshe idanunsa ya dad'a rungume pillon ya cusa shi cikin kirjinsa
sosai.
a hankali cikin wani irin sauti mai dad'i da zaki ta ce
"I love you!."
ajiyar zuciya mai sauti yasake tare da fad'in
"Godiya mara adadi hakika kin bani tukuici mai girma wannan tukuicin yafiye min kyautar gida
da mota har da karin mata ko da indiya ce."
fuska ta kwab'e ta ce "Me ye na sako wata mace cikin zancen."
dariya yy cikin tsigar zolaya ya ce
"To ke da za ayi miki kishiya bayan aure da shekara zaki hana zancen wata mace."
d'ip ta kashe wayar tare da jefar da shi gefe ta mike tana fad'in
"Ka auro uku rana d'aya."
ta shige bayin Mama, wanka tayi ta fito tatafi d'akin su ta shirya cikin riga da siket na atamfa
kalar ja.
tayi kyau sosai cikin shigar duk da batayi wa fuskarta kwalliya ba dan ita ba ma'abociya penti
wa fuska bace,
mai da pauda da manbaki sune kad'ai kayan kwalliyar ta.
waje tayi jin Mama tana kwad'a mata kira.
wayar ta Mama ta mika mata tana fad'in
"Karb'i tun d'azu ake ta kira."
tun kan Mama ta rufe baki wani yaro ya shigo yana fad'in
"Wai SEEDRAH tazo inji wani a waje."
karb'ar wayar tayi daga hannun Mama tana duba mai kiran nata
murmushi tayi ganin kiran Kamal yacika wayar, tasan za'a yi haka ko yanzu ma da akazo
kiranta tana da tabbacin shine yazo.
D'aki ta koma tad'au mayafin ta tafita,
a tsaye ta iske shi a kofar gida tacikin get.
baki ta turo tatsaya daga can d'an nesa da shi ta hard'e hannayenta a kirji ta kawar da fuskarta
daga kallon shi.
murmushi ya sake me sauti ya tako gabanta ya tsaya yad'an tsunkuyo tare da loko fuskarta.
fuskanta ta kuma juyawa gefe tare da kuma turo baki gaba.
fuska ya marairaice kamar karamin yaro yakai hannu yarike kunnuwansa ya narke murya kalan
tausayi ya ce
"A yafewa bawan Allah afuwa yake nima bazai kara ba."
baki ta murgud'a tare da kad'a kwayar idanunta ta ce
"Ka koma kaje ka sami 'yar india."
dariya ya tuntsure da shi sosai ita ko ta juya da sauri zata koma gida.
da sauri ya sha gabanta yakuma kai hannu yarike kunnuwan sa ya ce
"Yi hakuri mana rikicacciyata ai ko matan duniyar nan gaba d'aya zasu taro babu wacce ta
isheni kallo bare saurare, ayafewa bawan Allah, bazai sake sako wata cikin zance ba daga
yau."
baki ta murgud'a ta ce
"Oho ba ni inaruwa na ma."
dariya yy cikin zolaya yaleko fuskarta ya ce
"Ashe haka ake kishi na?." kwayar idanunta ta kad'a sannan ta ce "Waya fad'a maka."
murmushi yy ya ce "Gashi nan ina gani."
baki ta murgud'a ta ce "To ba haka bane."
dariya yayi yana mai jin shaukin tsiwarta da sonsa da yake hangowa tattare da ita.
nan suka shiga hirarsu cikin so da kaunar junansu, zuwa can sukayi sallama ta koma gida...
S.Man ne yafito cikin shigar manyan kaya, yayi matukar kyau cikin shigar, kasan cewar shi bai
cika saka jamfa ba yafi mu'amala da kananun kaya. idan kagansa da manyan kaya to yazo
Nigeria ne ranar juma'a ko halartar d'aurin aure sai ya saka manyan kaya.
cikin d'an sauri yake tafiya yakara so cikin parlour.
Ummi tadube sa tana fad'in
"Inazuwa da sauri haka Usman? yanzu nake shirin nimanka muyi magana."
hannunsa ya d'ago tare da duban tsadedden
agogon dake d'aure a hannunsa kana ya ce
"Zanje d'aurin auren wani abokina ne a Abuja sauri nake Ummi bayan sallar juma'a za'a d'aura,
idan na dawo sai muyi maganar."
"To Allah ya tsare adawo lafiya."
"Amen." yafad'a yana fita daga parlour'n...
da misalin karfe 12 na dare S.Man ya dawo, ganin dare yayi bai wuce gidan Abba ba.
gidan sa yawuce.
yana isa ya yi hon maigadin dake gadin gidan duk da babu kowa cikin gidan da akwai mai gadin
gidan, yabud'e masa get ya kusa hancin motarsa ciki.
A gajiye ya fito daga cikin motar yana amsa gaisuwar da maigadi ke miko masa ya wuce cikin
gidan.
direct d'akin sa dake sama ya wuce, yazuba wayoyin sa saman bedside yarage kayan jikinsa ya
fad'a bathroom.
minti 20 ya d'auka cikin bayin yafito d'aure da towel a kugunsa,
ya isa gaban wardrobe yazaro wata tattausar rigar bacci mai mad'aurin igiya had'e da boxes ya
saka.
ya haye lafiyayyen gadon sa dake a gyare tsaf sai baza kamshi yake, yarage wutan d'akin yayi
addu'a ya kwanta babu jimawa bacci yayi gaba da shi.
Washegari yana dawowa daga sallar asuba can gefen parluorn kasa ya isa in da na'u'rorin
motsa jiki suke.
bai sakaita ga motsa jikin da yake ba,
sai da yashafi tsawon awa uku.
yazube kan wata kujera dake gurin yana maida numfashi tare da share gumin dake sauko masa
da karamar towel yayin da d'aya hanunsa ke rike da gorar ruwa yana sha.
wayar sa ya d'aga ya lalub'o number Ummi, tana d'agawa ya ce
"Ummi yunwa kisa a kawo min abinci yanzu ina gida na."
yana gama fad'a ya kashe wayar.
mikewa yayi yahaura sama, bathroom ya shiga yayi wanka kana yafito d'aure da towel a
kugunsa yana tsane ruwan jikin sa da wata tattausan farar karamar towel.
yashirya cikin riga singlet da wando iya guiwa, sai tashi da daddad'an kamshi yake.
ya haye gado.
kwance yake a kan gadon yayin da waya ke rike a hannunsa yana d'an daddannawa.
hannunsa yakai saman cikinsa ya shafa.
number Ummi ya kuma dannawa kira
"Ummi har yanzu ba a kawo min abincin ba."
"Kasan dai sakanin nan da gidan ka akwai nisa Yusrah tana hanya tafita bada jimawa ba zata
iso."
Yana kashe wayar bada jimawaba Yusrah ta iso.
ko da yagama breakfast kwanciya yayi, sai wajen azahar ya farka. wanka ya kuma kana ya
shirya cikin kananun kaya, ya d'au makullin motarsa ya fita.
a masallacin dake jikin gidansa yayi salla kana yad'au motarsa yanufi unguwar rimi gidan Baba.
ko da ya isa gidan yana dai-dai ta parking a farfajiyar gidan ya fito ya jingina da jikin motar yayin
da ya hard'e hannayensa a kirji.
murya ya d'aga yashiga fad'in
"Alhj Musa Alhj Musa!."
a can cikin gidan kuwa SEEDRAH data fito daga d'akin Mama zataje kichin, rike da tray da
shingafar da zataje dafawa ciki.
cak tatsaya jin kiran da akewa Baba, ko ba a fad'a ba tasan S.Man ne da irin wannan rashin
darajar.
da sauri ta dire tray'n shinkafar kasa ta nufi waje cikin sauri tana fad'in
"Idan ba a ja masa layi ba zaiga kamar ko tsoronsa a ke ji, ai ba akan Baba kad'ai aka fara cin
bashi ba gwamnati ma tana ci."
ta karashe maganar da take acikin ranta dai-dai lokacin da take karaso wa inda yake.
kugu ta rike tana yi masa wani irin kallon sama da kasa.
cikin murgud'a baki cike da tsiwa ta ce
"Rashin daraja nagaba ne ko karancin tarbiyya? har idan zakazo kacigaba da yiwa Baba kiran
dirar mikiya batare da girmamawa ba kai ma baza a girmamaka ba, sannan kasani mu
musulmai ne mun iya amsa sallama,
kud'in ka kuma kaje duk san da Baba ya samu zai baka yanzu bashi da su."
Wani irin kallo mai had'e da zalrar mamaki yake bin yarinyar da shi, ransa yayi mugun b'aci.
wannan yarinyar da bata wuci sa'ar Yusrah ba itace ta tsaya a gaban sa take gaya masa
bakaken kalaman da babu wan da ya tab'a tsayuwa gaba da gaba ya fad'a masa.
da sauri ya kai yannu cikin aljuhun wandon sa ya zalo sigari had'e da makunnensa, makunnin
nasa kad'ai abin kallo ne dan ba irin na kasar mu bace haka ma sigarin irin na kasashen turai
d'in nan ce,
yasaka tabar a bakin sa kana yakunna sigarin.
ya zuko hayakin sigarin tare da huro hayakem waje, da sauri-sauri yake zuko hayaken tare da
huro shi,
sumar kansa ya shiga shafawa da d'aya hannunsa.
sai juya gefe da gefen sa yake, yama rasa me zaiyi wa yarinyar nan.
ji yayi kamar ya b'ab'b'allata ya zubar da ita a gurin.
da sauri ta kawar da kanta tare da toshe hancin ta tana yamusa fuska cikin yin kasa da murya
ta ce
"A she dai d'an shaye-shaye ne haba dole mana."
Zaro sigarin ya yi a bakin sa muraran kake iya hango matsanan ciyar b'acin ransa kan fuskarsa
kana ya ce
"Zan nuna miki halin d'an shaye-shaye kuwa!."
kafad'a ta d'aga kana ta juya cikin sauri dan ta d'an razana da jin kalaman sa da kuma yanda
taga yarikid'e yakoma mata na mijin zaki.
cike da karfin hali da dakiyar zuciya take fad'in
"Koma meye kayi Allah na tare da ni."
tayi cikin gida da sauri.
Shiko wurgi da sigarin hannunsa yayi yashiga motarsa yajata da mugun gudu yabar gidan.
gidan Abba ya nufa.
yana isa direct side d'in sa ya wuce batare da yabi ta cikin parlour'n Ummi ba.
yana shiga bedroom yad'au System d'in sa ya zauna bakin gado ya kunna kana yashiga
dube-dube aciki.
yad'au tsawon mintuna 15 yana sarrafa na'uwar kana ya rufe ya tura gefe.
d'an kishin gid'a yayi a kan gadon kana ya d'au wayarsa ya daddanna ya kai kunnensa.
magana ya soma wan da ni bana jiyo abin da yake fad'a, daga bisani ya kashe wayar.
ya mike yashiga tarkasa abubuwan da yake bukata kana yad'au laptop d'in yayi waje.
ta sashin Ummi yabi a parlour ya taddata,
ya zauna tare da gaishe ta.
ta amsa tana fad'in
"Dama ka shigo ne?."
"Ban jima da shigowa ba yanzu zan koma dan nayi ba'i."
"Abinci fa da dai ka tsaya ka ci kada ka tafi ka soma kiran a kawo maka."
mikewa tsaye yayi yana fad'in
"Bani abincin natafi da shi sauri nake."
Ummi ta mike ta nufi kichin tazubo masa abinci cikin kula ta sakashi cikin basket had'e da plt da
cukali, sai kwalin lemo da gorar ruwa had'e da cup ta fito ta samu har yayi waje.
Yusrah ta kira ta bata basket d'in ta kai masa cikin mota, ta bud'e sit d'in baya ta aje basket d'in
ciki.
tana rufe murfin motar ya ja motar da sauri yabar gidan..
Bayan kwana biyu
Yau da wuri SEEDRAH tagama aikin ta kasancewar yau asabar ne tana gida.
daren jiya Kamal yayi mata alkawarin kaita gidan kawarta Naseeba.
karfe sha d'aya tagama shiri tafita rike da waya a kunnenta tana fad'in
"Gani fitowa."
d'akin Mama ta shiga tayi mata sallama dan tun ajiyan ta fad'a mata zataje gidan Naseeba, ta
ce mata kada ta kai dare ta dawo da wuri.
Kamal natsaye a bakin get takaraso in da yake tare da hararar sa cikin tura baki ta ce
"Wannan kallon fa?."
numfashi ya sauke tare da kyakkyafta idanunsa da tun fitowarta yakafe ta da su ya ce
"Baby kinyi kyau fa kamar na kwana ina kallon ki."
'yar karamar dariya tayi ta ce
"Kwana a tsaye ko a kwance."
"Duk yanda kike so zaki shigo hanu ai zakiyi bayani."
fuska ta b'ata tare da turo baki ta ce
"Banson haka fa ni banja da tsawo ba."
dariya ya yi kana ya d'an kwanto mata da mashin d'in ya ce
"Hau muje nima ban warware zargen ba."
Suna tafe suna hirarsu cikin so da kauna har suka isa gidan su Naseeba, a kofar gidan ya faka
mashin d'in sa yana gaba tana biye da shi suka shige gidan da sallama.
Maman Zeey tana sakar gida tana d'an aikace-aikace, ta amsa sallamar tana fad'in
"A a yau ankawo min surukar tawa ce da kanka ba sai tazo abiyo ta ba."
murmushi tayi cike da jin kunya tayi kasa da kai.
"Ina yini Maman Zeey ya gida."
ta fad'a tana d'an murmushi da wasa da bakin gyalen ta.
Kamal kuwa dariya yayi tare da shafa gefen fuskarsa ya ce
"Maman Zeey kuyi kuje ku d'auko min ita dan Allah nifa hakuri na yafara karewa."
ido SEEDRAH ta waro cike da mamaki mai had'e da jin kunya tana aika masa da harara ta
gefen ido.
shiko gira ya d'aga mata.
dariya Maman Zeey tayi ta ce "Allah ya shirya Kamal zamu d'auko maka ita."
da sauri SEEDRAH ta d'aga kafa zata bar gurin.
Zeey data fito daga cikin d'aki da sauri cikin muryar dariya ta ce
"Tsaya-tsaya-tsaya, yauwa tun da kinzo yau zamuyi gwajin girki naji irin girkinki,
Allah in baiyi dad'i ba daga yau Ya Kamal ka daina yimin gorin girki ehe."
dariya tayi tawuce sashin Naseeba, Kamal yabi bayan ta yana fad'in
"Yarinya asalin girki ta iya ke dai kishirya zuwa gidan mu kwad'ayi."
Ihun murna Naseeba ta sake ganin SEEDRAH ta rungume ta tana fad'in
oyoyo.
SEEDRAH ta janye jikin ta tana fad'in
"Ke kada kije ki matse mana baby irin wannan runguma haka."
"Ai murnan ganin kine."
Nasiba ta fad'a tana dariya.
"So take ta janyo mana asara kibi a hankali fa."
cewar Kamal yana karasowa ciki
Mukhtar yafito suka tafa da abokin nasa, duk suka shige ciki.
a parlour suka ya da zangon su.
nan da nan Naseeba ta cike su da kayan ciye-ciye suna ci su hira.
SEEDRAH ta dubi d'an karamin cikin Naseeba daya fara tasowa ta ce
"Mace fa zaki haifa mana dan so nake nakoyi kitso a kanta."
"Yauwa fad'a masa nimafa mace nake so wai shi namiji."
Mukhtar ya ce
"To dai son kai za a gwada mana, Kamal ko kai ma kana bayan su ne."
kallon kasa-kasa Kamal yabi SEEDRAH da shi kana ya ce
"Namiji muke so ita shugaban 'yan maganan ma ta shirya rainon maza biyu."
baki SEEDRAH ta murgud'a masa ta ce
"Kabaryi da ni."
dariya Mukhtar yayi ya ce
"Kayi kokari abokina."
Hira sosai suke cike da zolayar juna, ko da aka kira sallar azahar Mukhtar da Kamal suka tafi
masallaci, basu dawo gidan ba sai da akayi sallan la'asar.
nan SEEDRAH ta ce zata koma gida Mama ta ce kada takai dare, kuma tana so ta shiga gidan
Nabeela. tayi musu sallama
Kamal ya d'auke ta sukayi gidan Nabeela daga nan ya mai da ta gida...
Zaune Baba yake a d'aki yana huta gajiyar daya kwaso