Showing 72001 words to 75000 words out of 78655 words

Chapter 25 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf

ta mike tashiga jawoshi tana fad'in
"Please dear zoka saka dan Allah karka yi min haka."
da sauri ya mike batare da yayi magana ba, ya d'au kayansa ya saka. yashige bathroom ya
barta a gurin tana ta aikin magiya.


Ruwa mai sanyi sosai yasakarwa kansa, ya rumtse idanunsa da karfi, tun da yasoma shafa
Teema baiji kwatankwacin abin da yake ji game da SEEDRAH ba ko da da kama hannunta ya
yi.
sam bayajin abun da yake ji kan yarinyar can meyasa yake jin mugun sha'awar ta haka.
tun lokacin da yasoma saka hannu jikin ta da zummar duka yacakalo wa kansa damuwa,
d'an guntuwar sha'awar sa da yake magance sa ta hanyar shan wasu tablet's sai gashi yanzu
basa yi masa aiki, a bun nasa ya faskara ya wuci misali.
ido yakuma rumtsewa da karfi.
"Yarinyar mayya ce yess mayyace kawai."
yawani dunkule hannu ya naushi jikin garu.

Har ya fito a bayin Teema na kwance ta ware kafafu tana jiransa.
da hannu ya yi mata alama da ta tashi.
jiki a sanyaye ta mike ya ce
"Sa kayan ki kije."
da sauri ta ce "Haba S.MAN sai da ka zuzuta ni please zo ka shiga dan Allah."
hannu ya d'aga mata kana ya ce
"I said Get out!."
yadda ya yi maganar babu wasa ya sa ta mikewa tana wani mammase ido sabar jaraba, haka
ta sa kayanta guiwa a sanyaye tabar gidan.
shima makullin motarsa yazara ya fice a gidan.........!





Mommyn Twins ce




🌺 *ƘARSASHI!* 🌺

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)

~Free page~


( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance
da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_




_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*🇦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

page 21



*INA CIGIYAR LITTAFI NA (ALFARMA) DAN ALLAH DUK WANDA ALLAH YASA YAGANSA YA
TAIMAKA YA TURAMIN TA WANNAN LAMBAR 08034690723*





Yau sati d'aya da komawar SEEDRAH gida, tun washegarin ranar da ta dawo Baban Kamal da
'yan uwansa suka zo a yanka musu sadaki.
badun Baba yaso ba duba da halin da yake ciki, da gudun abun da zaije ya dawo idan
SEEDRAH mai taimakon sa daga tozarcin S.MAN tayi aure.
haka nan dai ya yanka musu sadakin naira dubu d'ari uku, atake a gun kuwa suka biya basu bar
gidan ba sai da sa rana bayan wata biyu za ayi aure da yardar Allah.
dan su sunce a shirye suke kuma basa so a ja lokaci.

Baba dai nanan cikin zullumi yayi mamakin ganin har yanzu S.MAN bai kira sa ba kuma baizo
ba.

Tun da akasa ranar auren Mama ta kasa zaune ta kasa tsaye, ko cokali bata ajeba ga biki wata
biyu acikin watan kuwa har anci kwanaki 6.
a b'angaren Baba kuwa yanke hukunci ya yi zai saida motar hawan sa wanda acin kadddarorin
sa shi kad'ai ya rage masa,
yaki sai da shi ne sabo da dashi yake samu yake fita 'yar buga-bugan sa.
zai sai da shi yasamu ya yi hidimar bikin amaneji.

A b'anggaren amarya SEEDRAH kuwa ganin har zuwa wannan lokacin bataji Baba ya yi
magana kan komawarta aiki gidan S.MAN ba, sai ta saki jikinta,
dan dama tana ta langwab'ewa ita a dole bata da lafiya, tana da kuma tabbacin har yanzu
S.MAN bai kira shiba da taga tashin hankali ya bayyana gare shi.
yanzu shirye-shiryen auren ta tasa gaba duk da basu da kud'i amma akwai rufin asirin Allah.
biki saura sati uku dai-dai Mama ta tura SEEDRAH Zariya.
'yan uwan Mama sun yi mata goma na arziki duk da ba wani karfi sosai suke da shi ba.
duk abun da uwa harda ma uba zasuyi sunyi mata dai-dai gwargwado.
Aunty Rashida autar su Mama ita kam cewa tayi zata kwankwajeta ne ta hanyar gyara ta in da
zata mai da angon nata yazamo tamkar rakumi da akala.
gyara sosai take mata SEEDRAH ko ta bada had'in kai dan so take ta sakawa Kamal kan
soyayya da kaunar da yake mata.
duk wani maganin da zata bata komai rashin dad'in sa zata shanye babu wani gargada.

satin SEEDRAH biyu a Zariya sabar tasha gyara har wani ciccikowa ta dad'a yi komai yayi
zam-zam.
takara fari ta kara sheki ta kara wani irin bala'in kyau albarkatun jikin ta sun dad'a tumbasa.
Kamal sunzo gaisuwa amma ba a bashi damar ganawa da amaryarsa ba, al'adarsu ce haka
idan har an fara gyaran amarya tofa ango bazai sake ganinta ba har sai an kai masa ita gidan
sa, sai dai su rika waya.

Tun a sauran satin kuwa 'yan uwan Mama suka taho Kaduna da amarya SEEDRAH.
Mama tayi kukan farinciki ganin yan da 'yan'uwanta
suka share mata hawaye,
'yan gulma kuwa sai zuwa kallon kaya ake dan babu wanda ya yi zaton haka.
Halimatu da Suhailat kam kiri-kiri suke nuna hassadar su, duk kuwa wanda ya ce musu
kanwarsu zatayi aure ta barsu sai suce.
su boko suka sa gaba yanzu, aure kuwa sai mai gida da mota, ba irin Kamal me mashin ba.
SEEDRAH ko ce musu ta ke haka ta ke son abinta idan kuma kud'ine insha Allah zasuje su tara
tare su siya gida da motar..



Yau talata hakan kuwa ya yi dai-dai da saura kwanaki uku d'aurin auren SEEDRAH da Kamal.
gida yacika makil da dangi nakusa da na nesa, rufin asirin Allah duk wan da zaizo da
gudumawar kud'i ko abinci yake zuwa.
dan haka ake samu aci asha cikin rufin asirin Allah.
SEEDRAH ce tsaye cikin d'akin Mama rike da mayafi a hannunta ta dubi Hafsat 'yar Umma
Bishira kanwar Mama da suka taho tare ta ce
"Dan Allah Hafsat kibar wannan kwalliyar kamar wacce zataje gasar kyau, kizo mu tafi mana
yamma fa tanayi."
"Yi hakuri d'ankwali kawai yanzu zan d'aura."
cewar Hafsat tana gyara d'aurin d'ankwalinta.
Yusrah da ke danne-dannen waya ta ce
"Ki barta mana tayi kwalliyar ta kika sani itama Allah ya bata nata muna fita."
Aunty Rashida da yanzu shigowarsa rike da wasu kaya a hannunta ta ce
"Ke me zan gani haka wai SEEDRAH fita zakiyi?
oh so kike kije ki had'u da Kamal d'in ki b'ata mana al'ada, to babu in da zaki."
kafa tashiga bubbugawa a kasa cikin muryar shagwab'a ta ce
"Kai Aunty Rashida Allah ni ba wani Kamal d'in da zan had'u da shi, fa gyaran gashi zamuje."
aje kayan da ke hannunta Aunty Rashida ta yi tare da fad'in
"To zo ki karb'i nikaf ki saka sabo da tsaro."
dariya SEEDRAH ta yi ta ce
"Allah Aunty Rashida d'auke min numfashi ya ke ban iya sawa ba."
"To shike nan kuyi sauri ku dawo kada ki sake ku had'u."
ta ce to.
Hafsat da take ta dariya tun d'azu ta ce

"Wai dan Allah a hana mutum ganin matarsa, ni wannan al'adar a soketa daga kan SEEDRAH
kada ya iso kaina."
"Ungo naki ai har jikoki da tattab'a kunne sai sun samu."
cewar Umma Bashira.
dariya duk sukayi suka fice a d'akin.

Suna fita waje dai-dai lokacin wata mota ta dumfaro kofar gidan.
ido SEEDRAH tad'an zubawa motar tana son tuna in d ta tab'a ganin shi.
a b'angaren Yusrah ma kallon motar take dan ta gane motar yayanta ne.
daga can gefe motar ta faka a hankali aka zuge glass d'in motar.
karaf idanunau ya sarkafu da juna, wani irin mummunar fad'uwar gaba ne ya ziyarceta tasan
duk yanda akayi ba alkairi bane ya kawo sa.
da sauri ta dubi Hafsat da Yusrah ta ce
"Ina zuwa."
ta nufi inda motar take.
a hankali ya maida bayan sa yakwantar jikin sit ya yin da idanunsa ke kanta harta karaso jikin
motar, taja ta tsaya tare da bin sa da wani kallo sannan ta ce
"Wani rashin mutuncinne yakawo ka, ina mai had'aka da girman Allah kada ka tozarta mahaifina
cikin bainar jama'a, kaje idan mutanen da suka taru dan tayasa murna sun wase sai ka dawo,
amma kasani wannan karon mu zamu kai kararka kan tozarci da rashin d'a'ar da kake gwada
mana, dan talauci bata tab'a zamowa hauka ba." tun da tafara maganar idanunsa a kanta wani irin kallo yake mata kamar bai tab'a sanin ta ba, a
hankali yad'an lumshe idanunsa tare da shakar fitinannen kamshin dake fita a jikinta kana
yakuma bud'e idon a kan lips d'in ta.
a hankali ya gyara zamansa ya kunna motarsa yaja yabar gurin batare da yace da ita komai ba.
SEEDRAH ko numfashi ta sauke tare da yiwa Allah godiya da yasa baizubar mutu da mutunci
ba, tazo ta ja hannun su Hafsat sukayi gaba.
Hafsat na tambayarta shid'in wane ne ta ce d'an kanin babansu ne kuma yayan Yusrah.
sai wajen magriba aka gama musu gyaran gashi suka dawo gida.

Da daddare bayan sallar isha Baba na nan zaune a d'akinsa shi da Mama suna tattaunawa kan
yadda shagalin bikin zai gudana, kira ya shigo wayarsa.
ganin mai kiran yasa hankalin sa ta shi da sauri yad'aga kiran
"Gani a waje."
abunda ya ce ke nan yakashe wayar.
Baba ya mike da sauri bai ko tsaya shaidawa Mama ba yafita.
yana jingine jikin motar sa ya hard'e hannu a kirji Baba ya karaso inda yake jiki na rawa yana
fad'in
"Barka da zuwa alhaji Usman."
hannu yad'aga masa ya ce "Rike gaisuwar ka bashi ya kawo ni nan ba."
tsayuwar sa ya gyara kana ya ce
"Zaka iya sanar wa mutanen cikin gidannan su fita za a kulle gidan, hanzarta kada su b'ata min
lokaci, idan kuma baza ka iya ba ni naje da kaina."

da sauri Baba murya na rawa ya ce
"Dan Allah dan girman Allah Usman karufa min asiri idan suka fita ina zan kaisu, ka taimakeni
agama hidimarnan in yaso koma mene ne yabiyo daga baya."
"Okay bazaka iya ba ke nan."
ya d'aga kafa zai je da sauri Baba ya sha gaban sa hannu bibbiyu yashiga rokon sa da magiya
kamar zai zuba guiwowinsa kasa.
hannu S.MAN ya d'aga masa kana ya ce
"Ya isa, kana son zama cikin gidan nan ayi hidimar biki lafiya?."
da sauri Baba ya ce
"Wlh babu abun da nafi bukata sama da haka, idan ka koremu ina zamuje ina zan kai wad'an
nan jama'ar karufa min asiri."
"Okay zakaci gaba da zama amma da sharad'i."
jin haka yasa Baba har jikin sa na rawa sabo da farincikin ance zai cigaba da zama ya ce
"Fad'i ko ma mene ne na amince."
kai S.MAN ya girgiza kana ya ce
"Nawa nake binka?."
da sauri Baba ya ce "Miliyan 30."
"Kasan dai idan aka d'aga gidan nan za'a siyar da shi bazaikai 30 million ba ko."
kai Baba ya gyad'a ya ce "Nasani."
kai yakuma girgizawa tare da gyara tsayuwar sa da kyau kana ya ce
"Acikin 30 million aka cire 10 million saura 20 million to na yafe maka miliyan goman sannan
kuma zaka cigaba da zama a gidan nan."
wani irin waro ido Baba ya yi kamar a mafarki maganar tazo masa,
ji ya yi tamkar ya yi ta tuma tsalle dan farin cikin, kamar zai rungume sa yashiga zabga masa
godiya ba kakkautawa.
"Da kata har yanzu ban fad'i sharad'i na ba tukun."
"Fad'i ko ma mene ne kasamu."
cewar Baba yana washe baki.
baki ya tab'e kana ya juya yabud'e motarsa yaciro wata 'yar karamar jaka yamika masa.
ido baba ya zubawa jakar ya ce
"Wannan kuma mene ne?."
"Bud'e ka gani."
hannu na rawa Baba yashiga bud'e jakar ido ya zazzaro ganin kud'i ne d'aurin 'yan dubu-dubu
da zasu kai guda ashirin.
ya ce "Me za ayi da su?."
bayan sa ya jingina jikin mota tare da zura hannunsa cikin aljuhu ya zaro sigari had'e da
makunni ya kunna, kana yakai bakinsa ya zuko hayakin yabuso shi waje har kan fuskar Baba
sannan ya ce
"Zaka mai da auren waccan yarinyar kaina wanna kuma sadakinta ne, kada ka sake asami wata
matsala,
sannna sharad'i na gaba kada ka sake ka sanar wa Abbana wani abun da ba dai-dai ba, idan
kayi yunkurin yin hakan."
ya girgiza kai tare da yin kwafa yajuya ya shiga motar sa yabar gurin.

Baba kuwa mutuwar tsaye ya yi, ta ya za ayi hakan ta kasance to me ma zaicewa mahaifan
Kamal kafin ita SEEDRAH.
wani b'ari na zuciyarsa kuwa ce masa take.
"kai kam dai kakarka ta yanke saka ga yafiyar miliyan goma ga afuwan zaman gida ga wata
miliyan biyu a hannunka, ya ishe ka magance wasu matsalolin da zasu kunno kai.
idan kuwa baka amince da bukatarsa ba to tabbas zaka bar gidannan, sannan kuma zai janye
yafiyar miliyan goman da ya yi maka, sannan kuma ya karb'e miliyan biyu da ya baka madadin
sadaki shike nan katashi a ziro."
da wannna kwarin guiwar da zuciyarsa ta basa yashiga gida.
har lokacin Mama tana d'akinsa tana zaman jiran sa.
sai da ya isa ya bud'e durowa ya aje jakar kud'in nan sannan yadawo in da take ya zauna.
ta ce "Bakon har ya tafi ne?."
ya ce "Eh, Usman ne bakon namu."
kirji Mama ta buga ta ce "Wani Usman d'in badai S.MAN ba?."
kai yagyad'a ya ce "Shi."
"Innalillahi'wa'Inna ilaihirraji'un! Allah dai yasa yaji hakuri yau ma."
Mama ta fad'a a raunace.
d'an murmushi ya yi kana ya ce
"Insha'allahu harma da rangwami mai tarin yawa."
"Rangwami kuma wani irin rangwami?."
zama Baba ya gyara ya fuskanceta da kyau kana ya ce
"Wani babban al'amari yazo da shi amma idan zayi duba da mahanga mai kyau to hakan itace
kad'ai mafita a gare mu,
ya ce yana so nabashi auren SEEDRAH, sannan kuma ya yafe min naira miliyan goma cikin
kud'in da yake bina, kuma mucigaba da zama cikin gidan nan,sannan yabada sadakinta miliyan
biyu."
wani irin mikewa tsaye Mama ta yi tare da buga kirji ta ce
"Abashi auren SEEDRAH Alhj ko ka mance ne saura kwana uku d'aurin auren ta, sannan me
zamuce wa jama'a da dangin Kamal."
"Zauna dan Allah ki nutsu ki saurare ni."
ta zauna jiki ba kwari.
ya ce
"Lokacin da Usman ya ke zuwa gidan nan yaci min mutunci akwai wani mutumin daya tab'a
zuwa taimako na ne? su dangin Kamal d'in suna da kud'in da zasu iya biyan bashin da yake
bina ne,
abun da nake so ki fahimta, hakan fa shine kad'ai rufin asirinmu, daga zaran ya auri yarinyar
nan inada tabbacin nan gaba ma sauran kud'in zai ce ya yafe,
yanzu idan akace baza a bashi auren ta ba wani tsiyar zai tada,
karshe mukunyata a idon jama'a,
ke ba abun farinciki bane yaro da kud'i irin Usman ya ce yana son auren d'iyarki, karfa ki mance
shid'in fa d'ane ga Sulaiman kanina ko ba komai ai ko dun Sulaiman d'in za a bashi,

abun da nake so da ke kije ki natsar da yarinyar nan, kiyi mata bayani yanda zata fahimta kuma
nima zan kirata, sannan kiyiwa 'yan uwanki bayani idan kuma ba so kike yau ki nuna min
iyakata ba!
su kuma dangin Kamal d'in da shi kansa zanji da su."

Mama ta mike jiki a sanyaye ta fita.
ko da ta sanar wa 'yan uwanta abun da ke faruwa sun girgiza ba kad'an ba, sai dai ba'a
sanarwa SEEDRAH a daren ba.
washegari Baba yakira Abba a waya bayan sun gaisa Baba ya d'aura da fad'in
"Sulaiman zaka sami zuwa d'aurin auren nan kuwa?."
Abba ya ce "Da naso haka amma ayyuka sunyi min yawa inaga kawai zan saka maka
gudumawa na ta account, idan na dawo zanje na t
duba zaman ta a d'akin ta, Allah ya basu zaman lafiya."
Baba ya ce
"Amin amin sai dai yanzu auren ya sauya daga kan yaron da za ayi da shi zuwa kan Usman,
dan ya same ni ya ce min shi fa yana son ta wai bai fad'a bane kawai, na ce kaji min ja'irin yaro
gida bai koshiba za a kai wa na waje, idan Allah ya kai mu jibi da shi za a d'aura."
Abba ya ce "Usman d'in kada ya mai damu kananan mutane mana, yasan da yana son ta
tuntuni bai fad'a ba sai da aure yarake saura kwana biyu,
haba Yaya hakan ai bazai ma yiwu ba barima na kira shi kada ya mai damu mutanen banza
mana."
da sauri Baba yatari numfashin sa
"A'a da kata mana, ai babu batun wasu mutanen banza, ko sune ma hakan ta kasance da su
hakan zasuyi,
tun da Allah yasa ya furta yana sonta to a bashi ita,
harsai yaushe ne zaiyi aure yakai har i wannan lokaci baiyi aure ba, gida bai koshi ba a kaiwa
na waje."
"Yanzu Yaya kana ganin hakan bazai tab'a mutunci muba bazasuce munso kanmu da yawa ba."
"A'a babu abun da zasuce ni zanji da su."
Abba ya ce "To shi ke nan Allah ya tabbatar mana da alkairi."
sukayi sallama.
Abba a wani b'angare na zuciyar sa yana mai matukar jin farinciki d'ansa da 'yar d'an uwan sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login